← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 80

Sashe 15

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya babba dake gefe Tana kallon komi sai a wanan lokacin tayi murmushi,

A hankali komi ke tafiya tundaga lokacin da Fatima ta farka a firgice Tana kallon yarima har zuwa lokacin da ya koma gefe yanacin apple abinshi , daga Nan Kuma kawai sai aka Nuno Fatima Zahra rike da wuka ta dabamai,

Hayaniyace sosai ke tashi , hajiya babba Koh sai wani murmushin nasara take yi

Shiko Barrister Kabir mamaki ne da fargaba suka rufeshi don beyi tunanin anyi editing wani Abu a cassette din ba,

Dakyar ya Tattaro natsuwar shi da jarumta, sannan yace cikin karyewar zuciya

"Yamai shariah wannan cassette shike nuna Fatima Zahra itace tayi kisan da ake zarginta dashi na yarima habib,nagode ya Mai shariah" sannan ya koma mazauninshi,

Wasu zafafan hawaye ke zubowa a kuncin Fatima,hade da runtse idanuwanta,

Rubuce rubuce alkali yayi sannan yace "Koh lauyan wadda ake zargi sunada abin cewa?"...

A hankali Barr hauwa ta Mike take tafiya kamar wadda kwai ya fashemawa a ciki ,da alama zuciyarta a karye take game da case din Fatima Zahra.ta matsa inda Fatima Zahra ke tsaye Tana hawaye,

"Mal Fatima , zanso ki kwantar da hankalin ki Nan gidan adalci ne , kiyi bayanin abinda kika sani game da mutuwar yarima habib Dan sarki"

Sai da ta share kwallah da ke bisa fuskarta ,sannan taja majina tafara bayani a hankali ........ Daya bayan daya take yarfo bayani kamar yadda tafadama barrister hauwa , sannan ta karashe cikin kuka Mai karfi...

Hayaniyace ta kaure a kotun kowa da abinda yake fade ,

A fakaice Barr hauwa tashare hawayenta da ya digo Mata sannan tace

"Ya Mai shariah inaso kotu tayi laakari da cewa Fatima Bata kashe yarima habib daganganba inllah domin ta kare kanta *(self defense)*,

"Yamai shariah I refer to section 59 of d penal code ,.Wanda yake bayanin mutum yakashe wani a dalilin Kare kanshi Koh dukiyarshi,
Yamai shariah, inaso kotu ta duba lamarin Fatima Zahra duba da wannan section na penal code,nagode ya Mai shariah"

"Kotu zataje hutun Rabin lokaci intadawo zaa cigaba"

*Courtttttttt*.......

Bayan kowa yafita ciki kuwa harda tawagar gidan sarki,ya rage sai kawyoyi kadai cikin kotun suna rubuce rubuce, Barristers Abdul ,hauwa da yarima Kabir sukayi mahada domin Kara tattaunawa kan case din, domin dukkansu sun tsorata da cassette din da suka gani,dikda yarima Yana zargin akwai wata manakisa Wanda babu tantama hajiya babba ce ta hadata,

Sosai Barrister hauwa ke kuka wiwi , ta kalli yarima tace cikin kuka ,

" ranka ya Dade Fatima Zahra na cikin wani Hali wallahi, domin inde alkali be duba lamarin Fatima ba under section 59 to wallahii Babu Mai fitar da ita sai Allah don bamuda wata kwakkwarar hujja ta bayanin da Fatima keyi,". Jan majina tayi sannan tacigaba da cewa

" kaduba kaga cassette dinnan wallahi da gani ba complete bane, gashi mukuma bamuda wani shedar da zamu gabatar Wanda zai nuna Kare kanta tazoyi"😭😭😭😭

Sosai ta rikice ,a hankali Barrister Abdul ya rungumeta Yana bubbaga bayanta alamar tayi shuru sannan shima yace , "ki kwantar da hankalinki my jidda, Allah na tare damu insha Allah Fatima Zata kubuta"

Yarima Kabir wanda tunda hauwa ta Fara bayani yakarajin ya tsani wannan duniyar da bakomi cikinta sai San zuciya,da cuta da rashin gaskiya, dafe da kanshi yake wadda yakeji kamar zai tsage biyu,

