← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 80

Sashe 66

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi yarima ya sauke a hankali sanan ya furta cikin sanyin murya "shikenan Amma gaskiya saina koyawa Fatima hankali"...

"Bance idan mutum yayi laifi Kar a hukuntasa ba Amma a rinka Sara ana duban bakin gatari,....yanzun abinda zaayi ni Bari inje tunda dama inada office karfe Sha daya gashi yanzun har karfe goma gone idan Allah ya kaimu sai muje koh?"ya karashe maganar hade da mikewa Yana duban agogon hannunsa,

Mikewa yarima yayi ya bi bayan Ahmad har kofar gate ya rakashi inda yayi parking motarsa,....Fatima na hangensu ta sama a tsaye a jikin window,Tana kallo har Ahmad ya tada mota yarima ya juyo da nufin shiga gida,da sauri ya daga kansa sama setin windown Fatima Nan da Nan ta saki labule ta koma jikin bango tsaye ta dafe gefen zuciyarta dake bugawa sauri da sauri,....tsaki yayi don ya hangeta Sarai lokacin data saki labulen yayi cikin gida abunsa cike da bacin Rai....

*********

Koda ya shigo gidan ba kowa a parlor sai TV dake faman aiki ya je ya kashe tv din yayi shigewarsa bangaren deejahmah dikda yadda zuciyarsa ke axalzalarsa da soyayyar Fatima Amma hakan be hanasa zuwa inda zai huce haushin takaicinsa ba,

.
Tana zaune Kan kujerar madubinta Tana tsara kwalliya ya tura kofar ya shigo da sallama ciki ciki ya maida kofar ya rufe,..

Binsa tayi da kallo har Kan gado inda ya nemi waje ya zauna ya dafe kansa zuciyarsa cunkushe da takaici da bakin ciki,

Murmushi ta sauke ta Mike tsaye ta gyara daurin towel dinta dake makale jikinta iya saman cinyarta sai tashin kamshi takeyi ta taso Tana kwarkwasa har inda yake zaune,sai kawai tasa hannu ta cire Masa tagumin Wanda yasa shi dago jajayen idonsa ya sauke Mata su ,wani killer smile ta sakar Masa hade da nadewa saman cinyarsa ta zagayo da hannunta ta bayan wuyansa Tana kallon fuskarsa,cikin shagwaba tace"Haba yaayah dik fushin ne?ummM?kayi hakuri nidai nadaina insha Allahu kaji?"tayi Rau Rau da idanuwanta Tana kallonsa ,

Jinjina Kai yayi hade da sauke ajiyar zuciya yasa hannu ya tallabo kanta ya hada bakinta da nashi ya shiga tsotsa cikin wani irin salo Yana shafa wuyanta Tana Kara narkewa a jikinsa,ganin haka ya sashi Jan towel din jikinta ya shiga warwareshi tsaf....sai kawai ya jata suka fada Kan gado still bakinsa Yana Kan lips dinta Yana kissing hade da shafa ko Ina a jikinta,.....tun Bata maida Masa martani ta Soma Jin hannuwansa a Kan kirjinta Yana Mata wasanni Nan da Nan ta Soma sauke numfashi sama sama.....shiko yarima baa cewa komi jikinsa har rawa yakeyi saboda tsananin shaawar data taso Masa gadan gadan.....take Saida ya biya bukatarsa sanan ya kankameta a jikinsa Yana sauke numfashi....lumshe idanuwansa yayi lokaci guda Fatima ta fado Masa....tun jiya ya banbance tsakanin Fatima da deejahmah ko wacce da baiwar da Allah yayi Mata ,Abu daya ne jiya ya kasa gasgatawa sai yau da ya Kara kebewa da deejahmah ya tabbatar ba dadinsu daya da Fatima ba,....baya taba gajiya da Fatima har bayaso ya kawo idan Yana tarayya da ita saboda tsananin Dadi da niima da baiwar da Allah yayi Mata Amma deejahmah minti Sha biyar yayi yawa yayi realising a tare da ita to me hakan ke nufi?....bayajin dadin muamalar aure da ita kamar Fatima dikda itama deejahmah tanada nata niimar Amma ba kamar Fatima ba,....runtse idanuwansa yayi lokaci daya Dan tunanin Fatima da yayi wata sabuwar shaawarta ce ta bijiro Masa...

