← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 80

Sashe 44

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cakkk ta tsaya zuciyarta na harbawa sauri da sauri take wani Abu yazo ya tsaya Mata a kirji dakyar ta hadiye miyon bakinta ta karasa fita har zata rufe kofar ta leko da kanta Tana kallonsa cikin ido ya kashe Mata ido daya "idan har kaje to tabbas kasani kabar sake ganina sai Nan da sati biyu"

Dage kafadarsa yayi Yana murmushin mugunta tarkon daya Dana Mata ya kamata Nan da Nan ta nuna Masa kishinta a Fili....

Juyawa tayi da sauri tabar ledar maganin cikin motar saboda kidimewar da tayi hantar cikinta dik a Kade take addua kawai takeyi Allah yasa Babu Wanda ya ganta.....ga takaicin maganar da yarima yake fada mata Wai zaije wajen wata ,to yaje Mana ai ko be fadaba tasan cewa Yana son deejahmah boye Mata kawai yakeyi....

Har ta doshi shiga ta babban parlor ta fasa dabara ce ta fado Mata tabi ta kofar baya da sauri ta kwaso shanyar da tayi ta nufo cikin gidan kirjinta na bugawa....

Sashen hajiya ta shiga da sallama sai Raba idanuwa takeyi dakyar ta Tattaro jarumtar ta tayi sallama cikin sassanyar murya...

"Kin dawo daga yawon iskancin kenan?kin manta na baza idanuwana cikin gidan Nan Kuma dik akanki suke?...ya daukeki ya fita dake kunyi abinda zakuyi kundawo ko ?ai na dauka daga can wani waje zashi dake ya ajiyeki ya fiye Miki sauki Akan dawowa cikin gidan Nan"...

Wani mugun miyau Fatima ta hadiye a fakaice"Babu inda naje Ina bayan can anan nayi sallah na zauna har akayi ishai sai yanzun na dawo ai bilkisu ta taganni lokacin "

Da sauri hajiya ta juyo ga bilkisu wadda ke faman zare Ido "bilki Wai kinganta?"

"Naganta ranki ya dade niba shiga sabgarta nakeyi ba shiyasa nayi wucewata Kuma bansan maganarta kukeyi ba Dan ni ko sunanta ma bansaniba"..

Kwafa hajiya ta sauke ta wurgawa Fatima wata uwar harara "ficemun daga daki"

Mikewa tayi ta fice abinta har yanzun gabanta be daina faduwa ba ta fito ta babban parlor,

Hajiya karama ta gani zaune hannunta dauke da carbi Tana ja ta karaso ta tsugunna a gabanta ta gaidata ta amsa Mata Babu yabo Babu fallasa....

Dakinsu taje ta nemi waje ta zauna ta fada duniyar tunanin yarima....zuciyarta ke ayyana Mata yanacan tare da deejahmah suna Shan soyayya ke tsoro ya hanaki nuna Masa yadda kike sonsa,ki tsaya kallon ruwa kwado yayi Miki kafa,

Yatsanta ta ciza hade da Jan tsaki lokaci daya,

A gaggauce bilkisu ta shigo ta sameta daidai tanajan tsaki "ke kuma tsakin me kikeyi?angamo soyayya an dawo kinzo kina zare idon banza bayan ba tsoron da kikeji tunda kika iya awanni biyu tare dashi"

Duka Fatima ta Kai Mata "ni ki kyaleni abinda ya dameni ya dameni Dan yanzun fa fushi yayi Wai zaije wajen wata"

"Kadan kika gani wallahi inhar bazaki cire tsoroba kiyi yaki to watarana Zaki wayi gari ki nemesa ki rasa yanzun gogayya yakamata kuyi ta tsaya Jin Kai ke Kuma ki kwace miji dik kallon baiwa kuyanga da akeyi Miki ki barta a Tasha"

Dariya Fatima tayi "ni Bilki idan kina magana kamar wata uwar Mata mamaki kike bani"

Harararta bilkisu tayi "Dole inbaki mamaki ai tunda kin Gama koke koken kin warke yanzun ai Dole ki fadamun magana "

Toshe baki Fatima tayi tanawa bilkisu dariya wadda ke magana cike da kulewa, "ni yanzun babban tashin hankalina be wuce ranan da zata kasance an rabamu da yarima ba maana ranan da zaa daura Masa aure"

"Ki shirya kibishi gidan matar"

Tsaki bilkisu tayi ta juya tai tafiyarta tabar Fatima Nan.....

