← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 80

Sashe 14

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka sosai nakeyi harda shassheka ya juyo da kallonsa gareni a Karo na biyu yace "tunda bazaki wankanba na Baki minti biyar ki cire rigar jikinki domin idan xan kwanta da mace bana kwanciya da ita da Kaya"

Kallonsa nakeyi Ina hawaye nace "Dan girman Allah ka rufamun asiri kada ka rabani da budurcina"

Kyalkyalewa da dariya yayi a wanan karon yace "Fatima ai budurcin naki nake bukata,kinsan nawa na kashe Akan wanan kyakkyawan jikin naki da budurcin naki?Koda yake kudi ba matsalata bane,matsalata in kashe kishin ruwanki dake damuna,tunda nasaki a Ido dik macen da aka kawomin bana samun gamsuwa da ita Dana runtse idanuwana ke nake gani ke kawai nake bukata nikuwa ban taba neman Abu narasaba ,dik abinda nasa a gaba saina samu,ki yarda Dani in mallaki wanan Surar da Allah yayi Miki daganan Zan yantaki ki Zama baiwata Mai kula Dani a matsayina na Dan sarki Kuma sarki Mai jiran gado"

Gabana ne ya Yanke ya Fadi na shiga girgiza kaina Dana tunada Yaya yarima a kullum burinsa Bai wuce Allah ya bashi ikon ingantamun rayuwaba,Sai gashi Dan uwansa keda burin lalatamun rayuwa....runtse idanuwana nayi Ina Mai adduar Allah ya dauki Raina a wanan lokacin in huta....

Idanuwana a rufe,batare da nasani ba ya Mike ya kashe tv sanan yasa key a kofar yabar key din a jiki ,ya kashe fitulun dakin Sai wata Mai haske kadan ya Bari ya hayo saman gadon ,hannunsa naji ya rungumoni Yana fadin "taho inyi Miki masauki a jikina in share wadanan hawayen dake Bata wanan kyakkyawan fuskan da tazo a gidan marayu"

Zabura nayi Zan kwace ya rinkeni tsam a jikinsa tamkar zai ballani,dakyar nake numfashi Ina kici kicin kwacewa ya tura hannunsa saman rigata Yana lalubena,mutsu mutsu nakeyi rikon da yayimun bazan iya kwacewa ba kawai nasa hakorina a kunnensa na yanka Masa cizo zafin da yajine ya sakeni na Mike a guje nayi lungun kujerar da ya zauna yaci apple,

Biyoni yayi ya damkoni cikin zafin nama ya rungumeni ya haye jikina ,waige waige nakeyi Babu yadda xanyi in Kara cizonsa,hannunsa daya na cikin rigata Yana wasa da kirjina gashi ya sakarmun nauyi,sosai yake mutsukamin jiki inajin zafi Yana kokarin rabani da rigar jikina,

Gefe na hangi Wukar da yaci apple da ita na rinka matsawa da hannuna har nakai wajen Wukar na janyota a hankali na rike a hannuna Babu yadda zaayi inyi motsi,

Gyarawa yayi da niyyar hayeni,da sauri na da'go Wukar na ca...ka Masa.....

Kuka Mai karfi Fatima ta fashe dashi Tana numfarfashi tamkar zata hadiyi zuciya ta mutu.....

Dafe Kai barrister hauwa tayi zuciyarta na tsananin bugawa da sauri da sauri..... Ta dago Kai ta kalli Fatima dake kuka tace "tabbas kece Kika kashe yarima habib Amma kisan Kare Kai"

Kuka Fatima takeyi Tana fadin "anty kada kibari a sakeni,kicire hannunki daga kareni a matsayina na Mai laifi kibari a yankemun hukuncin da yayi daidai Dani".....

Tana durkushe Tana kuka barrister hauwa na gefe Tana sharar hawayen dake zubowa a idanuwanta,wani Dan sanda ya shigo yace "lokaci yayi madam"....

Ka'da Masa Kai barrister hauwa tayi ta Mike dakyar takejan kafarta ta fito.......

