← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 80

Sashe 50

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyara Zama fauziyya tayi tana fadin "kiyi hakuri banzo wajen Nan da wuri bane wallahi Kuma sakonki shi ya zaunar Dani a gida wallahi "

Cike da rashin. Fahimta Fatima tadan kalleta ,

"Ehh wallahi tsarabace aka kawowa mamanmu daga nijar shine na tsaya diba Miki kilishi da wani turare Dan agadaz Kya rinka shafawa idan kinyi wanka"

Dadine ya cika Fatima "Kai Amma nagode wallahi inason kamshi banida yadda zaayine insamu turare inrinka shafawa kodan shiga mutane"

Jinjina Kai fauziyya tayi tana kallon kyawun halitta da Allah yayiwa Fatima wani haushine ya turnuketa take taji tamkar ta shaketa,jinjina Kai kawai takeyi Tana kallonta Tana murmushi zuciyarta kawai ke Raya Mata "matukar kika shafa turaren Nan kin Gama yawo yarinya Domin jaba saita fiki mutunci a wajen Wanda kikewa rawan Kai"

Dan kallonta Fatima tayi ganin yanayinta dik ya canja yasa tace "faizah kodai bakida lafiya ne yau?"

"Mekika gani?"

"Yanayinki ne Naga dik ya canja bakida annuri a fuskarki Babu faraa kamar jiya"ta tsareta da idanuwa Tana karantar yanayinta....

Girgiza Kai kawai fauziyya tayi "no bakomi yau hayaniya tasamun ciwon Kai wallahi"

"Allah ya sauwake"

Daga Mata Kai kawai tayi batare da tace komiba,dik yanayinta ya canja ba kamar jiyanba sanan yau tanayi Mata magana a takaice...

Shagali kawai akeyi Yan matan amarya sai cashewa sukeyi yayinda hajiya babba da tawagar kawayenta suke zubar naira suna liki,fitowa dubu da amarya zatayi tai rawa yarima baya fitowa dik abinda sukeyi a zaune yake tamkar an dasashi...

Haka akaita shagali wajen Nan Wanda dik inda Fatima tasa kafa fauziyya na biye da ita tanayi Mata basaja .....komai dake faruwa akan idon bilkisu ne tunaninta gabaki daya ya karkata wajen abinda ke hannun Fatima ne a jakar leda....

Baatashi taro ba sai karfe takwas na dare sanan jamaa suka fara watsewa suna tafiya gidajensu yayinda wasu ke shigewa cikin gida ciki kuwa harda baki wadanda dama yau suka sauka a gidan saboda biki....

********
Hayaniya ce ta kacame sai surutu akeyi ta ko Ina saboda mutane dake cike a gidan ta ko wani bangare cike yake da mutane....

Sashen Yan matan amarya ne ya kacame da hayaniya ko wacce ta fiddo wayarta Tana kallon hotuna da videos din da akayi a wajen suna Hira suna dariya yayinda deejahmah zuciyarta take bakin Kirin Tana gefe a zaune Tana cika Tana batsewa da gudu kawarta tazo gefenta ta dafata Tana nuna Mata video dai dai inda yarima ya kafe Fatima da idanuwa wajen a slow yake tafiya "ranki ya dade kalli wani abu a wajen Nan wanan kawar mijin naki yadda suke jifan juna da wani kallo tamkar masoya"

A fusace deejahmah ta juyo ta kalli Mai maganar Wanda dama a cike take famm tace "ba soyayya sukeyi ba Amma zan nuna Mata tayi gangancin hada Ido da idanuwa masu tsada a duniya saina shayar da ita mamaki ,sanan sai ta Zama baiwa a gareni Mai hidimar cikin gida na"...Tana Gama maganar ta fice a fusace dakin yayi tsitttt kowa ya bita da kallo....

