← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 80

Sashe 67

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru yayi Yana nazarin maganarta,can ya Mike tsaye yayiwa hajiya rahina sallama ya fice, deejahmah ta sauke wani malalacin murmushi sanan ta juyo tayi hugging din mamanta "saina Kara dawowa ki gaida abbah"ta dagawa mamanta hannu sanan ta fice, hajiya rahina ta bita da kallo cike da so da kauna ta sauke ajiyar zuciya tace a fili"ya'daya tamkar da dubu uwar magajin sarki"....Tai murmushi ta shige daki...

*****

Takaicin Fatima yasa yarima kasa cewa komi tunda suka shigo motar yake wurga mata harara ta gefe gashi ya rasa dalilin da yasa ko motsi tayi idanuwansa sai sun kalleta,

Itama Tana kallonsa ta gefen idonta yadda yake watsa Mata harara,...sai kawai taji kwalla ta ciko a idanuwanta ta kwantar da kanta jikin window tasa hannu a fakaice ta cire kwallar dake taruwa a idanuwanta...

Driver ne ya karya kan mota da nufin zuwa gidan Mai martaba,take yarima ya dakatar dashi ta hanyar daka Masa tsawa "kaiii Ina zaka Kuma"....

Burki yaja sanan ya juyo cike da girmamawa yace "ranka ya dade na dauka zamuje gidan sarki ne"

"Juya ka kaimu gida kawai"ya kauda kansa gefe ransa a bace,

Ko karasa parking driver beyi ba Fatima ta bude side dinta ta fice a motar tayi cikin gida,

Dakinta ta shiga ta rufo kofar ta danne bayanta da kofar ta saki wani irin kuka Mai ban tausayi "ya ilahi...Allah kana gani Kaine gatana ban dogara da kowa ba sai Kai,Allah ka bayyana mun iyayena Koda sun mutu ne"...hawaye ke gudu a idanuwanta ta durkushe a jikin kofer Tana rusa kuka Mai ban tausayi.....sosai take kuka ba wani Abu bane ya tada Mata hankali kamar gorin iyaye da akeyi mata...tabbas rashin iyaye masifa ne,

Runtse idanuwanta tayi tasa hannu ta cire gyalen data yane kanta dashi tayi jifa dashi a kasa ta zauna Tana kuka durshan....shikenan tun kafin akai ko Ina yarima ya fara wulakantata Akan Yar uwarsa?....ta dafe kirjinta yadda zuciyarta ke bugawa sauri da sauri....Nan da Nan kanta ya shiga Sara Mata ta kwanta a kasa a wajen ta rufe idanuwanta....

*********

Har karfe Tara saura na dare Bata fito parlor inda suka Saba Zama ba deejahmah na kwance gefensa kanta na kan cinyarsa Yana shafa Mata gashin kanta,

A zahiri gangan jikinsa ke zaune a wajen Amma ruhinsa da tunaninsa gaba daya suna wajen Fatima...minti minti yakan daga Kai ya kalli sama ko zaiga gilmawarta Amma shiru....

Sai wajen goma saura na dare ta fito sanye da kayan bacci kanta Babu dankwali Riga dav wando ne na bacci purple a jikinta,wandon iya cinyarta ne ya Dan Kama Mata jiki sanan rigar Mai siririn hannu ce Mai gidan breziya sun masifar yi Mata kyauz

Hannunta dauke da plate da sauran Apple a Kai tazo center table ta ajiye ta kauda kanta dikda taga a yanayin data samesu sai Tai wucewarta ya bita da kallo ta gefen ido...

Dago Kai deejahmah tayi "nafarajin bacci muje mu kwanta"tace a shagwabe Tana kallonsa,..

"Owk muje"

Saita Mike shima ya Mike...

Maimakon yabi dakinta sai ya juya yayi sashin Fatima Saida yakai wajen matakala ya Dan tsaya taji muryarsa Yana fadin "Bari inje inyi sallama da yarinyar Nan"

"Ok"kawai tace ta Haye sama

*******

Tana kwance cikin duhu hawaye na gudu a idanuwanta tajiyo karar bude kofarsa da sauri ta rufe ido Dan Tana iya ganin inuwarsa ta jikin kofa,

Hannunsa yasa ya laluba jikin switch ya kunna globe Haske ya kauraye dakim...

