Sashe 68
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yarima da kansa ya fito yayi Masa godiya sosai ya Ciro kudi masu yawa a aljihunsa ya Mika Masa sukai sallama sanan ya juya ya shiga gidan gaba ya zauna,
Ta gefen ido Ahmad ya kallesa "Ina muka nufa?"
"Gidana zamuje"
Jin amsar da yarima ya bawa ahmad yasa Fatima saurin dago kanta Tana duban bangaren da yarima yake,....sai ta sunkuyar da kanta zuciyarta nayi Mata tsananin Kuna da zugi...ga tsantsar takaicin yarima dake kwance a zuciyar Fatima...dik yadda taso da suje gidan sarki taga ummunta Amma yarima ya Hana sai kawai ta kauda kanta ta cigaba da zubar hawaye,
A kofar gida ya saukesu ya juya abinsa suko a tare suka shiga gidan,
Deejahmah na tsaye tana Shirin Hawa sama suka shigo dik tabisu da kallo ganin yanayin da suka shigo....
Sama Fatima ta Haye a guje Tana hada matakala
Yarima dake Shirin bin bayanta deejahmah ta dakatar dashi "barka da dawowa"
"Barka dai"....ya Haye sama abinsa...tabishi da kallo hade da tabe baki,
******
Kan gadonta ta fada ta fashe da kuka harda majinu Tana juyi a haka ya sameta a dakin,
Bece Mata komiba ya jingina kansa da jikin bangon dakin shima ya runtse idanuwansa saiga wasu hawaye masu zafi na sauka a fuskarsa,..
Zuro kafafuwanta tayi kasa ta Tako gabansa ta tsaya "ka Tai makeni Kabir ka kaini inda iyayena suke Domin yanayinka gabaki daya ya nuna kanada masaniya game da inda iyayena suke...ka taimaki rayuwata ka kaini inda iyayena suke a daina kirana da shegiya"ta karashe maganar idonta kyar akansa,
Hannuwansa yasa ya tallabota lokaci daya ya saki lallausan murmushi dikda hawayen da suka wanke Masa fuska "tabbas Fatima nasan inda iyayenki suke ko Ince inada masaniya da su saboda kedin jinina ce"...
"Ta Yaya na Zama jininka?ko ka manta a inda ka sameni ne?ko ka mance a inda aka tsinceni ne sanan kaga a irin gidan da uwata ta haifeni"..
Hannu yasa ya share Mata hawayen idanuwanta "ke jinin masarautar barayar Zaki ce fatima"
Wani irin gigicewa da tayi ne yasata ja da baya Tana girgiza Kai "karkacemun ni jininka ce saboda bakason tayani neman iyayena,ni banida wani Abu daya danganci masarauta"
"Karki karyatani Fatima Domin rubutun dake makale a jikin hotonki Babu Wanda zai rubuta hakan sai Dan masarautar mu Kuma complete din rubutun Yana nufin masarautar barayar Zaki,sanan hoton wadda ta kasance mahaifiyarkice inayi Mata kallon sani"..
"Ban fahimci inda maganar ka ta dosa ba kana nufin cewa rubutun dake bayan hoton na masarautar ku ne?"..
"Ke jinina ce Fatima Domin kedin da namijice babu abinda zai Hana mahaifina yin murabus ya baki sarautar garin Nan"
Kan Fatima ya Kara daurewa ta kasa kauda idonta daga gareshi "yarima ka fahimtar Dani yadda zangane"
"Fatima Babu yadda zaayi inyi Miki fashin baki ki gani Domin Nima kaina a cikin duhu yake,saidai rubutun dake bayan hotonki ya nuna cewa mahaifinki shike da sarautar masarautar barayar Zaki Domin ainihin sarautar Bata mahaifina bace"..
Wani irin farin ciki ne ya lullube Fatima lokaci daya ta fada jikin yarima suka rungume juna suna kuka a tare.....
