Sashe 3
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Can gefen wata bishiya yayi parking motarsa inda ya Saba ajiyewa idan ya shigo Kuma wajen ne ya kasance wajen zamansu idan yazo,ya Dade a cikin motar Yana waige waige wajen shiru Sai kukan tsuntsaye ko alamar giftawar Yan Mata da ya Saba gani be gani ba ya Dade a wajen a cikin motar Yana kalle kalle ko Allah zai hadashi da daya daga cikin aminanta na gidan Amma bega kowa ba ya kwashi kimanin minti arbain shiru babu wani labari haka yayiwa motarsa key ya juya jiki a sanyaye ya nufi hanyar gida....
******
Hajiya babba CE zaune da hadimanta a babban parlornta inda take ganawa da mutane ake karbar gaisuwa Tana zaune ta Mike kafarta daya daga cikin bayinta Tana Dan matsa Mata kafa idanuwanta a runtse zuciyarta na tsananin tafasa ta jiyo sallamarsa ,a hankali ta bude idanuwanta ta sauke akansa take taji tausayinsa ya kamata, yadda ya rame lokaci daya ya fita hayya cinsa saboda mutuwar Dan uwansa,a hankali ta bude baki ta amsa da "walaikumussalam"
Tsugunnawa yayi har kasa ya dukar da kansa cikin sanyin murya yace "barka da war haka mama?"
"Barkadai kabir" Kara dukar da kansa yayi cikin girmamawa yace "ya Karin hakurin mu?"
"Hakuri alahamdulillahi"
"Allah ya jikansa Allah ya gafarta Masa"
"Ameen"
Jim kadan ya Mike har ya juya ta tsaidashi "khabir"ta Kira sunansa,tsayawa yayi Jim kadan sanan ya juyo a hankali ya tsugunna batare da yace uffan ba,Bata damu da rashin amsawarsa ba ta cigaba da magana cike da kasaita da gadara wanan Karan magana takeyi sama sama "khabir inaso Kai zakaja ragamar shariar Dan uwanka Habib,inaso kasa kakin ka na lawyer ka hau kan aikinka banaso a ragawa dik Wanda yayi wannan aika aikar,ko wacece ta kashe maka Dan uwa ka tabbatar da kabiwa Dan uwanka hakkinsa nasan Kai gwanine wajen shariah Kuma babu Wanda ya Dace da wanan shariar Sai Kai,anjima nakeso kaje can station din ka bincika Mana yadda ake gudanar da bincike Akan yarinyar akara Bata tsaro saboda kada ta tsere,na lashi takobin dik Wanda ya kashemun da' Shima Sai an kasheshi ko Dan gidan uban waye"
Wani irin firgici da tsorone ya ziyarci zuciyarsa a Karo na farko a rayuwa tunda yake babu abinda ya taba tada Masa da hankali ya furgita kamar wannan al'amarin daya kunno Kai Nan Nan zufa ta shiga karyo Masa ta ko Ina be Isa ya tsallake umarnin mama babba ba Amma ta Yaya zai tsaya a shariah a kashe Masa Fatima Zahra?kirjinsa ne ya cigaba da bugu da sauri Amma Sai ya dake yace"zaayi bincike sosai zaayi yadda ya kamata insha allahu"
"Allah yayi maka albarka tashi kaje dama maganar kenan"
Mikewa yayi jikinsa a sanyaye dakyar yake taka kasa ya haka yake tafiya kansa Yana tsananin Sara Masa tamkar zai rabe biyu haka ya lallaba ya shige bangarensa.....
*******
Tunda aka rufeta a cikin wanan dakin da kullum Sai anyi Mata tambayoyi Wanda babu Wanda ta taba amsawa ko abinci baa Bata,Yan hajinta babu abinda sukeyi Sai kukan yunwa dikda babu abinda zata iyasawa a bakinta Koda ruwane, makoshinta ya bushe, idanuwanta sun kasa zubda hawaye, kukan zuci kawai takeyi,babu wani Abu da take tsammani Wanda ya wuce kisan Kai kamar yadda tayi Dan batada sauran Amfani a wanan duniyar me cike da tashin hankali kala kala batada wani sauran Amfani a matsayinta na marainiya babu uwa babu uba babu Dan uwa babu gata Sai Allah.....shin menene makomarta Wanda ya wuce a kasheta ta huta?.....ta rigada ta cire Rai da rayuwa tasanyawa zuciyarta dik Wanda yazo ya Kara tambayarta zata sanar dashi Akan itace tayi kisan gara a kasheta kawai....
