Sashe 26
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Batayi Masa musu ba ta Mike tabi bayansa.....
********
Zazzaune suke a babban parlor Wanda dabiarsu ce zaman wanan parlor din kowace safiya Domin yin breakfast Wanda dokar Mai martaba ce hakan a cewarsa zasu Kara zumunci,tunda suka zauna Babu Wanda ya cewa wani uffan sai wani girgije girgije hajiya babba takeyi Tana cika Tana batsewa ita ga matar sarki....
Mama karama ce ta Dan kalleta ganin yanayin nata sai ta danyi murmushi tace"ni Kam hajiya wanna hukuncin da kika dauka akaina da yarana yayi tsauri a tunanina kome kabiru yayi Miki laifinsa bazai shafeniba saboda danki ne kinada damar yi Masa hukuncin daya Dace batare da hakan ya shafi zaman takewarmu ta yau da kullum ba"
Wani kallo hajiya babba ta watsawa mama karama kafin ta bude baki tace "ai Dole kice hakan tunda kina gudun duniya ta zageki ba ?bayan dik abinda kabir yayimun na kuntatawa dik Dasa hannunki"
"Dan kuka kenan Mai jawa uwarsa zunguri inda Kabir yaji maganata da bai aiwatar da abinda ya aiwatar ba hajiya har gargadi nayi masa bejiba musamman Akan dauko wanan yarinyar da baasan asalintaba ya kawota cikinmu "
Tabe baki hajiya babba tayi tace"wanan keta shafa ni yanzun hukuncin Dana dauka shine tunda Mai martaba yabani ita to cikin kuyangina zan jefata Dole tasa uniform"
Da sauri afnan ta kalli hajiya babba lokaci daya ta kauda kanta gefe batare da tace uffan ba....
Mama karamace ta sauke ajiyar zuciya ta bude baki zatayi magana shigowarsu yarima tasa ta hadiye maganarta dukkansu suka bisu da kallo Dan yadda suka jero suka shigo daka kallesu zakaga tamkar Miji da Mata ko saurayi da budurwa ko wanne fuskarsa dauke da murmushi....
Har kasa dukkansu suka zube a gabansu yarima ne ya fara magana "barkanku da tashi iyayena,fatan Kun tashi cikin koshin lafiya?"
Babu Wanda ya tanka daga hajiya babba har mama karama,.....dago idanuwansa yayi ya sauke Akan mahaifiyarsa dake jifansa da wani irin kallo Mai dauke da maanoni kala kala,
Itako hajiya babba kallon Tsana take jifansu dashi ji takeyi tamkar ta shakesu Dan wallahi ganinsu da tayi a haka saida gabanta ya fadi sanan Saida safiyar Nan ya Kara ganin tsantsar kyawun yarinyar....
Sunkuyar da Kai Fatima tayi gabanta ya tsananta faduwa cike da fargaba tace"Allah ya taimakeku,barkanku da tashi iyayen giji na"
"To hanshakiya kinada bakin gaishemu saboda bakida kunya?Dan cikin gida Dan asali Wanda kowa yasan tsarkakakke ne Dan sunna ya gaishemu bamu amsaba saike kazanta uwar iyayi Zaki bude wanan shegen bakin naki Mai wari ki gaishemu saboda tsabar iyayi irin na yaran bariki?"to ku rike gaisuwarku Miji da Mata wato da sassafe kazo ka dauketa kukaje gaida sarki tunda ubanta ne ko?"
Durkusar da Kai kawai yarima yayi ransa nayi Masa suya bashida yadda zaiyi Akan Fatima yasan Dole wadanan abubuwan su faru Amma alkawari ya daukarwa kansa kome zaayi Mata bazaisa baki ba bazai shigar mataba Domin hakan shine cikar burinsa...ba karamin zafi kalaman hajiya babba sukaiwa Fatima ba,wanan cin zarafi har Ina daga zuwanta?tun baaje ko Ina ba?
