← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 80

Sashe 39

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikinta na tsananin rawa tace"umm...ammm..dama aiki aka Sanya Fatima tun safiyar jiya muke kwasar Kaya tare to shine Bata gamaba har dare naje na zauna tare da ita"

"Me kikace?bilkisu kinsan me kike fada kuwa a wancen dakin kuka kwana?dakin da manyan maza barada jarumai ke tsoron shiga saboda mugayen kunamu da macizai da iskoki dake ciki kike nufin kuka kwana"

"Ehh Nan muka kwana yanzun haka ma faty Tana ciki kunama ta cije...."

Ai kafin ta karasa ta.. din yarima yayi wani irin zabura ya juya a guje ya nufin dakin.....

Kallo bilkisu tabisa dashi cikeda tausayi ta Mike ta nufi hanyar cikin gida Dan idan har ta koma tabi bayan yarima to tabbas asirinsu zai tonu batada zabin daya wuce ta lallaba ta shige ta kwanta....

Banko kofar yarima yayi Yana huci ,Tana ganin haka ta zabura hade da zaro ido tanajan jiki baya,ganin mutum da farar jallabiya ya Kara tsinkar Mata da zuciya.....

Gadan gadan ya shigo yayo kanta Yana fadin "bintu?nine yarima ki kwantar da hankalinki?Babu abinda ya sameki?menene"

Rushewa da kuka tayi tanayi Masa nuni da kafarsa Wanda sai lokacin idonsa ya sauka Akan kafarta wadda tafara kumbura "innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"...shine abinda ya furta a Fili da sauri yasa hannunsa ya sunkuceta a kafadarsa ya fito....a guje a guje yayi bangaren sa da ita batare da kowa ya gansuba....

Bai sauketa a ko inaba sai Kan babban gadonsa,yasa hannu ya cire jallabiyar jikinsa data bacci da datti da kurar dake jikin Fatima yayi jifa da ita,

Bathroom ya fada ya dibo ruwan zafi a Yar roba ya dauko towel yasa ciki ya zubo detol Dan kadan yazo bakin gadon,da hannunsa ya warware daurin da bilkisu tayiwa Fatima ga kafar Nan ta kumbura tayi jajir ya tsoma towel din ya shiga Danna Mata ai wata gigitacciyar Kara data saki yasa yayi watsi da robar ruwan zafin yayo kanta,ya janyota jikinsa ya rungumeta tsammm Yana shafa bayanta Tana kuka sosai "Dan Allah karka samun ruwan zafi ka taimakamun Dan Allah mutuwa zanyi Karin Nan Yana yawo a jikina"

Tausayinta ne ya lullubesa ya Kara rungumeta sosai a jikinsa yajin sautin kukanta dake fita dakyar saboda wahala...baisan lokacinda shima hawaye ke dugowa a idanuwansa ba,ya Dan dago kanta ya sumbaceta a goshinta.....idanuwanta a lumshe hawaye na gudu

Kallo ya kure fuskarta dashi yadda hawaye ke gudu a idanuwanta,fuskarta tayi jajir saboda tsabar kuka bakinta ya bushe kayau tamkar ta shekara bataci wani abuba....rungumeta ya karayi a jikinsa yasanya yatsansa Yana zagaye lips dinta dashi....

Ganin tayi shiru ya shimfideta Kan pillow,ya sauko ya shiga toilet ya dauko mopper da kansa ya goge inda ya barar da ruwan anata kiraye kirayen sallar asuba....ya dauro alwala ya kasa zuwa masallacin saboda tsabar tausayinta....dadduma ya shimfida ya tada sallah har ya idar idanuwanta na Nan a lumshe Amma yasan ba bacci takeyiba tsabar azaba ce....

Drawer jikin gado ya janyo ya Ciro paracetamol ya ballo ya dauko ruwan swan dake gefen gadonsa yazo da kansa ya tallabota jikinsa,...hannu tasa ta zagawo ta bayanshi ta kwantar da kanta a kirjinsa dik idanuwanta a rufe....

Daidai fuskarta ya sunkuyo yana Jin sautin futar numfashinta Mai zafi da alamar zazzabi takeyi ya furta a hankali "bintu Dan bude idonki kinji Kisha wannan maganin zai rage Miki radadi"

Bude idanuwanta tayi ta saukesu Akan nasa idon ta Dade Dana kallonsa sanan ta turo baki ta makale kafada "nifa banason magani"

Daidai fuskarta ya kusanto da bakinsa yana Mata Rada"sai allura?"