Sauke numfashi. Da yakeyi yasa deejahmah saurin dago kanta Tana karewa fuskarsa kallo wadda idanuwansa yake a rufe Yana numfarfashi,..hannu tasa Tana shafa sajen fuskarsa a hankali tanayi Masa waiwayi....hakan da takeyi Kara tada Masa da hankali takeyi saidai bejin zai Kara maimaita wani Abu a yanzu Kuma,sai kawai ya bude idonsa ya saukesu Kan fuskarta Yana kallonta Tana kallonshi fuskarta ta shigayi Masa gizo data fatima wadda idan Yana kallonta take runtse Ido Tana murmushi Mai kayatarwa saboda kunyarsa Amma ita Sam deejahmah Kara kallonsa ma takeyi....

Gira daya ya daga Mata ya janyota saman kirjinsa ya tura hannunsa a Kan kirjinta Yana shafawa Tana lumshe Ido haka bacci ya dauketa....Saida yaga tayi bacci sanan ya sauketa ya kwantar ya rufa Mata bargo....ya fice a daki,...

*********

Tsaye yayi a kofar dakin Fatima Yana sauraren saukar numfashinta dagaji ko baa fada ba kuka takeyi...

Sauka yayi kasa ransa Babu Dadi dakyar yake daga kafarsa haka ya nufi side dinsa Yana shiga ya fada toilet yayi wanka ya fito ya shafa Mai sama sama ya dare gadonsa ya lumshe idanuwansa abubuwa da yawa sunayi Masa yawo akai...

********

Bacci ne ya dauke Fatima Akan daddumarta bayan ta idar da sallah,Tana baccin ne Amma ajiyar zuciya take saukewa dikda sama sama yake figarta sai wajen karfe biyu ta tashi baccin sanan ta fada toilet tayo wanka ta zo gaban madubi ta zauna dikda yadda fuskarta ta canja saboda tsananin kuka Amma hakan be hanata Zama ta gyara fuskarta da powder ba ta canja kayanta ta sauya wasu hadaddiyar doguwar Riga ce a jikinta maroon Mai ado da stones masu kyakkyali da Haske ta dauko kwalli ta zizara a idanuwanta Wanda suke farare tassss tamkar Madara,kwalin ba karamin kyau yayi mataba (kwalli sirri ne na musamman da yake karawa Mata kyau)

Yane kanta da bakin gyale tayi ta dauko wayarta ta fito ta rufo koferta,

Waje tasamu ta zauna a parlo,gefenta zaituna ta zauna ta shiga matsa Mata kafafuwanta Tana game a wayarta,

Tsaf deejahmah ta shirya ta fito Tai shegen kyau rahane na biye da ita ta tsaya a parlorn Jin karar rufe kofar yarima Wanda shima a shirye ya fito yayi matukar kyau,

Fatima na zaune Tana game a wayarta,ko ta kansu batayi ba tanajin lokacin da deejahma ta kashe murya tace "ranka ya dade na fito"

"Owk"kawai yace a takaice har ya juya ya dawo ya wuce deejahmah ya shige parlon,har lokacin Kan Fatima a Kan wayarta yake,ya dade a tsaye a kanta sanan yayi gyaran murya fuskarsa a daure "kitashi muje gaida gwaggo rahi dake"

Dago eyeballs dinta tayi ta kallesa sanan ta kauda kanta tace "kuje kawai Allah ya tsare"

"Karki Bari in Kara magana ki Mike mutafi kawai ko daki ban baki umarnin shiga ba"yadda yayi maganar fada fada sai ya Bata mamaki da tsoro yasa ta Mike tacewa zaituna "muje koh?"

"Toh ranki ya dade"

Bakin ciki ne ya lullube deejahmah Jin yadda yarima yayi da Fatima har tana cewa bazata zo ba Yana wani cewa sai taje sai kace gidan ubanta....gaba tayi abinta cike da takaici

********

Horn driver yayi masu gadin gidan galadima suka bude gate motoci suka shiga cikin gidan guda uku,daya nasu yarima da matansa daya na kuyanginsu daya na excort dinsu dogarawa....

