← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 80

Sashe 5

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu fargaba babu wani tsoro yarima yace"Kaine wadanan abubuwan da ka lissafo zasu dama babu abinda zai dameni matukar Zan Kare hakkin Dan Adam "

Murmushi Ahmad yayi yace "kafara bani tausayi Anya baka samu matsala a kwakwalwarka ba kuwa sanadiyyar wanan mutuwar ta Dan uwanka?"

Haushine da takaici ya lullube yarima ya Mike a fusace ya kwashi makullansa yayi hanyar fita Ahmad ya bisa da kallo Yana girgiza Kai ya fice....

*******
Mama babba CE zaune tare da mahaifiyar kabir a parlor bayan sun Gama karin kumallo Wanda dabiar gidance da safe tare suke karyawa kowace mace da yatanta waje daya,

"Nikam tun jiya tunda Yaya kabir ya fita da yamma bincike be dawoba har yanzun banganshiba gashi ko abimci bana ganin yanasawa a bakinsa tunda Yaya habib ya rasu"cewar afnan karamar kanwarsu gaba daya,

Mama babba CE tace"nikaina tausayin kabir nakeyi domin Yana cikin damuwa na rashin Dan uwansa,ko jiya daya shigo naga dik ya rame yadanyi duhu,nadai sanar Masa da abinda muka xartar Kuma ya amsa nasan insha Allah zai tsaya Akan shariar Nan tunda gobe zaa mikata kotu "

"Ai Yaya kabir akwai kokari akwai fasaha nasan dik yadda zaibi yayi nasara a shariar Nan zaiyi,insha Allah Sai an kashe Mana yarinyar Nan da tayi kisan Nan"

Itadai mama karama batace komiba Sai Binsu takeyi da kallo batare da tace wani Abu ba,

Mama babba ta sauke ajiyar zuciya tace"ai dik Wanda ya kashe habib Sai an kasheshi ko Dan gidan uban waye a garinan"

Suna cikin wanan hirar yarima Kabir ya shigo,dik abinda suke fada tun daga farkon hirarsu ya Gama sauraronsu yazone da niyyar fada musu ya janye Akan shariar su nemi lawyan gwamnati Amma Sai wata zuciya ta hanesa da hakan nan da Nan ya zartar da wata shawarar a zuciyarsa.......

*Muje zuwa*

*SLIMZY🥰✍🏻*[
*🌩ANYI WALK'IYA.....🌩*

*💡 HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*

*NA SLIMZY*

_Wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata Faty D'an maliki*

05

Nesa kadan dasu kabir ya nema ya zauna sanan duka iyayensa daya bayan daya ya gaggaishesu suka amsa cike da kulawa sanan Shima kannensa dake gefe suka gaidasa ya amsa,

Shiru ne ya biyo baya kusan minti goma babu Wanda yace komi al'adarsu CE haka na rashin magana Koda kuwa dukkansu sun hallara a waje guda kowa Yana ji da irin tasa sarautar,

Mama babba CE ta kalli gefen wajen da yake zaune ya tankwashe kafa ya Lula cikin duniyar tunani itace ta fargar dashi ta hanyar jeho Masa tambaya "Wai nikam kabir jiya bakazo ka sanar Dani halin da ake ciki ba domin na Matsu da Inga karshen yarinyar Nan"

Da'go kansa yayi ya maida dubansa gareta sanan ya dukar da kansa cike da natsuwa yace "mama wallahi jiya bandawo gida da wuri bane shiyasa banzo wajenkiba mun tattauna,ki kwantar da hankalinki komi na tafiya yadda ya kamata insha Allah mune zamuyi nasara a wanan tafiyar domin na tabbatar da wanan yarinyar batada wata hujja da zata nuna cewa ba ita tayi kisan ba,sanan babban hujjarmu shine ta amsa da bakinta tayi kisan"

Dagowa mama tayi da sauri tace"Wai nikam wanan yarinyar Yar gidan uban waye?waye babanta a kasar Nan?meta taka da tazo har cikin gidan sarauta tayi kisan Kai?lallai zata da'n da'na kudarta saitayi danasanin zuwanta duniya ko waye ubanta"

Shiru yayi yarima batare da yace komi ba Yana Wasa da yatsunsa,hajiya babba ta Nisa ta Kara cewa "ansamu labarin iyayenta?waye ubanta?lawyoyi nawa suka dauka?"

