← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 80

Sashe 28

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka sosai takeyi ganin yadda jini ke tsurtuwa a yatsanta hankalinta a matukar tashe ta kalli dakin da zata gyara har tayi abinci hannu takai n tsintsiyar ta dauka ta shiga shara babuji Babu gani ga kura data turnike ko Ina a cikin dakin harta kayan jikinta Saida yayi butu butu tayi nisa da sharar ne Taji motsin kamar Ana tahowa da sauri ta dago kanta ta kalli hanyar kofa saade ce kuyanga a tsaye Tana jijjiga Kai irin na muna fuka tace"sannu shafaffiya da Mai wato tun da ranki ya dade tasaki aiki bakiyiba kenan zamanki kikayi ko to hajiya na bukatar ganinki"

Tana Gama fadin haka ta juya da sauri har Tana tuntube,....sakin tsintsiyar Fatima tayi ta Dora hannu akai ta ce a Fili "na shiga uku"...Nan da Nan hankalinta ya tashi hantar cikinta dik ta kada....

"Allah baki yawan Rai aikin da kikasa Fatima batayi shi ba"

Da sauri hajiya babba ta dago Kai daga kishingidar da tayi ta lumshe idanuwa...."uban me to ta tsayayi"

Saade ta bude baki zatayi magana kenan shigowar Fatima ta hadiye zancenta dukkansu kallonta suke yadda tayi biji biji da kura ga rigarta dik jini...

Durkusawa tayi har kasa tai kasa da kanta tace "gani ranki ya dade"

"Munafuncin ubanme kika tsaya yi bakiyi aikin Dana sanyaki ba?jinin uban meye a rigarki?wani kika kashe Mana a cikin gida"

Da sauri Fatima ta girgiza Kai baki na rawa tace "yankewa nayi da..."

"Da uban me kika yanke?da makami kikazo Mana gida dama ?makaryaciyar banza da wofi"...hajiya babba tasa kafa ta hambare Fatima a cikita fadi kasa warwas wani irin azaba Taji tamkar zaa dauki ranta yadda taji shigar hambarin....

Mikewa hajiya babba tayi tayo kanta da duka "tashi makira zakimun sharri daga Nasa kafa na tureki Zaki Fadi a kasa salon ace zan kasheki?to aniyarki ta biki"

Mikewa Fatima tayi da kyar ta Kara durkusawa numfashinta na sauka cikinta da kyar ji takeyi tamkar numfashinta zai dauke....

"To Bari kiji badai nasaki aiki kinje kinyi shashancinki kinkiyi ba to Ina Mai tabbatar Miki da a cikin wanan dakin Zaki kwana yau kina aiki ki tabbatar kafin gari ya waye kin aikace dakin Nan idan ba hakaba na lahira sai tafiki Jin Dadi"

Dakyar Fatima ta bude baki cikin sarkakkiyar murya a wahale tace "to ranki ya dade"

"Tashi ki bacemun daga gani kije kisamu su lantana da Mami a kitchen ki Dora Mana abinci Kuma wallahi kika kuskura kikai gigin kashemu wallahi sai an kasheki"

Kwallace ta ciko cikin idanuwanta ta taune lebenta da kyar tace "to ranki ya dade"

"Bace mun daga gani mujiya"....

Mikewa Fatima tayi jiri ya nemi daukarta dakyar ta take kafarta ta saita kanta ta cigaba da tafiya Tana takawa dakyar take sauke numfashi idanuwanta a lumshe take laluben hanya.....

Kitchen ta shiga ta tarar da lantana da Mami sunata shirye shiryen girki da kyar ta karaso cikin kitchen din tasa hannu ta dafe bango dukansu kallo suka bita dashi Mami ta dauke kanta,ta cigaba da aikinta Tana tabe baki.....kallon tausayi lantana kewa Fatima Harga Allah Tana kaunar yarinyar tun ranan data fara ganinta Amma hajiya ta tarasu tayi musu gargadi da babbar murya.....

Karasowa tayi tace "mezanyi muku?"

