Sashe 41
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dakyar ta iya farfadowa daga sumar zaunen da tayi ta motsa bakinta a hankali ta Soma magana"Allah ya baka yawan Rai banida iko da zan ja da hukuncinka Koda hukuncin kisa ka yanke mun,ballantana kasancewa ka adalin sarki uba a gareni kayimun zabi in iya bude baki ince bana son wanan zabin,hakika Kai adalin sarkine Mai kaunar al'ummarsa da ace duka sauran masu mulki haka suke da irin halayyarka da sai mu kirasu da Yan aljannah,....na daukeka tamkar uban daya tsugunna ya haifeni saboda haka dik hukuncin daka yanke akaina daidaine mahaifina".....
Hakika zancen Fatima ba karamin Dadi yasanya Mai martaba ba, yarinya ce Mai cike da ladabi da hikimar iya magana,wadanan kalamai datayi sunkara sa Mata tsantsar kaunarta a cikin zuciyarsa jinta yakeyi tamkarsu khausar da afnan,shi kansa Mai martaba murmushi yaki gushewa daga fuskarsa sai jinjina Kai yakeyi alamar Jin Dadi yace "Allah yayi miki albarka Yar aljannah"
Ta Kara durkusawa cike da ladabi tace'ameen ranka ya dade nagode Allah ya Kara maka lafiya da nisan kwana"....
Jinjina Kai kawai Mai martaba yakeyi Yana murmushin Jin Dadi sanan ya juya ga matansa dake gefe ko wacce kanta a kasa yake Tana sake sake...
"Idan akwai wata Mai abin cewa zata iya magana kofa a bude take"
Dago Kai hajiya babba tayi fuskarta a daure tamkar Bata taba dariya ba zuciyarta tafarfasa kawai takeyi wani kululun bakim cikine dankare cikin zuciyarta takasa boye hassadarta a Fili idanuwanta sun kankance dakyar ta bude baki tace"ka rigada ka yanke hukunci bamuda yadda zaayi muja da hukuncinka ranka ya dade Amma tabbas an cutar da Khadija da mahaifiyarta a wanan tafiya Amma Babu komi akwai Allah idan ma akwai wata makarkashiya da akeyi,to ko ba dade ko ba Jima zaayi walkiya asirin kowa saiya Tonu wallahi"
Harta Dora Aya Akan xancenta Mai martaba idonsa na kanta Saida tayi shiru Sanan ya Bata amsa da "naji maganganunki hajiya Amma fa kisani ban taba yanke hukumci na warware wannan hukuncin ba Saida kwakkwaran dalili saboda haka maganar da kike fadin an cuci rahina da yarta,ita raheenar Naga Yar uwatace jinina ce kuma inada damar da zan Yankee hukuncin dik da nagadama akanta da di'yanta bata Isa tayi maganaba saike to dik abinda kikaga yadace kuyi keda raheenar"
"Allahhh ya huci zuciyar Mai martaba"....cewar waziri dake gefen sarki Yana sauraron komi.....
Shiru ne ya biyo baya na Dan lokaci ganin Babu Wanda zaice komi Mai martaba yabawa waziri izinin rufe taro da addua,Babu Bata lokaci waziri ya kawo Fatiha da salatin annabi taro ya tashi......kowa ya shiga mikewa jiki Babu kwari Ana fita daya bayan daya,Saida kowa ya watse sanan Fatima ta Mike Tana dingisa kafarta ta fice,tafe take jikinta a sanyaye zuciyarta ta karye,Bata taba tunanin hukuncin da Mai martaba zai yankeba kenan dik tunaninta ya Kare Akan zaisa a koreta a gidansa,sai gashi yayi bazata,yau itace Fatima zata auri Dan sarki?Kuma sarki a Nan gaba?Allah buwayi gagara misali kenan.....ajiyar zuciya ta sauke data tuno da babban bala'i dake tunkarota.....tabbas tasan akwai yaki babba a Nan gaba...tafe take Tana tunani har takaraso kofar shiga sashen cikin gida Wanda Dole ta babban parlor zata wuce jikinta na rawa zuciyarta na dar darr haka ta shigo bakinta dauke da sallama a zuciyarta Kuma Babu abinda take janyowa sai innalillahi wa Inna ilaihi rajiun.....
