Sashe 48
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cike da ladabi bilkisu ta kakalo yake tadan durkusa "ranki ya dade Ina Nan,nayi gyaran parlor ne nace Bari idan kinfito in tambayeki idan kinada bukatar a kakkabe Miki cikin daki saboda yau Naga gidan ya kacame ko Ina da Dan datti "
Jim kadan hajiya babba tayi "kinyi tunani to a kakkabemun daki kafin mudawo idan kingama ki rufemin bedroom din da makulli ki bude waccan drawer din kisa makullin ciki sai kije abinki tunda dare yafarayi"
"Toh ranki ya dade"
Wani kallo hajiya rahina takewa bilkisu sanan ta rufawa hajiya babba baya suka fice,
Kamar jira takeyi ta fada dakin a guje direct drawer ta bude ta shiga waige waigen neman abinda suka ajiye,daga idonta sama tayi ta sauke idonta Akan gorar swan Wanda bashi da maraba da ruwa,jikinta ne ya Kama rawa tunani kala kala ta shigayi sanan daga karshe ta yanke shawarar canja ruwan ciki,
Da sauri ta nufi bayi ta bude ta shige ta rufo kofa jikinta sai kyarma yakeyi zufa na zuba a jikinta dakyar ta bude ta antayar da ruwan ciki,ta samu ruwan fanfo ta maida yadda ruwan yake ta goge gorar ruwan ta fice ta ajiye inda ta gani gabanta na tsananin faduwa....
A gaggauce ta kakkabe ko Ina ta gyera gadon ta rufo kofar yadda aka Bata umarni tayi ta fice,jikinta be bar rawaba tunanin tonuwar asirinta take....
*******
Kwankwasa kofar gidan tayi,da sauri Fatima tazo ta na kici kicin budewa sanin tasan bilkisu ce,
Tana bude kofar sukai Ido hudu da yarima wani kallon tuhuma yake binta dashi hade da mamakin abinda ya kawota Nan gidan,
Wucewarta tayi ciki ta nufi kitchen batare da tace Masa komiba kirjinta na tsananin bugawa,
Ciki ya shigo Yana kwalawa hajiya zainab Kira "ummu"(yadda suke kiranta dashi)shiru yaji ya shiga leka dakunan dik Babu ita Amma komi a gyare,
Mamakine ya kasheshi Tana tsaye ganan standing gas Tana juya miyar da takeyi kamshi ya karade ko Ina ya shigo ya tsaya a bayanta,gabanta ya tsananta faduwa saukar hannunsa taji a kafadarta ya juyo da ita Tana facing dinta Yana jifanta da wani irin kallo Wanda ita kanta taji ta kasa aiwatar da komi "bintu shine akayi banza Dani aka wuce aka barni bazaki tarbi mijinki ba ko "Yana Shirin janyota jikinsa taja da baya Tana fadin "Haba yaayah nidai kabari kada hajiya tazo Dan Tana gab da shigowa ta ganmu a Nan "
Ta juya ta kashe gas din ta Mika hannunta Tana kokarin Ciro kuloli ya fizgota jikinsa ya rike ta sosai "to tazo Mana bakisan ni Dan ganta bane a wajen ummu?inda zata ganmu ma ba abinda zatace"..
Turo baki tayi tana kunkunai hade da ture hannunsa'naji kabari inkwashe abincin Nan sai kace dik abinda zakace"
Makale kafada yayi ya sauya murya cike da shagwaba "umm umm naqi"
Dariya ta kamayi Masa Dan yadda yayi da muryarsa Dole ne ko waye yayi dariya,
Batare da tace komiba ta shiga kwashe abincin fuskarta dauke da murmushi,Yana tsaye a gefenta ya kafeta da Ido yadda take aikin Yana gefenta sai zuciyarsa ke ayyana masa sundace da juna tamkar Miji da Mata,
A bangarenta mamakinsa takeyi yadda yakeyin abubuwa tamkar ba Dan sarautaba,mafi yawancin masu mulki akwai kasaita da ji da Kai Amma Banda yariman ta ko dai itace yakewa haka oho a haka ta Gama gwashewa ta dibo kulolin tazo parlor ta jera dik inda tayi Yana biye da ita kamar bindi Tana faman kyalkyala Masa dariya a haka sukazo parlor ya jona tv ya kunna ya koma kujera ya zauna tazo ta bayansa ta durkusa da kanta daidai kunnensa cikin rada tace "yaayah barka a Nan ni zan wuce kafin hajiya tazo"....lumshe idanuwansa yayi Yana Jin wani Abu nayi Masa yawo a jiki yadda takeyi Masa rada a kunne hannunsa yakai daidai fuskarta ya shafa "kina nufin tafiya zakiyi?"