"Har yanzun baasamu labarin iyayenta ba don har yanzun babu Wanda yazo police station din da maganar"

Girgiza Kai kawai mama tayi tace"waya sani ko karuwa CE"....da sauri yarima ya da'go Kai ya kalleta domin kalmar ta daki zuciyarsa Nan da Nan yaji ransa ya baci,fatimansa ake jifa da kalmar sunan karuwa?....kallon yadda ya da'go Kai mama tayi tace "ehh babu mamaki ko karuwarce don zaa iya hada Baki Ayi komi dasu zasu iya Saida ransu saboda neman suna,babuko tantama kudi aka Shaka Mata aka hada Baki da ita don ta kasheshi!!!!.....to wallahi yadda ta kasheshi Sai an kasheta karuwar banza"

Zumbur yarima yayi ya Mike idanuwansa jajir zuciyarsa na tsananin harbawa sauri da sauri bazai iya jure sauraron wadanan mugayen kalmomin da ake jifan Fatima dashiba domin Fatima baiwar Allah CE....

"Mama Bari inje akwai binciken da nakeso in cigaba da gudanarwa domin kinsan gobe zaa Mika takaddar tuhumarta kotu jibi Kuma zamu shiga to banida sauran lokacin da Zan tsaya ya kamata in shirya komi kafin jibin"

Jinjina Kai mama babba tayi cike da gamsuwa da kalaman yarima tace"Allah ya bada saa kabiru"

"Ameen mama"ya juya da sauri ya fice a parlorn....Yana tafe Yana sakawa da warwarewa yadda zai bullowa wannan matsalar,Anya ba tunanin da ya bullo masa dazun zaiyi Amfani dashi ba?...Ina zai samu barrister Abdul da matarsa barrister hauwa u?tabbas su ya kamata ya nema domin sune zai kaiwa kukansa su share Masa su rufa Masa asiri su tsayawa Fatima batare da kowa yasani ba,

Jikinsa har rawa yakeyi ya Ciro wayarsa ya zauna cikin mota ya shiga scrolling contacts dinsa hankali a tashe yake neman number barrister,idanuwansa ya rufe ya duba contact yafi sau ashirin be ga contact dinba Sai da ya fidda ransa da ganin contact din sanan ya gani barrister.A. yayi Masa saving dashi Nan da Nan yayi dialing cikin saa ta shiga....

Daga can bangaren aka dauka "Ranka ya Dade barrister khabir Allah ya ja kwana dama kana duniya?"cike da barkwanci yayi maganar,

Dan murmushin gefen kumatu yarima yayi Wanda hakan be hana dipple dinsa shigewa ba yace cike da kasaita "banason shakiyanci"

Dariya sosai barrister Abdul yayi yace "badai ka kirani ka fadamin aurenka ba don nasan inba aure zakayiba bazaka nememuba barrister Dan rabona dakai tun shariar da muka gabatar last 2 years da muka nemi a gajin fasihin barrister"

Cikin kosawa da magana yarima yace"yanzun dik mu ajiye wanan maganar,nakira ne saboda wata muhimmiyar bukata data tasomin Wanda nasan insha allahu babu Wanda Zan tunkara da maganar Nan ya tsayamun idan ba kaiba"

Dan natsuwa barrister Abdul yayi yace "to Allah yasadai lafiya,meyafaru ne ranka ya Dade?"

Ajiyar zuciya yarima yayi yace "yaushe zansameka a gida kaida madam?"

"Ranka ya Dade bàma gari gaskiya"Saida gaban yarima ya Yankee ya Fadi,

"Amma yau insha allahu zamu biyo jirgin karfe hudu nida madam zamu dawo gari,zuwa bayan ishai zaka iya zuwa mu tattauna matsalar"

Wata sassanyar ajiyar zuciya yarima ya sauke tare da hurar da iska a bakinsa yace"alhamdulillahi Allah ya kaimu"

"Ameeen"

Sukayi sallama.....

