← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 80

Sashe 27

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kinga na mance ma wallahi wadda zankira aba tasa nakeso in fada Mata aikinta"

Murmushi matar waziri tayi Tana Yan dube dube don abinda ya kawota Taji daya saura daya ta bude baki zatayi magana kenan hajiya babba ta kwalawa saade Kira da sauri ta shigo ta zube a kasa kamar Tana jira tace"gani ranki ya dade"

"Kiramun Fatima"

Mikewa saade tayi da sauri ta tafi neman Fatima,

Tana tsaye jikin wata Yar baranda kusa da toilets din maaikatan gidan a Nan ta sa kaya Tana tsaye ta yane kanta da wani Dan gyale Tana sanye da doguwar rigar material ja tayi matukar karbar fatar jikinta,

Dafe habarta saade tayi Tana jijjiga Kai Tana kallon Fatima ta tabe baki tace"kizo hajiya nayi Miki Kiran gaggawa"

Saida kirjinta ya buga Jin abinda saade tace,Bata tsaya neman hijabi ta ba tabi bayan saade jikinta na rawa faduwar gaba ta tsananta,

A tare suka shigo dakin daga hajiya babba har matar waziri sakin baki sukai suna kallon Fatima da suturar dake jikinta ga wani annuri na kyau na fita a fuskarta durkusawa tayi har kasa tace"gani ranki ya dade"

Jijjiga Kai hajiya babba tayi Tana karewa Fatima kallo tace "ehh lallai kin nuna Mana ainihin ke wacece marainiyar Allah itace sanye da tsadaddun Kaya na alfarma shiyasa ko kurani kabiru zai hadiya bazan yarda da cewa ke tsintacciyar mage bace,hakkinmu ne yasama aka tsundumo dake gidan Nan kika kawo kanki da kanki"....kayan dake gefenta ta watsawa Fatima ta cigaba da cewa "bakizo Nan gidan Dan ki zauna kiyi kwalliya ki saki jiki kiyi Mana karuwanciba bakida sutura a cikin gidan Nan data wuce wanan ta kuyangi daga yau kin tashi daga Fatima kin koma kuyanga"...

Da sauri Fatima ta dago Kai saboda kalmar dataji hajiya babba ta fada sai tayi maza ta sadda kanta kasa,

Hajiya babba ta bude baki zatayi magana taga bayi na shigowa da Kaya leda leda, sanan sallamar Ahmad da yarima ya dakatar da ita daga maganar da take shirinyi,

Karasowa sukayi suka tsugunna suka hada baki wajen gaishesu itada matar waziri wadda ke faman raba idanuwa,

Shiko yarima satar kallon Fatima yakeyi don bakaramin kyau tayi masaba idanuwansa yakai hannunta da ke rike da wasu jajayen Kaya irin na kuyangi kanta a kasa batamasan yanayi ba...

"Mike kije ki canja wadanan kayan na jikinki kisa wadanda suka Dace da matsayinki kizo infada Miki aikinki"...

Mikewa tayi jiki a sanyaye Tana tafiya dakyar take daga kafarta tabar parlorn...

Kallon hajiya babba yarima yayi Yana neman Karin bayani...

Murmushin mugunta tayi Masa sanan tace "daga yau Fatima ta koma kuyanga"......

Wani irin shock ne ya ziyarci ilajirin jikin yarima dake tsugunne baisan lokacin da ya zauna dirshan ba ....

*Muje zuwa*

*SLIMZY✍🏼🥰*🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩

*HASKE WRITERS* *ASSOCIATION* 💡

*NA:SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an* *maliki*

*Tunda akayi walk'iya halin kowa ya bayyana na tabbatar Haske ya cancanci yabo wato Raina kama ne su kaga gayya....Tarayya sukai wurin ganin Tafaru takuma k'arewa me musu kallon raini*

21

Dafe kansa yayi Yana girgizawa wani irin bala'i ne wanan?yama zaayi ace Fatima ta fada cikin kuyangi?......girgiza Kai kawai yakeyi sallamar da tayi ce ta dawo dashi daga duniyar tunanin daya fada cikin seconds da sauri ya dago Kai ya kalleta karaf idanuwansu suka hadu waje daya wani shock ne ya tsargo Masa daga kwakwalwarsa har tafin kafarta kallonta kawai yakeyi cikin kayan kuyangi wadanda uniform dinsu ya kasance Jaja ye bayi Kuma koraye suke amfani dashi.....