Ta bude baki zata amsa aka kwankwasa kofa ....da sauri ta Mike daga durkuson da tayi jikinta har rawa yake Tana adduar Allah yasa dai ba hajiya bace...
Tana budewa sukai Ido hudu da bilkisu ta sauke ajiyar zuciya,
Kallon kallo suke yo da bilkisu "meye kikemun kallon rashin gaskiya"
Murmushi Fatima tayi takai Mata duka a kafada "kema yau kinamun kamada marasa gaskiya"....dariya Suka sa su duka a tare suka shigo da bilkisu,.tsayawa tayi turus Tana kallon yarima da ya hade Rai Yana kallon tv
Kallon Fatima tayi da tambaya a fuskarta ,....dage Mata gira tayi sanan ta rada Mata a kunne "tunda bakizo ba shi yazo jiran matarsa"ta kashe Mata ido daya Tana dariyar keta,
Tabe baki bilkisu tayi "aikinku kenan kamar chewing gum"...dage Mata kafada Fatima tayi tana dariya kasa kasa
Mikewa yarima yayi ya kalli Fatima ta gefe "Bari inje tunda kinsamu Yar Taya Hira dama na dauka ummu Tana Nan ne"
Ido ta kifta Masa Tana dariya ya wuce,
Waje suka samu suka zauna bilkisu na murmushi tacewa Fatima "wato yanzun kin Kuna bakijin tsoro ko?kin manta ke baiwace kaskantacciya inji su"
Dariyar takaici Fatima tayi sanan ta fuskanci bilkisu da kyau tace "a zahiri ni baiwace kaskantacciya ,Amma a badini ni yace cikakkiya Mai yanci,bazasu fahimci hakanba sai Nan gaba kadan zasu fahimci hakan lokacin da deejahmah ta koma baiwa ni nakoma uwargijiyarta"
Dariya sosai bilkisu keyi lokacinda sukaji karar zaa bude Kofa da sauri suka saisaita kansu,
Hajiya zainab ce hannunta dauke da sadik da sauri Fatima ta Mike ta amsheshi Tana fadin "barka da zuwa hajiya"
Kallon yadda Fatima ta gyara gidan hajiya zainab keyi Tana murmushi sanan ta nisa tace"Kar inkarajin kin kirani da hajiya ko ranki ya dade ki kirani da yadda kowa ke kirana ummu".
Sunkuyar da Kai Fatima tayi ta juya taje kwantar da sadik,minti kadan ta fito ta tadda hajiya zainab ta baje a parlor bilkisu ta Mike Dan su wuce ta kallesu ta gefe "dare yayi bazaku iyabin hanyar Nan ku kadaiba Nima kabiru nasa ya dakko mota ya kawoni Kuma Koda zai dawo sai anjima Dan akwai maganar da zanyi dashi,yanzun dai kusamin abinci kuyi zamanku anan da sassafe kwa koma cen din"
Kallon kallo bilkisu sukeyi da Fatima sumaiwa juna murmushi sanan Fatima ta tsugunna tafara serving ummu da abinci....
********
Wajen Sha daya na dare yarima ya shigo sashen hajiya zainab Yana sanye da jallabiya don har yayi Shirin bacci takirasa tanason magana dashi...
Suna zaune a parlor take shaida Masa Taji dik abinda ya faru tun daga farko har karshe har maganar aurensa da Fatima....shine ma yasa takeson magana dashi...
Ajiyar zuciya ta sauke ta sanan ta dubesa ta Soma magana kasa kasa Dan bataso su Fatima su jiyo "a yadda Naga yarinyar tanada natsuwa ga ibadah sanan jikina ya bani aurenku alheri ne Amma naji Mai martaba yace Wai sai ansamu lokaci kafin ayi bikin"
"Ehh ummu haka yace"....
