← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 80

Sashe 8

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina Kai kawai yarima yayi Dan har ga Allah mama na tsananin bashi mamaki Koda yake Babu abin mamaki Dan yasan kowaye ita wajen son Kai,

"Bari inje indan watsa ruwa mama"

Ka'da Kai kawai tayi alamar amsawa ya Mike ya fice daga sasan mama babba,kansa tsaye yayi bangarensa kayan jikinsa ya rage sanan ya nemi gefen gadonsa ya zauna ya maida kallonsa ga dakinsa da yayi kura kaca kaca,tunda bala'in Nan ya faru baisa an gyara Masa dakiba ko ta kan dakin ma bayayi saboda halin da yake ciki,

Kwanciya yayi rigingine ya zuro kafafuwansa kasa kansa na kallon fankar dakinsa dake kadawa a hankali,zuciyarsa ke ayyana Masa abubuwa da dama game da Fatima kaddara babu yadda Bata zuwama bawansa ga rashin gata ga babbar kaddara ta fada Mata wadda fitar da ita Sai allah.....Amma tabbas inhar Fatima nada sauran numfashi a duniya Sai ya zamar Mata gatan data rasa na rayuwar duniya....

Runtse idanuwansa yayi fuskarta ya hasko wani lokaci baya tanayi Masa murmushin Nan nata Wanda ya zame Mata tamkar dabiarta CE murmushi tace "da na cire Rai da samun gata a duniya Yaya yarima tunda na farka naganni a wanan yanayin Amma zuwanka rayuwata inasa Rai da Kai rahmane daga Allah zuwa gareni nasan inhar inadakai bazan yi maraicin uwa da uba ba ko yaayaah yarima?"

Kafeta da Ido yayi Yana kallon yadda take motsa bakinta Tana magana Mai cike da hikima tamkar wadda ake fadawa,

Itama kallonsa tayi Ganin yaki cewa komi Sai idanuwanta suka kawo ruwa tamkar zatayi kuka cike da shagwaba tace"Yaya kodai kafasa zamemun gatan da kayimun alkawari ne infara kukan maraici a Karo na biyu"

Hannu yasa ya goge hawayen daya sauko a daga idanuwanta Yana girgiza Kai "harbada inhar Ina Raye Fatima bazakiyi kuka ba kada insake Ganin wanan kwallar ta sakko daga wadanan kyawawan idon"

Kifta mishi Ido tayi Tana dariya kasa kasa......

Zumubur yarima ya Mike daga kwanciyar da yayi besan lokacin da ya tsinci kansa hawaye na gangaro masaba a fili yake furta "ya zaayi incika alkawarin Dana daukar Miki Fatima na harabada bazan Bari ki zubar da hawaye ba?,"

Kansa ya kifa a jikin bango Yana kuka tamkar mace Wanda tunda yake Bai taba zubar da hawayensa Akan wani abuba dik runtsi kuwa dik wahala Sai gashi yau Akan Fatima Yana kuka tamkar mace babban tashin hankalinsa hango Fatima da yakeyi Tana zubar hawaye a kotu Tana yiwa kanta ikirari itace tayi kisan Kai......kuka sosai yakeyi Wanda tunda abin ya faru besamu yayi irinsa ba...."inhar inada Rai Fatima bazakiyi kuka ba bazaki zubar da hawaye ba Ni Zan zame Miki garkuwa a rayuwa".....kuka sosai yakeyi jikinsa har rawa yakeyi,da sauri ya waiga kan wayarsa dake kan gado Tana ringing ,kafe wayar yayi da Ido Ganin bakuwar number CE har ta tsunke be ko motsa ba a Karo na biyu wayar ta Kara ringing...

Takowa yayi ya dauki wayar ya Danna receive daga can bangaren aka Fara magana "ranka ya Dade daga Nan head quarter of police ake magana"

Cikin dasashiyar murya yace "umhmm Ina sauraro meyafaru?"

"Dama game da case din yarinyar da ake tsarone oga ya bada damar aje Ayi bincikenta a tabbatar da Yar gidan marayun CE?ko kuwa karya takewa hukuma?shine akace a sanar maka a matsayinka na lauyan wanda suke Kara,dik statement din da aka samu zaa sanar maka ranka ya Dade"

"Ok badamuwa "shine abinda yarima yace be jira Mai Dan sandan zai fadaba ya kashe wayarsa domin dik yasan abinda Yan sandan Nan keso be wuce ace suna kokariba a Shaka musu kudi,

Gadonsa ya haye yayi rub da ciki ya rufe idanuwansa ya cigaba da lulawa duniyar tunanin Fatima.....

