← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 80

Sashe 56

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruke da hannun juna suke bilkisu ta Kare matse hannun Fatima tace "ki kwantar da hankalinki na Dan lokaci ne Amma maganar gaskiya kece a zuciyarsa shi kawai sunyi hatsabibancine sun janyo raayinsa ki Mike da addua kinji?"

Share hawaye Fatima tayi ta Kara duban bilkisu da kyau "karyane wallahi dama can Yana sonta munafurcine irin na da namiji Kuma zan bashi mamaki Domin zansamu miji inyi aure in shareshi Dan bazan yarda a nakasani ba shida yaji zai iya yaje can su daddatsa namansa"

"Idan kikace haka kinyiwa Allah butulci kinyiwa yarima butulci Domin Babu Wanda zaiyi jihadi irin yadda yayi akanki,karki manta irin wahalar da yayi akanki yakici yaki Sha ya rabu da kowa ciki kuwa harda iyayensa,haba Fatima kiyi Masa uzuri baya cikin hayyacinsa"

Take jikin Fatima yayi sanyi Amma can kasan zuciyarta tanajin haushi da takaicinsa ga wutar sonsa dake ruruwa a zuciyarta,..

"Ni Bari ummu ta dawo ma infada Mata ta nemi makaranta tasani kawai Kuma ni bazan sake bin ta kansa ba Dan nasan ba lallai ma ya Kara nemana ba'

Murmushi kawai bilkisu takeyi Tana kallon yadda Fatima ke jaraba saboda tsabar kishi....

Dakyar bilkisu ta lallasheta da kalamai masu dadi

A haka suka shiga Hira can ta daban...

*****
"Wai hajiya Kinga yadda yarinyar Nan ke zuba mulki daga samun yancinta har ruwan iskanci takeyi Wai harda Kiran bilki baiwarki tasata aiki ?bakiga yadda bilki jikinta ke rawaba saboda tsabar tsoronta da takeji"

"Dik wanan kafafar da takeyi da Jin Kai da sabon iskancin da takeyi Basu kamaceta ba saboda aransu tayi da Rana tsaka uwarta ba Mai sarautaba ubanta ba Mai sarautaba karewarta ma baasan danginta ko kiristoci bane dik take wanan iskancin to kashinta ya bushe tunda Kabir ya fara shigowa hannu,sanan tunda ta fara muamala da bilkisu to da ita zanyi amfani wajen hada Mata tuggu Dan watarana sai munyi abinda Mai martaba zaisa a ratayeta batare da Taji kamshin auren kabiru ba"

Dukansu sukasa dariya kasa kasa,....mikewa hajiya babba tayi da takun takama ta bude drawer ta Ciro gorar ruwan da suka ajiye ta mikawa deejamah"karbi wanan ruwan baba Sudan ne ki shanye shi tas ki shafe fuskarki saidai wani ba kabiru ba Dan gobe iwar haka kin Zama sarauniya"

Hannunta har rawa yake wajen karbar gorar ta bude ta zuciyarta fara Tass ta kwankwade ruwan ta shafe fuskarta dashi....

"Karfe Tara na safe zaa daura aurenki Wanda dagashi sai kuma auren khausar da afnan insha Allahu badai shegiya ba a gidan sarauta"

Dadi ya Kara Kama hajiya rahina wadda tun dawowarsu wajen dinner bakinta yaki rufuwa...

*******

Yarima Yana bangarensa dik minti biyar sai ya watsawa jikinsa ruwa saboda abinda yakeji take mararsa ta daure ko rufe idonsa yayi deejahmah ke tunanowa da kamshin turarenta,yayinda dayan bangaren zuciyarsa da ya tuna da baiga Fatima ba sai zuciyarsa tayi Masa nauyi,tunanin yadda zaayi ya fadawa ummu Fatima ta bace yakeyi Dan yasan akwai drama Amma tunanin da yakeyi yagansu da Ablah ko Tana gidanta,ya yi tunanin zuwa gidan ummu Amma yaganta lokacin data shiga fada wajen Mai martaba Allah yasa ba maganar batan Fatima taje yi Masa ba,yasa hannu ya sharce zufar goshinsa sanan ya janyo jallabiya yasa ya daga Kai ya kalli agogo karfe Sha daya da minti biyar na dare haka ya zura takalminsa ta nufo gidan ummu...