******
Zazzabi ne Mai zafi ya lullubeshi a cikin daki tun bayan daya baro wajen mama babba wadda kalamanta bakaramin tada Masa da hankali sukayi ba tabbas shi ya Dace ya tsayawa yayansa ya kwato Masa hakkin ransa Amma ta Yaya ta Ina zaifara shariah da yarinyar da soyayyarta ta Gama zagaye sassan jikinsa da jijiyoyin jikinsa?
Hannu yasa ya dafe kansa daga kwancen da yake tare da runtse idanuwansa saboda yadda kansa ke Sara Masa tamkar zai rabe biyu....
Ya Dade a wanan yanayin yakai minti goma Sha biyar sanan ya Mike ya fada bathroom dinsa don ya watsa ruwa a jikinsa ko zai Samu sassaucin damuwar da yake ciki,bayan yayi wanka ne ya bude wardrobe dinsa ya ciro kayansa kanana wando jeans da tea shirt ya sanya sanan yaje gaban madubin dakin ya dauki turarrrika ya feffesa a jikinsa sanan ya fito,Yayi bangaren mahaifiyarsa,
A kan daddumar sallah ya same ta ta idar da sallahr laasar da sallamarsa ya shiga dakin ta amsa Masa yanemi gefenta ya zauna yayi shiru batare da yace komiba,kusan minti goma da zamansa ta waigo ta Dan kallesa tace"hakuri ya kamata kayi ansan cewa mutuwa da ciwo musamman Dan uwanka Wanda ka shaku dashi kuka Saba tare kuka taso, Dole ne ka sanyawa zuciyarka hakuri da dangana haka Allah ya nufa"
"Hakuri ya Zama Dole mama Amma rasa Yaya habib tamkar na rasa wani bangarene na rayuwata saboda yadda na shaku dashi yadda da'n uwana ke matukar kaunata"
"Kaunar da yakeyi maka,itace ya kamata ka saka Masa da yi Masa addua sanan wanan case din da zaa Mika kotu ka tsayawa Dan uwanka ka kwatar Masa hakkinsa,shariar bazata dauki lokaciba insha allahu duba da yadda jarida ta nuna yadda yarinyar tayi kisan kaga kanada babbar hujjar da zaka nuna a kotu ba saikasha wahala ba"
Shiru yayi zuciyarsa na Raya Masa abubuwa da dama game da wanan al'amari Amma ta Yaya zai tunkari shariah batare da bincike ba?
"Ka kwantar da hankalinka insha allahu zakayi nasara Akan wanan shariar ai ba ita bace ta farko da ka tabayi,Dan Kaine ka Dace da ita dazun Mai martaba ya kiramu nida mama babba yake fada Mana abinda ya Yanke Akan cewa Kaine zaka tsaya"
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun kawai"kawai yake maimaitawa a zuciyarsa domin be Isa ya tsallake hukuncin Mai martaba ba.....
Har mama ta Gama maganganunta Sam hankalinsa baya wajenta shi so yakeyi ma yaje yayi tozali da ita ko zai Samu kwanciyar hankalin daya rasashi na kwana biyu....sallama yayiwa mahaifiyarsa ya Mike Yana tafe Yana hada hanya,kallo ta bishi dashi tausayinsa na ratsa Mata zuciya Dan tasan rashin Dan uwansa ne yake tabasa....
*******
Misalin karfe biyar na yamma ya shirya tsaf ya fito Dan zuwa station din bashi da bukatar Yan rakiya a wanan lokacin Dan Yana bukatar ganawa da Fatima Zahra sosai dikda yaji labarin dik tambayoyin da akeyi Mata a police station babu Wanda ta amsa Amma zaije ya gwada tashi saar ko zata kulashi dikda bashida tabbacin hakan Amma yasan ko ganinta yayi zai Samu kwanciyar hankali.....