Da sauri ta shiga girgiza Kai "ah ah banaso"....murmushi yayi ya shafa fuskarta "to me kikeso babyna?"

"Ni bakomi"

"Yi hakuri Kisha maganinki kinji zakiji Dan sauki kafin yanzun inkira doctor Ahmad ya dubamin ke"

Dago Kai tayi ta Bata fuska tamkar zatayi kuka "Amma dai bazaimun allura ba ko"

Kallonta kawai yakeyi yadda take shagwaba Tana shigewa jikinsa shikadai yasan me yakeji....zuciyarsa ke ayyana Masa inama matarsa ce?yau da har wanka zaiyi mata😨🙆🏻(kuji yarima da dangaga"....

"Kisha ba abinda zaiyi Miki bazan bariba"

Baki ta bude ya zuba Mata maganin hade da sa Mata bakin gorar a baki ta shiga Shan ruwan Nan babuji Babu gani dama kishi takeji...shiko kallonta kawai yakeyi cike da tausayawa....Saida Tasha Rabin gorar ya janye ya kashe Mata ido "karki shanye kiji fitsari Dan Babu Mai kaiki bayi"

Turo baki tayi hade da Dan harararsa '"kaifa"....ta cije lebenta saboda azabar da takeji a kafarta....

Yana lura da yanayinta yasan tanajin jiki Domin cizon kunama Babu Dadi....Yana rungume da ita idanuwanta a rufe yaji saukar numfashinta ya canja alamar tayi bacci...a hankali yaja jikinsa daga nata yasa pillow ya kwantar da ita ya fada toilets Dan yayi wanka.....

Har ya fito Tana bacci yadan kalleta yaga yadda minti minti take sauke ajiyar zuciya,wardrobe ya bude ya Ciro kananan kayansa ya sunyi matukar karbar jikinsa ya feshe jikinsa da turare ya fice ya janyo kofar...

*********
Dik inda ya suce kuyangi da bayi na gidan ke famar tsegumi na baaga Fatima ba tun jiya,Kuma har wajen masu gadi anje sunce basuga fitarta ba....

Sashin mahaifiyarsa ya nufa Nan ya gaisheta bayan sun gaggaisa har ya Mike zai fita ta tsaidashi "Wai kasan abinda ke faruwa kuwa?"

Da sauri yarima ya girgiza Kai Yana kallonta,

"Wai wanan yarinyar ce baaganta ba Fatima,tun jiya da Rana naji su hajiya sun aika kiranta Babu ita to kowa ya dauka Tana bakin aikintane Amma har safe baagantaba kasan hakkinta na wuyanmu fa dole asan makama"

Murmushi ya kubucewa yarima yace a ransa "Ashe dai kinasonta"...canja fuska yayi zuwa tsananin damuwa yace

"Tana Nan mama Amma Babu Wanda yasan inda take"

Wani kallo ta wurga Masa "kaika saceta kenan"

Cikeda ladabi ya Soma magana "mama yarinyar Nan fa kunama ce ta harbeta"

Da sauri mama karama ta ce "innalillahi yanzun Tana ina?,...sai Kuma ta wayance daga kidimewar da tayi tace"Allah ya kyauta saika kaita wajen malam ya'u ya dubata kasan anbashi daki gidan waziri"

Sarai yarima ya lura da basarwar da mahaifiyarsa tayi yasan halinta Sarai yasa shima yace "to shikenan Amma mama kiyimun alfarmar Kar kowa yaji anganta har saina kaita an duba kafar na dawo da ita"

Harararsa tayi hade da kada Kai kawai.....

*********
A dakin hajiya babba ya tarar da ita cike da farin ciki,bayan sun gaisa sama sama ta amsa Masa gaisuwar....

"Algungumi to Yar daka kawo ta gudu inace kaji labari"

"Naji hajiya Amma Ina kyautata zaton Tana cikin gidan Nan tunda masu gadi sun sanar Mana da cewa baaga fitarta ba sanan katangar gidan Nan tayiwa Fatima tsawon da zata haure"

"Kaidai kasani yau saika tanadi karyar da zakayiwa Mai martaba,Domin yau yace zai Yankee hukunci Kuma Yana bukatar kowa da kowa daga Kai har deejahmar zakuzo fada har ita Fatima dazun ya fadawa sarkin fada yazo yake sanar mun"

"Allah yasa a ganta"yarima yace hade da sunkuyar dakai..