Cirko cirko suke tsaye cikin parlorn deejahmah ce jingine Tana faman rusa kuka tamkar an Aiko Mata da mutuwa a haka Fatima ta shigo cikin parlon zata wuce Taji muryar hajiya babba cikin daga murya "keeee"....cakkk Fatima ta tsaya tsaye zuciyarta na harbawa sauri da sauri....Bata ankaraba Taji an fizgota da hijabin dake jikinta an nannadeta hade da shake Mata wuya deejahmah ce a haukace "wallahi baki Isa ki auremun mijiba kina baiwata,baki Isa ki shigo gidan Nan kice zakiyi kishi Dani ba a matsayinki na kucaka renon titi tsintacciya,wadda akayi cikinta a kwararo aka wurgar da ita a bakin hanya".....duka deejahmah take kaiwa Fatima ta ko Ina,a zuciye ta hankadeta kasa ta Fadi take idonta ya sauka Akan kafar Fatima dake kumbure tadanyi baki cikin zafin nama deejahmah tasa kafa ta take kafar..... wata gigitacciyar kara Fatima ta saki saboda tsananin azabar da ta ratso kwakwalwarta xuwa tafin kafarta.....ganin haka yasa deejahmah ta Kara take kafar......shiru Fatima tayi hade da lumshe idanuwanta azaba na ratsata ta ko Ina wani hawayene ya gangaro ta gefen idonta Tana ambatar sunan Allah a bakinta...... network din kanta gabaki daya ya dauke idanuwanta suna rufe hawaye na gudu....
Takowa hajiya babba tayi har inda Fatima ke kwance ta tsaya akanta....."wallahi tallahi sai kin gwammaci Harbin kunama dik second goma akan zamanki cikin wanan gidan,sai kin gwammaci haka kabari ki binne kanki da kanki zaifi Miki sauki Akan gigin auren kabiru da zakiyi.....azabar da kikasha a farko kadan ce akan wadda zakisha Nan gaba wallahi tallahi matukar kikace Zaki cigaba da zaman gidan Nan nayi Miki alkawarin nadama"...
Juyawa hajiya babba tayi ta nufi sashinta yayinda hajiya rahina da deejahmah suka rufa Mata baya....
********
"Wai malam yau Ina kajene bayan laasar na shigo dakinka na tarar bakanan na leka windon baya na hangeka Kanata sauri kayi Nadi sai nai tunanin ko fada kaje"....
Ludayin furar da waziri ya dibo yakai baki Saida ya kurba sanan ya ajiye,ya canje kwanon silvar da yakeshan furar dashi gefe,Saida ya hadiye furar dake bakinsa sanan yasa hannu ya shafa gemunsa yayi shiru na Yan dakiku sanan yayi ajiyar zuciya yace "kaiii innar fauziya yau Mai martaba yayi wani abinda ko a mafarki bantaba tunanin hakan zai kasance ba"
Gyara Zama matar waziri tayi Tana fuskantarshi sosai "malam fada kaje kenan meyafaru?wani Abu yasamu masaraunta ne?"
"Rigima ce dai Nan gaba kadan zata balle Domin Mai martaba ya amincewa kabiru da ya auri yarinyar Nan data kashe habibu,wadda rukonta yanzun haka a gidan akeyi'
Zaro ido Inna tayi waje Tana kirkida Kai "tabdijan lallai Mai martaba ya Dasa bomb dinda idan ya tashi fashewa hardashi zai fashe"ta cigaba da jinjina Kai take fuskarta ta sauya zuwa tsananin hassada da bakin ciki,Tana jujjuya Kai Tana jinjina lamarin sanan ta sauke ajiyar xiciya ta cigaba da magana "yanzun ya maganar auren deejahmah da kabiru "
Sauke hularsa yayi gefe wadda yayi Nadi da ita sanan yace "ehh to maganar na Nan Domin Nanda sati uku zaayi bikin da Mai martaba ni yaba kwangilar ginin gidan da khadeejah zata zauna da ita kanta fatimar kinsan gidan nasa akwai girma da fadi Dan na tabbatar zaa iya Gina gidajen sama biyar ma zuwa bakwai Nan gaba"
Murmushi kawai innah keyi na karfin Hali ita kadai tasan abinda yake boye cikin birnin zuciyarta,Domin dik maganganun da mijin nata yakeyi sauraronsa kawai takeyi zuciyarta na can wani waje daban.....
Faizah da fauziyya wadanda kamaminsu suka baci da juna suke zaune cikin dakinsu suna zancensu na Yan Mata ,
"Nikam fauziyya kinsan wani Abu?"
