Sashe 54
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kin iya wahala bintu keda zaakawo musu daga cikin gida kin Kama kin dora girki?,yanzun ba wanan ba waye zai kaiwa yarima abincin kike nufi"
Jimm kadan tayi sanan tace"akwai Rahane"
"Owk"
Ta juya ta fita ta shiga kitchen da sauri Jim kadan ta shigo parlorn tsaye tayi Tana karewa kowa kallo sanan ta nuna Rahane da Mami tace cikin Isa "cikinku waye zai kaiwa ranka ya dade abinci?Domin ni naso in ciyar shi saidai hakan be samuba Dan inaso in karrama baki"...
Dibbb parlorn yayi tamkar Babu kowa,
Ta Kara nunasu da yatsa "ba saina maimaita kalamaina ba kunji abinda nace"
Dan durkusawa Mami tayi tana jinjina Kai "munji ranki ya dade"
"Shawara ya rage gareku nida bukatata a cika umarnina"...ta dire basket din a wajen,
Ta juya abinta suka bita da kallon mamaki da al'ajabi,juyowa Fatima tayi tana jifansu da mugun kallo "inhar bakuje Kun cika umarnina ba to aikinku ya Kare"
Da sauri Mami ta sunkuci basket har tana tuntube Rahane tabi bayanta a sukwane,
"Dakata,ke haka zakije hannu Babu komi?tsaya inbaki ruwan zafinsa dan nasan Yana bukatarsa"....ta juya cike da yanga duka Ido yayi kanta har kitchen din haka ta dawo ta mikawa Rahane flask Tana binta da kallon raini da wulakanci,
Babu wani musu ta amsa ta juya Tana kallon uwargijiyata,Tana Jin tsoron abinda zai biyo baya....
Jinjina Kai kawai fauziyya takeyi a ranta Tana fadin "zakici ubanki lallai kinsamu waje,a zahiri kuwa ajiyar zuciya ta sauke kawai....
Wayar khausar ce tayi Kara da sauri ta dauka ta Kara a kunnenta "ki tabbatar deejahmah ta shafa abinda na Bata a jikinta da tafin hannunta ki fada Mata sakona"hajiya rahina ke magana ta can bangaren,
Kada Kai khausar keyi kamar Tana ganinta hade da cewa "toh in Sha Allah"ta kashe wayar
Kasa tai da murya daidai kunnen deejahmah ta kitsa Mata sakon da aka Bata,tsabar takaici ya hanata amsawa da baki Kai kawai ta dagawa khausar din....
*******
Saida akayi magriba sanan ake haramar tafiya wajen dinner inda Mai kwalliya yauma tazo ta tsantsarawa amarya kwalliya a fuskarta tayi balain kyau tamkar ba itaba kamar wata sarauniyar kyau,haka Yan matan amarya ma ko wacce aka bita da kwalliya tayi musu casual ciki kuwa harda Fatima wadda tunda akafara daga girarta fuskarta tafara canja kala ko kafin agama Mata kyawun da tayi baya misaltuwa su kansu Yan matan amaryan Babu wadda Bata Yaba da kyawu irin na Fatima ba musamman da aka canja Mata halitta da kwalliya....
Ankonta dama afnan ta hada ta amso musu tare,tasa doguwar rigar fited gown na less seagreen Wanda shine ankon wajen dinner din tayi masifar kyau ya amshi fatar jikinta,
Ita kanta deejahmah Saida ta daga Ido ta kalli Fatima data gifta ta gabanta hassada da bakin ciki hade da kishi suka tarun Mata a zuciya Wanda Taji tamkar ta shake Fatima ta huta,
Deejahmah Bata manta da sakon mahaifiyarta ba tayi yadda akace,sai wani kamshi takeyi na musamman Domin Babu karya Tasha gyara.....
