Sashe 53
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fatima tayi nisa bilkisu ta biyota Tana kwala Mata Kira cakkk ta tsaya har bilkisu ta karaso "wallahi tun dazun ke nake nema Ina kika shiga ne?"..
Dariya bilkisu ta kyalkyale dashi sanan tace "Ina makale Ina kallon dramarku a parlor gaskiya kinyimun daidai kinyi yadda nakeso Ashe kinsan Kan zance kika tsaya da anacin ubanku?"
"Malama sun Gama cin ubana watan cin nasu ne ya tsaya Dan dik saina Rama abinda sukamun"..
"Yayi daidai ta wajena haka nakesonki"...
"Wai meye tsakaninkine da wadancan Yan biyun?Naga daya daga cikinsu Tana shige Miki nifa tsoron mutanen Nan nakeyi "
Dafa kafadar bilkisu tayi tana jinjina Kai "karki damu wadanan basuda matsala sunada kirki babu abinda zai faru kinji?Bari inje inyi wanka sharp sharp"
Ta kada Mata Kai kawai ta juya cikin gida itama ta wuce,
Tana shiga dakinta t shiga cire kayan jikinta ta taciro wadanda zata canja kafin lokacin dinner ta Ciro turarenta ta Dora Kan kayanta ta fada toilet dinta don yin wanka....
Muje zuwa
*SLIMZY 😍*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
36
Ta dauki kimanin minti goma cikin bayi Tana wanka sanan ta dauro alwala ta bude bayin ta fito Tana goge fuskarta Bata lura da ummu dake zaune gefen gado ba Saida ta juyo da nufin zuwa bakin gado ta dauki kayanta Sukai Ido hudu da ummu hannunta rike da turaren Tana jujjuyawa....ja da baya Fatima tayi hade da dafa kirji "ummu yaushe kika shigo?wallahi banji shigowarki ba"
"In Banda abinki Fatima keda kike wanka ya zaayi kiji shigowata?bayan tahowarki sadik yasamun rigima shi indomie zaici to bansamu me kawoshiba shine nazo kawoshi nadade Ina sallama waje naji Shiru shine Dana turo kofar naji a bude,sai Kuma naji karar ruwa a bayi nasan wanka kikeyi"....
Wucewa Fatima tayi wajen dressing mirrow ta dauki Mai Tana Shirin sharawa ummu ta watso Mata tambaya"Fatima me kikeyi da turaren Yan bori?turare Dan d'uri?"
Da sauri Fatima ta juyo Tana kallon turaren hannun ummu,sai ta danyi murmushi tace "wayyoo ummu turarena ne na ajiyene idan na fito wanka Nasa Kaya in shafa"
Takaicine ya lullube ummu tafara masifa Tana fadin "baki da hankali Amma,da ranki da lafiyarki Zaki shafa wanan turaren?Wanda idan kika shiga cikin jamaa na tabbatar da tushe hanci zaa rinkayi so kike ki janyowa kanki raini ma kenan cikin manyan mutane da ya'yan attajirai,to ki rufamin asiri ki rufawa kanki kar in kuskura inji kina kamshin wanan turaren Domin ni Zaki zubarwa da mutunci,ai kin wuce wanan lokacin Kuma Fatima,yanzun ke Yar gatace Yar ummu da abbah ko"...ta karashe maganar da sanyin murya yadda taga jikin Fatima na rawa,
Gyada Mata Kai Fatima tayi baki na rawa tace "insha Allah bazan shafaba ummu dama banida turarene"
Murmushi ummu ta sauke "nasani ai naji dazun kamshin turarena kikeyi koh?meyasa yanzun baki daukoshi kin Kara shafawa ba ai na mamanki ne koh"
Ta sunkuyar da kanta kasa "toh ummu"
"Kokefa yanzun gobe da wuri zansa akaiki kiyi siyayya hardasu turarruka da gyaluluwa da takalma da jakunkuna ko Yar ummu "
Dadi ne ya Kama Fatima Wanda har saida murmushi ya subuce Mata sanan ta rufe fuskarta Tana dariya,itama ummun dariya ta shigayi Tana fadin "ja'irar yarinya Zaki sa magauta suyi Mana kallon banza"
Itadai Fatima murmushi kawai take ta cigaba da shafa manta sannan ta dauki kayanta ta sanya, ta shimfida daddumarta ta tada sallahrta,bayan ta idar ne ta nade daddumar ta nufi kitchen sadik ya rufa Mata baya yayinda ummu ta Dan kishingida bacci ya dauketa....