Ya Dade tsaye Yana kallon fuskarta wadda idanuwanta ke rufe tankar me bacci Amma hawaye na gudu a fuskarta. Jikinsa ne yayi sanyi ya tako a hankali ya Haye saman gadon har inda take ya sunkuyo da fuskarsa daidai fuskarta Amma Bata bude idanuwanta ba dikda kirjinta dakeyi Mata lugude

Bakinsa ya Dora Kan nata ya shiga kissing dinta Amma ko motsi batayiba....ya dade a haka sanan ya dago kansa still yana kallonta idanuwansa jajir ya maida idonsa Kan kirjinta wadanda suke a tsaye tsaye...take yaji wani Abu na tsarga Masa yakai hannunsa ya shafasu....dikda haka Bata motsabba sai hawaye dake Kara gudu a fuskarta,

Tausayinta ne ya lullubesa ya ja jiki ya sauko daga gadon yaje ya kashe globe yadan juiyo ya kalleta jin ta motsa,Amma sai ya fice kawai zuciyarsa Babu Dadi...

********
Da asuba bayan tayi sallah kanta keyi Mata ciwo Tana zaune Kan dadduma wayarta tayi Haske ,

Tasa hannu ta duba wayar Tex ne ya shigo kamar haka "fatan kin tashi lafiya bintu,...ki shirya da wuri zamuje gidan mutumin Nan da Ahmad"

Tana Gama karantawa ta ajiye a gefe ta Mike ta fada toilet tayo wanka ta fito ta shirya,...

*******.
Wajen karfe Tara Ahmad yazo kofar gidan be shiga ba ya Kira wayar yarima ya sanar Masa da Yana kofar gida,..

Sauri sauri ya shigo dakin Fatima Tana zaune ta shirya fuskarta jajir saboda kukan data kwana tanayi "ki fito ga Ahmad a waje shi zai daukemu"

Batace komiba ta Mike ta biyo bayansa,....kusan a tare suka sakko kasa

"Allah ya kiyaye ranka ya dade"deejahmah dake tsaye gefe tace,

Daga Mata hannu yarima yayi ya fice,Fatima tabi bayansa

*******
A mota ahmad ne kawai suke Hira da yarima ita kuwa Fatima tamkar kurma haka take a motar tafe suke zuciyarta na tunani kala kala yadda zata Rama abinda deejahma tayi Mata,...shi kansa yariman ba kyalesa zatayiba saita horasa....

Zuciyarta ke kudura Mata irin abinda zatayiwa Deejahmah na ramuwa.......

Tafiya Mai nisa sukayi tamkar zasu bar garin har suka shigo cikin wani Dan karamin gari inda Nan ne Ahmad yayi parking ya fita ya shiga wani gida Jim kadan suka fito da wani tsoho sai kawai Ahmad ya bude gaban motar ya cewa yarima "koma Baya zai shigo zamuje gidan mutumin da ya kawo Fatima gidan marayu ne"

Fita yayi ya bude baya ya shiga mutumin ya shiga gaba Ahmad ya tada motar...m

Ta glass Fatima ke kallon tsohon mutumin Wanda Babu tantama tasanshi a gidan marayu da dadewa shine tsohon me Zama a store wajen ajiye record.

******

Wani tsohon gida wanan tsohon ya nunawa Ahmad Nan sukayi parking Ahmad ya kashe motar kowa ya fito...yara ne suka zagaye motar suna kallon tamkar Basu taba ganin mota ba,

Wani yaro Ahmad ya Kira ya aika cikin gidan ya nema musu izinin shiga ,

Jim kadan ya fito "baabah kuluwa tace ku shiga"....

Ahmad na gaba tsohon Nan na biye dashi yarima da Fatima na biye dasu,

"Lale marhabun da zuwan baki"wata tsohuwa dake zaune a babbar tabarma a tsakar gida tace....

"Yauwa"cewar wanan tsohon maaikacin gidan marayu sanan suka zazzauna a tabarma....

Tsohuwar kebinsu da kallo daya bayan daya sanan tace "bangane Kuna,suwayeku?daga Ina kuke?"

Tsohom maaikacin gidan marayu ne ya Soma magana "sunana isyaku yakubu,ni tsohon maaikacin gidan marayu ne sanan ni abokin me wanan gidan ne malam sani suleman"

Shiru tadanyi sanan tace "to meke tafe daku?"