******
"Bilkisu dare yayi ki kwana a Nan kawai idan kika tafi tsoro nakeji ummu har yanzun Bata dawoba"

"Baki gudun ummu tasan tsakaninmu?"

"Zan sanar da ita idan lokaci yayi ki kwantar da hankalinki"buga kofar akayi da sauri fatima ta Mike Tana fadin "ga ma tanan"tayi hanyar kofar t bude da sauri taja da baya ganin yarima a hargitse yasata mannewa da bango,ta hade ranata tamkar Bata taba dariya ba kallon mamaki yakeyi Mata kawai ya karasa shigowa ciki Yana binta da kallo da kyar ya bude muryarsa a dishe yace "shine kika tafi ko?"...

Cike da tsiwa tace "mezan tsaya inyi Kuna soyewarku kaida amaryarka Wai nabaka wurine kaji Dadi ka nunawa duniya yadda kakeson abarka"

"Ke ni kikewa tsiwa da rashin kunya Ina Wasa dakene?"

Ya daure fuskarsa Yana watsa Mata mugun kallo,

Juyawa tayi tai wucewarta "Dan Kinga Ina sonki Zaki Raina ni ko?ya kamata kisan matsayinki a zuciyata be Dace ke nemi rainani ki wulakantani gaban kawarki ba"

Takaicine ya rufeta kawai ta fashe da kuka wato ma yayi Mata laifi Amma yazo yanayi Mata masifa lallai ya nuna Mata tabbas shi Dan halak ne,

Shigowa ummu tayi dauke da sadik a kafadarta da sauri bilkisu ta je ta amsheshi ta karbi jakar hannun ummu tayi daki yayinda ummu ta bi yarima da mugun kallo ta juya taga Fatima na shasshekar kuka,

Hanyar fita ta nuna Masa "zoka fita mun a gida tunda abinda kayi Mata be ishekiba kazo ka Kara Akan nada koh?fitamun a gida kabiru kafin in sassaba maka"

Shiru yayi Yana mamakin ummu yadda ta sauya lokaci daya take kaunar Fatima fiye da kowa takaicine ya lullubesa tayi masa rashin kunya Amma an bige da korarsa to tabbas idan ya tafi sai ya hora Fatima bazai sake dawowa garetaba Dan yafi karfin korar Kare...juyawa yayi cikin takaici yace "Saida safe"ya fita abinsa Fatima tabisa da kallo Tana hawaye...

"Kiyi Shiru kidaina kuka dik sainayi maganin ko wani Dan iska a gidan Nan Dani suke zance ki kyaleshi idan ya gadama Kar yasake zuwa sai an kaiki dakinshi saime idan ankaiki ya koro min ke,sauran Yan iskan nagama dasu tunda nasamu Mai martaba zasuji result"

Ta wucewarta daki bilkisu na Shirin fita ummu tace ta zauna suyi aiki da safe dare yayi hakanan ta zauna dakin Fatima ,har biyun dare Fatima batayi bacciba Tana kuka Abu goma da ashirin gobe Kabir zai agwance gashi yanzun bayasonta....

Sai wajen asuba bacci barawo ya saceta,haka ta tashi da safe jiki Babu kwari ga masifar ciwon Kai.....

*******
Da sassafe aka shirya deejahmah akasa mata alkyabba tayi kyau da ita wajen karfe takwas gida ya rude da busar algaita ta ko Ina manyan mutane da sarakuna kawai ke shigowa yayinda aka bude babbar kofar fada inda anan ne zaayi daurin aure...

Babbar Riga da Yar ciki Kabir yasa yayi kyau kamar wani babban mutum maroka dik inda yabi suna bnsa da kida da kirari.....

