Sashe 18
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
********
Zubewa yayi a gabanta a durkushe Yana fuskantarta,ganin yadda ta daura fuska yasan tabbas akwai matsala fuskarta babu walwala Rabon da ya ga hakan a tattare da ita ya manta,shiru tayi sai Jan carbi takeyi batare da tace Masa komi ba,sanin sarauta da miskilanci irin na mahaifiyarsa yasan inhar bashi ne yayi Mata magana bazatayiba sanan yasan Harga Allah cewa yayi laifi yadda ya tada muryarsa bisa ta iyayen nasa,sassanyar ajiyar zuciya yayi sanan ya Nisa yace"naso ace Kun fahimci abinda nake nufi game da wanan daukaka karar naso ace kunsan cewa yin hakan tamkar tozarcine ga wanan masarautar da bacin suna ga Dan uwana dik wanan abun da nakeyi inayinsane don inkare mutuncin kanmu Dana gawar Dan uwana banaso ace sunan masarautarmu ya baci a idon duniya,dalilin hakan yasa nake boye wanna shariar data gabata na Hana dik wata maaikata da zata yada abinda ya faru a gidan radiyo da talabijin halartar wanan shariah Amma saidai Kash bakuso hakanba sanan ga babban abin dubawa shine yin abinda zaaci mutuncin maraya dik Wanda ya wulakanta maraya yaci zarafinsa Allah baya barinsa mama ki duba wannan lamarin ki sassauta wanan fushin da kika dauka akaina ki fahimceni"
Tunda ya fara magana ta kafesa da ido Tana kallonsa cike da gamsuwa da maganarsa Amma tasan nuna Masa goyon baya bazai yuwuba.....
"Dik naji maganarka na fahimceka sanan Nima ba goyon baya nakeyi Akan daukaka kararba Domin shi kansa Mai martaba babu hannunsa a ciki abinda nakeso dakai shine ka janye hannunka a cikin shariar Nan banaso kace zaka tsaya akai ma wanan yarinyar Domin zaka daukarmun magana"
"Mama naso ace kin bani goyon baya wajen yin aikin lada Domin Allah kadai yasan dumbin ladan da zansamu wajen Kare hakkin marainiya a matsayinta na wadda aka cuta Dan girman Allah ki yi hakuri kiyimun addua kada ki hanani aikin lada"
Ajiyar zuciya tayi ta Nisa tace"babu hannuna a ciki dik abinda ya biyo baya ka kuka da kanka sanan kasani harabada bazan kaunaci wanan yarinyar ba kaidai da kaji ka gani kaje gatanan Amma bana kaunarta saboda ta sanadiyyarta na rasa habibu Dan uwanka Wanda Kai kanka yadda na shaku dashi ban shaku dakai haka ba tashi ka fita"
Yaji zafin maganar mahaifiyarsa Amma yasani tsakaninta da habib akwai kauna Mai karfi a tsakaninsu Domin Dan dakinta ne,babu yadda ya iya haka ya Mike jiki babu kwari ya fice sanan beji dadin kalaman ummansa ba na rashin kaunar Fatima......
*********
Washe gari da sassafe ya shirya can Court din da aka gabatar da shariah yaje don yayi bincike Akan abubuwan da ke gudana yanaso ya tabbatar da hajiya tasa a daukaka Kara ko Yaya,
Wani office ya shiga ya tarar da wani lawyer zaune da takadda a hannunsa,gaisawa sukayi sanan yake tambayarsa Akan maganar,
Da sauri ya dauko wata takadda yace"ranka ya dade maganar daukaka Kara tun shekaran jiya akayita Domin hajiya ta dauki lawyoyo guda uku ta biyasu Akan tsaya Mata Akan shariar yanzun haka ma takadda ta Isa supreme Court jibi zaafara sauraron karar"
Saida gabansa ya fadi Amma ya dake ya Mika hannunsa ya karbi takaddar ya gyara Zama ya fara dubawa,can kasan takaddar ya duba ya kalli sunayen wadanda zasu tsaya Mata a kotu akwai Barrister Nasir da Barrister Muhammad da barrister Ibrahim dukkansu lauyoyine masu zaman kansu Wanda ake daukarsu a biyasu Akan shariah su tsayawa mutane kwararrune Wanda Suma ansan da zamansu a wanan jihar,ko darrr yarima bejiba hasalima dukkansu yasansu don babu Wanda be taba shariah dashiba Kuma sun buga sunbarshi indai wadanan ne aikin banza ya daukesu dukkansu sunsan wayeshi saboda haka a shirye yake da ya Kara Dasu....