Faizah kuwa dik inda Fatima tayi suna tare sai hotuna sukeyi a wayar faizar saboda yadda Fatima tayi Mata kyau,
Yan matan amarya aka fara kwashewa zuwa wajen dinner inda abokanan ango gigaggun Yan boko kowa yazo da motarsa ta wanan Tana wane wanan,....tunda Fatima ta fito hannunta cikin na faizah su deejahmah na biye a bayansu da kawarta kwaya daya wadda ta rukota suka fito tare,kallo ya koma Kan Fatima dik wani Wanda yayi tozali da Fatima sai yace Masha Allah,
Sai kuss kuss abokanan ango keyi yayinda yarima ya kafeta da idanuwa yaji kishi na taso Masa ganin idon kowa a wajen na kanta,...dakyar ya hadiyi mugun miyau ya radawa Ahmad a kunne "ga bintu can ta fito ka tabbatar Kai ka dauketa sanan karka Bari kowa ya rabeta....dik Wanda ka gani kusa da ita kafada Masa matar aurece"....dariya Ahmad ya hauyi Yana fadin "Kai abokina ga amaryarka Amma ta Fatima kakeyi?kasan Allah banganetaba gara da ka fadamun Dan Nima ita nake kallo"
Wani mugun takaicine ya Kara lullube yarima ya bugi kafadar Ahmad....
Koda suka karaso Ahmad ya tarbesu ya nuna musu motarsa yace su shiga Nan ba musu Fatima ta shige fuskarta dauke da faraa...
Motar wani abokinsu Nan aka tanadarwa amarya da ango suka shiga suka zauna....take kamshin turaren deejahmah ya daki hancin yarima.....yaji wani Abu nayi Masa yawo a cikin jikinsa,Wanda ya haifar Masa da tsantsar shaawarta cikin seconds wadanda basu wuce talatin ba.....hakan ne yasashi juyowa yadan kalleta,ya kauda kansa,din Tana lura dashi...Kara gyara hancinsa yayi ya Kara shakar kamshin turaren Wanda take network din jikinsa ya fara canjawa idanuwansa suka kankance....ya shiga Dan mutsu mutsu da jikinsa a haka suke tafe a motar Amma samm hankalinsa baya jikinsa wata matsananciyar shaaawace take fuzgarsa....
Ko kafin su karasa hall din idanuwansa sun Gama kankancewa haka suka Isa wajen,Wanda suka fito tare ya riko hannunta Dan shiga hall din,dakyar yake taka kafarsa savida yanayin da take ciki,ganin ya ruko hannunta yasa deejahmah yin Dan murmushi a haka suka shiga jamaa sukai caaa suna kashe musu hoto ta ko Ina,abokanan ango suka shiga barin naira na liki har wajen zamansu....
Fatima na zaune gefen faizah Taki an dafa kafadarta ta baya da sauri ta juya wacce ta gani ce yasata saurin mikewa ta rungumeta Tana fadin "ablahhhhh wayyoo Dadi kece"
Bakin barrister hauwa yaki rufuwa Tasha leshinta me shegen tsada cikin tsananin farin ciki tace "Fatima kece haka?lallai nayi farin gani alhamdulillah"...
Dakyar Fatima ta saketa ta juya ga Ashmah dake tsaye tana murmushi "Aysha Ashe zamu sake haduwa?"..suka rungume juna cike da farin ciki suka zauna table daya da Ablah wadda mamakin ganin Fatima a wanan yanayin ya cikata....
Yarima Yana high table Amma hankalinsa na wajen fatimarsa dikda mawuyacin halin daya tsinci kansa be hanasa kafeta da wani irin kallo ba Yana kallon yadda take faraa da jamaa zuciyarsa nayi Masa tsananin lugude....
Dinner sosai ake gudanarwa inda aka umarci amarya da ango da su sauko Dan nuna farin cikinsu deejahmah na gaba Yana biye da ita idanuwansa suka sauka akanta abinda yakeji ya sake karuwa a jikinsa fiye da dazun,Koda yazo daidai ita besan lokacinda ya rike kugunta ba suna rawa a haka a hankali Mai ban shaawa nanfa jamaa sukai caaa wajenyi musu liki,idanuwan Fatima kyarrr akan hannun yarima dake sagale da deejahmah....dakyar ta sauke numfashi ta Mike cike da yanga ta karasa daf dasu ta bude Yar pos dinta da ummu ta Bata da canjin Yan hamsin hamsin ciki, ta shiga yi musu liki, hajiya babba na gefe tanayi musu, batare da ta lura da Fatima dake gefenta ba,....kallonsa takeyi Ido cikin ido shima idonsa Yana kanta ya sakar Mata da lallausan murmushi,kasa mayar Masa tayi saboda abinda takeji cikin kirjinta.....daga inda yake Yana iya hango Yar kwallar data taru cikin idanuwanta...a haka takeyi musu liki Tana kallonsa Yana kallonta,ganin haka yasa deejahmah babu kunya ta kwantar da kanta gefen kafadarsa....
