← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 80

Sashe 58

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dago jajayen idanuwansa yayi cike da balai ya fara magana "karki kuskura ki Kira fatima da karuwa a gabana kingane ko?yadda kike matata haka itama matata ce"...ya Mike a haukace ya fara masifa "waini ya kukeso inyi ne ke baa aure aka aureki?Koko kukadaine mutane?koba Fatima kina tunanin ke kadaice Zaki zauna a gidana?dama banida raayin Zama da mace daya wallahi saboda haka kisani ki bude kunnuwanki daga ke har Fatima Babu Wadda zata shigarmun gida Tana min iko baku isaba wallahi"...Yana nunata da yatsa,...mikewa Ahmad yayi ya kamosa ya zaunar da shi Akan kujera Yana fadin "cool down my friend ka kwantar da hankalinka please kayi hakuri zafin kishi ne irin na mata kawai,Kuma kaga batada lafiya kai meta a hankali"

Hura hanci kawai yarima yakeyi zuciyarsa na tafarfasa,....ko Ina xafi Babu inda zaisa rayuwarsa ya huta ,yanzun ya Gama jiyo hayaniyar su cikin gida yasan dik Akan maganar ne ga babban bala'i dake damunsa Wanda ya rasa dalilinsa na fadawa wanan jarabar ta bukata......

Kuka sosai deejahmah takeyi harda shassheka ta dafe kanta kawai hawaye ke gudu a fuskarta,dago kansa yayi ya kalli yadda take kuka tamkar marainiya,wani irin tausayinta ne ya lullubesa,Dan tabbas yasan wanan abun da akayi Mata akwai ciwo Amma shi kansa yasan hikimace babba Mai martaba yayi Dan inba hakanba Babu yadda zaayi ya mallaki bintu,. Tasowa yayi ya dawo kusa da ita ya janyota jikinsa kawai saita fada kirjinsa Tana kuka da shassheka tausayinta ne ya lullubesa ya shiga babbuga bayanta a hankali...

Mikewa Ahmad yayi ya fice zuwa parlor ya barsu ciki,..

Kasa cewa daita komi yayi sai lallashinta da yakeyi yayinda tsigar jikinsa ke tashi ta ko Ina,...ganin haka yasata yin shiru hade da lafewa kirjinsa Tana sauke ajiyar zuciya gabaki daya deejahmah kanta ya Gama daurewa babu abinda zatayi ta samu sassaci a cikin zuciyarta Sai kukan,tabbas tasamu Dan relief na zubda hawayenta da tayi ganin bece Da ita komiba yasata mikewa jiki babu kwari Tana takawa a hankali har parlornsa inda ta tadda Ahmad zaune ya rafka uban tagumi ya bita da kallo har ta fice....

Fitarta yasa shi fitowa parlor ya zauna gefen Ahmad...."ya kamata ka canja kayan Nan na jikinka Dan Kai ango ne tunda wadanan sun yamutse kasa wasu kasan dai karfe biyu akwai walima koh?..."

Juyowa yayi ya dubi Ahmad fuskarsa dauke da damuwa yace "wallahi ganin komi nakeyi tamkar a mafarki,Amma kasan wani Abu kasan zuciyata farin ciki nakeyi da samun wanna baiwa da Allah yayi mun na amsar adduata cikin sauki na mallaki Fatima a matsayin matar aure Kuma bazan mutu ba sai na cika Mata burinta na mallaka Mata dik wani farin ciki....saidai wasu canje canje da nake gani a wajenta na kishi da ta dorawa kanta'

"Nasani friend karka damu yau zaku angwance zaka Kuma lallashi abinka"....

"Hmmmm"ajiyar zuciya kawai yarima ya sauke ya nufi Mike yace "Bari insake wanka"

"Owk".....

