← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 80

Sashe 69

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsananin bacin Rai yasa idanuwan yarima rufewa take ya mikawa hajiya karama hoton hannunsa "hajiya Dan Allah Dan annabi ki duba hoton Nan bazaki rasa sanin wacece a jikin hotonba wadda a yanzun take itace uwar Fatima"..

Hannu Mama karama tasa ta karbi hoton ta maida idonta a Kan hoton......ta Dade Tana kallon hoton ko kafin ta dago kanta idanuwanta sun cika da hawaye fuskarta ta jike da zufa ta ko Ina...."wanan hoton sarauniya zahrau ne a gefen ta kuwa diyarta ce tunda ga kamanninsu Nan sak da juna"....

"Alhamdulillah mama wacece sarauniya zahrau?"yarima ya jehowa mama karama tambaya yayinda wajen yayi tsitttt

"Sarauniya zahrau itace matar sarki abdallah yayan mahaifinka....wanda shine asalin Mai sarautar garin Nan....sarauta ta koma hannun mahaifinka ne ta silar saifiya"....

Hajiya karama ta nuna hajiya babba Tana hawaye...dukkansu sukabi hajiya babba da kallo...

"Me kike shirinso kice?koko kema kin yarda da wanan bakin hoton da aka kawo akace zahrau ce matar sarki abdallah?wallahi wanan ba zahrau bace karya ne "Tana karashen zamcenta ta juya da sauri Tana jaraba deejamah wadda tayi mutuwar tsaye dakyar ta taka kafarta tabi bayan hajiya babba...

Zama yarima yayi ya tankwashe kafa Fatima ta zauna gefensa jiki a sanyaye "Mama banso kukasan maganar Nan ba nasone infara samun sarki da maganar kafinku sai Kuma naje banaameshi ba ance yaje gaisuwar mutuwa gidan sanata shine na shigo Nan naje gaida hajiya na tarar da ita tasa Fatima gaba Tana hayaniya shegiya ce tsintacciyar mage shine abinda yasani tsananin takaici na fallasa Kwan"

Kuka sosai ummu takeyi Tana fadin "Fatima Ashe yata ce ke?Ashe Yar wana ce uwa daya uba daya?banyi mamakiba da nakejin tsananin kaunarki.... alhamdulillah Ashe zahrau ta haife cikin dake jikinta?Ashe zahrau ba mutuwa tayi ba?"..

Kuka sosai mama karama keyi dakyar ta tsagaita ta dubi Fatima na Yan mintoci ta sauke ajiyar zuciya sanan ta dubi yarima Wanda dik ya kosa yaji yadda akayi hakan ta faru...."da Fatima ta kasance da' namiji da Babu abinda zai Hana mahaifinka beyi murabus ya Bata sarautar garin Nan ba....Domin sarautar ta mahaifinta ce,...."

Cikin kosawa yarima yace "mama ta Yaya hakan ta kasance?"..

"Dole in sanar dakai abubuwan da muka aikata a baya Koda zamu samu sassauci da kwanciyar hankali a duniya da Kuma lahirar mu....Domin munada sa hannu a komi".....

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"...shine abinda yarima ya ambata a Fili Yana share zufar fuskarsa ...

*Muje zuwa*

*SLIMZY😍*
[8/29, 14:50] 🥰slimzy🥰: 🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

_Wanan shafin sadaukarwa ne ga dik wani maraya dake fadin duniyar Nan....._ 👏🏼😊

45

"Tun bayan rasuwar kakanka,ya kasance sarki abdallah shine babban danshi sai mahaifinka Sanan sai zainab sai rahina itace autarsu,

Mahaifinka ya Riga yayansa aure Dan ko lokacin da kakanka ya rasu dukkanmu babu Wanda baa auraba Dan lokacin ma habibu yanada shekara kusan goma Sha takwas a duniya,shiyasa Koda kakanku ya rasu nida safiya muka shiga farin ciki Akan mahaifinka shi zai gaji sarauta saboda shine yake da iyali shi ya cancanci abashi sarauta ba sarki abdallah ba,