Gaba abinta deejahmah tayi Bata tsaya jerawa dasu ba a babban parlor ta tadda mahaifiyarta da kanwarta baby da murnar ta take fadin "yeee mama gani nazo ganinki"

"Lake marhabun da zuwan sarauniyar masarautar barayar Zaki....barkanki da zuwa diyata"

Fatima dake bayansu ta amshe da "yauwa ranki ya dade naji Dadi da wanan tarbar"

A fusace hajiya rahina tace "ke Kuma asuwa?uban waye ya baki damar zuwa mun gida ma tukunna?"

Murmushi cike da kasaita Fatima tayi ta nemi daya daga cikin kujerun gidan ta zauna ta Dora kafarta daya Kan daya fuskarta dauke da murmushi "nazo gaida uwa a gareni ne tunda ai matsayin surukata kike Kinga kuwa inda mutunci kedin uwata ce"..

Tana rufe baki yarima yayi sallama cikin parlorn Wanda yasa hajiya rahina yin Yar dariyar yake dikda kasan zuciyarta mamakin Fatima da al"ajabinta ne kwance...

"Barkanki da yamma ranki ya dade"....yarima ya katse Mata tunani,

A wayance ta juya bakinta na rawa hade da inda inda tace"umm ammm barkanka dai kabiru ya Iyali?"

'alhandulillahi"yace kansa a kasa.....

Hada Ido rahina tayi da Fatima take ta sakar mata wani malalacin murmushi Tana kada kafafuwanta...

Samm yarima ko kallon Fatima beyi ba Dan be lura da irin zaman da tayiba saboda yadda ya dau fushi da ita...

"Zauna Mana kabiru?ko kaje parlon babanku"

"To"kawai yace a takaice ya Mike ya fice....

Cikin daki deejahmah tayi mahaifiyarta ta rufa Mata baya...kallo Fatima ta bisu dashi ta tabe baki Tana Kade kafa,

A can cikin daki gwaggo rahi ce suke tattaunawa da diyar Tata Tana Bata labarin irin zaman da sukeyi...

"Kina nufin kenan abinda muka kashe kudi akayi be yuwuba?Kuma beyi aiki ba?"

Dan Bata fuska deejahmah tayi "be yuwuba wallahi mama Amma yanzun abinda na fahinta shine yarima besan kissa ba to da ita zanyi amfani inyita hadasu fada Dan yanzun haka ba shiri sukeyi ba"

Yar dariya gwaggo rahi tayi "yauwa deejahmah ai nasan Babu inda kika Bari a halayena,Dan haka karki kuskura kibari ta kwace Miki miji kicimun uban shegiya...Koda yake ba uba gareta bama"

Dariya suka kwashe dashi har parlor Fatima na jiyosu,

Sun kusan Awa daya tare ciki sanan suka fito fuskokinsu dauke da farin ciki,

"Ni bansan wace irin mayya bace wanna yarinyar,yanzun ke da kikeda gidan uba ma sai an biyoni Dan zakije gidan ubanki?meyasa ita bazataje gidan ubanta ba"

Dariya deejahmah ta sheke dashi Tana tafa hannuwanta "kin manta Wai batada uba?iyayen ma tanadasu ne?kaji mama da wata magana"

Harara hajiya rahina ta Kara watsawa Fatima "af na manta fa shegiya ce Yar gaba da fatiha"

Ran Fatima ba karamin baci yayi ba zuciyarta na tsananin yi Mata suya Nan da Nan idanuwanta suka kawo ruwa ta Mike ta kallesu tamkar zatace wani Abu sai ta fasa ta fice zaituna ta rufa Mata baya,

Dariya dukkansu sukeyi sanan suka zauna Kan kujera suna Kara tattaunawa inda hajiya rahina ta dauko wani Dan kulli tabawa deejahmah ta rada Mata a kunne...

Yarima ne yayi sallama a dakin ya shigo"ku fito mutafi"

Waigowa yayi inda yasan Fatima ta zauna saidai be ganta ba,

"Ina fatimar?"

Ya tambaya Yana kallon deejahmah,....Saida ta kauda kanta sanan tace "ai ta tafi mota tun tuni Wai bazata iya zamana don Kai ka matsa Mata ma tazo tunda ba gidan ubanta bane"
Chapter 66 · 0% Book details