← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 80

Sashe 71

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin faduwar gaba ne ya ziyarci hajiya babba da rahina suka dago a lokaci daya suka kalli juna Sanan suka maida kansu suka sunkuyar,

Juyowa Mai martaba yayi ya dubi waziri Wanda ke gurfane Yana jiniina Kai "waziri me kake gani dangane da abinda ya faru?maana ga Fatima Nan diyata ta bayyana kasan ubanta tun Yana Raye kakeyi Masa waziri to yanzun menene shawararka?"

Gyaran murya waziri yayi "ni a ganina anawa tunanin ranka ya dade bazai yiwu ace daga ganin hoto da kamanni ace an amince da wanan yarinya a matsayin Yar marigayiba ya Dace ayi bincike kafin a tabbatar da hakan,abinda yasa nace haka shine hoto da kamanni suna iya yuwuwa ta ko wani yanayi,Sanan zamanine yanzun na computer zaa iya hada hoton Fatima da sarauniya zahrau data bace,gaskiya be kamata sarki yayi saurin karbar wanan maganar ba"..

Wani mugun kallo yarima yake watsawa waziri lokacin da yake maganar,Sanan take ya juya ya maida dubansa ga hajiya rahina da hajiya babba wadanda suke faman jinjina Kai tunda waziri ya Soma magana,

Shiru Mai martaba yayi Yana nazarin kalaman waziri wadanda yanada nashi point din a wanan lokacin,sai Mai martaba ya gyara zamansa kqdan yace "hakika kanada taka hujjar waziri duba da Babu wata kwakkwaran hujja da ya nuna cewa Fatima din diyar Mai martaba marigayi ce sai kamanni sai Kuma hoton da ya bayyana surar marigayiya zahrsu da ita Yar Tata zaa duba maganarka,..

Ummu ce dake gefe bude baki muryarta a sarke "Niko a ganina tunda bayanai da hujjar hoto ya bayyana be kamata a tsaya jainja Akan yarda da maganar Fatima din diyarmu ce saboda idan akace bazaa yardabd da wanan hoto da bayanin da zahrau ta rubuta a baya to a Ina zaa samu ita zahraun ta bayyana abinda ya faru?...Niko xanso ace hajiya karama ta fito a gabanka ta fasa Kwan abinda ya faru tsakaninsu da zahrau da safiya da rahina"a tausashe ummu ta karasa bayanin ta Wanda hakan ne yayi sanadiyyar gigicewar hajiya babba da rahina .....

"Hajiya karama menene boyayyen Al'amari daya faru a baya Wanda ni din bansan da zamansa ba?"

Gurfanawa mama karama tayi "Allah ya taimaki Mai martaba,.....Nan ta kwashe dik abinda ya faru Wanda tabawa su Fatima labari ta Kara bayyanawa a gaban Mai martaba harda abinda ta boye da Bata fadaba dik ta fada na Hari da aka kaiwa zahrau Dan akasheta Wanda shine musababbin barinta gidan sarauta baasan inda take ba har yanzun,

Tunda Mama karama ta Soma koro bayani jikin Mai martaba Babu inda beyi sanyi ba Nan da Nan jikinsa ya jike da zufa sharkaf tamkar an jijasa da ruwa harta karasa bayaninta...

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun "shine abinda Mai martaba yake fadi Yana jinjina Kai

A fusace ya bude baki yace "lallai Kun cuceni Kun zalunceni Kun hada Kai Kun hainci masarauta Dan haka dukkansu zaku fuskanci mummunan hukunci"

Da sauri Fatima taja jiki ta karasa gaban Mai martaba ta ruko kafafuwansa "Ina neman agajin sarki Mai adalci Akan hukuncin da yake Shirin yankewa batare da yin shawara ko bincike ba Akan lamarin,....inaso sarki yayi watsi da wanan lamari na hukunci da yake Shirin yankewa zuwa Nan gaba kadan idan an tabbatar da nidin jinin sarauta ce,Koda an tabbatar da hakan ni nayafewa su hajiya cutar da mahaifiyarta da sukayi...Dan haka nake gurfane a gaban Mai martaba Akan ya janye wanan hukunci na Roki arziki a karo na farko"...hawaye ne ke diga a idanuwanta lokacinda take gurfane a gaban Mai martaba Tana ratabbo wadanan kalaman...