*******
Zuciyarsa cunkushe da tsananin fargabar yadda zai ganta be tabba tsintar kansa a yanayine tsoro da tashin hankaliba irin na wanan lokacin,Yana zaune inda ake ganawa da masu laifi yajiyo tashin tafiya hade da Karan kacha.....tun daga kafafuwanta ya Soma kallonta wadanda suke sanye da kacha an rufe da makulli,ya daga idanuwansa ya sauke a kan gangar jikinta Tana sanye da Riga wadda tayi kaca kaca da jini da ya bushe ya dago kansa ya sauke Akan kyakkyawar fuskarta Wanda ta dukar a kasa Tana tafiya har ta iso Dan sandan da ya rakotane ya juya abinshi tare da sarawa yarima khabir.....
Kamshin turarensa ne ya gauraye wajen Wanda tunda ta iso bugun zuciyarta ya tsananta tabbas tasan Mai irin wanan kamshin turaren,to me ya kawoshi Nan?
Tsayawa tayi a wajen kanta a kasa shi kuwa gogan ya kafeta da Ido jijiyoyin kansa gabaki daya sun fito a gaban goshinsa wani irin tashin hankali ya tsunci kansa kallonta kawai yakeyi baya ko kifta idanuwansa besan inda hankalinsa ya tafi ba tsintar kansa yayi da zubar hawaye.....Wanda tunda aka haifesa yaune na farko da damuwa ta sanyashi kwalla besan yanayi ba.....
Jin shiru yayi yawa ya sanya Fatima dago idanuwanta ta sauke akansa aikuwa Nan da Nan ta firgita ta Fara ja da baya a hankali a hankali....
"Fatima kada ki gudu ba nazo Nan wajen Dan in tuhumeki bane da kisan Kai nazone Dan in bincikeki Akan abinda duniya ke zarginki dashi na kisan Kai"
Girgiza Kai ta shigayi sai yanzun zuciyarta ta karaya hawaye suka Fara sakkowa daga idanuwanta Tana girgiza Kai hade da runtse Ido.....
"Fatima kiyi magana Dan Allah ki bude baki kicemun bake kikayi kisan kan Nan ba"
Girgiza Kai kawai takeyi hawaye na gudu a idanuwanta kamar an bude famfo batare da tace komiba....
Cikin tsananin damuwa da kyar ya Kara bude baki yace "Fatima na kasa gasgata kece Kika kashemun Dan uwa,Dan Allah ki fadamun gaskiyar lamari Ni Kuma nayi Miki alkawarin kubuta"
Bude idanuwanta tayi ta sauke akansa,da sauri ta kauda kanta gefe batare da tace komiba
Babu abinda yarima yafi tsana ya gani a rayuwarsa irin kukan Fatima zahra,idan hawayenta na diga ji yakeyi tamkar Ana zuba Masa wuta a zuciyarsa runtse idanuwansa yayi ya budesu sinyi jajir ya saukesu akanta......
Takowa yayi ya matso inda take a tsaye ya tsaya har tanajin hucin sautin numfashinsa ya daga murya cikin kakkausar murya yace "Fatima kifadamun gaskiya waye ya kashemun Dan uwana?kifadamun idan kece Kika kasheshi menene dalilinki na kasheshi?"......
Dago rinannun idanuwanta tayi ta saukesu akansa,Shima kallonta yakeyi tausayinta na ratsa jikinsa tun daga babban Dan yatsansa har zuwa kwakwalwarsa.....girgiza Kai kawai ya shigayi.....
*Muje zuwa Dan Jin yadda zata kasance*.....
*SLIMZY CE😍*
*🌩ANYI WALK'IYA.....🌩*
*💡 HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*
*NA SLIMZY*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata Faty D'an maliki*
04
"Kitaimakeni Fatima ki tausayawa rayuwata ki tausayawa kanki ki dubi maraicinki ki fadamun gaskiyar lamari Fatima kitaimakeni".....
Kallonsa kawai takeyi batare da tace komiba ganin kallon yaki karewa yasa yaja jikinsa ya jingina da jikin bango ya maida kallonsa ga ceiling din wajen batare da yace komiba...
Fargabar data tsinci kanta a wanan lokacin tafi wadda ta tsinci kanta ciki a Daren shekaran jiya shin ta Yaya zata kalli tsabar idon yarima ta fada mishi itace ta kashe dan uwansa?....wani sabon kuka ne ya kubuce Mata Wanda rabon da tasamu tayi kuka hankalinta ya kwanta tun Daren da mummunar kaddara ta fada Mata....