Sashe 4
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyo da dubansa gareta yayi fusace yake kallon yadda take kuka a duniya babu abinda ya Tsana a rayuwarsa sama da kukan Fatima bayaso yaga fatimansa Tana zubar da hawaye ji yakeyi tamkar ya tafka babban sabo,bashida burin da ya wuce ya dauketa ya zame Mata gatan duniya Amma wannan babban ala'amari ya faru,zuciyarsa na tafarfasa tamkar zai bugeta ya Fara magana "look Fatima,banazo wajen Nan Dan sauraron sautin kukanki bane,ki kasa bude baki kiyi magana nayi tunanin kaf duniyar Nan bakida kamata komenene Zaki iya fadamunshi Koda kuwa kisan Kai kikayi Wanda ake zarginki dashi yanzu,na shiga matsananciyar damuwa Wanda fada mikishi a yanzun Bata lokacine babban damuwar Dana shiga be wuce cewa ankamaki da laifin kisan Kai ba,Fatima ta Yaya kikayi kisan Kai kifadamun gaskiya Fatima bazan taba gudunki ba duk runtsi dik bala'i nayi Miki alkawarin kasancewa dake a kowani Hali Koda kece Kika kashemun Dan uwa kifadamun Wanda yayi kisan Nan aka kulla Miki sharri nayi alkawarin tsayawa Akan shariarki matukar kinada gaskiya"
Kallonsa takeyi cike da tausayawa,wasu zafafan hawaye na kara zubuwa daga idanuwanta ji takeyi inama ba itace tayi kisan kan Nan ba?inama dik wanan abun dake faruwa mafarkine ba gaskeba da idan ta farka bazata taba komawa bacciba harabada matukar zatayi mafarkin kashe Dan uwan yarimanta....
Takowa tayi ta tsaya a gabansa sanan ta durkusa kasa ta sunkuyar da kanta cikin dasasshiyar murya tace "Nina kasheshi da hannuna"
Wani irin faduwar gaba yayi Wanda tunda yazo duniya be tabayin irinta ba Nan da Nan ya kidime jikinsa babu inda baya rawa cikin daga murya yace "Nooooo"sautin muryarsa babu inda be amsaba a wajen saboda yadda yayi maganar a razane,jijiyoyin kansa suka fito rad'a rad'a a gaban goshinsa bakinsa har rawa yakeyi wajen magana,
"Fatima bake Kika kashemun yaayaah habib ba,fatima inada tabbacin bazaki taba kisan kaiba ,ko kiyashi baki taba kashewa ba balle mutum Dan Adam Mai Rai da Kuma lafiya,Fatima bakiyi kisan Kai ba wallahi bake kikayi kisan Nan ba,idan bakinki ya Kara cewa kinyi kisan Kai zan dauki mummunan mataki akanki"sambatu kawai yakeyi a haukace batare da sanin abinda yake fadaba
Dagota yayi daga tsugunnen da take Tana rusa kuka ya shiga girgizata"Fatima ki tausayamun kada in rasaki ki duba halin da muke ciki kada ki furtawa kowa kece kikayi kisan kan Nan kamar yadda kikayi kuskure wajen fadamun Fatima"
Kallonsa kawai takeyi tausayinta na Kara narkar Mata da zuciya yau yarimanta jarumi Wanda ko magana zaiyi yanayinta ne cikin kasaita da sarauta namiji Mai tsananin kwarjini da jarimta shine ya haukace akanta yake fadan maganganu wadanda Tana da tabbacin fadansu kawai yakeyi a matsayinta na tsintacciya maabociyar zaman gidan marayu?
Cikin tsananin kuka tace "saidai kayi hakuri yarima Amma tabbas ninayi kisan Kai Kuma bazan taba maka karyaba abinda nakeso dakai shine ka gafarceni kashe maka Dan uwa da nayi....banida wasu kalmomi da zanyi Amfani dasu wajen Kare kaina Akan aikata mummunan aiki da nayi ,idan na boyewa duniya bazan boyewa mahaliccina ba daga amsawar Nan da nayi maka bazakaji wani Abu daga bakina ba fatana Allah ubangiji ya gafarta min yasadani da rahamarsa idan an kasheni"
Tana Gama fadin haka ta juya da sauri da kyar take taka kasa Koda ta juya Dan sandan da ya kawota har yazo batare da Bata lokaciba yace "ranka ya Dade lokaci yayi har ka wuce time din da ake badawa"
Shiru yayi tamkar an dasashi a wajen Yana bin bayanta da kallo,har Dan sandan ya Gama magana ya juya bece komiba harta bace Yana kallon hanyar databi....