Kuncin da yake ciki yasashi yake kawai yakeyi haka ya shiga gaisawa da mutane haka ya Raba ya shiga fadar yayi kicibis da mahaifin deejahmah yasha Nadi ya dawo daga Egypt har kasa ya tsugunna ya gaidashi ya amsa cike da faraa ....jamaa ne cike da wajen wadanda ya kallon mutum ne aminin sarki Wanda yazo tundaga wani gari sarki ya sashi ya zauna gefensa maimakon galadima dake Shirin Zama Dan ya Mika auren yarsa,damin kudi sarki ya mikawa aminin nasa Yana murmushi Yana fadin Allah yasa alheri Nan akafara gudanar da daurin aure inda aka sanar a loud speaker akwai wani daurin aure Wanda shi zaafara gabatarwa ,..

Take me sanarwa ya fadawa jamaa aka shiga gudanar da daurin aure yadda musulunci ya tanada Saida aka daura auren sanan Mai martaba yayi murmushi yace "alhamdulillah aminina babba na Mika Masa sadakin diyata Fatima marainiyar Allah Akan naira dubu dari biyar Wanda aka daura da Dana kabiru shine auren da muka fara daurawa jamaa ku shaida"take Mai shela ya shaidawa jamaa an daura auren kabiru da Fatima,kallon kallo mutane keyi dama Mata biyu zai aura?"

Cikin minti biyar aka Kara yin shela ta daura auren deejahmah akaro na biyu da Dan sarki yarima"....Nan maroka da makida suka fara kidi tamkar jira suke a har gitse galadima ya mike yana fadin "ban yardaba ban amince da wanan auren ba,matukar kabiru zai auri shegiya bazai zauna da diyata ba Dole ya saketa"...Nan jamaa wuri ya dau hayaniya sarki bece komiba sai gaisawa da jamaa da ya cigaba da yi ya shiga bayarda kyauta ga wadanda Allah ya ciyar sukazo daurin aure.....yarima kuwa daskarewa yeyi a zaune dik jamaar dake Mika Masa hannu kasa dago hannunsa yayi ya Mika,yayinda waje ya kacame da hayaniyar galadima da tawagarsa....

Cire malum malum dinsa yayi yai cikin gida mutane Yan kallo suka rufa Masa baya.....

*Muje zuwa 🙆🏻hajiya zainab ta hada gurmi....*

*SLIMZY😍*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

38
Bankado labulen parlorn yayi a fusace "Ina khadijar take "...da sauri deejahma ta dago fuskarta a furgice Jin yadda aka Kira sunanta,

"Tashi muje sai dai ya zaba ko ke ko Yar shegu Dan bazai yuwu da mutuncina da komi a wulakantani a tozartani cikin dubban jamaa ba wadanda sukazomin daurin aure"

Kallon mahaifinta takeyi fuskarta dauke da furgici cikin rashin fahimta bakinta Yana rawa dakyar ta lalubo kalmomin ta hadasu tace "meya faru abbah?"

"Au ku bakusan meke faruwa ba Kuna cikin gida ne?"

Hajiya rahina wadda ta fito daga daki ta karbe zancen da "Wai meke faruwa ne naganka haka a furgice"

Ya bude baki zaiyi magana yarima yayi sallama a parlorn take jakadiyya ta rangada gu'd'a...

"Ga munafukin Nan ya shigo,wato dik kananan maganganun da akeyi da dik wata gutsuri tsoma na maganar aurenka da Yar gidan marayu Ashe dagaske ne ,tunda yau ta tabbata cewa Kai din Dan halas ne tunda ka hada baki da Mai martaba andaura aurenka da Mata biyu"

Dafe kirji hajiya babba tayi "Mata biyu"

'kwarai da gaske Mata biyu sanan wani wulakanci ma Saida aka daura aurensa da waccan sanan aka daura da yata saboda tsabar cin fuska ban taba tunanin Mai martaba zaimun haka ba"

Jikin deejahmah ne ya Kama rawa take kafafuwanta suka dauki rawa tamkar wadda akasawa shocking ta shiga ja da baya a hankali har ta jingina da jikin bango saboda yadda jiri ke dibarta,

Takaicine ya rufe mahaifin deejahmah ganin yadda yarima ke faman raba idanuwa,cikin kumfar baki ya Soma zazzaga balai "cikin biyu zaayi daya, matukar kanason Zama da yata saidai a warware wannan auren munafurcin da aka kulla ko Kuma wallahi ka sakar min yata yanzun Nan Dan ba neman Kai nakeyi da ita ba"
Chapter 56 · 0% Book details