← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 80

Sashe 63

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bazan iya saniba Domin nidin sabon maaikaci nee wajen Nan wanan tambayar Taki amsarta Naga tsohon maaikacin gidan Nan Wanda shine yasa hannu aka karbeki ga sunansa a kasa MALAK SANI SULEMAN...ni bazan San wani abuba dangane dake Domin dik Wanda ya kawo yaro sai ya fadi dalilinsa na kqwosa din kodai tsintarsa yayi ko Kuma iyayensa sun mutu Babu Wanda zai iya rikesa ko Kuma baasan danginsa baz

Bude takaddar kasan file din yayi ya Ciro wani hoto na Yar yarinya Mai tsananin Kama da Fatima sak ya Mika Mata

Kallon hoton takeyi Tana jinjina Kai tabbas wanan itace lokacin Tana Yar shekara hudu to,...kallon hoton takeyi daga sama har kasa suturar dake jikinta masu kyau ne Domin blous ne na yara kanta sanye da hular blous din Tana dariya akai Mata hoton....yarima dake gefenta ya karbi hoton Yana dubawa shima mamakin ganin suturar dake jikinta yakeyi kuma aka kawota gidan marayu?

Gauron numfashi yarima ya sauke "yanzun sir ya zamuyi muga wanan tsohon maaikacin na gidan Nan?"..

"Tabdijan ni bansanshi ba da dai akwai wani tsohon maaikacin ne a gidan kila zai iya saninsa"

Jinjina Kai yarima yayi "owk badamuwa zan bincika insha allahu mungode"

Ya kamo hannun Fatima ta mikar da ita "muje koh?"

Jiki Babu kwari ta mikawa manager wanan hoton ya maida cikin file din sanan ya ajiyesa a gefe sukai Masa sallama hade da bashi sakon cewa zasuyi aike na kayan abinci abqwa marayu...

Dakyar Fatima ke take kafarta suka fito excort dinsu suka rufa musu baya har mota...

*********
Fauziyya ke rike da hannun deejahmah suna tattaunawa "yanzun kenan tun safe suka fita gashi yanzun sun Kai karfe uku Basu shigo gidan ba kamata yayi muyi aikin da zamuyi kafin su dawo koya kikace?Dan ni na Matsu da Inga karshenta"

Khausar wadda ke gefensu itama tazo ba dadewa fauziyya tazo tace "ai hajiya tace wanan auren Babu inda zaije sanan sabon maganin Nan Dana kawo Miki matukar kikai amfani dashi an wuce wajen"

Dadine ya lullube deejahmah "ai ya Gama Mata kwanakinta daga jiya Kuma Ina Mai ji a jikina tayi bankwana dashi"

"Yanzun dai wannan abun a dakinta zaasashi a tabbatar ta diga ko yayane q dakin kwanansu to tabbas bazai taba iya Zama cikin dakinta ba ko ya shiga zaiji tamkar Ana Hura Masa wuta a jikinsa zai tsani dakin,...ita kanta da take cikin dakin kwana uku kacal zaiji tsanarta..."

Tafawa sukai dykkansu suka Mike a tare suka nufi sama bangaren Fatima...

********
Tunda suka shigo motar da nufin dawowa gida Fatima ta kasa ce Masa komi saidai kwantar da kanta da tayi a kafadarsa minti minti takan ja numfashinta ta sauke Babu abinda keyi Mata yawo a kwayar idanuwanta sai wanan hoton nata Tana yarinya da kalaman mutumin Nan na cewa "tun kina Yar shekara hudu da watanni aka kawoki gidan marayu kuma Wanda ya kawokin namiji ne"...da wanan farucin yazo Mata kunne gabanta sai ya yanke ya fadi tunaninta dik ya tafi ne a yadda zata gano bakin zaren?.....shin ta Ina zata fara?ya zaayi ta gano itadin ko wacece?