"Ba Amin ba bakar jaraba Allah ya Kara kadata"...

Murmushin gefen kumatu kawai yarima yayi batare da yace uffan ba ya Mike ya fice,hajiya babba ta bishi da harara...

Yana fita ta sheke da dariyar mugunta,Allah yasa bayan fyade da isyaku yayi Mata ya kasheta uban kowa ma ya huta,....wayarta ta janyo ta Kira hajiya rahina ta sanar Mata da sakon Mai martaba da abinda ta faru sukai sallama.....

*********
Murna a wajen deejahmah baa magana jin labarin Fatima ta bace baagantaba har rawa Saida tayi burinta ya cika a cikin ruwan sanyi.....

Ji takeyi tamkar ta janyo bayan sallahr laasar suji Mai sarki zaice yake nemansu?minti minti take sauke murmushin Jin Dadi...

********
Yarima Yana fita direct gidan Ahmad yaje ya daukosa ya sanar Masa da abinda ya faru saboda haka a gaggauce suka dawo gidan ko sashinsu hajiya Ahmad be jeba direct sashin yarima sukaje....

A durkushe ya tarar da Fatima a kasa gefen bayi tayi zufa sharkaf Tana yarfe hannu da sauri yayi kanta "menene Fatima?"

A wahale ta bude baki tace"bayi zan shiga cikina ke murdawa gashi kafata tamun nauyi"

Kinkimarta yayi ya shigar da ita bayin ya fito ya janyo Mata kofa suka koma parlor shida Ahmad....

A furgice Fatima ka kallon cikin toilet din ganin zawon da tayi ya canja kala zuwa jini jikinta ya hau rawa tasa ruwa tayi flushing ta daddafa bango ta fito dik a tsorace take menene wanan ya fito a cikinta ?...kashin jini?....meyasameta? innalillahi shi kawai takeyi....

Jin karar fitowarta yasa yarima shigowa bedroom din da sauri yaganta zaune gefen gado tanata zufa ga kuka tanayi "menene Kuma bintu?kafarce?"

A shagwabe tace"jini nagani kashin jini nakeyi"...

Waigowa yarima yayi Yana fadin "friend zokaji Wai kashin jini tayi"

Da sallamarsa Ahmad ya shigo Yana murmushi "ka kwantar da hankalinka sharrin cizon kunama ne Karin ne yake fita ta bayan gida tayi arziki already nazo da allurar da zanyi Mata takara samun sauki"

Ai Fatima najin zancen allura ta fashe da kuka Tana fadin "wallahi na warke tunda k'arinta ya fita Dan Allah karkamun"

Tausayinta ya lullube yarima ya riketa da kyau Yana fadin "Babu zafi nine zan rikeki a hannu zaiyi Miki ma daidai tsoka kinji"

Kwantar da Kai tayi a kafadarsa Tana shasshekar kuka haka ya juyar da ita cikin dabara aka tsira Mata allurar,sai kuka takeyi Tana shagwabewa a jikinsa shiko Yana aikin lallashi...

Fita yayi yakira bilkisu cikin gida ya Bata umarni da ta kawo musu abin karyawa....

Baafi minti gomaba saiga bilkisu dauke da tray hannunta daya rike da flask ta shigo sai zare Ido takeyi Ahmad Yana ta daddana waya yarima na gefensa,

Darewa Ahmad ya sheke dashi Yana kallon bilkisu dake wurga idanuwa....da sauri yarima ya juyo yaga dariyar me Ahmad keyi shi kansa yadda bilkisu keyi da idanuwa ga uban datti tayi Saida yadan murmusa ta gefe...

Daure fuskarta tayi ta gefe ta kalli Ahmad dake dariya,wani kululun bakin cikine ya tsaya Mata a kirji Tana ajiyewa ta yi hanyar kofa"ke bilki karki nisa kijirani kofar sashina zan nemeki"

Takaicine ya lullubeta na dariyar wulakancin da Ahmad keyi Mata yasa dakyar ta bude baki ta amsa a ciki ta fita ta rufo kofa garammmm

Kallon juna sukayi shida Ahmad sukai dariya "kasan Allah abokina kadainawa kanwata dariya Dan kaganta haka?jarumace"
Chapter 39 · 0% Book details