Nan malam isyaku yayi Mata bayanin komi da dalilin zuwansu,

Ta Dade sunkuye da kanta kasa batare da tace komiba Tana faman jinjina Kai,..yayinda kowa ya watsa Mata Ido Yana jiran me zatace,

Fatima wadda ke gefe gabanta ya tsananta faduwa Babu abinda take ambata a zuciyarta sai innalillahi wa Inna ilaihi rajiun....fatanta Bai wuce Allah ya cika Mata burinta ba,

Sun Kai minti goma Sha biyar sanan tsohuwar Nan ta dago fuskarta jike da hawaye Tana bin Fatima da kallo "tabbas Nan ne gidan malam sani suleman Amma ya rasu shekaru da dadewa saidai inada wata sheda guda daya Wanda ya barmun yace saboda wata Rana"...Tana Gama fadin haka ta Mike ta shige daki,

Suna Nan zaune na Yan mintoci sanan ta fito hannunta rike da hotuna guda biyu ta mikawa Fatima "amshi yarinya ki duba hotonki ne keda uwarki domin a Nan aka haifeki dikda uwar Taki ba Yar Nan bace Amma a bayan hoton tayi wani rubutu"

Hannun Fatima har rawa yakeyi ta amsa ta kafe hoton da idanuwa...itace Tana Yar shekara uku Akan cinyar mahaifiyarta dukkansu suna dariya akai musu hoton....juya bayan hoton tayi ta duba wani rubutu haka...M.B.Z...shine abinda aka rubuta a jiki sanan kasan anyi wasu rubutu kanana masu yawa...

Muryar tsohuwar sukaji "kuje da wanan hoton akwai adreshi a kasa na mahaifarsu ne idan har baku samuba baa yardaba kuzo kusameni inada sauran Karin bayani"....ta Mike ta shige daki,

Itadai Fatima hawaye kawai ke gudu a idanuwanta yayinda ta kafe dayan hoton da Ido shine na mahaifiyarta ita kadai Tana murmushi....

Hannunta Yana rawa kanta a kasa ta mikawa yarima Wanda jikinsa har tsuma yakeyi Yana duban hoton da sauri ya juya bayan hoton idonsa suka sauka Akan bakin da ya gani kamar haka M.B.Z...wani irin faduwar gaba ne ya ziyarceshi ya Mike a zabure ya tsaya Yana Kara ware idanuwansa.....Yana maimaita bakin a bakinsa....

Kallon yadda jikinsa yake rawa takeyi idanuwanta taf da hawaye take binsa da kallo....

*Muje zuwa*

*SLIMZY😍*
[8/28, 20:00] 🥰slimzy🥰: 🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

44

Kallon hoton yarima yakeyi Babu ko kifta idanuwa....hannuwansa ne kawai yake rawa yayinda zuciyarsa ke bugawa tamkar zata fasa kirjinsa ta fito,

Ahmad ne ya Mike Yana duban yarima yadda dik tashin hankali ya bayyana a fuskarsa yace "ranka ya Dade lafiya kuwa?meke faruwa ne"....still yarima Yana tsaye idonsa Akan hoton bema San Ahmad Yana magana ba Saida ya gaji ya bugi kafadarsa "malam da Kai nake magana fa meye ya faru ne?ko kasan wani Abu dangane da wanan hoton ne?"

Murmushi kawai yarima ya sauke yayinda ya cije lebensa kwalla ce cike a Ramin idanuwansa sai kawai ya kada kansa dakyar ya iya juya kansa ya kalli Fatima wadda ke durkushe da daya hoton Tana kallo Tana kuka,

"Tashi muje gida"

Wanan tsohon ne ya sauke ajiyar zuciya "iko sai Allah wanan al'amarin akwai boyayyen lamari cikinsa Allah ya warware muku yara"

Ahmad ne yayi karfin halin cewa "ameen"... yayi gaba yarima na biye dashi hannunsa rike da hoton,

Fatima ce karshen fitowa daga gidan Tana kuka Mai ban tausayi tanayi Tana waigen kofar gidan,....dakyar ta shiga mota suka tafi,

Gidan tsohon maaikacin gidan marayu suka fara zuwa suka saukesa,
Chapter 67 · 0% Book details