********
Sashen hajiya karama ya sake shiga Yana dube dube ko zai ganta Amma be ganta ba ya dade ciki a zaune har kanwar hajiya ta gaji ta tambayeshi wa yake nema?ko Yana bukatar wani abune
Shafa keyarsa yayi sanan yace "dama ummu nake nema kuma bangantaba"....Nan ne ake sanar Masa da ta tafi gida,
Yana fitowa sauri sauri ya nufi sashen ummu yayinda rahane ta ruga aguje ta sanarwa da deejahmah taga yarima yayi sashen hajiya zainab da alama wajen Fatima zaije....hankalinta ba karamin tashi yayi ba tunanin yadda zaayi taje taga me sukeyi takeyi.....
Shikuwa yarima ya Dade tsaye Yana bugun kofa sanan sadik yazo ya bude Masa ya dauki sadik ya dagasa sama Yana fadin "oga sadik Kaine da bude kofa?rigima babu ko?"...ya karasa shigowa dakin Yana kalle kalle sanan ya dubi sadik yace "Ina ummu ne?"
"Tana dakin anty Fatima Tana bacci"...
"Owk Ina antyn naka?"
"Kitchen ta shiga Tana dafamin abinci"....
Jimm kadan yarima yayi sanan ya radawa sadik daidai kunnensa "jeka ce Ina kiranta"...
Da gudu sadik ya shiga kitchen din Yana fadin "anty kizo inji uncle yarima"....gabanta ne ya yanke ya fadi,Jin abinda sadik yace,da kyar ta daure ta dubi yaron tace"tsaya ka tafi da abincinka idan kaje kace Ina zuwa"...ta karasa barewa sadik kwai tasa Masa a gefenn indomie dinsa ya fice parlorn,
Saida ta Gama dauraye tukunyar da tayi amfani sanan ta fito fuskarta daure ta karaso gefen kujerar da yake zaune tadan zaune jikin kujerar,....shi kuwa yarima tunda ta zauna gefensa ya nemi natsuwarsa ya rasa,kasa jurewa yayi ganin batace masa komiba tsawon minti uku yadanyi gyaran murya yace "ranki ya dade dik fushin ne?menayi Miki kikeson yimun horo?"
Dage kafadarta tayi tai Farr da idanuwanta sanan ta Dan dubesa ta kauda Kai ta turo baki gaba tace "oho Nima bansaniba"
Murmushi yayi "sarautar Taki ta motsa kenan?shiyasa kike wani ciccin magani kina shamun kamshi"
"Wayasani"shine amsar data bashi,
Hannunta ya janyo ta fuzge hade da cewa "kaje wajen wadda kace kanada ita Mana?ai tanada hannu sai ka taba"ta murguda Masa baki
Mikewa tsaye yayi ya damki hannunta da kyau ta saki Yar Kara Tana kici kicin kwacewa cikin Jin zafin rukon da yayi Mata tace 'ni ka sakeni?da zafi Allah hannuna zai karye'...kwalla ta ciko a idanuwanta yasa hannunsa daya ya dago habar ta Yana karewa fuskarta kallo sai ga hawaye sharrr sharrr Yana gangarowa a idanuwanta....sassauta rukon yayi ya matso da fuskarsa daff da Tata "kishi bintu?kishi be kamaceki ba Domin ke ya kamata ayi kishinki ba wata ba haba fatyna"...hawaye kawai ke zuba a idanuwanta Wanda batasan dalilinsuba,
Hannu yasa Yana sharewa wasu na zubowa a idanuwanta ya matseta a jikin bango hade da shafa kanta Yana fadin "is ok banason kukan kinji?nayi laifi bazan sake cewa zanje wajen wata ba insha allahu"
Dago idanuwanta tayi ta sauke Akan fuskarsa da sauri ya shiga girgiza Kai "ya Isa banason kukan kinji?"
Kara shagwabe Masa tayi ta Dora kanta a kirjinsa cikin sigar shagwaba take fadin "Nima bansan dalilin da yasa naji wanan yanayin ba,kawai dai nasa tun daga ranan da kacemun kanada wata zuciyata tafara waswasin watarana zaka iya juyamin baya,Dan kawai nayi maka wasa sai kacemun kanada wata ni banaso kabari"...hannunsa yasa Yana shafa gefen fuskarta cikin sigar lallashi "ya Isa nadaina ai Nima wasa nayi Miki koh?".....