*********
Shiko yarima Yana ganin shigewar Fatima cikin gida ya fito ya rufe motarsa ya shige bangarensa Yana murmushi Domin Harga Allah dariya ma abin ya bashi....

**********

Bayan kwana shida,

Ya kasance befi kwana takwas bikin yarima da deejah ba gida ya fara rikicewa da baki na cikin gida da waje saura kwana biyu a fara event kamar yadda deejahmah ta tsara itada aminiyarta teemah dollar.....

Zaune Fatima take can bayan gida inda ya kasance Nan ne wajen zamanta Nan take makalewa taita kukanta dik ta fige ta rame ta shiga matsananciyar damuwa hakika sabo turken Wawa ne ta tabbatar da hakan Dan ta Saba dashi sosai fiye da tunanin Mai karatu,

Durkusar da kanta tayi Tana kuka Mai ban tausayi Wanda batasan dalilinta na yinsa ba,..

Nemanta bilkisu takeyi tun safe Bata gantaba har ta cire Rai da ganinta saita tuna da inda suke Zama saboda mutane da suka fara yawa cikin gidan....

Yarima ta gani yanata dube dube tamkar me neman wani Abu can ya hangi bilkisu ta nufi bayan gidan su inda bishiyoyin mangwarori suke....bayanta yabi har suka Isa a tare wajen bishiyar da Fatima ke tsugunne Tana kuka

Ganinsu ya sanyata saurin mikewa Tana share hawayenta hade da wayancewa,

Kallon yadda ta canja yakeyi dik ta rame tayi bakin Kirin idanuwanta sunyi zuru zuru....

Tsugunnawa yayi a gabanta ya rike kunnuwansa alamar ban hakuri.....kuka ne ya taho Mata lokaci daya kawai ta durkushe a gabansa Tana kuka Mai ban tausayi.....besan lokacinda hawaye ya shiga fita a idanuwansa ba,....ita kanta bilkisu dake jingine jikin bishiya hawaye takeyi Domin dik Wanda ya kalli Fatima a wanan yanayin saita bashi tausayi.....

Dakyar ta tsagaita da kukanta ta matso kusa dashi tasa gefen rigarta Tana share Masa hawaye hade da girgiza Masa Kai...."...banason ganin idon jarumin namiji Yana fitar da hawaye,....idan har bakayi shiru ba bazan gafartawa kainaba"tana maganar ne Tana kuka....

Hannu yasa ya share hawayensa sanan yasa hannunsa Yana share Mata hawaye "banason ganin kyakkyawar fuskar Nan cikin damuwa, kiyi shiru ki dainamun asarar hawayenki Fatima,hawayenki sunfi komi tsada da kima a idanuwana da inada Hali da na hanasu zuba har abada meyasa kike nisanta kanki Dani cikin kwanakin Nan"..

Cikin shasshekar kuka taja hancinta "nafara koyawa kaina rayuwa batare da kaiba,kukan Nan da kaga inayinsa inayine saboda zan rasa farin cikina.....banida gatan daya wuceka a rayuwa,...ka manta Kaine inuwar dake zagaye Dani a cikin gidan Nan?babu wata inuwar da nake rabawa insamu farin ciki in samu sassauci daga zafin Rana sai inuwarka....banida uwa bani da uba sai Kai ya bazanyi kuka ba?ya bazanyi kukan rashin masoyi ba?".....

Tunda ta Soma magana hawaye ke gudu a idanuwansa tausayinta shine abinda ya mamaye ilahin sassan jikinsa.....hakika Fatima a bar tausayi ce Fatima batada gatan daya wuceshi cikin wanan duniyar.....

Kammo hannunta yayi ya rike Yana murzawa yayinda take durkushe a kasa Tana kuka Mai ban tausayi.....

"Ki dago kanki kidaina wanan kukan Domin idan kinayinsa ji nakeyi na tsani kaina a rayuwa ji nakeyi tamkar na cutar dake naci amanarki ki dago ki fadamun abinda kikeso inyi Miki nayi alkawarin yi Miki ko meyeshi a fadin duniyar Nan matukar Zaki daina zubar hawaye"....

