← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 80

Sashe 33

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki tashi ki bacemun daga gani domin ko ganinki banasonyi mujiya,idan ma kinje kikace bakije ba asirinki zai Tonu idan kere na yawo zabo na yawo watarana zaa hadu dik ranan Dana kamaki da shi wallahi saina shayar dake azaba,bacemun daga gani munafukar banza Kuma anjima kisani akwai aikin da zakiyimun "

Sumi Sumi Fatima ta Mike ta fice,dikda haka tsoro be fita a zuciyarta ba yauce Rana ta farko da tayi jarumta a gaban hajiya lallai a gaida bilkisu da badan itaba yau bakaramin azaba zaa kurba Mata ba,

Direct inda tasaba zuwa tayi ibadah na taje ganin ankira sallahr laasar tunda dadewa,alwala ta dauro tazo wajen ta shimfida dankwalinta ta tada sallah.....

Hajiya karama ce tafe Maryam na biye da ita baiwarta sun fito daga fadar sarki har sunbiyo ta wata hanya sai hajiya karama ta fasabi ta canjo hanya suka bullo ta inda Fatima ta tada sallah....

Tundaga nesa mama karama ke kallon Fatima wadda yau shine Karo na uku da ta ganta Tana ibadah tunda take bayi da kuyangin gidan Nan Bata taba ganinsu suna ibadah ba Amma wanan yarinyar Tana yawan ganinta,sunkaraso daidai Fatima tayi sallama ta zauna Tana cikin yin tasbihi da yatsunta ta hango mama karama da sauri ta kwashe shimfidarta ta zube a kasa "barka da yamma ranki ya dade"

Cikin sanyin murya irin na mama karama ta amsa da "barka"....ta wuce abinta Maryam na biye da ita suka hada Ido da Fatima sukaiwa juna murmushi....

Har cikin zuciyarta Fatima Taji dadin amsa Mata da mama karama tayi,Dan tunda tazo gidan Bata taba gaisheta ta amsaba sai yau alhamdulillah Koda hakan zata rinka amsa Mata zata gaisheta dikda a takaice ta amsa Mata.....

********
Zaune mama karama suke itada yar autarta afnan suna Hira sama sama anan ne mama karama ta jeho zancen Fatima "Niko afnan kin taba ganin bayi da kuyangin gidan Nan suna sallah Koda ta asuba ne?"

Girgiza Kai afnan tayi "ah ah mama"

"Akwai wani abin mamaki Wanda yau shine Karo na biyu Dana gani,wanan yarinyar Yar gidan marayu Ina yawan ganinta Tana ibadah sanan sallahr asuba ma baya wuceta,ranan da Mai martaba yayi zazzabi na kwana a bangarensa wajen hudun asuba na ganta zaune a kasa Tana nafila kafin ma ayi asuba"

Murmushi afnan tayi "mama ai dik kuyangin gidan Nan Babu Mai kirkinta babu Mai hakurinta ga ibadah gata shiru shiru kamar magana bai dameta ba"

"Umm dik kirkinta bazan sotaba saboda abinda ta aikata,dikda dai ance ba laifinta bane Amma dai idan batasaba bin mazanba bazaa kaitaba"

Sallamar yarima ce ta dakatar dasu daga hirar da sukeyi,....a tare suka amsa Masa da afnan,

Gefen mama ya takwashe kafarsa hade da durkusar da Kai kasa cike da ladabi yace "barka da yamma ranki ya dade"

Dan juyowa tayi ta kallesa,take tausayin Dan nata ya lullubeta hade da soyayyarsa dake ratsa ko Ina a jikinta,horone takeyi Masa Akan rashin Jin maganarta Amma Harga Allah ita kanta kewar Dan nata takeyi....ajiyar zuciya ta sauke "barkanka baka fita bane?"

"Ehh mama banje ko inaba Ina daki"

Dan kauda Kai tayi gefe "hakan nada kyau,ka gaida mamanka ko?"

"Yanzun na fito nakeson inje in gaisheta sai indan fita"

"Badai nisa zakayiba ko?don kasan anjima zamu hallara a fadar Mai martaba"

"Insha allahu"

Jinjina Masa Kai tayi "zaka iya tafiya"

Durkusawa ya karayi cikin girmamawa "nagode ranki ya dade"....kallon kanwarsa dake gefe yayi yadanyi Mata murmushi itama ta mayar Masa sanan ya Mike zuciyarsa fari tasss Domin adduarsa ta fara amsuwa mahaifiyarsa ta fara sakkowa daga fushin da takeyi.....