Harara hajiya babba tabi Fatima dashi sanan tace "ke ga Yar gida ko harda tashi da sassafe ya daukeki ya kaiwa sarki ke neman suna ko?to Bari kiji infada Miki yaranmu sune yara a cikin gidan Nan dik Wanda ya shigo daga baya to bare ne Dan haka Ina Kara gargadinki da ki Kama kanki idan ba hakaba wallahi saina halakaki"
Da sauri yarima ya kalli hajiya babba sukai Ido hudu "ko dukana zakayi na taba zuciyarka?wani shin kabiru yarinyar Nan asiri tayi maka ko?idan ba hakaba to menene Koko son zuciyane yasa kuka hada baki ta kashe maka Dan uwa Wanda kake ikirarin kana sonsa fiye da kowa a duniya?sai gashi ka nunawa duniya cewa ba son gaskiya bane tunda ka dauko wanan kajagar da tayi silar Kai Dan uwanka lahira cikinmu?to kasani ka fada Mata,idan akayi aurenka da deejahmah babukai babu ita Dan bazata illata Mana Suruka ba"
Dik bala'in Nan da hajiya babba ke zazzagawa Babu Wanda yace uffan daga yarima har mahaifiyarsa,...sauraronta kawai sukeyi yadda take shiga batanan take fitaba.....zuciyar yarima tamkar ta Kama da wuta haka yakeji itakuwa Fatima dake durkushe a kasa hawayene ke diga a kasa wadanda ke gangarowa daga idanuwanta suna sauka Akan carpet din....
Mama karama ko haushin yarima kawai takeji Domin dik cin zarafin da hajiya babba tayi vataga laifintaba sai nashi Domin shi yajanyo komi da kyar ta ta daga kanta ta kalli inda Fatima ke durkushe kanta a kasa want haushi da takaicin yarinyar ya Kara lullubeta dik itace silar wargajewar gidan tace"tashi ki fita zamu karya da yaranmu"
Kallon mahaifiyarsa yarima yayi Aiko ta wurga masa harara ya sadda kansa kasa,....
Mikewa Fatima tayi ta juya Tana tafiya hawaye ya gama wanke Mata idanuwa tabar parlorn.....
Kallo ya bita dashi tamkar ya tashi ya bita yakeji zuciyarsa babu Dadi bashida yadda zaiyi wanan karon ba yakin wulakantata da zaayi zaiyiba yakin cikar burinsa Domin Fatima itace farin cikin rayuwarsa.....ko Fatima batai farin ciki yanzunba akwai lokacinda farin ciki dawamamme zaizo musu dagashi har ita....dikda har yanzun bai sanar Mata da kudurinsa na boye ba....
Abincin karyawa aka shiga shigowa dashi parlorn Mai Rai da lafiya aka shiga direwa a gabansu har aka Gama ,lantana itace ke serving din kowa a wajen....Koda tazo kansa tambayar Mai zaici ruwan zafi kawai ya Bata umarnin ta sa mishi....da sauri sauri ya kukkurba ya Mike ya fice....
*******
Nemanta yakeyi tunda ya fito zuciyarsa ke harbawa sauri da sauri Allah yasa Fatima ba gudu tayi ba lungu da sako na gidan babu inda bebi ba harya cira Rai da ganinta ya hangeta jikin wata bishiyar guava a durkushe kanta cikin gwiwoyinta,tun daga nesa yasan aikin kuka takeyi haka Nan ya tako jiki a sanyaye har wajen motsin tafiya ya Sanya ta dago kanta da sauri Tana ganinsa tasa hannu ta share hawayenta da sauri ta kirkiro murmushi....
A gabanta ya tsugunna Yana kallon kyakkyawar fuskarta da tayi jajir saboda kuka,...durkusar da kanta tayi kasa Tana murmushi....
Hannunsa yasa ya dago fuskarta Yana kallonta cike da tausayawa yasa hannu Yana share sauran hawayen dake gefen idonta ba tare da yabar kallon fuskata ba,runtse idanuwanta tayi tanajin wani bakon lamari a tattare da ita Wanda kallon da yakeyi Mata ne ya haifar da hakan sun kusa minti goma a haka harta fidda Rai zaice wani Abu saita tsinkayo muryarsa Yana magana cikin taushi da kasala,
"Bintu Ina nemawa iyayena gafara a wajenki na cin zarafinki da sukayi Wanda hakan Sam bai daceba banji dadiba da inada Halin hanasu Danayi hakan saboda in nuna Miki babban muhimmanci da matsayin da kike dashi a rayuwata"
Murmushi tayi sanan ta Dora idanuwanta cikin nasa Tana Masa wani kallo Wanda ita kanta batasan tanayinsa ba dakyar ta iya sauke ajiyar zuciya tace"dik muhimmancin Fatima a gareka baikai ga iyayen da suka kawoka duniyaba,iyaye daban suke a rayuwar ya'yayensu kome sukayi maka Dole ka daure kayi musu biyayya,saboda haka ka kwantar da hankalinka Babu abinda ya batamun Rai ciki don dik abinda suka fada akaina gaskiya ne sanan harabada sune iyayena da Allah ya bani koma menene watarana zai Zama tarihi yaayah saboda haka Ina rokonka Dan Allah kada kasamu sabani da iyayenka akaina".....