Dago Kai fauziyya tayi daga kwancen da take Tana faman chat ta kalli Yar uwar Tata tace"umhmm Ina sauraronki meye Kuma?"
"Wallahi Harga Allah Ina kaunar wanan fatimar,ni Dan inajin tsorone da wallahi na rinka zuwa wajenta Ina Bata taimako don Allah ya hadata da kajaga,zan kulla kawance da ita"
Wani malalacin murmushi fauziyya tayi sanan ta yunkura ta zauna ta watsawa Yar uwarta harara "to kwadayayya,kinji labarin zata auri Dan sarki kenan shiyasa zakije ki fara manne Mata tun yanzun?"
Murmushi faizah tayi wadda ta kasance itace hassana tace"wanan ke ya dama ni bedameniba kece dama kike sonsa ni be taba burgenba ita Kuma da kikaji nace Tana burgeni Harga Allah Ina kaunarta ne"
"Ki tattara kayanki ki koma gidan kuyi bauta tare karewar kauna kenan mtsww"
Dik hirar da sukeyi mahaifiyarsu na tsaye Tana sauraronsu,Domin ita kanta abin ya dameta tunda waziri ya sanar Mata zuciyarta ke yi Mata saka da warwara Akan yakin biyu zai zame Mata Amma na Fatima me saukine Dan ba power garetaba kamarsu deejahmah saidai batasan hanyar da zatabi ba tayi yakin Fatima Dan Dole Saida Wanda Fatima ta yarda dashi,inko haka ne faizah na kaunar Fatima to ita da fauziyya zatayi amfani tunda kamarsu daya sakkk har maganarsu iri daya ne Kaya iri daya suke sawa Dole zatayi amfani da wanan damar wajen yiwa Fatima Wasa da hankali......ajiyar zuciya innah tayi ta shigo dakin da faraarta dauke da fuska wacce iya lebenta kawai ta tsaya,
Gefen gadon faizah ta zauna Tana murmushi "Yan biyun innah zancen me akeyine Wai tun dazun ina sauraronku sama sama"
Da sauri fauziyya ta karbe zancen "Wai faizah ce kecewa Tana kaunar Fatima tsintacciya"ta karasa maganar da harara...
Murmushi Inna tayi "to ai Mai saukine fauziyya ki kyaleta suyi amincinsu ai kaunarta takeyi Kuma idan jininsu ya hadu ai shikenan"
Murguda baki fauziyya tayi want kululun takaici ne ya tsaya Mata a wuya don me innah zatace haka?,ita kuwa faizah fuskarta ta fadada faraarta "nagode innah gobe zanje gidan"....jinjina Kai Inna tayi Tana faraa tace"hakan nada kyau,yanzun ki Mike ki hadamun dambu gashican yau malam yace shi yakesonci saura kuma fauziyya ki batamun girki in gamu dake Dan nasan halinki"....
Kunkuni fauziyya ta shigayi yayinda faizah takai hannunta Kan wayarta ta janyo ta kunna karatun kur'ani ta fice ta nufi kitchen din....
Kallo innarta tabita dashi Tana murmushi,....mikewa tayi ta dawo gefen fauziyya ta janyota jikinta ta rungume Yar Tata Tana lallashinta,Saida ta tabbatar ta saukar da ita sanan ta shiga rada Mata maganganu kasa kasa,.....Nan da Nan fauziyya ta koma dariya harda kyalkyalewa......Niko Ina gefe sai zare Ido nake da kumburarren hannuna😜lol
********
"Yanzun tunda burinka ya cika friend zaka auri Fatima,to ya Zama wajibi ka cika umarnin Mai martaba nayin adalci a tsakaninsu Dan kaima da naka iskancin,Dan idan bera da sata daddawa nada wari"
Dage girarsa yarima yayi sanan ya saki wani malalacin murmushi yace "wanan Mai saukine Amma kasani zuciyata kwaya daya ce tal da ruhina kuma Fatima suke kauna,wallahi bazan iya hada son wata Diya mace da son da nakewa bintu ba"....yanzun haka ita nakeson gani Domin nasan Tana can Tana kubar azaba,bedameniba tunda ko naji ciwon abun dole xan lallashi abuna"
Kallon juna sukayi suka sheke da dariya hade da tafawa,dakyar Ahmad ya tsagaita da dariyarsa yace "angon Khadija da Fatima"