*SLIMZY🥰✍🏻*🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA:SLIMZY✍🏼*

_wattpad@slimzy33_
*sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

12

Tafe take Tana sharar hawaye har ta karaso wajen mota inda barrister Abdul tun fitowarta ya kafeta da idanuwa,ta wani fannin zuciyarsa keyi Masa lugude cike da fargabar me zai biyo baya,

Mota ta bude ta shigo idanuwanta jajur tamkar wadda akayiwa dukan tsiya,kallonta mijin nata keyi cikin kosawa yace "madam badai yarinyar nan tayi taurin Kai ba"

Girgiza Masa Kai tayi cikin dasasshiyar murya tace "ko daya,tayi bayani yadda akeso inaso ka Kira yarima kafin muje gida kace mu hadu a gida"

Wayarsa ya zaro a aljihunsa nan da nan yayi dialing number yarima,Wanda bugu daya ya dauka kamar me jira, barrister Abdul yace "ranka ya Dade gamunan zamu taso daga police station kazo gida mu hadu"

"Ok"kawai yarima yace ya datse wayar....

Driving barrister Abdul keyi Amma minti minti yakan juyo ya kalli barrister wadda har yanzun hawaye be daina gudu a idanuwantaba,hankalinsa ba karamin tashi yayi,ya kosa su Isa gida yaji meke faruwa?

Yana kwanar unguwarsu daike GRA yarima Yana karyo kwana da tasa motar Yana biye dasu Mai gadi ya bude musu gate suka shige a tare,

Koda barrister ta fito,kallo daya yarima yayi mata yasan akwai matsala,dik inda hankalinsa yake a wanan lokacin a tashe yake,

Haka sukaja jiki barrister hauwa ta kwankwasa kofa,wata matashiyar budurwa Mai tsananin Kama da ita ta bude musu kofa wadda ko baa fada ba kawanwarta ce ,Dan tsugunnawa tayi tace "barkanku da zuwa"

Babu Wanda ya amsa sai yareema da ya karba a ciki,sanan tace "Ina yini Yaya yarima"

"Lafiya lau Aysha,ya makaranta?"

"Alhamdulillah"tace ta juya ta shige dakinta,su Kuma sukai maxauni a parlor....

Barrister hauwa ce ta gabatarwa da yarima da barrister Abdul recording din bayanin Fatima.....

Saurare sukeyi Amma ko kafin su Gama barrister Abdul jikinsa ya jike da gumi,yayinda yarima fuskarsa ta jike da hauwaye da zufa a lokaci da'ya,dakyar suka iya karasa sauraren audio din....

A haukace yarima ya Mike ya kauwa iska nushi,idanuwansa tamkar garwashin wuta yayinda jijiyoyin kansa suka fito a goshinsa Rada Rada yace cikin kakkausar murya "biri yayi Kama da mutum,tabbas habib zai aikata hakan domin a rayuwarsa ta duniya Babu abinda yake kauna fiye da mace,gashi mace tayi sanaddiyar aikasa lahira,shin wasu kalamai ya tanada domin yiwa Allah bayani akan abinda yaje aikatawa yayi sanadiyyar bakuntarsa lahira?shin da wani baki zaiyiwa Allah bayanin cewa marainiyar Allah yaje lalatawa rayuwa Allah ya karbi rayuwarsa a wanan lokacin?.....nasani ko Fatima Bata kasheshiba,tunda Allah bai kaddaro zai lalata mata rayuwaba Allah bazai bashi damar yin hakan ba,dik dukiyarsa dik takamarsa da mulki Allah zai karbi numfashinsa a lokacin da yaso,ya godewa Allah ma ba aikata zinar yakeyiba Allah ya karbi numfashinsa"kuka sosai yarima yakeyi Yana kaiwa da komowa cikin parlorn ya rasa inda zaisa rayuwarsa...

Hawaye barrister hauwa ta share tace" *ANYI WALK'IYA* halin kowa ya fito,shin wanan muguwar dabiar da akesa yara aikatawa masuyi suna tunanin Allah zai kyalesu?ko asirinsu bai toniba a Nan duniya Allah zai tona musu asiri a lahira ballantana dik Wanda ya cutar da maraya daidai da kwayar zarra sai Allah ya fitar Masa da hakkinsa tun a duniya,yanzun gashi tun baaje ko inaba *ANYI WALK'IYA* halin kowa ya fito...asiri na gab da tonuwa"kuka takeyi tamkar wadda akaiwa mutuwa,

Cikin alhini barrister Abdul Wanda jikinsa gabaki daya ya mutu dauriyace da jarumta yasa Shima bai zubarbda hawayen ba yace "kuyi shiru ku kwantar da hankalinku yanzun abinyi zamu tattauna,yadda shariar Nan zata gudana"