Mikewa tsaye yayi juwa na dibarsa muryarta CE take amsawa a kunnuwansa na kalamanta na karshe"fatana Allah ya gafartamun ya sadani da rahmarsa idan an kasheni"hannu yasa ya toshe kunnuwansa Yana girgiza Kai......"innalillahi wa Inna ilaihi rajiun ,shikenan tafaru ta Kare babbar kaddara ta fada musu yasan Fatima batayi Masa karya Bata tabayi masaba Amma yau yanada tabbacin abinda ta fada karya takeyi......hannu yasa ya sharce zufar dake digowa daga sumar kansa,zuciyarsa na ayyana Masa Anya kuwa maganar Fatima babu kamshin gaskiya ciki?.....Fatima bazatayi kisan kaiba haka kawai Saida dalili,menene dalilinta na kashe Masa Dan uwa?waye yasata?Fatima bazatayi kisan Kai haka kawai batare da samun taimako ba.....ya yarda da maganarta itace tayi kisan Kai Amma meye kwakkwaran dalilinta menene silarta na kisan Kai?.....gabansa ne ya tsananta faduwa daya tuna da kalaman mama babba"dik Wanda ya kashemun da' bazan taba Bari a kyalesaba batare da ankasheshi ba yadda ya kashemun wallahi Sai ankasheshi ko Dan gidan uban waye"
"Kabir Kaine ya dace ka tsaya ka kwatarwa Dan uwanka hakkin kasheshi da akayi Dole kasa kaki ka koma fanninka na lawyer"...jikinsa ne ya mutu daya tuna da wadanan kalaman....
Haka Nan ya Mike ya fito jiki babu kwaro ko komawa office din DPO besamuyi ba saboda tashin hankalin da yake ciki....
*******
Ana kiraye kirayen sallahr magriba ya Isa gida,masallacin gidansu ya shiga ya bisu sallah saboda ya tarar zaa tada sallah,bayan ya idar da sallah a massalaci ya Dade a zaune Yana addua sanan ya shafa ya fito....ya doshi hanyar shiga gidansu Koda ya shiga bangaren Mai martaba ya nufa Saida yayi kimanin minti goma sanan ya Isa bangaren a gajiye yake ga faduwar gaba da yakeyi minti minti,
Iso ya nema akayi mishi sanan ya shiga lokacin Mai martaba Yana zaune akan katuwar daddumar dake parlorn nasa Wanda aka kawatasa da kayan adon daki irin na sarauta,
Tsugunnawa yayi a gaban sarki ya kawo gaisuwa cike da ladabi da girmamawa sanan ya koma gefe ya zauna ya tankwashe kafarsa,sarki ya juyo da dubansa ga da'n nasa yace "kabiru meke tafe dakai ne?ya ake ciki game da case din mutuwar Dan uwanka kaje wajen jami'an tsaron ne"
"Ehh Allah ya taimakeka naje"
"To Masha allahu,me bimcike ya nuna?ansamu cikakken bayani daga yarinyar ne?"
Gabansa ya Yanke ya Fadi cikin tsananin fargaba yace"ehh to har yanzun dai batayi wani bayani ba game da kisan Amma dai tace itace tayi kisan kan"
Murmushi sarki yayi yace"a binciketa da kyau ta Fadi gaskiya Amma bana tunanin Wanda yayi kisan Kai zai amsa cewa Shi yayi batare da wani tunani ba,a Kara bincikata sosai zuwa ranan Monday kamar yadda sukace ranan zaa mikata kotu"
Cikin tsananin damuwa yarima yace "toh zaa bincika ranka ya Dade"
"Allah yayi albarka yanzun saika Fara shirye shiryen gudanar da shariar ko?nasan iyayenka sun fada maka hukuncin da masarauta ta zartar na cewa Kaine zaka tsayawa Dan uwanka Akan wanan shariar"
"Eh ranka ya Dade"
"Tashi gaje dik abinda yake Nan Sai a sanar Dani Allah ya bada nasara"
Jiki a sanyaye yarima yace "ameeen ranka ya Dade,a huta lafiya"
Mikewa yayi tamkar Wanda babu kashi a jikinsa haka ya juya Yana tafiya Mai martaba kallonsa kawai yakeyi Yana girgiza Kai Dan bakaramin tausaya Masa yayiba na rashin Dan uwansa da suke matukar son juna Wanda suka taso tare komi tare sukeyi saidai banbancin wasu abubuwa na halayya....