Jinjina Kai kawai yayi ya Ciro wayarsa ya dauki number wayar daya daga cikinsu yasa a wayarsa sanan ya gabatarwa Wanda yazo wajensa a matsayinsa na lawyer da zai tsayawa Fatima a kotu ta gaba......a rikice yake kallonsa cike da mamaki wanan ala'amari Amma sanin halin yarima yasa bece komiba sai takadda da ya bashi ya Sanya hannu ya fita.....
*********
Tun kafin ya tada motarsa yayi dialing number barrister nassir bugu daya ya dauka daga can bangaren barrister Nasir yace"ranka ya dade barka da warhaka"
Mirmushin kasaita yarima yayi yace"Ashe kanada number ta"
"Ehh ranka ya dade"
Jinjina Kai yarima yayi sanan yace"nakiraka ne in shaida maka nine barrister Wanda zai Kare wadda ake Kara wato Fatima Zahra inaso ka shirya da kyau"
Saida gaban barrisiter Nasir ya yanke ya fadi Dan dik a tunaninsa yarima bashida lokacinda zai tsayawa shariar ne yasa hajiya babba tasa aka nemesu tabdijan shine abinda ya ambata a ransa sanan yace"to ranka ya dade Allah ya kaimu nagode sosai"
Murmushi Mai sauti yarima yayi sanan ya kashe wayar Yana murmushi shi kansa yasan yanzun dik inda hankalin barrister Nasir yake ya tashi Domin sun taba gabatarda shariah beji da dadiba yayi hakan ne ya Dana musu tarko......yasan cewa kudin hajiya babba kawai zasuci Domin babu abinda zasu iya a wanan shariah da gaskiya take kuru kuru.....
Motarsa yaja yayi gaba abinsa Yana tuki cike da kwanciyar hankali da karfin gwiwa.....
*********
Tunda aka kawo takaddar daukaka karawa barrister Abdul hankalinsa ya tashi Dan tausayin yarinyar da yakeji ta wani fannin kuwa yanasamun kwarin gwiwa idan ya tunada cewa shariar a hannun yarima take yasan waye yarima.....
Gidansu yazo a parlor dukkansu ya tarar Dasu sunyi jigum jigum Fatima na gefe Tana famar rizgar kuka kamar wadda akayiwa mutuwa yanayinta kadai ka kalla saita baka tausayi yadda ta rame tayi fari fat tamkar wadda batada jini....
Koda yayi sallama dukkansu kallo suka bisa dashi har ya karaso tsakiyar parlorn ya tsaya ya zura hannunsa a aljihunsa ya zurawa Fatima idanuwansa Yana kallon yadda hawaye ke ambaliya a idanuwanta tamkar an bude famfo,kallonta yakeyi cike da kunar Rai a duniya Babu abinda ya Tsana sama da ganin Fatima Tana kuka.....
Idanuwanta ta daga a sanyaye ta saukesa akansa taga itace yake kallo ko kiftawa bayayi ta Sanya hannu ya goge hawayenta tana sauke ajiyar zuciya....
Barrister Abdul ne yace"ranka ya dade angama komi ko?"
"Ehh angama yanzun abinda ya rage shine ka mikawa hukuma Fatima yau don dole sune zasu gabatar da ita a kotu tunda shariar a hannun gwamnati take Kuma baa gamaba"
Nan da Nan taji jiri na dibarta numfashinta na fita sauri da sauri shikenan ta tabbata cewa tafaru takare Mata a rayuwa itadai Tana cikin balai da mummunar kaddara wani irin kuka Mai karfine ya taso Mata ta toshe bakinta tanayinsa,barrister hauwa ce take famar lallashinta itama idanuwanta sunkada sunyi jajir dauriyace tasa Bata iya zubar da nata hawayen....janyota jikinta tayi ta rungumeta Tana shafa bayanta.....