**********

Koda deejahmah ta shiga gida direct dakin hajiya babba ta shiga ta taddasu zugum zugum a kuryar daki tamkar anyi mutuwa,

Gefen gado ta nema ta kwanta wasu sababbin hawaye na gangarowa a gefen fuskarta,

"Kidaina kukan Nan da kikeyi yanzun min rigada munyi sabon shiri....Kuma yau din Nan zamu aiwatar dashi ai wajen walima zamuje ko?to nasan abunyi wanan gida kece Zaki Soma shigarsa Kuma kece zai fara Tarawa da ita....nasan abunyi na tabayin wanan muguntar da dadewa wadda shine silar samuwar farin cikinmu kema Kuma abinda zanyi Miki kenan....zuciyata ta Gama bushewa nagama Shirina tsafff daga safe zuwa yanzun....ai hajiya zainab tabar shiri tun Rani ta mamayeni ne ta Kuma Sami saa Amma wanan karon bazatayi nasaraba Dan batasan Shirina ba.....

********
Tsaf Fatima ta kwashe labarin rayuwarsu na gidan marayu taba ummu a inda suke zaune a kuryar daki Tana kuka ta fayyace Mata komi dake tsakaninta da bilkisu...

Sosai ummu ta jinjina lamarin ta ja dogon numfashi ta sauke..."bilkisu itace zata zame Mana babban makami Domin da nayi niyyar kwatarta ta karfin Hali tunda banida wata baiwa yanzun Amma zamanta a can din alheri ne...saboda Babu Wanda zai rinka samun information Akan abinda suke ciki Dan haka zanbarta a can sanan xan Bata damar Zama babbar aminiyar ta don ta hanyarce zamusan halin da suke ciki Domin yanzun dik yadda zaayi su dauki fansa shi sukeso Dan inada yakinin hajiya babba zata iya kisa tunda itace silar babban al'amari daya faru a masarautar Nan a baya Dan nadade Ina zarginta shiyasa nake tsoron mugun nufinta yasa na bullo Mata ta bayan gida...."

Jinjina Kai Fatima tayi cike da gamsuwa sanan ta rusuna tace "nagode ummu Allah ya saka Miki da alheri"

"Yauwa Fatima kece fa uwar gida Dan haka dakinki ya kamata yarima ya fara tarewa Dan haka nakeso in Miki wata tambaya "

Sosai Fatima ta maida hankalinta Akan ummu "tambayar itace da dai nasan kinada tsarki Amma yanzun bansaniba ko kinyi bako"

Kunyace ta lullube Fatima ta dukar da kanta kasa ta girgiza Kai alamar aa

"Good jeki wanka ki fito inbaki wani sirri wadda na tabbata inhar hakan ta kasance to babu wadda zata wuce gabanki a wajen miji"

Murmushi Fatima tayi ta Mike tayi Shirin wanka ta shige bayi,ta Dade Tana kuka a bayi Tana fargabar abinda ummu ke Shirin Bata umarnin yi Wanda batada agendarsa a yanzun....dikda itama akwai tarkon da tayi da tayi niyyar danawa yarima...

Haka Nan tayi wanka jiki Babu kwari ta fito ko kafin tasa Kaya Saida ummu ta turare kayanta da turarruka kala kala sanan ta bita da wasu ta shafeta dasu Tass sai kamshi ke tashi Mai sihirtaccen Dadi...

"Nasan yarima yayi Miki laifi Amma tabbas Dole ki bashi kanki yadda Zaki samu damar ramawa....ki kwantar da hankalinki kinji diyata yanzun lokacinki ne Dan haka kiyi abinda nace kawai"

A furgice bilkisu ta shigo dakin Tana waige waige tayi zuru zuru daga ummu har Fatima kallonta sukeyi cike da fargaba.....

*Yanzun aka fara Wasa dikda munzo gangara*

*SLIMZY🥰*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

39

Cakk bilkisu ta tsaya Tana zazzare idanuwa Tana kallon ummu Dan batasan cewa Fatima ta bayyanawa ummu ko ita wacece ba,

Dukkansu suka zura Mata idanuwa suna jiran suji meke tafe da ita Amma sai ta sauke murmushin karfin Hali ta juya da niyyar fita,

Ummu ce tai maza tace "dakata bilkisu nasan komi dake tsakaninki da Fatima Bata boyemin komiba ta fada mun Dan haka ki kwantar da hankalinki kizo ki fadamun meya faru"

Juyowa tayi jiki Babu kwari ta tsugunna a kasa,...ummu da kanta ta dago da ita ta zaunar da ita a kujerar dake jikin madubi tace"umhmm Ina sauraronki"

Kasa tai da muryarta "hajiya ce naji tace Zata samu daya daga cikin bayin Fatima ta Basu magani da zasu sa Fatima bazata taba haihuwa ba harabada.....sanan cikinsu zatasamu wadanda zasu rinkayi Mata aiki Akan Fatima yadda zasu cutar da ita cikin ruwan sanyi....zasu nakasa rayuwarta batare da kowa ya fahimci sune ba,a yadda naji ma Ashe deejahmah ta auri Kabir ne don ta samu ciki ta haihu yadda zasu kashe shi"......