Kwatsam bayan anyi sadakar bakwai na kqkanku sai mukaji labarin babban aminin kakanku ya aikowa abdallah da yazo zai bashi diyarsa zahrau ya aura tunda bashida Mata ya Kuma manyanta a lokacin,.. Jin haka yasa abdallah beyi musuba ya amshi auren wanan yarinya da akayi Masa tayi zahrau ranan da aka daura musu aure ranan aka nadashi sarautar garin Nan mahaifinka yayi matukar farin ciki da aka nada Wanda sarautar garin Nan sabanin mu matansa da mukayi bakin cikin hakan,

Tunda aka wanke zahrau aka kawota gidan Nan muka hade Mata Kai nida hajiya babba Kuma hakan dik yasamu asaline da tsananin kishinta da safiya takeyi itace ta kawo shawarar mu hade Mata Kai Babu wata muamala da take shiga tsakaninmu da ita saboda dik mun girmeta ko a wanan lokacin batafi shekara ashirin zuwa da dayaba sukai aure....

Babban burin safiya be wuce zahrau ya Zama Bata haihuwa ba saboda mijinmu ya gaji sarauta idan har zahrau Bata haihuwa to Babu makawa mijinmu ne zai hau sarauta....

Shiyasa safiya ta hada baki da dik wata baiwa dake cikin gidan Nan maaikata masu girkin abinci take Basu abubuwa suna sawa zahrau cikin abinci na Hana daukar ciki,wani lokacin ma har kwayoyi muke tasata nida safiya mu Bata dikda ni Ina baya baya saboda gudun kamuwar da Allah zaiyi Mana,

Dik wadanan abubuwan da mukeyiwa zahrau na tsangwama da tsananin tsana mazajenmu basu sani ba saboda bama taba nunawa a gabansu Dan su kansu a hade yake,

Rahina dama ta kasance ita Yar dakin safiyace tun Tana kqrama dik abinda safiya takeso shi takeyi Bata tsallake umarminta wasu abubuwan dayawa Tare da rahina suke yinsu dikda Nima Ina Taya safiya kishi Amma bana taba yarda in muzgunawa zahrau ko nayi daga baya zan koma in nemi gafararta,..

Samm zahrau Bata fitowa Tana bangarenta Koda yaushe cikin kuka take saboda yadda mukabi muka sawa kowa tsanarta cikin gidan Nan harda bayi da kuyangi basa ganinta da mutunci dikda kasantuwarta matar sarki a wanan lokacin Amma samun waje da fuska da sukayi a wajenmu yasa kowa ke tsula iskancinsa,

Kwatsam bayan shekaru biyu da aurensu zahrau tasamu ciki Wanda bamu San dashi ba saboda yadda muka saki jiki Akan mahaifarta ta lalace saboda mugayen abubuwan da safiya ke amsowa Ana Bata yasa ta rame ta koma tamkar me wani mummunan ciwo,Dan haka Koda tasamu ciki bamu saniba Saida ya Kai wata biyar Amma shi mijinta da mijinmu sunsani dik a tunaninsu muma munsani,

Ranan muna zaune a parlor da mijinmu nida safiya ya Dan kishingida kadan idanuwansa a lumshe yace "Kuna dai kula da zahrau koh?kunsan yarinya ce wani Abu sai an rinka sa Mata idanuwa dikda gabaki daya ta canja ta rame tamkar me wani mummunan ciwo"

Gyara Zama safiya tayi cike da kissa tace"ranka ya dade ai kulawa da zahrau ya zame Mana Dole tunda Yar Amana ce ko jiya na shiga bangarenta mun Dade tare Mina Hira Ina tambayarta yadda zaman nasu yake da maigidan nata"

"Ai kullum ya kamata ku rinka shiga yanzun saboda sauraren haihuwar Tata tunda cikinta yanzun zai Kai wata shida ko biyar"..

Kamar hadin baki muka hada baki wajen fadin "ciki fa kace ranka ya dade"

Sai yadan bude idonsa Yana binmu da kallo cike da mamaki ganim yadda ko wacce a cikinmu ta furgice "au bakusan tanada ciki ba kenan?koko baku lura bane?"

Wayancewa mukai a tare muke fadin "yo ranka ya dade aimu bamusan da wanan labarin farin cikin ba,kasan fa matar wan naka akwai kunya Sanan kullum cikin alkyabbar take babu Wanda zaaiyi ka fahimci akwai ciki a jikin nata"

Yar dariya yayi "aikuwa abdallah ya kusa samun magaji insha allahu,Allah dai ya sauketa lafiya"

Dakyar safiya ta bude baki ta amsa saboda yadda gabaki daya ta furgice da lamarin,Allah Allah mukeyi ya fita zuwa fada muje bangaren nata,aikuwa Yana fita muka zari gyalenmu muka nufi sashin zahrau,

Tana zaune Akan daddumar sallarta gefenta Kaine zaune dama tun kana karami jininka ya hadu da ita Koda yaushe kana tare da ita Nan ne wajen hirarka,..