Sunfi minti 20 batare da sun samo solution ba, kowannan su ranshi a dagule yake,ganin saura 10minutes, Barrister Abdul yayi karfin halin Basu kwarinvgwiwar kan sucigaba da adduah insha Allah Fatima Zahra zata kubuta......,

*Bayan Rabin Awa*

" Bayan tattaro dukkannin bayanai da shedu da aka gabatar a gaban kotu , kotu zata gabatar da hukunci kamar haka,"

"Fatima Zahra ba zaa iya guaranting dinta self defense ba, saboda a cassette din da aka gabatar gaban kotu ya nuna kawai anga ta chakamasa wuka batare da sanin meyamata tayimai hakanba"

Gaban barrister yarima ya yanke ya fadi,ya dago idanuwansa hade da kafesu akan alkali,

"A bisa dalili da Haka kotu ta yankewa fatimazahra hukuncin kisa ta hanyar,.....

"A dakata ya Mai shariah ,adakata" wani maaikacin gidan guest house na gidan sarkine ,Wanda ranan da hajiya babba ta je guest house din ya labe ya saurari komi gameda tattaunawarsu da yakubu ne yashigo Yana haki kamar anjehoshi,

Kowa kallonshi yakeyi cike da mamaki , hajiya babba dake gefe kallonsa takeyi cike da fargabar abinda yazoyi, ta tashiga firgici,hade da juyawa gefe da gefenta,ganin habu daya daga cikin masu tsaron guess house din,ta juyo da dubanta hade da kafesa da ido,

Sai da ya Dede ta natsuwarshi sannan ya Fara bayani dallah dallah

"Yamai shariah wannan shine asalin cassette me dauke dakkannin bayanai game da kisan yarima Kabir"

Gaban hajiya babba ne ya yanke ya fadi,tayi kurrr da ido Tana kallonsa,

"Wanda aka gabatar a kotu bashi bane na gaskiya,domin an goge wurare da dama a cikinsa...Wanda hakan ya farune a sanadiyyar umarni da aka bada ayi hakan,Wanda basaina fadi Wanda ya bada umarnin hakanba"

Nan kotu ta har gitse da hayaniya,saida alkali yayi gyaran murya ya bada umarnin ayi shiru ,Shima ya maida dubansa ga wanan bawan Allah Yana Mai sauraronsa,

"Mai shariah na gwammaci in Fadi gaskiya ne domin ubangiji bazai barni cikin kwanciyar hankaliba in har nabari aka yankema wannan marainiyar Allah hukunci bisa kuskure,Wanda ni nasan gaskiya na take sanin,"

Mika cassette din akayi sannan akasa yafito tar a projector kowa na kwalalo idon ganin ya abin yake......

*Muje zuwa😂🏃🏻‍♀....na gudu tunkafin hajiya babba ta kamoni*

*SLIMZY🥰✍🏼*🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩

*HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*

*NA:SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

_Allah ubangiji ya jikanki yayi Miki rahma_ *HAFSAT RADDA* 😭😭😭

13

Tiryan tiryen duk abinda ya faru tsakanin yareema habib da Fatima Zahra ke fita tar a projector da aka kunna a court,

Mamakine dankare a fuskokin alumma , Nan da Nan kotu ta kaure da hayaniya,

Barrister hauwa farincikinta a lokacin be misaltuwa, ita da Barrister Abdul ganin Allah ya bayyana gaskiya,..gogan Koh hamdala kawai yakeyi Yana kara godema Allah abisa wannan gaskiya da ta bayyana ,sosai yakejin farinciki mara misaltuwa a cikin zuciyarshi,

Hajiya babba duk ta rikice take sai zare ido take yi,Amma can kasan zuciyarta ita kadai tasan abubuwan da take ayyanawa,

Bayan bubbuga tebir, sannan aka bukaci kowa yayi shuru domin alkali ya gabatar da hukunci,

Dattijo Mai cike da kamala da natsuwa wato alkali abubukar assadiq ne ya Gyara zaman gilas dinshi sannan ya dago Kai ya kalli alummar cikin kotun cike da natsuwa hade da kwarjininshi,yayinda kowa yayi tsit tamkar babu jamaa a ciki don sauraren mai alkali zai yanke,

"Abisa shedu da suka gabata a gaban kotu , bayan dogon nazari kotu ta yanke hukunci kamar haka"

" Kotu tayi laakari da cewa Fatima Zahra Bata kashe yarima habib da ganganba inlla domin Kare kanta,
Abisa dalili da Haka kotu tayi granting release na Fatima Zahra akarkashin tsari na section 59 of d penal code,don Haka kotu ta sallami fatyma Zahara (discharge and acquitted)

"Sanan kotu tabawa jamian tsaro damar kamo maaikatan gidan marayu wato hajiya halima da haruna,
Don kotu ta yanke musu hukuncin zaman gidan kaso na shekara biyar,
Duk wani Mai complain zai iya daukaka Kara zuwa kotu ta gaba..."