Saida kudinta ya Kare ,ta juya Tana taku daidai cike da yanga da izzah Wanda Saida ta dauke hankalin daukakin jamaar dake fuskantar wajen,....maimakon ta koma table dinta sai tayi hanyar fita hall din,a idon yarima,Wanda tunda ta juya yabita da kallo zuciyarsa tayi Masa nauyin gaske, gabansa ya shiga tsananin faduwa hade da firgici lokaci daya ya furta a zuciyarsa....."Ina Fatima zataje?"abinda ya tambayi kansa kenan..ya kasayin wani yunkuri sai dai gabaki daya ya rasa yanayin da ya tsinci kansa...Dan ba karamin furgici ya shigaba,
Hankalinsa baya jikinsa deejahmah na lura da yanayinsa Amma sai ta share,...
Ganin Fatima tayi wajen hall din yasa Ahmad dake gefensu Yana kallon dik abinda ya faru,yayi saurin juyawa ga abokinsa ya Mika Masa drink din dake hannunsa yabi bayanta....
Murmushin mugunta deejahmah tayi a fakaice hade da lumshe idanuwa ta budesu....wani farin ciki ke ratsata Domin tunawa da tayi da plan dinsu na gaba.....
*Muje zuwa*
*SLIMZY😍*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
_Ku shaida na sadaukarwa_ *SUNITA* _wanan shafin _kyauta saboda tsananin kaunarta ga wanan littafi inayi Miki son so bae😍_
37
Hanyar fita gate Ahmad yaga tayi da azama ya daga muryarsa yace "Fatima"....cakkkk ta tsaya hawaye na gudu a fuskarta wadanda ita kanta batasan dalilinsu ba a haka Ahmad ya taddata tsaye ko motsin kirki batayi sai hawaye dake gudu a fuskarta,
"Meya faru kika fito Nan Ina zakije?Kuma?sokikeyi wani Abu ya sameki?"....dakyar ya karasa zancensa da yayi tozali da fuskarta wadda ta jike da hawayen bakin ciki,
Shiru yayi hade da zura hannunsa cikin aljihun wandonsa batare da yace kokiba,
Hajiya zainab ce ta fito daga hall din kunnenta manne da wayarta da alama waya takeyi Tana fadin "idan Kun shigo kuyo hannun damanku zakuga hall din akwai motoci wajen Ina kofar gate"...kamar a mafarki take ganin fatyma tsaye da wani tun daga Dan nesa dasu ta Gane itan ce harta karaso wajen Tana Taku daidai takalminta Yana Kara kwass kwass Wanda shine ya dauki hankalin Fatima ta juya da sauri Dan ganin waye,Aiko idanta ya hadu Dana ummu a guje ta fada jikinta ta fashe da kuka Tana fadin "muje ummu ni banason zaman wajen Nan tafiya zanyi"cikin kuka take maganar harda shassheka,...ba karamin tashin hankali ummu ta shiga saboda irin kukan da taga fatyma Tana rusawa ta Kara rungumeta Tana fadin "me akayi Miki wanene?fadamun ko waye shi sai na tabbatar ya zubar da hawaye kamar yadda kika zubar"....kuka kawai takeyi Tana Kara kankame hajiya zainab,..
Juyowa ummu tayi tanayiwa Ahmad kallon tambaya,da kyar ya sauke numfashi yace "ummu wallahi bansan meya faru ba kawai dai Naga Fatima ta fito hall a yanayin yadda ta fito nasan akwai wani Abu shine kika biyomu Kuma ni Bata ma yimun magana ba"
Ajiyar zuciya ummu ta sauke daidai Nan babbar kawarta ta shigo da motarta,wajen da sauri ummu taja Fatima a hankali har sunfara tafiya ta juyo ta kalli Ahmad "jeka kawai Bari muje gida"...
Wajen motar kawar Tata suka karasa daidai Nan ta sauke glass din motar Tasha kwalliya itada yaranta Yan Mata guda biyu cikin faraa tace "ranki ya dade muje ciki koh"..
"Ah ah muje gida kawai ku saukeni yata Babu lafiya"....