Sosai jikin sarki yayi sanyi ya durkusa da kanshi ya dagota ya zaunar da ita a gabansa "hakika nayi dacen samun suruka ta gari Kuma ya'ta gari a gareni da masarauta baki daya,babu wani arziki Wanda Zaki nema a wajena Wanda banyi Miki shi ba Fatima nayi Miki wanan arzikin na bar maganar hukunci harabada saidai idan ke dince kika bukaci hakan"

Fatima tasa hannu ta share hawayen dake gangarowa a idanuwanta "Abu na gaba ranka ya dade shine maganar da waziri yayi Akan hanya take na cewa ayi bincike sosai Sanan a aminta Dani din jininku ce,.... banida zabi Wanda ya wuce Mai martaba yasamun hannu wajen neman mahaifiyata"

Wani irin tausayin Fatima ne ya lullube dattijon sarkin Wanda har saida kwalla ta cika a idanuwansa,....tabbas Fatima jininsa ce shi yanaji a jikinsa tunda dadewa Babu Kuma wani Abu da zaisa ya kasa gasgata wanan hoto daya gani baro baro na zahrau da Fatima saidai Dan Cece kuce da zai biyo a cikin garin da masarautar,

"Na yarda na amince da kedin jinina ce Kuma diyata ce fatima ki kwantar da hankalinki inada yadda zaayi asamu labarin mahaifiyarki Amma sai mun koma can inda akasamu wannan hoton naki munji bayani cikakke daga garesu"

Jinjina Kai Fatima tayi cike da gamsuwa "nagode ranka ya dade Allah ya Kara lafiya da nisan kwana,Allah yasa kafi haka",...

Mahaifin deejahmah Wanda ke gefe ya cika famm da tsananin takaicin ganin dik abinda ke faruwa yasashi cewa "ranka ya dade a gaskiya wanan lamari karyane tsantsa da makirci Wanda aka hada ciki harda matarka mahaifiyar kabiru,anyi haka ne saboda a tozarta diyata da mahaifiyarta wanan makircin shiryayyene wallahi,haba dik shekarun da suka wuce baasamu labarin wata zahrau ba sai yanzun?labarin ma Wai a hoto Dan tsabar an rainawa mutane hankali?"

Dubansa Mai martaba yakeyi cike da mamaki da al'ajabin wadan kalaman da yake jefowa batare da wani tunani ko tauna magana ba,..

"Shin ka manta a gaban Mai martaba Kuma sarki kake jeho irin wadanan kalaman galadima?kanada hankalinka kake fadan irin haka?"

"Ranka ya dade wanan maganafa abun dubawa ce ya zaayi kabiru da matarsa subi dare subi Rana su hada makirci da karya Rana tsaka su fito da hoto suce Wai Fatima Yar gidan sarauta ce?harda wani rubutu na karya a bayan hoto?saboda yanajin tsoron irin zagi da tozarci da yayansu zasu fuskanta Nan gaba idan aka gano uwarsu shegiya ce batada iyaye?"

"Dakata galadima bazan dauki dik wani wulakanci da cin Kashi ba a cikin fada ta bazai yuwu ka rinka shegantamun y'a a gabana ba bazai yuwuba idan kanada hujjar da zakuce ku baku yarda da fatimaba zaku iya cewa sai an fidda hujja kwakkwara,Amma ba kazo kana jifanta da mummunan lafazi ba"

"Gaskiya bamu yarda ba da wanan hoto da wani labarin kanzon kurege da aka bada dangane da wanan yarinyar sanan Nan wajen nasan da yawa Basu yarda da hakan ba"...Nan da Nan fada ta dauki hayaniya magana kasa kasa kowa Yana fadin albarkacin bakinsa,..

Tsawa Mai martaba yayi "ya Isa,dik wani Wanda yake da ja Akan wanan yarinyar kofa a bude take ya fadi raayinsa dikda Ina Nan Akan bakata"

Tsulum hajiya babba ta tsoma baki "magana ta gaskiya Fatima ba jinin mu bace ba Kuma tsatson masarautar Nan bace makirci ne kawai aka hada Wai hoto Fatima Yar sarki abdallah ce ta Ina?"..