Sun Dade rungume da juna suna kukan farin ciki Wanda dakyar Fatima ta kwaci kanta daga rukon da yarima yayi Mata "tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin sammai da kassai....hakika Allah shine Kun fayakun....nagodewa Allah daya kasance Kaine miji a gareni....ba abun mamaki bane idan Dan uwa ya kaunaci Dan uwansa a ko wani Hali....tabbas soyayya ta dakai daga Allah ne...Kuma hakan yanada nasaba da Kai din jinina ne"
"Nadade inayi Miki kallon jinina Fatima saboda abubuwa da dama Dana Gama fahinta dangane dake saidai banida wata kwakkwaran hujja da zn iya fitowa in bayyana hakan"
Ruko hannunsa tayi suka nemi gefen gado suka zauna ta Dora kanta a Kan kafadarsa wasu sababbin hawaye na Kara sauka daga idanuwanta suna diga a kafadarsa....
"Ba kuka ya kamata kiyi ba farin ciki ya kamata kiyi Fatima sanan ki godewa Allah da yasa kika Fado a hannun iyayenki"
Jinjina Masa Kai kawai tayi batare da tace komiba....
Hannunsa yasa ya zagayo kugunta ya rukota jikinsa sosai ya sumbaci bakinta "tashi kiyi wanka ki canja kayan jikinki muje gidan sarki"...
"Amma inajin tsoron zuwa mu tunkari Mai martaba da wanan maganar bamuda kwakkwaran hujja"
"Karki damu nasan zamusha fama kafin kowa ya yarda da hakan dikda akwai hoto Wanda dolene ma su yarda"..
Ta Mike tsaye a gabansa ta shiga cire kayan jikinta tsaf sanan ta nufi toilet shima ya Mike ya fuce a dakin....
********
Tunda suka nufo gidan Mai martaba gaban Fatima yake faduwa zuciyarta na cike da tsananin zullumi har suka iso Bata daina faduwar gaba ba...
Dukkansu suka fito daga motar yarima yayi musu nuni da su shiga ciki shi zai je bangaren Mai martaba,
Ganin deejahmah tayi bangaren hajiya babba yasa Dole Fatima tabi bayanta Dan bataso su shiga daban dabn hannuwanta na sake da hotonta a cikin alkyabbarta suka shiga,
Da faraa hajiya babba ta amshi deejahmah Tana fadin "lalw marhabun da zuwan Amar..."
Kasa karasawa tayi ganin Fatima biye da ita yasa hajiya babba saurin cewa "me kika zoyi bangarena?yau ma kinzo ne kiyimun rashin kunya kamar yadda kikaimun ranan irin naku na ya'yan shegu?"..
Deejahmah ta karbe zancen "au rashin kunya tayi Miki hajiya?....hmmmm Koda yake kinsan dik Dan da akace shege ne shi bashida uba Dole ya Zama Mara kunya"
Yar dariya hajiya babba tayi "kinsan wani Abu kuwa?ni mamaki ma ranan ta bani yadda tazo tanamun zakewa Akan Wai itadin da take shegiya zata haifamun jikokin shegu kiji fa?Wai Mara asali ke fadin wanan maganar har yasamu damar tsula iskanci"..
Dariya sosai Fatima tayi tana musu kallon mahaukata ganin yadda suka takarkare suna sakin maganganu tamkar suna jiranta ko Zama basuyi ba,
"Tunda baa bani wajen Zama ba Bari in zauna ni"Fatima tayi maganar tana gyara inda zata zauna,suka bita da kallon yadda take sauke murmushi fuskarta cike da annuri,
"Ya kamata ki zauna hajiya Domin yau nazo Miki da babban albishir Wanda inada tabbacin har goro Zaki bani idan kikaji wanan albishir din sanan inaso ya Zama sirri tsakanin nidake uwata da kishiyata Kuma Yar uwata"..
A tsiwace deejahmah tace"karki kuskura kiyi gigin kirana da Yar uwarki Dan Babu abinda muka hada Dan nidin ba shegiya bace da ubana,Abu daya muka hada Miji,shima Kuma kaddarace ta Riga fata da ko a hanya bazakiga me Kama damiba"..
"Uhmm kayya deejahmah banaso kina furta kalaman da minti kadan ya rage kiyi danasani Domin nidin ba shegiya bace da iyayena....sanan ba wasu bane iyayena face jininku"
A zabure hajiya babba ta Soma balai "karki kuskura kice Zaki hada kanki damu shegiya tsintacciyar mage"
Yunkurawa Fatima tayi zuciyarta cike da fargaba da tsananin bacin Rai ta shiga zagaye parlorn sanan ta tsaya cakkk a tsakiya "banso ace kunji ko nidin wacece ba daga bakina saidai kalamanku sun tunzurani da Dole in sanar muku da ni din ba kowa bace face Yar asalin masarautar Nan....dikda ba lallai bane ku yarda da maganata Amma nasan idan mijina ya sanar da Mai martaba hakan Dole ya sanar daku"...