*Muje zuwa*

*SLIMZY😍*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

32

Dago Kai tayi tana Kare Masa kallo har ya Kai karshen maganarsa,Kara damke hannuwansa tayi cikin nata,dayan hannunta ta Sanya ta share hawayenta

"Kaima ka share hawayenka kaji ?kaga Nima na share nadaina kuka kaji?".. ta langabar da kanta Tana kallonsa,

Hannu yasa ya share hawayensa ya maida dubansa gareta "Ina sauraronki fadamin bintu na mekikeso umm?"

"Ni tsoro nakeji kada kayi aure ka mance Dani ka manta da wata Fatima na rayuwa a doron kasa,gashi ka sabamin da rayuwa da Kai ba lallai bane kullum inganka shiyasa na shiga damuwa"

"Idan har zan mance dake faty to tabbas zan mance da kaina da rayuwata,kisawa zuciyarki ninakine ke kadai harabada bazan taba rabuwa dake ba numfashina"

Kallon yadda yake motsa bakinsa takeyi soyayyarsa na yawo cikin jinin jikinta,ta shagala da kallonsa har ta mance da wani bacin Rai da take ciki a wanan lokacin,

Duko da kansa yayi Yana kallon cikin idonta ,da sauri ta kauda Kai Tana murmushi "yaayah Dan Allah ka rinka zuwa wajena kaji?"ta marairaice fuska,

Mikewa tsaye yayi Yana kakkabe jikinsa "rigimarki yawa ne da ita Fatima Allah Ina gab da fara zaneki don wanan kukan da kike yi wata rana hawayenki zasu Kare"

Mikewa tayi tsaye tana murmushi "inhar kukan Nan ne bakaso to na Bari "..

Gira daya ya dage Mata "kin tabbata?"

Daga Masa Kai tayi tana dariya.

Aiko Dole inbaki chocolate,ya zura hannunsa cikin aljihunsa ya Ciro chocolate guda biyu ya bare da hannunsa "oya taho ki amshi kyautar soyayya"

Tana dariya ta Miko fuskarta ta Dan bude baki ya tura mata chocolate baki ta hade da yatsansa ta rike Tana dariya...

"Aushhhh da zafi Mana wallahi kinci bashi saina Rama"

Kada Masa idanuwa tayi "yanzun sai ka Rama?"...

"Ehh Mana kibari indawo daddare zan Rama zan siyo muku kayan da zaku canja kuci biki dashi keda bilkisu da Maryam"

Gyada Masa Kai tayi "Allah ya tsare"

Waige waige ya shigayi hade da leka bayan bishiyar sanan ya juyo Yana dubanta "Ina bilkisu?"..

Sai lokacin Fatima ta tuno da wata bilkisu itama waige waige ta shigayi sanan ta juyo tace mishi "Ashe ta wuce"

Jan hancinta yayi kadan "yaushe zakisan ta wuce kinatawa mijinki rigima?umm?"...yasa hannu ya zagayo kungunta ya riketa sosai Yana kallon fuskarta,itama shi take kallo Tana murmushin sannan taja da baya cikin dabara ta kwace daga rukon da yayi Mata "saika dawo"

Gyada Mata Kai yayi ya juya cikin sauri Yana kallon agogo ya bar wajen,kallo ta bishi dashi hade da sauke ajiyar zuciya....

Ta Dade zaune wajen Tana tunani kala kala yadda zuciyarta batayi Mata Dadi kwata kwata.....

**********
Yau ta kasance Ana gobe zaafara event din biki yayinda gida yake cike makil da jamaa na ciki Dana waje Kuma yau ne hajiya zainab da tawagarta suka sauka daga Saudi Arabia bangaren mama karama ta sauka Domin sunfi shiri da ita,..

Tunda garin Allah ya waye ake girke girke kala kala dik wata baiwa da ke cikin gidan Bata Samu tsugun ba saboda aikace aikace da suke famar yi yayinda deejahmah da tawagarta gabaki daya suka dawo gidan sarki Nan ake biki sosai....

Zaune da kawayenta can wani daki Wanda ya kasance Nan anyisa Domin masaukin baki dakine safe content da bayi biyu ciki a Nan suka sauka suke lalle itada kawayenta da kannenta ciki kuwa harda su khausar afnan,faizah da fauziyya sai wasu friends dinta guda uku,..
Chapter 44 · 0% Book details