Hawaye na gudu a idanuwanta ta dago Kai da sauri tace"Dan Allah kiyimun Abu guda daya kafin a kashe ni"
Dukkansu ido suka zuba Mata tace"ku taimakeni ku kaini in ziyarci Yar uwata a gidan marayu inaso inganta inyi Mata ganin karshe Dan Allah"
Saida yarima yayi Mata kallon minti biyu zuwa uku sanan yace"tashi muje"
Da sauri ta Mike Tana share hawayenta,gaba yayi abinsa ta zari hijabinta dake kan kujera tabisa a baya,kallo barrister Abdul da madam dinsa Suka bisu dashi suna tsananin tausayinsu.....
******
Tunda suka shiga mota yafara driving bece Mata uffan ba har Suka iso kwanar da zata sadasu da gidan marayu Nan Fatima ta rushe da kuka tamkar wadda zaa cirewa Rai da sauri yaja burki ya tsaya ya daure fuskarsa a fusace yacee"meye haka?Zaki fada musu abinda ke faruwa ne?kokuwa satoki nayi kin tasani a gaba kinamun kuka?kissa hannu ki share hawayenki tun ban juya da motata ba"
Da sauri ta sa bayan hannunta ta share hawayenta batare da tace Masa komiba sanan ya taka mota suka wuce,horn yayiwa me gadi ya bude Masa gate a guje ya shige da motarsa sai wawware idanuwa takeyi babu abinda ya canja a cikin gidan....sai yara datake gani suna wucewa da alamar islamiyya zasu shiga,wajen da ya Saba parking ya parker motarsa bece komiba itama batace masa ba can ta hango wata na tahowa a hankali tamkar Tana kirga tafiyarta Tana kallon kasa,kafeta tayi da ido hartazo gab da motar zata gifta da sauri Fatima ta bude mota ta fito ta kwala Mata Kira "bilkisu"
Ko a mafarki bilkisu taji muryar Fatima bazata mantaba da sauri ta dago kanta zuwa inda tajiyo Amon sautin Kiran,aikuwamotar da bazata mantaba ta hanga da wata a tsaye da dogon hijabi,a guje ta runtumo da gudu ta karaso suka rungume juna hade da fashewa da matsanancin kuka,
Saida sukayi Mai isarsu sanan suka saki juna ko wannensu kallon Dan uwansa yakeyi.....
Bilkisu ce hawaye na gudu a idanuwanta ta kalli Fatima Tana murmushi tace"Fatima Ashe xan sake ganinki a rayuwata?Allah na gode maka da ka amshi adduata yar uwata ta kubuta"
Hawaye na gudu a idanuwan Fatima ta taka kadan zuwa jikin bishiya ta hada kanta da bishiyar hade da fashewa da kuka karasawa bilkisu tayi wajen ta tsaya,dik abinda sukeyi yarima kallonsu yakeyi a cikin mota shima yanaji tamkar yayi musu kuka saboda tausayi.....
Cikin kuka Fatima ta kwashe abinda ya faru da Wanda ke faruwa ta bawa bilkisu labari dukkansu kuka sukeyi,
Tsagaitawa da kukan bilkisu tayi tace"labari ya iso mana Amma cikin mu bakowa yasa niba Nima a wajen uwaliya a kitchen nakeji, alhamdulillah Allah ya kwatar Miki hakkinki Domin har gidan Nan yan sanda sukazo suka tarka hajiya da haruna gashi lokacin sun tarar Ana rigimar zainab tayi ciki hajiya ta Bata magani jini ya balle tamkar zata mutu muna cikin tashin hankali lokacin kwatsam saiga Yan sanda saida sumayiwa haruna jina jina da duka don yayi yunkurin guduwa suka tunkuda keyarsa a mota itama hajiyar da suka cafketa saida suka bubbuga Mata kan bindiga Nan fa mukai cincirindo muna kallo Ashe abinda ya faru kenan"
Girgiza Kai kawai Fatima keyi tanajin tausayin kansu da tausayin rayuwar da suka tsinci kansu labarin xainab da abinda yasameta ya matukar girgiza ta Allah sarki marainiyar Allah anyi Mata sanadiyyar lalacewa anjefa rayuwarta balai wayasan adadin wadanda sukayi ciki Ana zubarwa yanzun ne Allah ya tona asiri.....