Babu ko sallama muka shiga a tare,Tana ganin mu yadda ta furgita a wanan lokacin kaidin da Mai hankali ne saika fahimci wani Abu sai ta baka tausayi savoda tsananin tashin hankali daya bayyana karara a fuskarta,..

Harararka nayi nace "rasa kunya ka tsaya ne kaji me zamuce?"...sai kawai kabi zahrau da kallo batare da kace komiba ka fice a dakin,...

Safiyace ta gyara tsayuwa "zahrau dama ciki gareki?dayake ke munafuka ce kinsan abinda kika kulla yasa kika kasa sanar Mana?saboda dama kudurinki kizo ki haifi magajin sarki koh?shiyasa ubanki ya daukeki sadaka ya mikawa abdullahi ke Dan yasamu jika sarki koh?to wallahi baki isaba yayanmu su zasuyi gadon sarautar barayar Zaki ba Dan Yar sadaka ba"..

Kuka zahrau ta shiga rerawa Mai ban tausayi ni kaina da nake gefe Saida jikina yayi sanyi ganin yadda dik ta furgice ta gigice Tana bamu hakuri....

"Ciremun hijabin dake jikinki mugani muna fuka?"cewar hajiya babba,..

Jikin zahrau Yana rawa ta cire hijabin jikinta saiga ciki ya fito sosai.....

Nan muka saka salati muna tafa hannuwa,....safiya batai wata wata ba ta shararawa zahrau Mari "wallahi baki Isa ki haifi abinda ke cikin Nan nakiba Dole ma a cireshi kodai ki yarda a cire cikin Nan ko Kuma ko ki haifeshi babu Rai"...

Nai saurin cewa "safiya bedace ace mu kashe Mai Rai bafa?mu kyale cikin kawai ta haifi abinta"..

"Idan ke wawuya ce niba wawuya bace wallahi ai Dole ma kice haka tunda Kinga ai Koda sarki ya mutu ba danki bane zai gaji mulki saboda bashi bane babba shiyasa kikace haka to wallahi yanzun ba sai anjima ba Dole ta haifeshi"..

Zaro idanuwa nayi waje inabin safiya da kallon mamaki,

Wata kuyanga ta kwalawa Kira Ana ce Mata uwaliya,Babu dadewa uwale ta shigo ta tura uwale dakinta ta Kira Mata rahina,Nan da Nan sai gasu tare da rahina,..

Fuska babu walwala safiya ke duban rahina "Ina tsumin madacin Nan da nace ki jikashi saboda wanan shegiyar?to amfaninsa yazo "

Juyawa rahina tayi jimm kadan sai gata da Koko cike da ruwan magani Kore sharrr safiya ta amsa ta mikawa zahrau dake tsaye jikinta na rawa Tana shasshekar kuka fuskarta tayi jajir,

"Dan Allah kiyi hakuri hajiya karki kashemun abinda ke cikina inason Dana idan zamana ne bakuso zanbar muku garin"

Wata tsawa safiya ta dakawa zahrau Nan da Nan ta amshi maganin Nan jikinta na rawa ta kafa Kai,tasss ta Sha kusan rabi idanuwanta suka canja kala savoda tsananin azaba da dacin maganin.....

Minti kadan muna Nan tsaye zahrau tafara murkususun ciwon ciki ta durkushe a wajen Tana kukan azaba Tana Kiran mutaimaketa Babu Wanda yabi ta kanta tunda mukaga jini ya fara bin kafarta muka fice muka rufo Mata kofar Sanan safiya tabawa bayin bangarenta doka Akan Kar Wanda ya shiga wajen da zahrau take,..

Har wajen laasar Ina jimami da tunanin yadda muka baro Yar mutane,tsananin furgici da tsoron Allah ya sa na Mike nayi sashinta Koda na shiga tasamu sauki Tana zaune Tana faman sharar hawaye dik ta Bata ko Ina da jini,..
Chapter 69 · 0% Book details