Turo kofar yasashi saurin juyawa kawai yayi Ido hudu da tawagar kawayenta deejahmah ciki kuwa hadda ita ko wacce da Jakar kayanta a hannunta,
Shigowa parlorn sukayi da sallamarsu a bakunansu da sauri Fatima tasa hannu ta goggoge kwallar dake makale a idonta ta shiga faraar Dole "barkanku da zuwa,kune da laasar din Nan"
Kallo kawai suke binsu dashi Dan ko wacce fuskarta dauke da mamaki,...dakyar Sunita taja numfashi cikin inda inda tace"ehh mune wallahi baki sunyi yawa can shine mukace Bari muzo Nan dik muyi wanka mu shirya a Nan idan lokacin dinner yayi ko?"
Murmushi Fatima ta sauke tadan bugi yarima dake tsaye kamar statue "yaayah kaje zan kawo maka abincin,me kakeson ci ne?"ta kifta Masa Ido,
"Nima naji shaawaer indomie din sadik Amma ni ki soyamun kwai"
"Angama ranka ya dade,ango kasha kamshi"...hannunsa yasa yaja hancinta "sai kinsha duka"
Ta Dan turo baki gaba ta juya yabi bayanta da kallo,sanan ya fakaici kallon side din deejahmah yaga ta kauda kanta tamkar batasan Yana Nan ba....
Juyawa tayi daki ta tashi ummu ganin lokacin laasar yayi Dan tayi sallah,bayan ummu ta tashi ne Fatima ke sanar Mata da tanada baki....
A parlor tagansu zazzaune Tasha mamaki Dan Bata taba tunanin deejahmah zata tako kafarta gidanta ba kila dai akwai wani dalili,..
Dan fad'ada faraarta ummu tayi tace "ah ah lallai gidana yayi albarka Yan matan amarya ne da amaryar kanta?to sannunku da hutawa"
Suka hade baki suka gaidata ummu ta amsa cike da kulawa ta shige dakinta....
Tunda suka shigo Fatima ke kaiwa da komowa a kitchen Tana hidimar abinci,
Fitowarta daga kitchen yayi daidai da Jan tsaki da deejahmah tayi tana fadin "ayi dai mugani idan tusa zata Hura wuta,ai mun rigada munsan komi munsan cewa karuwa ce"....
Cakkk Fatima ta tsaya zuciyarta nayi Mata zafi Amma saita danne ta danyi yake hade da juyowa Tana fadin "ai karuwanci ma sai a gidan yaayah wayyoo masoyi"....tace Tana murmushi ta shige,
Babu Wanda ya fahimci abinda Fatima ke nufi sai khausar da deejahmah wadanda sunsan komi su Yan matan amarya da ka kawai suke zaune,
Shigowa faizah tayi baki dauke da sallama itada Yar uwarta hannunsu rike da jaka cikin faraa faizah tace"munje can akace Kuna Nan Ashe Nan kukayo Ina ummun?"
Khausar ce tayiwa faizah nuni da Tana daki ta dire Jakarta ta shige dakin da sallamarta suka gaisa da ummu,bayan ta fito ne sukai Ido hudu da Fatima ta fito kitchen take suka sakarwa juna murmushi,
Kallon mamakin ganin Fatima cikin wanan yanayin faizah takeyi Dan rabonta da ita tun ranan da suka gaisa da yarima,
Karasawa tayi ta mikawa Fatima hannu suka gaisa suka shige kitchen din tare,kasa boye farin cikinta faizah tayi tace"kaiii k'awata haka kika koma?nayi matukar farin cikin samun yancinki Allah ubangiji ya Kara Haske a lamarinki"
Farr da Ido Fatima tayi tace "bayan tun bayan rabuwarmu ranan biki bansake jinki ba"
Murmushi faizah tayi Dan tasan ba itabace fauziyya ce kila fatimar Bata ganesuba ta bude baki da niyyar cewa ai ba ita bace aka kwalawa Fatima Kira ummu ce daga daki,
Da sauri Fatima taje"yarima yace ki Kai mishi abinda yasaki"...
Bata fuska tayi tace"ummu wlhy Yaya takuramun zaiyi nagama nasa a bascket Wai da bakin Nan nake nemawa abinda zasuci"