Muryar mijinta ta jiyo Yana fadin "idan har samun tsofaffin maaikata a gidan Nan shi zai bamu damar sanin iyayenki to tabbas zamu ganosu"

Dago kanta tayi ta kallesa fuskarta cike da damuwa tace"yaayah ta Yaya?zaka taimakamin?ka taimakeni Dan Allah kayimun wanan gatan"tai maganar a raunane

"Zan taimaka Miki Fatima harabada Babu abinda Zaki nema ki rasa a wajena akwai wani da nasani da dadewa nida Ahmad zan binciki Ahmad din ko yasan inda yake shi maaikaci ne a gidan marayu munsaba dashi tun bamukai hakanba muna zuwa Kai taimako gidan marayu shike taimaka Mana to nasan bazai rasa sanin malam sani SULEMAN din ba,zan bincika inji saimuje indayaken koh?"

Ta jinjina Masa Kai Tana murmushin karfin Hali Wanda iyakarsa fuskarta bai Kai zuciyarta ba,....ji takeyi tamkar ta bude Ido taga iyayenta....

Maimakon taga sun karya hanyar gidansu sai taga driver ya juya Kan mota zuwa hanyar masarauta....

*Muje zuwa*

*SLIMZY😍*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

42

Tsayawar motocinsu yayi daidai da fitowar bilkisu da niyyar zuwa bayan gida hannunta dauke da mopper ganin motoci sababbi yasata tsayawa kallon motocin cike da kosawa da bukatar ganin kosu waye....

Murmushi Fatima ta sauke ganin Yar uwar Tata tsaye tana kallon motocin tamkar Yar kauye ta juyo ta kalli yarima shima murmushin yakeyi ya daga Mata gira sama "Ali yaga Ali ko?"

Jinjina Masa Kai tayi tana mai maida dubanta ga bilkisu wadda har yanzun tana tsaye motocin take kallo sanan ta juyoga yarima ta ruko hannuwansa

"Lokaci nake jira a yanta Yar uwata daga kangin bauta,"

"Kefa kin fiye rigima tayaya hakan zai kasance?bayan kinsan baiwar hajiya babba ce"

"Bedameniba inhar baa yantata ba zansa a daukemun ita Nan gaba kadan"

Lakuce Mata hanci yayi "rigimarki yawace da ita yanzun mubar wanan maganar"

Ta Bata fuska Tana kallonsa "to zan roki Mai martaba da ya nemamin alfarmar a bani ita a matsayin baiwata idan yaso a dawowa da hajiya bayi guda biyu Nan"

Bata Rai yayi "nibanason rigima bintu Kinga kibar wannan maganar ba yanzun ba"

"Shikenan tunda haka ka zaba ganin Yar uwata a kangin bauta ni Kuma Ina ya'ntacciya tunda ka rigada ka mallakeni Dole kace hakan"..ta bude mota ta fito Bata jira cewarsa ba bayin dake zagaye da motocinsu suka rufa Mata baya,

Zubewa bilkisu tayi fuskarta dauke da faraa "Allah ya taimaki sarauniya Fatima....barka da zuwa'

Dagota Fatima tayi cikin kasa da murya tace "harabada Yar uwata bazata taba durkusaminba,kiris nake jira in daukeki daga kangin bauta"Tana fadin haka tai wucewarta sauran kuyangin suka Mara Mata baya,

Shiko yarima dage kafadunsa yayi yai hanyar fadar sarki tunda yaga cikin gida tayi.....

********
Sashen mama karama ta nufa Tana tafe Tana takama dik inda ta gifta maaikatan gidan na zubewa suna kawo gaisuwa

Bakinta dauke da sallama ta shiga parlorn hajiya karama a nan ta tararda ummu zaune da afnan suna zaune sun idar da sallahr laasar

"Lale marhabun da zuwan diyata daya tamkar da dubu yanzun nake cewa kewarki ta isheni mijinku yaki kawoku ki gaida Mai martaba yanata fada"

Kunyace ta lullube Fatima ta zube a kasa a gaban ummu hade da kamo hannayenta "Ina kewarki uwa ta gari na durkusa a gabanki Ina me neman afuwarki na rashin ganina da bakiyiba"

Jinjina Kai ummu takeyi cike da farin ciki "ai idan kaji danka shiru a gidan miji to lafiyar kenan karki damu a dik inda kike inayi Miki addua"

Gyada Kai Fatima tayi sanan ta juya gaban hajiya karama wadda tunda Fatima ta shigo take binta da kallon shaawa fuskarta dauke da murmushi Tana gyada Kai.....kwana bakwai kacal yarinya ta canja ta Zama tamkar balarabiya ga wani kyau da tayi sanan babban abinda ya karawa fuskarta kyau shine ladanin sallah dake manne a saman goshinta Dan karami yayi bakin Kirin dashi,

"Allah yaja da ranki ya kareki ya Kara daukaka barka da warhaka ranki ya dade"

Daga Mata hannu hajiya karama tayi "barka dai Fatima ya gida?ya abokiyar zaman naki?"