Harara Mami ta wurga Mata sanan tace "taruugu Zaki gyara Mana kiyi Nika ki hada miyar burabusko"

Kallon hannunta Fatima tayi sanan ta dago Kai tace "na yanke a hannuna kutaimakamun ku canjamun wani aiki"

"Lallaima wanan yarinyar wato Dadi kikazoji kenan a gidan sarauta ko?muba mutane bane da muke tikar aiki Kuma bamuda ciwo a hannu saike Yar lelen Dan sarki to Dole kiyi idan ba hakaba in hadaki da hajiya"

Murmushin takaici Fatima tayi tace"ba sai yakai Nan ba zam gyara"

Hakanan Fatima ta warware daurin da taiwa hannunta ta wanke hannun ta tsomashi cikin kayan Miya tafara gyarawa dikda azabar dake ratsa ilahirin jikinta bai hanata gyaran kayan miyan Nan ba tass sanan ta nukashi suka cigaba da aiki tare....

*********
Sai wajen karfe uku na Rana yarima ya dawo gidan a gajiye ga uwar yunwa da yakeji bai zarce ko inaba sai dakin mahaifiyarsa Nan ya yada zango lokacin Tana zaune ita kadai a daki....

"Barka da Rana ranki ya dade"...

Kallonsa tayi ta gefe Tana lura da yadda Dan nata ya rame yayi baki daka ganshi kasan Yana cikin damuwa Dan sakin fuska tayi ta amsa Masa a takaice

Gyara Zama yayi ya Dan Bata fuska yace "inajin yunwa mama "

"Ai abinci ya sauka kasa su kawo maka Mana?"

Kararrawa ya Danna a dakin....ko cikakken minti biyu baayiba Mami ta shigo ta zube a kasa Tana kwasar gaisuwa batare da ya amsa mataba yace "Ina bukatar abinci"....da sauri ta Mike ta fice...

Itada Fatima suka shigo a tare dauke da kulolin abinci kala kala tunda suka shigo idanuwansa suka sauka Akan Fatima wadda ko kallonsa batayiba ta dire kulolin ta fita yabi bayanta da kallo sanan ta dawo dauke da sauran plates da abubuwan bukata ta ajiye...idanuwansa kirrr akanta musamman jinin da ya gani a jikinta Wanda bakaramin tashin hankali ya shigaba,

Itace tayi serving dinsa komi da komi sanan ta fice....kallo ya bita dashi sanan ya maida dubansa ga abincin da ta zuba Masa a gabansa.....ji yayi gabaki daya abincin ya fita akansa ko ganinsa bayayi da kyar yayi cokali biyu na burabusko ya ajiye ya fice batare da yayiwa mahaifiyarsa sallama ba.....

*********

Kaiwa da komowa yakeyi a dakinsa Yana tunanin yadda zaayi ya ganta ya tambayeta meke damunta yaga jini a jikinta,

Dabarace ta fado Masa ya leko bangarensa Yana waige waige wata baiwa dake sashensa ya hanga ya ya fitota da hannu da sauri ta zo ta zube a kasa "kiramun Fatima"...

"Toh"....da sauri ta juya har ta fita ya kirata "saude"

Ta dawo da sauri "banaso kowa yaga lokacinda Zaki kirata"....."insha Allah ranka ya dade"...

Juyawa yayi ya shige abinsa ita Kuma ta tafi Kiran Fatima....

Tadan Jima Tana nemanta Bata gantaba harta juyo zata dawo ta koma,....dakin kwanan kuyangin gidan ta shiga da sallamarta aikuwa ta hangi Fatima can gefe ta shimfida dankwalinta a Kai Tana sallah Tana zaune Tana addua saudatu ta shiga ,gefe ta nema ta tsaya Tana waige waige har Fatima ta shafa "Fatima kizo inji yarima Dan sarki Mai jiran gado sanan baya bukatar kowa yasan da zuwanki bangarensa"

Dammmm kirjin Fatima ya buga jikinta ya hau rawa,....saude juyawa tayi abinta da sauri hakanan Fatima tabi bayanta don batasan bangarensa ba....

Waige waige suke kamar marasa gaskiya har suka Isa...

Kwankwasa kofar saude tayi daga ciki ya amsa da "waye"

"Nice saude ranka ya dade tafe nake da Fatima"

"Ta shigo".....gaban Fatima ya tsananta faduwa haka ta Murda kofar shiga dakin tayi sallama....Yana zaune a kujera gabansa Dan karamin table ne sai TV dake manne a dakin dake faman aiki... Kamar wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta shigo parlorn ta tsugunna a Dan nesa dashi....