"Toh ni zanyi karambani Dan zansamu shi Mai martaba mu tattauna Akan ayi auren nan karshen shekara tunda yanzun muna watan biyu ko?"
Dadine ya lullube yarima ya shiga faraa yace "ehh ummu da zaayi hakan da zaifi"
Ta juyar da Kai fuskarta a daure "insha allahu zan nemi Mai martaba da maganar nasan zai saurareni Allah ya zabi abinda yafi Zama alheri Amma kayi shiru ko yarinyar karka fada Mata"
Yarima ya sunkuyar da Kai Dadi na ratsashi "insha allahu"....
"Tashi kaje dare yayi"....Dan Dadi dakyar yarima ke taka kafarsa ya fice....
******
Washe gari da wuri wuri su bilkisu suka gyarawa ummu gidan ummu sukai Mata abin karyawa sukayiwa sadik wanka sanan sukai Mata sallama suka wuce.....
Shirye shirye yau kawai akeyi na kamu har masu decorations aka Kira sukayi sukayi decorations a babban filin da aka ware Dan yin shagalin biki suka sassaka kujeru da runfuna sosai wuri ya tsaru tsayawa fadar yadda wurin yayi kyau Bata lokaci ne.....
Tunda Fatima ta wayi gari take faduwar gaba haka kawai saidai ta ambaci innalillahi wa Inna ilaihi rajiun,hasbinallahu wa niimal wakil kawai takeyi.....
*******
"Na Gama shirya dik yadda komi zai wakana a wajen Nan ranki ya dade yadda kika zubar da hawaye Akan shegiyar Nan itama saita zubar akanki saitayi danasanin shiga hurumin da ba nataba"cewar Rahane dake tsugunne gaban deejahmah wadda ke faman shiri Mai kwalliya zatayi Mata,
Murmushi deejahmah tayi ta jinjina Kai alamar gamsuwa sanan tayi Mata nuni da ta fita.....ta Mike ta fice a dakin....
Shirye shirye kawai akeyi gida ya rikici da Yan uwa da manyan masu kudi wadanda akeji dasu su kawai ke shigowa gidan ana parking hadaddun motoci....
*****
"Fauziyya ki tabbatar kinyi abinda ya Dace yadda na fada Miki kada asamu matsala,Dan inaso ingama da karamar alhakin ne kafin inkoma Kan babbar dikda itama cikin sauki zanyi yadda yadace"
Fauziyya tayi murmushi tace"insha allahu innah ai bazata ganeba"
"Nasani shiyasa ma nasaki ki tabbatar kin Bata Kuma kinyi yadda nace"
"Insha allahu"
"Tashi kije faizah tun dazun ta shirya Tana jiranki ".....
*Muje zuwa*
*SLIMZY😍*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
34
Yan matan amarya uku ne tare da amarya a wani kebabben daki inda nan ne ake tsarawa amarya kwalliya wadda ta fito da ainihin kyawunta Domin ita kanta deejahmah ba baya ba wajen kyau da diri wadda fatarta ta kasance ita ba faraba ita ba baka ba fatarta tamkar mutanen Etopia ga manyan idanu da take dasu farare tas da yalwar Zara zaran gashin idanuwa sanan ita ba doguwa bace ba gajereba Tana cikin matsakaitan Mata Mai Dan jiki da shape dai dai ita....doguwar Riga ce jikinta kalar golden da kyalli kyalli na net da stones Wanda akai kwalliyar rigar dashi head dinta ma golden colour tayi matukar kyau na kece raini fuskar Nan Tata wadda ta kasance Koda yaushe a daure take yauma hkn ya kasance Amma hakan be tsantsar kyawunta bayyana ba...
Mayafi aka kawo Mai tsadan gaske aka lulluba Mata akanta wayarta ce ta fara Haske da sauri ta cire pin din wayar Tex ne ya shigo kamar haka ... _HELLO IN D NEXT 5 MINUTE IDAN BAKI FITOBA WALLAHI BAZANJE WAJEN TARON BA WAYE YARONKI DA ZAKI SHANYA...MTSWW_.