Har kasa ta tsugunna a gaban hajiya babba ta sunkuyar da kanta cikin sassanyar murya tace "gani ranki ya dade"

Murmushin mugunta hajiya babba tayi tace "daga yanzun kin Zama kuyanga,Zaki Zama cikin jerin maaikatan gidan nan kin Gane ko?nayi Miki Mai sauki da ban jefaki cikin bayi ba yadda zan iya sawa a sokeki kibar duniyar gaba daya Amma hakan shi yafi cancanta dake Domin sai kin gwammace kida da karatu yanzun ki tashi kije ki nemi saade ta kaiki dakin tsohuwar ajiya ki gyarashi tsab kafin lokacin shiga kitchen ki shiga cikin maaikatan girki,sanan zan sa Miki masu tsaro yadda bazaki faki Ido kisa Mana guba a abinciba ki kashemu"

Dan durkusawa Fatima ta karayi tace "to ranki ya dade"

"Zaki iya tafiya ki nemi saade Dan aiwatar da abinda nasaki"

"To ranki ya dade"....mikewa tayi jiki a sanyaye tabar parlorn matar waziri kallo tabi bayan Fatima dashi Tana jinjina Kai....

Dik jikin yarima a sanyaye yake bashida iko ko da ja da umarnin hajiya babba haka ya Mike Ahmad shima ya Mike har sun wuce ya dawo zai dauki kayan da ya siya Mata ya Kai hannu zai dauke yaji muryar hajiya babba na fadin "Ina kuma zakaje da kayan?ai wadanan Kaya bai Dace ka daukaba ka ajiyesu zan aikawa deejahmah"

Da sauri ya dago Kai ya kalleta kallon data wurga Masa yasa ya juya ya fice a cikin gidan direct Ahmad ya samu a cikin mota....

Iska ya huro Mai zafi a bakinsa sanan ya dago rinannun idanuwansa ya saukesu Akan Ahmad bashida wani kuzari ya bude baki yace wani Abu ji yakeyi idan har ya bude bakinsa to tabbas zai iya fashewa da kuka....

Girgiza Kai Ahmad yayi ya dafa kafadar yarima yace "cool down gwarzon namiji bai kamata wanan Dan abun ya tada maka da hankali ba"

Cikin dasasshiyar murya yarima ya bude baki yace "wanan ba karamin Abu bane friend marainiyar Allah na dauko na kawo sanan a jefata cikin kuyangi?kace wanan Dan abun?"

"Da kayi shawara Dani tun farko da baka daukotaba Amma hakan yanada faidah,Domin yin hakan shine zaisa kasamu cikar burinka,sanan Kai kanka kasan Babu yadda zaayi ka dauko Fatima ka kawo batasha wanan wahalar ba friend Dole kaji kaki ji kagani kaki gani,...sanan inaso inyi maka wata tambaya"

Kallonsa kawai yarima yayi ya gyada Masa Kai batare da yace uffan ba,Ahmad ya cigaba da magana "Ina fatan ka sanarwa da yarinyar Nan kudurinnka na sonta da kakeyi Dan ko baa fadaba dik Mai hankali yasan soyayya kukeyi"

Ajiyar zuciya yarima ya sauke sanan yasa hannu ya share zufar da yakeyi dikda sanyin AC dake cikin motar "ban fada Mata ba"

Girgiza Kai Ahmad yayi sanan yace "kayi babban kuskure,abinda ya kamata kayi yanzun Dan ka share Mata hawaye dik wahalar da zaasata da gallazawar da zaayi Mata zaisa ta samu sauki shine ka rikide mata ka rinka samun lokacinda zaka kebe da ita kana nuna Mata tsantsar soyayya da kulawa hade da kauna to tabbas zata shaku dakai Kuma zata saki jikinta damuwa bazatayi Mata yawa ba"

"Haka ne friend zanyi hakan"...

