← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 80

Sashe 80

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan Yan jawabai da Mai martaba ya Kara Nan aka Shiga gudanar da liyafa Wanda sarki ya shirya Domin murnar dawowar mahaifiyar Fatima Sanan ya roki iyayen zahrau da Subar zahrau ta zauna a masarautar a sashen da zaa Gina Mata nata daban da masu hidimarta kasantuwar tanada gado a gidan nata Dana yarta da Wanda sarki abdallah ya bada wasiyyar Bata Koda ansameta a raye...

Bayan komi ya Lafa wajen yamma Fatima ta baro sashin ummu ta nufo sashin cikin gida direct bangaren hajiya babba ta Shiga,

Zaune ta sameta a kasan carpet Babu kowa a bangaren ta tayi shiru,

Tsaye Fatima tayi a kanta Tana dubanta shekeke,

"Ranki ya dade sarauniyar sarkin masarautar barayar Zaki,yau Ina sarautar?Ina mulkin?sanan Ina jiji da Kai?Ina cikar asalin Taki?Ina hadimanki da bayinki hade da kuyanginki wadanda kike sawa ki Hana dik Ina suke?shi kanshi auren naki Ina yake?....."

Ta sunkuyo ta dago fuskar hajiya babba Tana Kare Mata kallo cike da faraa "naso ace kin dawwama a cikin farin ciki a cikin daular mulki saidai son zuciya da rudin duniya da kururuwar shedan ya janyo Miki babbar asarar da na tabbata cikin awannin da suka shude kinyi Dana sani yafi sau million hajiya.....yau Ina asalin naki?na tabbatar da son zuciya irin naki yasa kin guji danginki saboda daukar mulki yau gashi an wayi gari Babu ko daya Zaki Kare a zaman kurkuku kurkukun ma na masarautar da kika zuba mulki a da.....yau Fatima wadda ta kasance shegiya Mara asali Yar kwararo itace Mai mulkin da kike takama dashi...mshiyasa idan zaka Gina Ramin mugunta ka ginasa daidai kwaurunka wata Kila ya rufta da kai to gashi ke Ramin miguntar naki ya rufta dake ya zame Miki kabari....a karshe inaso in sanar dake cewa ni saina shayar dake azaba fiye da wadda kika shayar Dani....a dakin da Zaki zauna a kurkuku nasa an cikasa da kunamu masu harbi saboda inaso in dandana Miki irin azabar Harbin kunama"....

A fusace Fatima ta juya saboda tsananin bakin cikin da takeyi idan ta dubi hajiya babba,da sauri ta ruko kafafuwan Fatima "ranki ya dade ki taimakeni karki mun azaba ki tallafi rayuwata wallahi summa tallahi nayi danasanin abinda na aikata"ta karashe maganar tare da kukan nadama,

"Au har na Zama ranki ya dade kenan?tun kafin aje ko ina?yau Fatima baiwarki da kike wulakantata a idon jamaa yau ita kika Rika kafafuwanta kina neman gafararta koh?hmmmm bakiga komiba sai bayan shekara biyar kin Zama baiwata nida yayana in aikeki daga kitchen zuwa dakina insaki kiyimun abinda na gadama Ina zaune na harde kafafuwa Ina tare da mijina da yayana da kishiyata zakisha mamaki Amma yau tabbas kwana Zaki kunamu suna harbinki"...

Rukota hajiya babba ta karayi tasa kafarta ta take hannun hajiya babba Wanda Saida ta saki Yar Kara....

********
A kurguje bayan watanni biyar da faruwar hakan komi ya Lafa,

Fatima na zaune da cikinta Dan wata takwas Wanda ya girma haihuwa ko yau ko gobe itada deejahmah ne zaune a parlor suna kallon wani series film,

Yatsina fuska Fatima tayi tana Dan cijewa,

"Yadai Fatima?mekike bukata?ko abun yazo ne"

Girgiza Kai kawai fatima tayi ta saki kukan shagwaba ....Nan da Nan hankalin Deejahma ya tashi ta dauki wayarta ta Kira yarima,

Yarima Yana tare da Ahmad sunje siyayyar kayan aure na Ahmad da bilkisu wadanda tuni suka daidaita kansu sanan rukon bilkisu gaba daya ya koma hannun mahaifiyar Fatima zahrau tamkar itace ta haifi bilkisu haka takeji,

Daukar wayar yarima yayi Yana fadin "menene kuma?badama in fita Kun rinka kirana kenan"

"Uwargida keda bukatar mijinta a kusa da ita Dan yanzun haka kuka tasamun narasa yadda zanyi da ita shine na kiraka"

Dafe kansa yayi "shikenan gamunan zuwa"...ya datse wayar

"Yadai abokina?"Ahmad ya tambayi yarima

"Rigimar Fatima ce ta motsa Wai kuka takeyi so takeyi inje gidan kawai tasamun rigima Wai incire Mata cikin da nayi Mata kaji fa?Haka tamun jiya wallahi dakyar na lallasheta"

Dariya sosai Ahmad keyi "to Kai waye yace ka Mata cikin?"ya tambayesa cike da zolaya....dariya dukkansu sukasa...