Motarsa ya tada da sauri ya tada kura ya fice daga gidan a guje,

*******
Gidan amininsa Ahmad ya nufa,ya tarar dashi Yana Shirin fita aiki ya shirya tsaf cikin shigarsa ta suits hannunsa dauke da rigar doctor's Fara Kal yanata sauri,yarima ya shiga,"ah ah ai Ina Shirin yau inje bikonka ne tunda jiya daga shawara naga kayi fushi saboda soyayya ta rufe maka Ido kana nema kajawa kanka matsala"

Kujera ya nema ya zauna ya Dafe kansa batare da yace wa doctor komiba,

Doctor ne cikin tsokana yace"kaifa miskili ne ayita magana kanajin mutane ga sarauta da kake fama da ita itama ta taru tayi maka yawa"

Dan tsaki yarima yayi yace "nasamo mafita"

Shima Ahmad da sauri ya nemi waje ya zauna Yana fuskantar yarima,

Da'go rinanun idanuwansa yayi ya sauke akan doctor Ahmad sanan ya Fara magana cike da kasaita fuskarsa daure tamkar be taba murmushi ba "na janye Akan tsayawa Fatima sharia,nakira barrister Abdul dazun Zan dorasu su biyu akan shariar shida matarsa barrister hauwah,nasan insha allahu zasu tsaya Mata Kuma zasuyi nasara!!!"

Hmmmmm"ta Yaya zasuyi nasara kana nufin kafisu iya gudanar da shariah ne?sanan ta Yaya zasuyi nasara akan shariar kisan Kai?shariarda duniya ta shaida itace tayi kisan?"

"Dik wanan ba damuwa bane inada tabbacin barrister hauwa matar Abdul ta iya shariah tasan kan komi sanan macece dik yadda zaayi ta bincike Fatima zatayi zanbata tips akan komi yadda bazaa samu matsala ba"

Girgiza Kai kawai ahmad yayi yace "to shikenan Allah ya bawa Mai rabo saa,sanan ka kiyaye kada asirinka ya tonu Dan idan asirinka ya tonu kasan sauran a masarauta"

Murmushi kawai yarima yayi ya kwantar da kansa jikin kujera yace "kaidai jeka aikinka kawai ka barni a Nan inaso inyi nazari"

Dage kafadarsa🤷🏻‍♂ doctor yayi ya juya yace "saina dawo"

"Ok"kawai yarima yace tare da runtse idanuwansa,ya fada duniyar tunanin Fatima....

*******
"Babban bala'i Yana Shirin tunkaromu hajiya,ko kinsan Fatima Tana hannu?sanan ta tabbatarwa da hukuma cewa itace tayi kisan Kai?"

Dafe kirji hajiya tayi hade da kidimewa tace"tabbas Dole inbar garin Nan domin kuwa kasan yadda akayi Fatima tabar gidan Nan,yanzun Ana shiga kotu zaa bukaci Fatima ta Fadi ita wacece cewa zatayi ita Yar gidan marayu CE kaga kuwa Dole a nemomu,Dan Dole a kiramu mune masu kula da gidan marayu"

Tagumi haruna yayi ya shiga girgiza Kai "lallai muna cikin bala'i Amma shawarar da zanbaki itace kada mu gudu hajiya"

Zumbur hajiya ta Mike Tana kada Kai cike da masifa tace"me kake nufi haruna?kada mu gudu mu tsaya a kashemu?mu tsaya Fatima ta tona Mana asiri ta fadawa duniya abinda ake aikatawa a gidan marayu?hukuncin da zaa Yanke Mata mu a Yanke Mana kenan ,to kaga idan zakaje kabar jirana"

Girgiza Kai haruna yayi tare da kasa da murya yace"hajiya kwantar da hankalinki kiji,inaso kiyi tunani kiyi aiki da hankali,idan muka gudu aka tsare Fatima ta Fadi gaskiya to tabbas komi Daren dadewa Sai ankamamu,hotonmu zaayi yawo dashi a fadin jahar Nan domin kamar munyi fada da gwamnati ne sanan kada ki manta yaron da ta kashe jinin sarautane zaa dauki mummunan mataki akanmu,Abu daya ne idan Fatima ta tona asiri muce bamu Santaba bamu Taba ganinta ba dik maaikatam gidan Nan zamubi mu rufe musu Baki sanan kinsan ko sauran yara bakowa yasan Fatima ba saboda Bata shiga harkar jamaa sanan Abu na gaba kawarta zamu boye bilkisu,shikenan mun rufawa kanmu asiri"

Tunda haruna ya Fara bayani hankalin hajiya ya Fara kwanciya tabbas ya kawo shawara hakan zaayi,neman waje tayi ta zauna tace "tabbas maganar da kayi Akan hanya take...idan ba haka ba to wallahi zaayi *WALK'IYA* asirinmu zai tonu asirin kowa ma zai fallasa"

"Hakan zaayi"...Nan suka cigaba da kulle kullensu a inda suke Zama can baya wajen kitchen....
Chapter 5 · 0% Book details