*******
Bangarensa ya koma ya xurfafa kansa a cikin tunani lallai Yana cikin tsaka me wuya,menene yake Shirin faruwa dashi?rasa Dan uwansa da rasa masoyiyarsa yarinyar da ya Dade Yana renon soyayyarta tun Tana kankanuwa ?shin idan ya tsayawa Dan uwansa ya karbar Masa hakkinsa ya tsayane Don kashe Fatima?koko zaiyi watsi da maganar iyayensa ne ya tsayawa marainiyr Allah?
Wata zuciyar CE tace 'kada ka manta Kaine kayi alkawarin tsaya ma Fatima dik halin da zata tsunci kanta Kuma baka da tabbacin kisan da ake zarginta dashi ita tayishi,kayi watsi da maganar tsayawa matacce ka tsayawa rayayya ka tsiratar da ita da halakata da zaayi don tabbas Fatima bazatayi kisan Kai da gan gan ba"
Mikewa tsaye yayi Yana nazarim shawarar da zuciyarsa ke bashi Amma ba Sai yankewa kansa shawara Kai tsayeba batare da ya samu amininsa ya fada Masa ba,tunda wanan abu ya faru Sai yanzun ya tuna da doctor Ahmad amininsa da suka taso tare sukayi makaranta tare.....kallon agogo yayi yaga karfe Tara da rabi na dare,dare be wani yiba ya Mike da sauri ya zuri key din motarsa ya fice...
********
Zaune suke a parlor yarima Yana korowa Ahmed labarin abinda ke faruwa cikin damuwa da tashin hankali,shi kansa Ahmad ya furgita da Jin wannan lamari dikda yasan da mutuwar na habib don har gaisuwa yaje,dukansu shiru sukayi a parlorn na tsawan lokaci sanan Ahmad ya Nisa yace "friend banaso ka saka kanka cikin matsalar da bazaka fitaba zuciyarka ta rigada ta makance da soyayyar wannan yarinyar da ka dauki yarda da'ri bisa da'ri ka Bata,bakada wata masaniya Akan wani Hali nata na boye sanan bakada tabbacin tanada gaskiya a wanan lamarin"
Kallonsa kawai yarima yayi sanan ya kauda kansa yace"friend wallahi tallahi ko kaffara bazanyiba nasan Fatima ba dagangan tayi kisan Nan ba,Ni abinda nake gani wanine ya sata tayi kisan Nan ko Kuma ta taka sahun barawo"
"Ta Yaya zata taka sahun barawo a guest house na gidan sarauta kabir ka rinkayin abubuwa da tunani fa yadda akayi ta shiga gidan shine babban kalu bale shawarar da Zan baka shine ka fita lamarin yarinyar Nan da ta taso gidan marayu yaran dake tashi su Zama terrorist a kasa Ni Ina guje maka saka kanka a matsala,babbar matsalar da zaka fuskanta da iyayenka na ka guji shariar Dan uwanka ja jini ka marawa bare baya yarinyar da baasan asalinta ba kadau son duniya ka Dora Mata"
Girgiza Kai kawai yarima keyi don ya Dade da sanin Ahmad matsoracine dalilin haka yasa yakiyin course din lawyer a cewarsa hatsarine"bazan juyawa Fatima baya ba bayan da can banyi Mata hakanba Ni Zan tsaya Mata Koda duniya zata juya Mana baya nida ita"
A furgice Ahmad keyi Masa kallon tuhuma da alamar tambaya,gira daya khabir ya daga Masa yace "yess Zan tsaya Mata Koda zaa kashemu tare zanyi jihadi Zan sadaukar da komi nawa dan farin cikin marainiyar Allah "
"Lallai kasamu matsala kabir ,saika tanadi amsoshin da zaka baiwa Mai martaba da mama babba da mama karama,sanan ka tanadi audugar da zaka toshe kunnenka da ita akan zagin da zakasha a idon duniya,sanan katanadi kalaman da zaka fadawa alkali Dan Kare wadda aka Kama da kisan Kai wadda akwai kwararan hujjoji da suka nuna cewa itace tayi kisan kan Nan ciki ko harda na'urar computer "