Kallonta yakeyi tausayinta da wata iriyar soyayyarta na ratsa dik wata kaba ta jikinsa,

"Bintu"...maimakon ta amsa sai ta dago Kai suka hada ido kallon dataga yanayi Mata shi yasa Tai saurin sadda kanta kasa....murmushi takeyi Wanda shi kansa dake kallonta yasan karfin Hali take....

"Tasonan kusa Dani"....batayi mishi musuba ta Mike ta tako har inda yake ta tsugunna...idonsa na kanta haka ya zamo kasa gab da ita Yana kallon kyakkyawar fuskarta,

"Bintu ko kowa ya gujeki bazan gujekiba ko kowa ya kyamaceki harabada bazan kyamaceki ba Allah shine gatanki ni zan zame Miki gata kinji?"

Gyada Kai tayi Tana wasa da yatsunta,...hannunsa yakai hannunta ya rike ya dagosa Yana kallon zara zaran yatsunta ga yanka alamar ciwo a babban yatsanta...."bintu badai ciwo kikaji ba"

Narai narai tayi da idanuwanta tamkar zatayi kuka ta kallesa cikin Ido tace "yankewa nayi yaayaah"hawaye ya sauko a kumatunta...."nooo banason kukanki yi hakuri kinji Yana Miki zafi ne umm?"

Dan turo baki tayi tace "ehh Mana har kuka dazun nayi"tace cike da shagwaba....hannun yakai bakinta ya shiga hura ma ciwon iska a hankali kusan minti biyu sanan ya dago Kai yace "yadaina"

Juya idanuwanta tayi sanan tace "ehh Mana ai ka hura mun,yadan daina ni sakar mun hannuna"

Kara murza yatsunta yayi yace "ban saki saikince sun daina"

"Ni wallahi zafi sukemun ka Bari yaayah😩"
Wani irin Abu yakeji a jikinsa na yi Masa yawo ji yakeyi tamkar su kasance a hanka...dakyar ya saki hannunta ya Mike ya bude Dan ward drob dinda ke parlon ya Ciro wasu chocolate a hannunsa ya dawo gabanta ya tsugunna da kansa ya bare sanan ya kalleta ya kashe Mata ido "bude bakin'

Kifta Masa Ido tayi sanan Babu musu ta bude ya saka Mata chocolate din "oya tauna"....

Yadda take motsa bakinta Tana tsotsan chocolate din bakaramin Burgesa tayiba ya shagala da kallonta tamkar zai hadiyeta harta shanye ta kallesa taga idonsa na kanta ko kiftawa batayi "nidai kabar kallona"

"Idan ban kallekiba wa zan kalla umm?baki hanani kallon matana"....

Batare da tace komiba Dan bawai ta fahimci mgnrsa bane ta Mike da sauri data tuna da inda take Dan Harga Allah ta mance da komi "yaayah zantafi idan hajiya tasan nazonan na shiga uku"

A kasalance ya Mike ya tsaya daf da ita Yana iya Jin saukar numfashinta yasa hannunsa ya dago fuskarta Yana kallo idanuwansa sun canja launi zuwa jajir saboda yadda yakeji a dik lokacinda yake tare da ita musamman da suka kebe yau,

Dayan hannunsa yasa ya shafo fuskarta har lips dinsa da sauri ta juya zata wuce ya damkota ta Fado jikinsa ya riketa tsammmm. Kiciniyar kwacewa ta shigayi muryarta na rawa tace "ka sakeni Dan Allah yaayah wallahi inajin tsoron hajiya"ta karashe mgnr muryarta na rawa...

Matseta yayi yace"Ina sonki fatima,banida farin cikin da ya wuce kasancewa tare dake wasu lokuta idan na zauna babu abinda nake tunawa sai rayuwarmu ta baya a gidan marayu.....yau gashi muna waje daya Amma inkasance tare dake Saida dabara....nikadai nasan abinda nakeji game dake"

Kalamansa sun matukar sanyaya Mata jiki da kyar ta iya ture hannunsa ta fice da sauri....

Waige waige takeyi Tana duba hanya ko akwai Wanda ya ganta sauri sauri takeyi harda tuntube sukai kicibis da saade "daga Ina kike munafuka?"

Jiki na rawa Fatima tace "na zauna can gefen ne"
Chapter 28 · 0% Book details