*******
Kafin Yan sanda suje gidan marayu labari yakai musu da zaazo bincike, domin haruna da kansa yaje station yaba wani Dan sanda cin hanci Akan dik abinda ke faruwa ya rinka sanar musu,Babu musu kuwa ya amince,

Ba karamin tashin hankali daukacin maaikatan gidan marayu suka shigaba domin,manyan maaikata da kanana sunsan abinda ke faruwa Dan ana San musu nasu,Nan da Nan hankalin hajiya yayi kololuwar tashi ta rasa inda zatasa kanta,yayinda Shi kansa harunan baya cikin kwanciyar hankali....

Kaf yaran dake gidan marayu wadanda ke kwana wuri daya da Fatima aka tarasu tamkar masu assembly,hajiya CE ke magana da kakkausar murya

"Ku tabbatar kunyi aiki da abinda muka fada muku,wallahi tallahi dik Wanda yayi kokari tona Mana asiri Sai ya fuskanci azaba,sanan bazamu kyaleba zamu bawa hukuma mutum ya tafi dashi a hada dashi da fatimar a kashe gabaki daya"

Wuri yayi tsit Sai wurga idanuwa yara sukeyi batare da fahimtar meke faruwa ba,shasshekar kukan da akaji ne akafara waige waige Jin daga Ina kukan ke zuwa,

Sakkowa hajiya tayi a hankali Tana taka takalminta Mai tudu Wanda ko da yaushe irinsa take sawa saboda rashin tsawonta har ta iso inda taga anbada fili an Mar matsa tsawaya tayi a gabanta Tana Kare Mata kallo yayinda yarinyar Ganin hajiya a gabanta yasa tayi shiru kamar anyi ruwa an dauke,

Cire gyalen kanta hajiya tayi ta ratayeshi a kafadarta tace cikin daga murya"au munafuka kukan muna furci kikeyi mun?kekadaice kikeson kawo Mana matsala?to wallahi tallahi Ni halima sainayi Miki cikin da Kika kasa haifeshi matukar Kika kuskura Kika fallasa asirinmu ya tonu to wallahi kinsa kanki a bala'i bilkisu,ki bude kunnuwanki da kyau ki saurareni wallahi summa tallahi matukar kikayi gigin fallasa asirinmu kin shiga uku Dan saina kulla Miki sharrin da aka hadaku keda fatimar aka kasheku gaba daya matsiyata marasa asali"

Ba karamin ciwo wanan zagin yayiwa bilkisu ba take ta da'go kanta Babu alamar tsoro a tattare da ita tace"ai bamu mukayi kanmu ba,Kuma Allah ne ya haliccemu Yana sane damu"

Kyakkyawan Mari hajiya ta sauke a fuskar bilkisu Wanda Saida ta gigice kokafin tayi yunkuri hajiya ta rufeta da duka ta ko Ina Tana janta a kasa suka bar wajen.....dukkansu yaran ba karamin tsorata sukayiba da Jin kalaman hajiya na zaa kashe mutum sanan da hukuncin da tayiwa bilkisu a gaban kowa,Nan da Nan kowa ya shiga taitayinsa suka shiga watsewa.....

Can wani daki Mai Nisan gaske cikin daji dajin gidan marayu hajiya ta wulla bilkisu ciki ta rufo kofar....tai tahowarta Dan fadan karfin Hali kawai takeyi ta Gama firgita da lamarin yarinyar Dan tsab bilkisu xata tona Mata asiri Dan mugun taurin Kaine gareta da kafiya. ...

********
Koda Yan sanda sukazo gidan marayu bincike tun daga kofar gate din gidan suka nunawa Mai gadi hoton yarinyar,sanin abinda zai biyo baya yace besanta ba,

Dik Wanda aka nunawa hotonta Sai yace besanta ba cikin maaikata har akazo kan yara kowa aka nunawa hoton Fatima Sai gabansa ya Fadi Amma daya tuno kalmomin hajiya Sai yace besanta ba.....haka Yan sanda suka Gama zagayensu kaf basusamu wani labari game da Fatima ba suka koma sukayi station....