Daskarewa ummu tayi Bata Bari bilkisu ta Gama bayanintaba ta Soma salati Tana fadin "lallai dik abinda hajiya safiya tace zatayi zata aikatashi Koda kisan Kai ne kuwa karamin aikinta ne,...zamanki da hajiya ba karamin taimako bane ga wanan yarinyar Domin da badanke ba da bamuji wanan babban tuggun da suke Shirin yi ba.....Kai safiya anyi shedaniyar mace,Babu Allah a ranta kwata kwata,batada burin da ya wuce taga tafi kowa ,Babu abinda ke tattare da wanan baiwar Allah sai son zuciya"....

Bilkisu ta sunkuya kadan sanan tace"a yadda naji sunce a al'adar ba haushe wadanda akai aurensu Rana daya dik wacce aka fara kaiwa gidan itace uwar gida saboda haka zasu dauki deejahmah su kaita gidan saboda maganin da suka Bata ya zamana itace uwar gida idan har yarima ya kwana a dakinta to Babu shi Babu Fatima"

"Innalillahi wa Inna ilahi rajiun.....tabbas maganar haka take daura auren Fatima a farko bashi zai Bata damar Zama uwar gida ba a al'adar bahaushe sai wadda aka fara kaiwa dakin miji,wanan haka yake nagode sosai bilki tashi kije"

Jiki Babu kwari bilkisu ta Mike tai hanyar kofa Tana waigen Fatima wadda ke jingine a jikin bango hawaye na gudu a idanuwanta,

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun narasa dalilin da yasa mutanen Nan suka tsaneni bansan me hakan yake nufiba,Allah kana gani dik abinda na aikata banyi hakan da gangan ba nayi ne Domin Kare mutuncina,jarabawa da kaddara tasa na aikata kisan Kai Wanda dik wanan dalilin shi ya janyomin Tsana da kin jini,kodan nakasance Mara iyaye shegiya yasa ake kyamata ake tsanata"...toshe Mata baki ummu tayi 'kar insakejin wanan furucin daga gareki idan ba hakaba zan sassaba Miki"

Bude drawer ummu tayi ta Ciro Mata sababbin Kaya wadanda zatasa zuwa wajen walima....

Lafaya ce Mai shegen kyau irin ta shuwa Arab Mai shegen tsada da kyau shi Fatima tasa sanan ta canja Mata wata akyabbar...ta shiryata tsaf ta Kara turare Mata jiki da turarruka masu shegen kamshi ta zaunar da ita a gefen gado,

"Fatima kiyi hakuri da dik abinda ya sameki a rayuwa kinji? Babu Wanda yafi karfin kaddara irin wadda ta fada Miki ta fada mishi kinji?Kuma inhar iyayenki nada sauran rayuwa nasan zasu nemeki Kuma Zaki hadu dasu kinji?ki rike mijinki da kyau ki bashi kulawa wadda dik wata macen aure ya Dace ta bawa mijinta kinji?abinda nakeso dake shine yanzun gaskiya bazan baki damar zuwa wajen walima ba Domin mamayarsu zanyi a karo na biyu tunda har ga abinda suka bullo dashi zan bullo musu ta bayan gida"

Wasu siraran hawaye ne Suka zubowa Fatima a kumatu tasa gefen hannunta ta share,

"Toh ummu"....tausayi Fatima kawai take bawa ummu....

*******
Shiri sosai sukai na zuwa wajen walima ko wa yasha kayansa masu shegen kyau da tsada,na wanan Yana wane wanan haka waje ya cika da milliyoyin jamaa daga fanni daban daban....wajen da aka tanada Domin zaman amare da ango Nan deejamah da yarima suka zauna,
Chapter 58 · 0% Book details