← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 80

Sashe 75

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon yanayin deejahmah yarima yayi yasan akwai magana Amma sai ya basar kawai ya mikawa Fatima hannu ta rukoshi ya dagata yasa a kafadarsa,Tana dariya kasa kasa "idan kintashi ki kashe kayan wutan zan kwanta ne Saida safe"Yana karasa maganarsa ya wuce,

Lallai Kabir ya Raina Mata wayau wanan wani irin cin Kashi ne sukeyi Mata a gabanta batare da ko damuwa da ita ba,....Dole ta dauki mataki Akan hakan,sanan babban bala'i yadda fatima takeyi Mata gadara tanayi Mata ruwan rashin mutunci....

********
Bayan kwana uku da faruwar haha,

Hajiya babba da rahina suka shirya sukazo wajen deejahmah ganin daki don rabonsu da gidan ita hajiya babba tunda aka kawo deejahmah,

Zazzaune suke a parlor suna Yar hirarsu harda su fauziyya sukazo da khausar,

Hajiya babba ce ta dubi Deejama "Wai lafiya Naga dik kin rame Kim susuce aure wata daya da kwanaki tamkar Ana dibarki Ana Miya kodai munsamu Dan jika ne?"

Murmushi deejahmah tayi "hajiya wallahi babukomi yanzun haka ma period nakeyi wallahi"

"To Allah ya kawo kinji?Dan na Matsu ace kece kikafara kawo Mana jika ba waccen shegiyar yarinyar ba rasa kunya"....

Ddga bayansu suka jiyo sautin muryar Fatima Tana fadin "idan Allah ya bani sai ku amshe ko Kuma idan kune ke badawa ku hanani"ta cigaba da tsotsa lemon Zaki dake hannunta tazo ta nemi kujera ta zauna ta Dora kafarta daya Kan daya ta dauki remote ta canja Tasha,

Dukkansu tamkar anyi ruwa an dauke Babu Wanda ya sake magana Domin zuwa yanzun hajiya babba cike take da fargabar abinda zaije ya dawo ranan da uwar Fatima ta dawo Dan tasan ba karamin rashin mutunci Fatima zatayi misu ba,

Zaituna Fatima ta kwalawa Kira tazo da sauri "yi sauri ki kawomin abinci wata sabuwar yunwar nakeji wallahi kamar inci Babu"

Yar dariya tayi zaituna "to uwargijiyata angama"ta fice,

Koda aka kawowa Fatima yadda takecin abincin ne dukkansu dake gurin yabasu mamaki hannu baka hannu kwarya haka ta share abincin plate daya ta ajiye a Nan ta Dan jingina da kujera ta runtse idanuwanta sai bacci,

*********
"Narasa Gane kanki bintu a Yan kwanakin Nan baki samun lokacina kwata kwata,ga yawan fushi da kikeyi wani lokaci har mamaki kike bani banyi Miki komiba zakidau fushin duniya ki dauka Dani haba babyna"

Kwantar da kanta tayi a kafadarsa "habeeby Nima bansan meyasa nake hakanba wallahi kayi hakuri kaji?baa son Raina bane kawaidai ni yanzun Babu abinda na hada da abinci"

Lakuce hancinta yayi "to acici ai gashinan kinyi kumatu suku suku mazaunanki sum Kara Zama da kyau"ya shafi gefen fuskarta,

"Nidai kabari nidai kabari banaso"😩

Toshe bakinsa yayi Yana Mata dariya hade da Kara rungumeta a jikinsa....

********

Da sassafe sarkin fada ya nufi gidan da a alkawari yau ya cika sati biyu zaije Dan jiya akesa Ran suna dawowa tunda yau biyu ga wata,

Kwankwasa kofar gidan yayi da sauri Mai gadi ya bude kofa hade da leko da Kai,ganin sa da rawani da malulmalum irin na masu sarauta yasashi saurin fitowa ya tsaya a kofar gidan,

"Kai ranka ya dade wallahi banji dadiba saboda dai ranan da kazo katafi da kwana uku sukazo gidan Nan kamar daga sama sanan sunkai kwana takwas a gari sanan suka tafi Dan yanzun haka kwanansu uku kenan da tafiya Amma abinda nake gani kamar lokacin dawowarsu ya canja ne tunda kamar Mai gidan beda koshin lafiya"