Shima kallonta yakeyi kamar yadda take kallonsa ya shagala da kallon yadda black lips dinta kanana ke motsawa Tana furta wadanan kalaman Wanda yasan dauriyace da tawakkali da karfin zuciya irin nata Babu Wanda zaaiyiwa wanan cin zarafin da wulakanci beji zafi da radadi a ransa ba Amma ita Sam ta nuna masa Babu komi....yayi nisa cikin tunani Yana kallonta besan harta karasa kalamantaba ....kallonta kawai yakeyi idanuwansa sun canja kala sun kankance,...hura Masa iska tayi a ido ya lumshe idanuwansa sanan yayi murmushi yace cikin dasasshiyar murya "Allah yayi Miki albarka Yar aljannah Allah kadai yasan tarin baiwar dake tattare dake bintu..."
Murmushi tayi Masa sanan tadan tura baki tace"banason zugafa yaayaah"...
Yatsansa yasa ya Dan bugi lips dinta yace "shagwabatu....komi sai kinyi shagwaba ni yanzun ki tashi kije kiyi wanka ki canja kayanki cikin wadanda kikazo dasu zan fita yanzun daganan zan suyo Miki sababbin Kaya da dik wani Abu da kike bukata"
Kifta mishi ido tayi tai Farr da idanuwanta sanan ta Mike tace"Allah ya tsare ya kareka yaayaah saika dawo"...Tana karasa fadin haka ta juya abinta batare da jiran me xaice ba,kallo yabi bayanta dashi Yana murmushi hade da sauke sassanyar ajiyar zuciya....dakyar ya iya mikewa ya Kama hanyar parking space....
*******
Gidan Ahmad abokinsa yarima ya je ya daukesa suka fita yawo dagacan Basu dire kobinaba sai boutique Nan suka shiga yarima ya shigo jidan Kaya babuji Babu gani dik abinda ya daga sai ya siyawa Fatima shi musamman danginsu dogayen riguna ready made masu shegen kyau da tsada sanan ya shiga danginsu atamfofi ya jidar Mata Suma shidai Ahmad kallonsa yake kawai Yana mamakin yadda yaga yarima na kashewa Fatima kudi kamar hauka dikda dama yarima akwai kyauta,
Bill akayi musu ya biya sanan da suka fito yarima ya roki Ahmad da su biya gidan barrister Abdul can zai bada wadanda zaa dunka Mata sukaiwa tela ba musu ya bisu.....
*****
Matar waziri ce zaune a gaban hajiya babba Tana kawo gaisuwa bayan ta shiga ta sun gaisa da mahaifiyar yarima,
"Ranki ya dade naji labarin abun farin ciki na shawarar da aka yanke na hada deejahma da kabiru gaskiya nayi farin ciki da hakan Allah ya Sanya alheri"..
Washe baki hajiya babba tayi tace"ameen labari yakai Miki kenan"
"Ehh kin Manta jiya su fauziyya sunzo Nan da suka koma ne suka sanarmun yaushene bikin?"...ta kalli hajiya babba a fakaice taga yanayin fuskarta,
Murmushi hajiya babba tayi tace"yadda dai bikin yake tun farko baa canjaba Kinga Nan da Yan watanni kenan"....jinjina Kai matar waziri tayi har zuciyarta taji dadin wanan bayanin dama shine muhimmin abinda yakawota don ta shirya,
"Allah ya nuna Mana wanan babban bidiri da shagali da zaayi a wanan masarauta bikin Dan sarki"
"Aikuwa dai"...
Waigawa matar waziri tayi tai tozali da wasu jajayen Kaya da ke gefen hajiya babba irin uniform din da kuyangi ke sawa tadan gyara Zama tace"ranki ya dade ankaro kuyanga ne Naga sabon uniform irin nasu"