Dakin hajiya babba ta shige a Nan ta taradda Fatima ansata aiki bayan ta tube Kaya sai mopping takeyi Tana hada zufa tana Ana kyararta hade da hantararta ai deejahma nayin tozali da Fatima tayi kanta Wanda hakan yayi daidai ta shigowar ummu dakin

"Munafuka kin gamo karuwancin kindawo asalinki na baiwa?wallahi dik abinda kikeyi inasane dashi nasan cewa kin mallakeshi ne yasa yake kulaki Amma yafi karfinki"

Rirriketa kawar mahaifiyarta tayi tana fadin "lafiya deejah meyafaru?meke tsakaninki da Yar aiki Kuma"

Daga gefe hajiya babba ta sakarwa Fatima rankwashi a tsakiyar Kai ta shiga dukanta ta ko Ina Tana fadin "munafukar Allah kin zame Mana karfen kafa wallahi Dole ma ki hada kayanki kibar gidan Nan Dan ke balai ce annoba"

A fusace hajiya zainab ta daka tsawa cikin dakin "meye haka kukeyi?Tara Mana mutane kukeso kuyi?Koko so kuke ku fallasawa duniya asirin da yake rufe a kasa kowa yaji?"

"Wani asiri Banda Wanda itace tayi sanadiyyar mutuwar Dana daya tilo sanan saboda cin Amana aka dauko shegiya aka kawota cikin gidan Nan Wai ita marainiya bayan munji komi a gari cewa karuwa ce to wallahi saita bar gidan Nan tabar Mana zuriah yau din Nan ba sai gobe ba"

Kuka sosai Fatima keyi yayinda hayaniya ta kacame cikin daki Wanda hakan yasa jamaar cikin gidan suka cika bangaren hajiya babba kowa na tofa albarkacin bakinsa,wadanda suka hayi maganar a sama suka shiga yiwa Fatima tofin Allah tsine,

Jin hayaniya tayi yawa yasa yarima shigowa cikin gidan a guje yayo sashin hajiya babba Yana shigowa yayi tozali da Fatima Tana famar rizgar kuka,bece komiba yasa hannu yajata yayi waje da ita...

A haukace hajiya babba ta Soma surfa balai Tana fadin "kamar yadda kakeson ganin karshena kabiru sai Naga karshenku a cikin gidan Nan daga Kai har ita matsiyaciyar yarinyar wallahi tallahi yau din Nan saita bar gidan Nan Kuma kaida aurenta saidai a kiyama"

Yadda take kumfar baki kawai hajiya zainab ke kallo Tana watsa Mata wani irin kallo dakyar ta bude baki cike da takaici tace "Haba hajiya wanan wani irin Abu kikeyi haka kamar karamar yarinya sai a shigo cikin gidan Nan aga da yaran cikinki kike balai saboda waccen haddasanar ta kunno balai ko?to wanan rantse rantse da kikeyi na banza ne Domin Babu abinda zai yuwu a cikin maganar da kike fada,wanan yarinyar da kuka dau Karan Tsana kuka Dora Mata saboda Bata da gata ku kune masu gata Kuna ganin Allah ba zai saka Mata ba?to wallahi Allah zaiyi Mata mummunan sakayya sanan Ina Mai gargadinki Akan ki gaggauta canja tunaninki idan ba hakaba zan shayar dake mamaki".....

Dik jamaar dake wajen shiru akayi tamkar anyi ruwa an dauke sautin muryar ummu kawai ke tashi a wajen,....

Takaicin maganganun ummu ne ya lullube hajiya babba ta zaburo ta tsaya a gabanta Tana fadin "Akan kabiru da wanan tsinanniyar yarinyar kikeson yimun rashin kunya zainabu?kikeso ki nuna mun Isa?me kika Isa kiyi a wajen Nan Koko kece kikeda damar yanke hukunci Akan baiwata kutanga ta"

Dariya kawai hajiya zainab keyi Tana tafa hannu Tana kallon hajiya babba ido cikin ido sanan ta nisa tace"zan nuna Miki isata kuwa,Domin Fatima baiwarki ce kuyangarki ce Amma yau cikin bainar jamaa kowa zai shaida cewa na ya'nta ta zuwa cikakkiyar ya'sanan rukonta kacokan zai dawo hannuna Kuma ko kinki ko kinso Dole kibi wanan umarni"

"Karya kikeyi zainabu baki isaba wallahi kinyi kadan.....