*Courtttttttttttttttt*

A hankalinki Fatima Zahra ta runtse idanuwanta tanamai hamdala ga ubangijinta a lokacin da Alkali ya wanketa,ta rasa a wani yanayi ta tsinci kanta a wanan lokacin,farin ciki ne koko bakin ciki?....idanuwanta ta bude karaf sukai ido hudu da yarima,murmushi ya sakar mata a fakaice hade da kanne mata ido daya take ya waske tamkar bashiba,

Barrister hauwa kasa boye farincikinta tayi saida ta mikama Barrister Abdul hannu sukayi wani musabaha cikin kauna irin ta Mata da miji,

A hankali Barrister Abdul ya Rada Mata a kunne , "yade madam kuka ya karekoh" ......murmushi tayi sosai har saida hokoranta suka bayya cikin tsantsan farinciki,

Suna a hakane yarima Kabir yayi gyaran murya sannan ya mikama Barrister Abdul hannu sukayi musabaha,sanan ya juya ya shiga ayarin tawagar gidansu don tafiya gida,

Takowa Fatima tayi a hankali har ta iso inda su barrister Abdul ke tsaye shida madam dinsa,Tana kokarin tsugunnawa barrister hauwa ta dagota ta Kai mata runguma ,wani kukan Dadi Fatima ta fashe dashi barrister hauwa na bubbuga bayanta alamar lallashi,

Dago kan Fatima tayi tasa hannu ta share Mata hawaye tace"kuka ya Kare Fatima,ai kinyi kuka iyayinki yanzun lokacine da Zaki godewa Allah Akan bayyanar da gaskiya da yayi,lokaci da'ya kika tsinci kanki a balai na duhun masifa Wanda muka kasa bayyana Haske,sai Allah da kansa ya bayyana , *ANYI WALK'IYA* halin kowa ya fito saiki godewa Allah da niimar da yayi Miki"

Jinjina Kai Fatima tayi hade da yin murmushi Mai kayatarwa sanan barrister hauwa ta sauke ajiyar zuciya tace"ya kamata muje dake gidana yanzun kiyi wanka ki huta zuwa wani lokaci kafin musan abunyi ko"

Harga Allah Fatima bataso haka ba saidai a yanzun batada burin da ya wuce yiwa barrister hauwa biyayya domin ta nuna Mata kauna a lokacin da take tunanin babu Wanda zai kaunaceta a duniya....

Babu musu tabi bayansu har wajen motarsu suka shiga barrister Abdul yaja mota......

*********

"Bazan taba samun kwanciyar hankaliba matukar ban karbi hakkin da'na daya tilo ba,Domin wanan shariar akwai manakisa a cikinta akwai wata kulalliya Kuma wallahi dik Wanda yace zaija Dani to zan iya ganin bayansa"

Kallonta khausar keyi sanan tace "Niko a ganina mama bamuda wata hujja da zamu Mika wanan Sharia zuwa want kotu Domin ko mun daukaka Kara Dole sai munbada hujja Kuma bamuda ita"

A fusace hajiya babba ta fara balbala masifa tamkar ta Ari baki "meye amfanin mulkin da nake dashi?meye amfanin dukiyar da Allah ya bani?da bazanyi amfani da itaba wajen kwatarwa Dana yancinsa bayan anyi sanadiyyar ransa sanan anbishi da sharri to wallahi da sake"

Kamshin turaren yarima ne ya karade dakin lokacin da ya shigo Yana sauraron furucin da hajiya babba keyi,

Goya hannunta tayi ta baya Tana kaiwa da komowa cikin parlorn fuskarta babu annuri,sallamarsa ta juyo da ita tace"yanzun nake Shirin aikawa a kiraka don kaji hukuncin Dana yanke na daukaka Kara zuwa supreme Court Dan ni ban yarda da wanan hukuncin ba"
Chapter 15 · 0% Book details