"Good.....sanan Abu na gaba kafin ka auri deejahmah to ya Zama Dole ka fadawa Mai martaba kudurinnka na auren Fatima"

Da sauri yarima ya kalli Ahmad Ido waje yace "noo no friend ba yanzunba"

"Abin nufi a Nan gara ka fara shiryawa yakin da zaka fuskanta tun yanzun kafin lokacin da yakin zai gagareka"

Jinjina Kai yarima yayi kalaman Ahmad na neman juya Masa da kwakwalwa dakyar ya hadiye wani mugun miyau yace "friend Anya hakan zai yuwu?"

Kallonsa Ahmad yayi Yana murmushi yace "ka kwantar da hankalinka ka natsu zamuyi maganar "

Daga Masa Kai yarima yayi sanan yasa hannu ya dafe kansa dake Sara Masa kamar zai rabe biyu Ahmad yaja motar suka fice....

********
"Bilkisu Niko ko wani Hali Fatima ke ciki oho?ko a raye ko a mace mudai tun bayan tafiyarsu hajiya bamu karajin duriyar komi ba ko wajensu uwaliya Mai kitchen"...Maryam ta karashe maganar cike da damuwa

Gyara Zama bilkisu tayi tace "Fatima tazo kece dai baki gantaba Kuma Tana cikin koshin lafiya damuwace daya nake ciki Ina yawan mafarke mafarke akanta Allah yasadai Tana cikin Jin Dadi"

"Ameeen Amma ni ai na cire Rai da Kara ganin Fatima Kuma saidai a darussalam"

Hmmmmm"Maryam kenan bazan taba cire Rai da ganin fatimaba sai ranan da nadaina numfashi a wanan duniyar,nafi kowa tsananin kewar Yar uwata da Dadi babu Dadi muna tare Fatima mutum ce Mai hakuri ko a zamanmu muke cutar da ita muyita Mata abubuwa daban daban sai gashi lokaci kankani Allah ya tsameta a cikinmu"....wasu zafafan hawayene suka shiga gangarowa a kuncin bilkisu tasa hannu ta share sanan ta kifa kanta a tsakiyar kafafunta Tana kuka Mara sauti ...

******

Wani daki Mai duhun gaske can cikin gidan aka Kai Fatima da tsintsiya da tsumma na goge goge dakine da ya Sha kura da bola Wanda dik Wanda yayi tozali da dakin sai kayi tunanin yayi shekara sama da goma baa shareshiba an wanke,

Kayan gargajiya ne irin na sarauta a ciki cike ga uban girma da dakin yakeda shi kallonsa Fatima kawai takeyi kanta na juyawa Domin batasan ta inda zata fara gyara wanan daki dake hargitse da karikitai na ajiya na tarihi ba....

Tari ne ya sarketa a tsaye saboda tsananin kurar dake ciki kalle kalle takeyi da kyat ta hangi wani Dan karamin window can sama a makale....

Takowa tayi a hankali ta iso wajen waige waige ta shigayi Domin tsawonta bazai Kai ba idonta ya hango Mata wani katon tum tum Wanda ya wanci gidan sarauta akafi amfani dashi ganin yanada tudu yasa Bata damu da kurar dake jikinsa ba tasa hannu ta kinkimeshi zuwa jikin windown ta taka dik da haka hannunta bai kaiba dage tayi tasa hannunta dakyar ya karasa taja sakatar windon aikuwa garin ja da karfi ya yanki hannunta azabar data ratsata ce yasa ta mance da abinda ta taka garin saurin sakin sakatar kafarta ta zame ta fado kummm ta buga kanta a jikin bangon wajen na siminti Mai karfi irin na da.....

Yar Kara ta saki ta dafe kanta da hannunta biyu biyu kanta na juyawa jini na gangarowa ta hannunta zuwa fuskarta......hawayen azaba Suka shiga zurarowa a idanunta ta Dade a haka wajen minti biyar sanan ta Kai dubanta ga hannunta da tayi mugun yanka jini na tsurtuwa....mikewa tsaye tayi da sauri Tana waige waige hankalinta a matukar tashe Tana neman yadda zatayi da jinin hannunta....

Rigarta Yar doguwace har kasa tasa hannu ta yaga ta shiga kici kicin daure hannun Wanda jini ke zuba dik ya Bata Mata gaban rigarta haka ta daure batare da jinin ya tsayaba.
Chapter 27 · 0% Book details