Wats iriyar dariyar rainin wayau deejahmah keyi itada hajiya babba sun nuna Fatima take hajiya babba ta tsagaita "au tanan kuka bullo keda mijin naki?Mana kisar da kuka bullo da ita kenan?to wanan karyar Bata shiga ba sanan Ina me Miki albishir da sarki shirye shiryen barin kasar yakeyi zaije Domin duba lafiyarsa...ba lallai bane wanan karyar Taku ta shiga"....
A fusace Fatima ta wurgawa hajiya babba hoton dake hannunta "nasan Zaki iya sanin hoton wadda ke jikin wanan hoton inma bakisan yarinyar ba ki duba da kyau"
Daidai Nan yarima yayi sallama a dakin,..
"Yauwa alhamdulillah nagode Allah daka shigo kabiru ka fitar mun da wanan shegiyar yarinyar tsintacciyar matar Nan taka Dan ko ganinta banasonyi,nace ta firarmun a daki tunda bada ubanta aka hada kudi aka Gina Mana gida ba,kaidai da kaji ka gani sai ka auri shegiya Bismillah"
Mummunan bacin Rai ne ya darsu a zuciyar yarima Jin mugun furucin da hajita babba ke jifan Fatima dashi jikinsa har rawa yakeyi "lokaci yayi da zaku daina Kiran Fatima da shegiya savoda ita din ba shegiya bace da iyayenta....Dan asalin Fatima ma Yar masarautar Nan ce"
"Kabiru rashin kunya kazo kayimunkenan?wato kun hado baki kaida ita kunzo kuce ita Yar sarauta ce saboda kana gudun ta haihu ace uwarsu shegiya ce diyanka a zagesu a idon duniya"
"Da Zaki kalli hoton da ta baki da kin tabbatar da abinda nake fada din karyane ko gaskiya?"..
A fusace hajiya ta durkusa ta dauki hoton ta Dora idanuwanta akan hoton.....take gabanta ya yanke ya fadi...ta dago da sauri Tana duban Fatima....wadda Nan da Nan kamannin Fatima suka juye Mata tamkar ta jikin hoton...
Miyaun bakinta ne ya kafe ta shiga tsananin furgici da tsantsar tsoro....a zahiri saita dake ta Tattaro dik wata jarumtatata "wannn hoton karya ne hadasa akaje akayi wanan hoton ba gaskiya bane cuta ce da hainci akeson hada baki da Kai saboda ka samawa Fatima gurbi a gidan sarauta"
Idanuwan Kabir ne suka kankance sukai jajir dasu "bedace kiyi wanan furuciba Domin gabaki daya yananinki ya nuna kinsan gaskiya kikeso ki take sani"
Deejahmah ta karbe "wallahi Fatima ba jininmu bace baka Isa ku kirkiro karya kuce ita jinin mu bace"...
"Dakatamun Khadija bansa bakinki a wanan maganar ba kin Gane ?Domin nidin ba saanki bane"
Farin ciki ne ya lullube Fatima ta Tako a hankali ta ruko hannun yarima "ka kwantar da hankalinka mijina Domin hajiya tasan gaskiya take ta kawai takeso tayi,lokacin data dauki hoton Tana kallo zan iya kirga iya bugun zuciyarta daga inda nake tsaye....jarumtace irin tamu ta Mata irinta masu sarauta ainihin jinin sarauta shiyasa kaga ta dage Akan hakan.....Amma lokaci yayi da ya kamata kisan cewa nidin ba tsintacciyar mage bace"...Tana Gama fadin haka taja hannun yarima sukai hanyar fita Aiko hajiya babba ta biyo bayansu Tana surfa ashar har dakin mama karama suna zaune ita da ummu....
Mikewa tsaye sukai a tare ganin hajiya ta shigo Tana hayaniya bayanta deejahmah ke biye yayinda yarima da Fatima suke ruke da hannun juna...