Bata karasa maganaba yarima ya shigo dakin fuskarsa Babu walwala dakyar ya iya bude baki yace "Mai martaba Yana kiran taron gaggawa yanzun a fadarsa"....

Yana Gama fadin haka yayi ficewarsa kowa ya bishi da kallo yayinda hajiya zainab ta rufa mishi baya......

*Muje zuwa*

*SLIMZY🥰*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

35

Hajiya zainab ita tafara Isa fada bayan yarima,a can ta iske fatima a gaban Mai martaba Tana faman zubar da hawaye tamkar an bude famfo kallo daya tayi mata ta kauda kanta saboda tsananin tausayin yarinyar da ya lullubeta take taji idanuwanta sun ciko da hawaye ta nemi gefen da Fatima ke zaune ta zauna da kyar ta bude baki tace "ya Isa haka Fatima kiyi Shiru insha allahu komi zaizo karshe Domin wannan cin zali yayi yawa na tabbatar da Mai martaba adalin sarki ne zai duba lamarinki kinji share hawayenki"ta kamo Fatima zuwa jikinta ta shiga goge Mata hawaye,a haka su hajiya babba suka shigo kowa ya hallara cikin fadar...

Wanan karon sarki ransa yayi mummunan baci a fusace yake sai kaiwa da komowa yakeyi Saida kowa ya Gama zuwa sanan yanjuyo da kakkausar murya ya Soma magana "Kun bani mamaki kun zubarwa kanku da mutunci sanan Kun dauki wuka Kun dabawa cikinku yadda kuka taru waje daya Kuna hayaniya kuka kokarin fallasa asirin cikinku na tabbatar cikin gidan Nan ba zallar Yan uwa bane ciki harda na waje,yau Koda Yan uwane bai kamata kutaru ku nemi zubarwa da wanan masarautar mutunci ba "

Gyara Zama ummu tayi ta ce cikeda ladabi "Allah ya huci zuciyar Mai martaba baa kyautaba sharrin shaidan ne"

"Babu ruwan shaidan a wanan lamari sai sharrin zuciyoyinku wadanda gabaki daya Babu abinda kukasa a Rai sai son Kai da son zuciyane"

Ya juyo inda hajiya babba ke zaune kanta a kasa Tana famar hura hanci "hajiya safiya kinbani mamaki ban taba tunanin ko kowa zaiyi rashin hankali ke zakiyi ba"

Da sauri ta dago "ranka ya dade..."

"Dakatamun hajiya Babu abinda kowa zaicemun a wajen Nan Domin ba yarda zanyi daku ba tunda kunci amanata kunci amanar marainiyar Allah Kuna neman aikata lahira to na yanke shawarar dauketa daga gidan Nan kafin ku kasheta" ..

Jin haka yasa hajiya zainab saurin fadin "Allah ya huci zuciyarka ranka ya dade ai idan aka Bari har aka fita da yarinyar Nan zuwa wani waje Domin rukonta munyi asarar ladan da muke samu ta sanadiyyarta bazan taba bada goyon baya a fita da yarinyar Nan daga gidan nanba"...

Harara kawai hajiya babba ke jifan ummu da shi,Jin furucin da tayi,

"Yanzun ke zainabu nasan kinada hankali Kuma kin girmi rahina kinsan ya kamata inaso ki fadamun yau abinda ya faru a cikin gidan Nan a gaban kowa Dan banaso daga baya inji wani gutsiri tsoma Yana tashi...

Murmushin Jin Dadi hajiya zainab tayi sanan ta gyara Zama murya kasa kasa ta kwashe kaf abinda yafaru Wanda tagani a idanuwanta ta fadawa Mai martaba sanan ta Kare maganarda "dama da Naga haka shine na yanke hukuncin yanta yarinyar ta dawo hannuna da Zama tunda ni dama Allah be bani haihuwar ya mace ba sai in riketa har zuwa lokacinda zaayi aurenta da shi kabirun,...shine nakeso a yanta ta"
Chapter 50 · 0% Book details