"Dakatamun safiya banso kice komi Akan wanan lamarin saboda ke banida magana dake da rahina"yace a kausashe,

Juyowa yayi gefensa na dama "waye yake da ja a wanan lamarin Kuma?"sarki ya watso musu tambaya Yana dubansu daya bayan daya,

Waziri da matarsa da sarkin fada tare da galadima dik sukace Basu aminceba Basu yarda ba da sauran jamaar dake wajen Yan rakiyar sarki dik sukace Basu aminceba,

"Dik naji bayaninku Sanan ku din Kun rinjayi wadanda sukace sun amince Dan haka,bazan fasa aminta da din Fatima diyata bace,diyar Dan uwana Dan haka yanzun bincike zai tashi Dan Gane da haka,yanzun Ina umartar kabiru da Fatima da su gabatar mun da matar da suka samu wanan hoton a wajenta me kunshe da wadanan bayanai,

Sanan zanyi bincike dangane da gidan mahaifiyar Fatima dikda banida tabbacin samunsu a cikin garin Nan Dan haka zan tsaida tafiyar da nayi niyyar yi zuwa wani lokaci sai gaskiya ta bayyana"..

Harara hajiya babba ta watsowa Fatima da yarima wadanda ke zaune gefen Mai martaba,wani murmushi Fatima ta maidawa hajiya babba Sanan ta sunkuyar da kanta,

"Fatima"Mai martaba ya Kira sunan Fatima wadda ke zaune a gefensa,..

"Allah ya taimaki Mai martaba"....

"Ki kwantar da hankalinki karkice Zaki tada hankalinki Akan wanan batu kinji?insha allahu gaskiya zatayi halinta Kuma inaji a jikina kedin diyatace jinina ce,...naji Dadi nagode da halarcin da kikayi Allah yayi Miki albarka ya baku zaman lafiya"

Sunkuyar da kanta kawai tayi cike da kunya batare da tace komiba,

Haka Mai martaba yasa akatashi taro kowa ya watse,

********

Can dakinsa nada yarima ya shiga ya zauna a parlor ya kunna tv zuciyarsa Babu Dadi,saude kuyangarsa yayi Mata umarni da ta Kira Masa fatima a dakin hajiya karama,

Fatima na tare da bilkisu a bangaren ummu tasa aka Kira Mata ita suka hadu a can,

"Nayi matukar farin ciki daya kasance kedin ba shegiya bace da iyayenki Yar uwata Fatima naji Dadi saidai wani hanzari ba gudu ba,dazun da kuka baro fadar sarki naji wasu kananun maganganu suna tashi wajen hajiya babba da rahina cewa Wai karyane makirci kuka hada"

Murmushin takaici Fatima tayi "ki kwantar da hankalinki dik suna tunanin cewa karyane ba hotona bane Dana mahaifiyata,gaskiya zatayi halinta lokacin zanyi maganinsu daya bayan daya don har ke zansa a y'antamunke Yar uwata?"

"Nayi matukar farin ciki da Jin hakan daga gareki Fatima,Koda bansamu iyayena ba a rayuwa inada ke nasan bazaki gujeniba"..

"Ki tayani adduar samun mahaifiyata a raye,idan hakan ya kasance to karki Kuma Kiran kanki marainiya don itace uwa a garemu nidake"...

Bilkisu zatayi magana wayar Fatima ta hau ringing,da sauri ta duba number yarima ce baro baro a fuskar wayar,

"Ranka ya dade nawan nikadai?"tace cike da kissa,

A kausashe yayi magana "Ina kika shiga?na aika saude nemanki a sashin hajiya Wai bakya Nan?"..

"Ina zanje mijina?Wanda ya wuce sashen uwata?umm?me kakeda bukata ne!"

"Kizo kawai inason magana dake kafin mutafi gida"...

"Angama ranka ya dade?"Tai murmushi ta datse wayar ta juyo ga bilkisu wadda ke binta da kallo cike da shaawa da burgewa,

"Yar uwata Mai gida yayi Kira Bari inje inji wace rigimar ce kuma?Dan Naga hakan a idanuwansa tunda muka fito fada"

Murmushi bilkisu tayi "to me Miji?wato kin Zama Mara kunya ko? hmmm aje a lallasheshi"...

Sukai sallama fatima ta fice a gaggauce ta nufi sashen yarima zaituna na biye da ita,
Chapter 71 · 0% Book details