*******

Sauri sauri yakeyi zashi sashin hajiya babba ita Kuma ta fito hannunta dauke da faranti da cups kanta a kasa take tafiyarta,....ta bullo wata Yar kwana sukai kicibis Yana ganinta yaja ya tsaya a hanya harta karaso,

Batasan da mutum ba tai Karo dashi,da sauri taja da baya zata juya don har ga Allah Bata kalli fuskar ko wayeba hannunta ya janyo ta fado jikinsa ta saki farantin a kasa ta bude baki zatayi magana,..yasa hannu ya toshe Mata baki Yana kallon fuskarta Yana murmushi "sarkin tsoro.....yanzun kin kasa tantance kamshin jikin mijinki koh?"

Zaro ido tayi ya sakar Mata baki da dayan hannunsa daya Yana rike da kwankwasonta "Dan Allah yaayah ka rufamun asiri ka sakeni kaga dazun an ganmu fa har hajiya aka fadawa"

Kara matseta yayi a jikinsa yasa fuskarsa daf da Tata "nafiso aganmu a haka Kinga idan aka kaiwa Mai martaba karar anganni a jikinki ko muna wani Abu to tabbas zaice saina aureki"

Hararsa tayi"nidai kasakeni"

Kara rungumeta yayi a jikinsa Yana shafa bayanta "bazan sakekiba saikince kina Sona"

Runtse idanuwanta tayi zuciyarta na harbawa ga tsoro da ya cikata Dan babu makawa dik Wanda ya bullo bangaren hajiya saiya gansu "naji Ina sonka"....ta kauda kanta gefe

Murmushin mugunta yayi Mata ya Bata peck a kumatu"kece ruhina bintu"

Motsin tahowa sukaji da sauri ya saketa ,jikinta na rawa ta shiga kwashe cups dinda ke yashe a kasa jikinta na tsananin rawa....

Bilkisu ce ta taho Tana murmushi, zubewa tayi a kasa fuskarta dauke da murmushi ta fara kawo gaisuwa "barka kadai ranka ya dade Yaya yarima"

Murmushin shima yayi Mata "barkanki bilkisu ya bakunta?"

"Alhamdulillah"

Jinjina Kai kawai yayi ya wuce Yana murmushi hade da shafar fuskar bilkisu dake rabe a gefe.....

Yana wucewa bilkisu ta Mike tsaye Tana dariya "sannu sarauniyar soyayya harda rungumeki akayi kika lafe Ina kallonku ai,...gadi na tsaya yi muku wallahi da saade ta ganku Dan hajiya ita ta aika nace nice zanje shinefa ta zauna da hajiya kafin indawo"

Kunyar bilkisu ce ta lullube Fatima Tana murmushi kasa kasa "nidai banason sharri kindai tsaya Kinga gulma"

"Ohh hakama zakice?danasani na Kira hajiya ta kamaku"

Zaro ido Fatima tayi "da nashiga uku"

Dariya bilkisu ta sheke dashi harda rike ciki "Amma gaskiya soyayyarku na burgeni fa?hmmm anaso Ana kaiwa kasuwa su wata"

Wucewarta Fatima tayi Tana fadin "kedai kikasani".....

Kallo bilkisu tabi Fatima dashi ta saki sassanyar ajiyar zuciya a Fili ta furta "Fatima baiwar Allah kina bani tausayi dikda ni dake bamuda banbanci dukkanmu tsintattu ne Amma jarabawarki tafi ta kowa"....wasu kwalla masu zafi suka sulalowa bilkisu a kuncinta,tasa hannu ta share ta tafi Aiken da akayi Mata"

******
Yarima zaune gefen hajiya babba bayan sun gaisa Babu yabo babu fallasa dukkansu sukai shiru na Dan wani lokaci sanan hajiya ta kasa Shirun da cewa "ya kamata kaje wajen deejahmah ku daidaita kanku Domin inaga zaa dawo da aurenku Nanda wata daya"

Gyara Zama yarima yayi Dan Harga Allah ya mance da wata deejahmah da wani zancen aurensu burinsa be wuce ya ga Fatima ba suyi Yar soyayyarsu ta boye Amma hakanan zai auri deejahma kafin yasamu farin cikinsa,....sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yace "insha allahu anjima daddare zanje gidan nida Ahmad bayan ishai"

Murmushi hajiya babba tadanyi irin na manya "Allah yayi albarka"