********
Bayan wata daya a yau ya kasance jumaa yau ne Kuma alkawarin Allah ya cika Fatima ta haifi yaranta biyu dik maza kyawawan gaske masu kamanni sakk da ubansu identical twins wadanda tsabar kamanninsu yasa akayi musu sheda,

Fatima taga tsananin gata wajen wanan family din gabaki daya ba karamin hidima akayiba tun daga haihuwar Fatima har ranan daya kasance ranan bikin suna...komi da akayi a wajen deejahmah ce ta shiryashi itada kawarta Sunita wadda dama tun yarinta suke tare Dan haka tare da ita akai hidimar suna....sosai jamaa suka hallara wadanda basu samu damar zuwa bikin Fatima ba saboda yadda akayi bikinta Babu shiri,....masoyan Fatima Basu faduwa Dan hussy luv tun ana jibi suna ta dira a gidan Fatima itada Hindu dasu akai komi Naga wasila getso (waseey)ta halarci bikim suna da yawa ma masoyan Fatima Basu faduwa a wajen sunan Nan inda yarima yayita barin kudi da kyaututtuka kakannin Fatima ma baabarsu a bayaba Dan Inna wuro shanu dari ta bawa Hasan da hussaini wadanda sukaci sunan Umar da aliyu.....

*********
Hajiya babbace ke zaune dik ta fita hayaccinta tayi bakinkirin ta rame gabanta robar abinci ce Wanda ake Bata shi Babu Dadi haka takeci maganin yunwa

Turo kofar akayi da kafa Fatima ce ta shigo Hassan da hussaini na sagale a kafadarta gabanta da bayanta dik hadimanta ne da escort dinta,

Tsayawa tayi tanabin hajiya babba da Ido sai cannn ta nisa tace"nakawo Miki jikokin sarki ne wadanda suka fito daga cikin shegiya kigansu magada mulkin ubansu"

Hawaye hajiya babba ta Shiga matsowa a idanuwanta hade da shasshekar kuka Wanda baya fitowa saboda tsabar wahalar da take ciki,

Dik jikinta yayi rudu rudu tamkar me borin jini ga wari da takeyi na rashin wanka,

"Kukanki da kwallarki Basu zasu sa inyafe Miki laifin da kikamunba Domin kukanki ma Kara tunzurani yakeyi Dan kece sanadiyyar da narasa ubana....inda bakisa anbi uwata akashe ba da ubana be Shiga matsanancin Hali ba Wanda ya saukar Masa da mummunan ciwon da yayi ajalinsa Dan haka ki shirya kuka Dan vaki Gama kukaba tukunna ma,Dan Mai martaba ya mance da wata halitta safita...."...Tana Gama fadin hakan ta juya abinta hade da tsirtar da miyau...

********
Bayan shekara uku Fatima na dauke da wani cikin yayinda Hassan da hussaini sunyi girma sunyi wayau Kuma rukonsu gabaki daya Yana wajen deejahmah Dan tsakaninsu da uwarsu saidai idan sunje gaisheta,

A wanan shekarun ko batan wata deejahmah batayiba balle asa ran zata haihu Wanda hakan ba karamin damuwa ya haifarwa da Fatima ba kullum cikin yi Mata addua take na Allah ya Bata tunda ga bilkisu Nan Dan yarta surayya Tana goyo...

Fatima Babu dadewa ta Kara haihuwar mace inda yarinyar taci sunan deejahmah wato Khadija akai Mata takwara tayi tsananin farin ciki da hakan Taji dadin karar da yarima da Fatima sukai Mata Kuma ta gode musu,

*******
Bayan wata biyar da haihuwar Mimi wato deejahmah karama itama Deejahmah Allah ya Bata nata Rabon murna a wajen wanan family din baa magana tuni labari ya Isa ko Ina cewar deejahmah na dauke da ciki kowa yayi farin ciki da wanan labari.

Anata shirye shiryen bikim khausar da afnan da Maryam da faizah da fauziyya deejamah ta haifi yarta mace Nan itama ta roki yarima yasawa Yar Fatima suke kiranta da Noor......

Zaman lafiya da kwanciyar hankali ne ya wanzu a cikin wanan masarautar inda dik wata Fatima sai ta kaiwa gidan marayu taimako ta dubasu ta tallafawa rayuwar yaran dake cikin wanan gidan Wanda ya zame Mata gidan tarihi.....

*ALHAMDULILLAH*

DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH DAYA BANI DAMAR YIN WANAN RUBUTU ALLAH YASA MU AMFANA DA DARASIN DAKE CIKI KURAKURAN DAKE CIKI KUMA ALLAH YA YAFE....NA SADAUKAR DA WANAN LITTAFIN GABAKI DAYA GAREKI FATI DAN MALIKI KAUNARKI A CIKIN ZUCIYATA TAKE HARABADA KEDIN MASOYIYATA CE TA HAKIKA MEENARKI NA KAUNARKI DAN ALLAH ALLAH YA BARMU TARE....

INA MIKA GODIYATA GA DUMBIN MASOYA WANAN LITTAFI NASAN BAZAKU KIRGU BA SHIYASA BAZAN IYA LISSSFA SUNANKU BA AMMA KUSANI A DIK INDA KUKE INA KAUNARKU SOSAI.....

GODIYA TA MUSAMMAN GAREKI UWA TA GARI ABAR ALFAHARIN KO WACE DIYA DIK WADDA TASAMEKI A MATSAYIN UWA HAKIKA TA MORE....BANIDA KAMARKI A KULLUM INA FADA BILKISU MUSA GALADANCI ...SLIMZY DIYARKI CE HARABADA....

NAGODE SOSAI HAUWAU MUAZU AMIR (UMMU AFEE)MASOYIYA TA HAKIKA TUN YARINTA INA KAUNARKI.....ALLAH YA RAYAMUM ADNAN YAR AMMIEY SLIMZY....

NAGODE

SLIMZY😍
Chapter 80 · 0% Book details