"Lafiya Lau tace a gaisheku itama zatazo ko zamuzo tare "

"Masha Allahu,kinje kin gaida hajiya babba ko?"...gaban Fatima ne ya fadi Dan shaff ta mance da wata hajiya babba Domin Bata ita takeyi ba

"Yanzun zanje insha allahu"

"Tashi kije ki gaidata"....

Cike da ladabi Fatima ta Mike dukkansu suka bita da kallo suna Mai tausayawa rayuwarta

**********

Hajiya babba na kishingide a jikin kilisarta Tana kada kafafuwa gefe da gefenta dik kuyanginta ne zaune sun gurfana a gabanta,

"Nakejin kamar hayaniya cikin gidan Nan koh?sautin gaishe gaishe nakeji a waje"

Dada gurfanawa mami tayi "sarauniya fatimace da yarima sukazo"

Mikewa tayi zaune "tazo?shine Bata fara shigowa Nan ta gaisheniba sai taje sashin uwar mijinta kenan koh?niba uwarta bace"

Shigowar Fatima ya dakatar da Mami da yin maganar datai niyyar yi,....kaff hirar da sukeyi Fatima ta sauraresu wannan ne ya Bata damar sakin Yar dariya....

Gaida Fatima suka shigayi daya bayan daya Tana tsaye kerere takai mintuna tsaye Tana karewa hajiya babba kallo yadda take cika Tana batsewa Tana faman hura hanci

"Ku tashi ku ficemun da gani inason zantawa da uwata"...shine abinda Fatima tacewa kuyangin hajiya babba ciki kuwa harda bilkisu suka Mike Sumi Sumi suka fice,

Gefen hajita ta zauna ta janyo plate din da takecin soyayyar gyada ta diba ta watsa a bakinta Tana taunawa Tana lumshe idanuwa yayinda hajiya babba kebinta da kallon mamaki

"Waya baki damar samun hannu a cikin kwanon da nakecin abinci?bayan kin manta da kedin kazanta ce?"

Saida Fatima ta hadiye abinda ke bakinta sanan ta dubi hajiya babba Tana watsa Mata kallon raini tace "ehh na dibi gyada na zuba a bakina ne na tauna saboda shaawar da naji gyadar ta bani Dan bansaniba ko shegiya Tana dauke da cikin jikanki ko jikarki shiyasa kada tazo da rowa.....Domin a kwana bakwai din Nan danki yayi jarumta wajen bani hakkina a matsayina na matarsa ta Sunnah ba karuwarsa ba"

Wani zabura hajiya babba tayi tamkar zata kaiwa Fatima duka tace"keni nayi Kama da Saar wasanki ce da zakizo har dakina kiyimun rashin kunya?ki fadamun maganganu marasa Dadi Wanda ko saarkice ya Dace kiji kunyarta bawai ki fada Mata wadanan maganganun Kai tsaye ba"

Yar shewa Fatima tayi "hajiya kenan,kin manta yayan karuwai basuda kunya?ko kin manta dik Dan da akace Dan kwararone to tabbas Zaki sameshi bashida kunya ko kadan a kwayar idonsa....ai bedace in Ari Hali na ya'yan Sunnah insawa kainaba Ina matsayin shegiya"

Sakin baki hajiya babba tayi kawai tanabin Dan bakin Fatima da kallo yadda take zaro maganganu Tana watso Mata su,

"Surukarki ce ta turo ki kiyimun rashin kunya ko uwar goyonki?wadda tagama zaman saudiyya ta dawo?Saida kikaje kuka Gama munafuncinku sanan kika kwaso kafa kikazo gaisheni koh?"
Chapter 63 · 0% Book details