Da sauri ya kalleta yaushe rabon yaji wanan kalmar a bakinta ?mamakinsa ya danne ya amsada "ameen"

Yana zaune bilkisu ta shigo ta zube gaban hajiya cike da ladabi tace "Allah ya baki yawan Rai na aiwatar da umarninki"

Murmushin kasaita tayi ta daga Mata hannu bilkisu ta koma can gefe ta rabe Kai a kasa,

Kallon yarima hajiya babba tayi "inajin dadin wanan sabuwar baiwar da ka kawo Domin tanada hankali da natsuwa ga biyayya dik abinda zan sata tanayimunshi cikin gaggawa batare da Raina ya baciba inaga itace zata Zama baiwar fadata maana amintacciyata"..

Murmushi yarima yayi "hakan nada kyau hajiya"

"Zaka iya tafiya"

"Nagode ranki ya dade"..ya Mike abinsa ya bar sashin.....

******

Waya hajiya babba tasa takira hajiya rahina lokacin suna zaune a part din yaran harda babban danta daya zo daga kasar waje Kiran hajiya babba ya shigo wayarta....

Kallon wayar tayi sanan ta kalli deejahmah tayi murmushi"hajiya babba ce"

Gyatsine deejahma tayi "ki dauka Mana"

Dauka gwaggo rahi tayi suga gaisa....take sanar Mata da deejahmah ta gyara yau yareemah zai kawo musu ziyara,....bakin hajiya rahina yaki rufuwa saboda murna haka sukai sallama ta kashe wayar...dukkansu kallonta suke suna jiran Karin bayani

"Gyarawa zakiyi Domin yau yareemah zai kawo Miki ziyara"

Tabe baki deejahmah tayi "me Kuma zai kawoshi?shida ko kallona bayayi ta wanan tsinanniyar yarinyar yake?shegiya Mara iyaye ni dama yayi zamansa"

"Nasha fada Miki ki boye wanan kiyayyar da kishi da kikeyi akansa ki Bari ki mallakesa yadda Zaki juyasa son ranki Kuma ki azabtar da shegiyar yarinyar Mai kamada mayu"

Tura baki deejahmah tayi batace komiba gwaggo rahi ta cigaba da lallashinta Tana faman zuba shagwaba....

********

Shirinsa yayi tsaf zuwa fadar sarki bayan yayi sallahr magriba ya sha Riga da Wando na kaffani Ash colour da bakar hula akansa anyi Masa design Mai kyau irin na sarakai.....

Yana tafe ya bullo ta parlor Babu kowa ciki kasantuwar dik sun tafu fadar sarki daga hajiya babba har mama karama khausar da afnan dik suna can sai maaikatane ke gilmawa sama sama....

Sauri sauri yakeyi yayi lattin zuwa fada Dan yasan shi suke jira a tattauna Akan matsalolin yau da kullum,

Tana tsaye Tana kalle kalle ya hangeta murmushi yayi Saida yazo daidai gefenta zai wuce yasa baki daidai kunnenta ya rada Mata "zan tafi fada yanzun zanje neman aurenki wajen Mai martaba"...Yana Gama fadin haka yayi wucewarsa....zubewa tayi a kasa Tana ganin jiri na juyawa a duniyarta....

*******
Shiri kasariki akeyi a gidan galadima na tarbar yarima Wanda ya kasance yaune na farko da zaizo zance wajen deejahmah....

Uwarta ta saki jiki Tana faman gyara Yar Tata,bakaramin kyau deejahmah tayiba Domin it's kanta ba baya bace wajen kyau sai shiryata mamanta takeyi da taimakon kuyangi dake Miko wancan kawo wancen....

Murmushi kawai gwaggo rahi takeyi Tana kallon yadda yar Tata takai karshe wajen haduwa.....

"Kinyi kyau harki gaji ya'ta....matar yarima Dan sarki....kwanan nan sunanki zai fito a cikin jerin sarauniyoyi na duniyar sarauta na tabbatar da babu wata wadda zata hada kanta dake wajen jerin kyawawan matan sarakan wannan duniyar tamu....Nan gaba kadan Zaki tashi daga matar Dan sarki zuwa matar sarki Kuma uwar Dan sarki Mai jiran gado"

Murmushine ya subucewa deejahmah cike da zumudi tace"gaskiya mama kin iya kirari kinji Wai yadda kaina ke Kara girma?"
Chapter 33 · 0% Book details