********
Yarima ba karamin mamaki bane ya daure Masa Kai gameda labarin da yaji na cewa Wai Fatima ba Yar gidan marayu bace ta Yaya?to akwai wani kulli kenan a kasa sanan dolene ya nemi bilkisu don Jin cikakken bayani Akan abinda ke faruwa a gidan marayu,domin Dole bazata rasa sanin wani abuba idan har ya karyata cewa Fatima Yar gidan marayu CE to tabbas asirinsa zai Tonu zaa fahimci yanada dangantaka da ita,lallai mutane basu da imani wato saboda kaddara ta sameta yasa suka hade Baki sukace basusanta ba?Koko akwai wani Abu ne a kasa?....ajiyar zuciya kawai ya sauke tare da tattaro wayoyinsa ya fice ....

*******
Mama babba CE cikin guest house na gidan sarki dik wani maaikaci dake gidan ya hallara a babban parlor dake floor na biyu,kafin kowa ya tsaya Sai sun kawo gaisuwa wajenta ko wanne cikinsa ya duri ruwa kowa da fargabar da yakeyi a zuciyarsa game da zuwanta Dan sun San halinta tsab zatasa a Kori mutum daga kan aikinsa,

Shugaban gidan ta nema gabaki daya Shi yayi mata iso zuwa dakin da computocin gidan suke inda dik abinda ke faruwa na cikin gidan ake kallo ko meye mutum keyi na alheri ko sharri suna kallonsa,

Rusunawa yayi sanan ya kawo gaisuwa ta amsa cike da Isa da izza irinta masu mulki,

Kujeru biyu ya janyo musu ya goggoge sanan suka zauna ita da khausar dake gefe tanata Harare Harare....

"Abinda ya kawoni gidan Nan shine inaso ka tattaro mun dik wani bayani na abinda ya faru ranan da aka kashe habibu ka fitomin dashi in kalla sanan kabani Shi a hannuna Dan ya zame Mana hujja a kotu,abinda yasa nazo da kaina shine saboda sarki na Lura komi a hankali yake binsa sanan be bawa wanan shariar muhimmanci ba Niko tunda nice aka salwantar da da'na Dole in Mike tsaye dik yadda xanyi Inga jinin Dan Dana haifa be tafi a banza ba,shiyssa na bukaci a kawoninan dikda aikin ba nawa bane aikin kabiru ne Amma kabiru rashin Dan uwansa yasa bashida wani kuzari ,to shiyssa nayi tattaki da kaina"

Rankwafawa yayi yace "toh ranki ya Dade yanzun zaa aiwatar da umarninki"

Ta gyada Masa Kai,..

Mikewa yayi ya shiga jone jone Nan da Nan ya hada komi ya kunna sanan ya shiga tariyo Mata abinda ya faru a wanan ranan tun daga laasar har safiyar washe gari,

Kallo takeyi Amma gabaki daya Tana neman fita hayyacinta saboda tsananin furgicin abinda tagani,Babu inda jikinta baya rawa Babu inda zufa Bata karyo Mata.....har suka Gama kallon video din ....

Waigawa tayi ta kalli khausar wadda tayi mutuwar zaune ko motsin kirki batayi.....

Jiki a sanyaye khausar ta kalli mamanta tace"turkashi mama?Kinga abinda nagani kuwa?"

Ajiyar zuciya mama babba tayi tace "nagani khausar yanzun menene shawararki?"

Shiru kausar tayi sanan tace"mama Anya ba shiyssa Yaya kabir ya kasa komiba Akan shariar Nan?shiyssa bashida kwarin jiki ba?"

Da sauri mama ta girgiza Kai tace"baisan komiba khausar banajin idan kabir yazonan tunda habib ya mutu,Kinga kuwa inhar hakane to akwai mafita"

Mama ta kalli gefenta su kadaine cikin dakin zaune Dan bayan ta kunna musu fita yayi,mama tace"dolene kudurina ya cika akan yarinyar Nan yadda ta kashemun da'itama a kasheta"

"Ta Yaya mama?bayan idan mukasake videon Nan yaje kotu mune a ciki?asirin Dan uwana zai Tonu sanan mutunci da kimar masarautar Barayar Zaki Dole ya zube a idon mutanen gari da duniya Baki daya"
Chapter 8 · 0% Book details