Shiru yayi sarkin fada sanan ya sauke numfashi "gaskiya banji dadiba wallahi da kazo ai ka sanar min da dawowar tasu"

"Malam bansankabafa a Ina zanyi tunanin ganinka nida nake gadi ko kofar gida bana zuwa"

"Daga masarautar barayar Zaki nake"

Jinjina Kai dattijon Mai gadi yayi Yana dubansa cike da nazari sanan ya nisa yace "gaskiya kasha wahala Dan zuwanka na biyu kenan Allah beyi haduwarku da masu gidan ba,yanzun taimakon da zanyi maka daya ne"

Da sauri sarkin fada ya ruko hannunsa "Ina jinka malam ka taimakeni Dan Allah"

"Ka kwantar da hankalinka yamzun ka rubutamin number wayarka dik lokacin da suka duro garin Nam zan nemeka"

Da sauri sarkin fada ya Ciro biro a aljihun gaban rigarsa ya zaro ta karda a aljihunsa ya rubuta Masa number waya ya Mika Masa sukai sallama ...

********
Zazzabin da Fatima keyi ba karamin tadawa yarima yayi da hankaliba saboda yadda take tsananin galabaita saboda zafin zazzabi har surutai takeyi Tana ambatar sunan mahaifiyarta Tana fadin a taimaketa a hadata da ita,

Hakan ne yasa yarima ya tsorata ya daukota ya kawowa ummu ita ya ajiye,

Ahmad ya Kira abokinsa ya dubata yayi Mata Yan gwaje gwaje hade da dibar jininta ya tafi Dashi ya barsu Nan zaune da ummu wadda ke rungume da Fatima a jikinta Tana sauke numfashin wahala dik ta fita hayyacinta,

"Niko kabiru gami nake wanan zazzabin kamar ciki Fatima ke dauke dashi Dan gabaki daya yanayinta ya sauya ta koma sakk masu ciki"

A sanyaye yarima ya dubi ummu sanan ya kalli Fatima dake sauke numfashi Tana bacci lakadan yace "to nidai ummu banida masaniya Akan hakan sai abinda gwaji ya bamu"....

"Allah yasa muji alheri"...

"Ameeen"

******""

"Nifa na furgita da kikace Wai Fatima batada lafiya Tana fama da masassara Anya ba ciki ta rigaki yiba?"

Gaban deejahmah ya fadi ta Shiga girgiza Kai Tana duban mahaifiyarta "ah ah mama batada ciki insha Allah Fatima bazatayi cikibama kawai dai zazzabi ne"

Hmmmm kawai hajiya rahina tayi "to Allah yasa Amma ni Ina tsoron hakan Dan idan Fatima ta rigaki haihuwa mun Shiga uku"

Yatsina fuska deejahmah tayi "matar dake wasiyya zata mutu?ai Bata amai balle ace cikine zazzabina me zafi takeyi Tana Kiran sunan uwarta wadda nasan ita da ita sai a kiyamah kila"

"Allah yasa kedai Dan wanan yarinyar idan tasamu ciki ai kashinmu ya bushe"..

Shiru deejahmah tayi batare da ta Kara cewa komiba ta dauki kofin ruwa ta Sha sanan ta sauya maganar zuwa wata

********
Cikin tsananin farin ciki yarima ya ruko Ahmad "kana nufin Fatima Tana dauke da ciki har na tsawon sati hudu?"

Jinjina Masa Kai Ahmad yayi Yana dariya "kwarai dagaske abinda gwajina ya nunamin kenan shine ma ya haifar Mata da wanan zazzabin me zafi Amma ga magunguna Nan Nazo dasu Wanda zasu Dan Sanya jikinta tasamu sauki Taki karfi Kuma"

Rungume Ahmad yarima yayi cike da tsananin farin ciki,

Ummu dake gefensa sai faraa takeyi bakinta yaki rufuwa tashafa fuskar Fatima ta furta a Fili "lallai kainuwa dashen Allah Bata mutum ba Allah ya inganta Miki wanan ciki"

Ta gyara Mata kwanciya ta sa zaituna ta Shiga kitchen ta dafa abinci kafin Fatima ta tashi...

*****
Tun safe wayarsa ke ringing Amma yaki daukar wayar ganin bakuwar number ce ya share ,

A karo na hudu kenan wayarsa na ringing Yana zaune a kofar fada gefensa wani dogari ne sarki suna Dan tattaunawa "Wai sarkin fada ba wayarka bane ake Kira Tim dazu?"