Juyowa yayi yarima daga kallon gefe daya da yakeyi ya sauke rinannun idanuwansa akan barrister Abdul sanan yace "insha Allahu Fatima zata fita ,a wanan shariar domin self defense ta zo yiwa kanta,sanan koba haka ba akwai casset na CCTV da hajiya babba tace ta anso wadda inada tabbacin akwai komi a ciki Kuma Bata kalla ba ballantana tasan wani Abu,shi zan gabatar a kotu Wanda shine a matsayin shaidata na kisan habib kaga Ina gabatarwa wanan casset shi zai wanke Fatima"

Murmushi barrister hauwa tayi Tana hawaye a lokaci da'ya tace"to alhamdulillah insha Allahu nasara na garemu"

"Allah yasa"cewar yarima dukkansu suka amsa da "ameeen"

Juyowa barrister hauwa tayi ta kwalawa sister dinta Kira "Ashmah!!kawo Mana abinci Dan Allah "

"Toh"ta amsa daga cikin daki,sanan ta fito ta shiga shigowa da kululin abinci,Nan suka baje sunaci,dikda yarima cin abincin yakeyi tamkar magani......

********
Da dawowarsa gida bangaren hajiya babba ya nufa direct,da sallamarsa ya shiga sanan ya durkusa a gabanta ya kawo gaisuwa,ta amsa Masa cike da kasaita,ko kafin yayi magana ta juya gefenta ta dakko wani sabin casset sai WALK'IYA yakeyi ta mikawa yarima ,ya amsa yace "Allah ya bamu nasara"

"Ameeen "tace hade da lumshe idanuwanta Tana ayyana abubuwa da dama.....

*********
Daren ranan yadda yarima yaga Rana haka yaga dare,da ya kwanta ya rufe idanuwansa amsa kuwwar muryar Fatima yakeji na audio Wanda take bayani,bayasanin lokacin da yake tsuntar kansa cikin hawaye masu dumi Wanda shi kansa besan yanayinsu ba,haka har asuba ta gabato....

*******
Washe gari ko kafin ya shirya ya fito daga bangarensa tawagar motoci da securities dik sun shirya domin wanan tafiyar da hajiya babba zaaiyita wargidan sarki,Wanda yarima yasha mamakin Jin hadda hajiya babba zaaje,tare da kannensa,da tawagar bayi masu take mata baya,

Haka kawai ya tsunci kansa cikin faduwar gaba,haka ya daure ya gaida iyayen nasa,sanan yayi musu jagora don tafiya.....

*******
Tun daga harabar kotu zaka tabbatar da yau shariar Mai zafice jamaa cike makil har waje, securities ne suke gyarawa Ana budawa tawagar gidan sarki hanya ,inda idanuwan mutane sukai caaa akan sarauniya da yaranta Yan mata Wanda suka fito suna taku daidai suna kallon mutane a wulakance har cikin kotu,

Babu wajen Zama Amma haka aka tashi jamaa don matar sarki da yaranta su samu wajen Zama,Nan dogarawa da bayi duka zagayesu....

*Courtttttttt*

Kowa ya mike lokacin da maigirma alkali ya shigo kotu...

Bayan ya zauna ,sannan kowa ya samu wurin Zama a don sauraren wannan shariah Mai sarkakiya da chakwakwiya...

"Ya Mai girma Mai shariah, a yaune kotu zataci gaba da sauraren karar da akeyi akan Fatima Zahra wadda ake zargi ta kashe yarima habibu Dan sarki"...

" Koh lauyoyi masu karewa da wadda suke Kara suna kotu?".cewar alkali.....

"Eh ,yamai shariah" yarima Kabir ya rankwafa alamar girmamawa

Itama Barr hauwa da Abdul suka rankwafa cikin girmamawa.....

" Kotu na saurarenku".....

A nutse yarima Kabir ya tashi tsaye sannan yace ...

"Yamai shariah zanso kotu ta bani dama domin ingabatar da sheduna, Akan kisan da fatyma Zahra tayi"

"Kotu ta baka dama Barrister Kabir"..

"Ya Mai shariah ranar 20 ga watan june Fatima Zahra ta ziyarci guess house na masarautar barayar Zaki, inda aka Kamata da kisan Dan gidan sarki habib..."

"Objection my Lord ,"Barr hauwa tafada cike da kunar Rai kamar batasan yarima Kabir ba, "yakamata Barrister ya gyara salon tambayarshi, domin har yanxu zargi ake ba a tabbatar da Fatima a matsayin a Mai laifiba"

"Ka gyara salon tambayarka Barrister"

"Nagode ya Mai shariah"

"Ya Mai shariah zanso kotu ta bani dama domin a kunna wannan CCTV cassette na yadda kisan ya kasance"
Chapter 14 · 0% Book details