"Mtsww Ina ganin kamfanin Zain ne shegu sun Saba kirana in dauka su kwashe kudi to bazan daukaba"

"Wanan yafi karfin kamfani tunda tun dazun ake kiranka muna zaune yanzun gashi har yamma tayi suna Kira?kana ganin ba wani bane ke kiranka?"..

Yana Gama maganar wayat ta tsinke ,sarki fada ya bude baki zaiyi magana kenan Kira ya shigo a fusace ya zaro wayar a aljihunsa ya Danna dauka ya Kara a kunnensa hade da yin shiru....

"Ranka ya dade dama nine nakeso in shaida maka me gida yadawo tare da iyalensa gabaki daya Kuma naji kamar suna fadin umara zasu tafi gobe da yamma"...

Yatsina fuska sarkin fada yayi "wake magana?"

"Nine mutumin da nayi maka alkawari Akan idan me gida ya dawo zan sanar da Kai"...
Dibb wayar ta tsinke,wata zabura sarkin fada yayi ya Mike tsaye Yana sake dialing number wayar.....

*Muje zuwa*

*SLIMZY😍*
[9/4, 16:50] 🥰slimzy🥰: 🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

48

Tallafe yake da Fatima a jikinsa Yana faman riritata sai zuba Masa shagwaba takeyi Tana kakkaucewa saboda ummu dake kaiwa da komowa daga daki zuwa kitchen dinta,..wayarsa dake gefensa ce ta hau ringing be dubi wayarba ya Kara rungumota jikinsa Yana famar shafa kanta,wayar ta tsinke a karo na biyu ta Kara shigowa Dan tsaki yayi "mtsww Wai waye ne kuma?"ya janyo wayar Yana kallon me Kiran,

Receive ya Danna ya Kara a kunnensa "umhmm ya akayi sarkin fada?"

Daga can bangaren aka bashi amsa da "ranka ya dade iyalan gidan malam liman ne yanzun Mai gadin gidan da yake nabashi number ta ya kirani yake sanarmun sun shigo gari tun jiya gobe Wai zasu tafi umara"....

"Ganinan zuwa sarkin fada ka kirani a kofar fada"ya datse wayar ya dubi Fatima da tunda ya fara wayar ta kafesa da ido dikda batasan me akeyi ba,

Gyarata yayi ya janyo pillow ya Dora kanta akai Sanan ya durkuso daidai fuskarta "zanje indawo kinji babyna ki kulamin da kanki kina bukatar wani Abu ne?"

Girgiza Masa Kai tayi tana binsa da kallo har ya Kai kofa ta tsaidashi "habeeby"....cakkk ya tsaya ya juyo a gaggauce "ya akayi Fatima?mekikeso ?"

"Ka fadamun inda zaka dik ka kidime sai kace wani Abu ya faru"....jimm kadan yayi Yana Dan tunani bayason sanar da ita koma menene Dan saboda yasan rigima zatasa mishi sai taje gashi ba lafiya gareta ba,

"Mai martaba ne yakeson ganina shine zanje bada dadewa zandawo kinji?"

Yatsina fuska tayi hade da tabe baki ta juyar da kanta gefe cike da kishi tace"kodai me martabiya ba,Kila ma wajen matarka zakaje"...

Agogo ya kalla 'koma menene sai na dawo "be jira cewarta ba ya fice,

Idonta yayi kwalkwal,Kila wajen matarsa zaije suci soyayyarsu ita Tana Nan shine zaiyi Mata wayau yace Wai me martaba ke kiransa,....janyo bargo tayi ta rufe har kanta ta shige Tana sharar hawaye saboda tsabar kishi da ya taso Mata....

**********

Bacci sosai Fatima takeyi lokacinda hajiya karama ta shigo sashen ummu Domin ta duba jikin surukar Tata ,dikda kunya hakan be hanata zuwa ba,

Bayan sun gaisa da ummu mama karama ta dubi sashin da Fatima ke kwance fuskarta tayi fayau ta Dan rame hancin Nan ya fito zirr,

"Wai hajiya zainab meke damun surukar Taki ne?umm?"

Yar dariya ummu tayi "diyar tawa karuwa muka samu"
Chapter 75 · 0% Book details