Sashe 51
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ran Mai martaba ba karamin baci yayiba a fusace ya karbe zancen da "ai yarinya ya'ntacciya ce Domin yace kamar kowa tunda baa yaki aka siyota a kasuwar bayi ba balle a kirata da baiwa sanan maganar kikeso a yantata?aike kin Isa ki yanta kowa a gidan Nan Domin inda ke macece da idan na mutu banida da' namiji kece Zaki gaji mulki bayan ni Domin bayan yayana da Allah ya saukarwa kaddarer rashin lafiya ai saini saike sanan ita rahinar saboda haka ni da kaina na ya'nta Fatima na Kuma danka Miki amanarta halak malak harabada nabaki Fatima diyarkice"
Juyowa hajiya zainab tayi ta kalli Fatima ta bude hannuwanta ta fada jikinta ta rungumeta Fatima ta fashe da kuka Mai ban tausayi,
Mai martaba ya dubi Fatima wadda ke faman kuka yace "ke Fatima daga yau na mallaka Miki kanwata jinina ta Zama mahaifiyarki Niko dama a matsayin ubanki nake Kuma harabada a haka muke har karshen rayuwarmu idan Allah ya nufemu da ganin iyayenki shikenan idan bamu gansuba kina Nan a Yar amanarki kinji?ki share hawayenki inajin kaunarki cikin jinin jikina kamar khaussr da ummul khairi".
Tsittt fadar tayi bakajin karar komi sai karar AC da fankar sama dake aiki a hankali.....
Murmushi kawai ummu takeyi Tana jinjina Kai "nagode ranka ya dade Allah ya bani ikon rikon wanan Amana da aka bani"...
"Ameen"..yarima ya amsa sanan Mai martaba ya shigayi musu nasiha Mai ratsa zukata Akan muhimmancin Amana da rikon maraya Wanda Saida jikin kowa yayi sanyi a wajen Banda hajiya babba da rahina wadanda inda zaasa takadda a zukatansu sai sun Kama da wuta....
Saida ya Gama nasiharsa sanan ya bawa kowa damar yin magana Amma kowa yace bashida abin cewa sanan yasa suka yafi juna gaba dayansu sanan akayi addua aka watse a wajen....
Ummu ce ta ruko hannun Fatima ta fito tare da ita daga fadar wajen goma na dare taron ya tashi....
********
"Wanan makircin shiryayye ne yanzun na gano inda suka dosa Amma in Allah ya yarda bazasuyi nasara ba,idan zainab tayi nasara wanan karon to tabbas zamu hadu a Wasa na gaba"...cewar hajiya babba dake faman sunturi cikin dakin zuciyarta tamkar ta fashe Dan takaici,
Kuka kawai deejahmah takeyi ta kifa kanta jikin mahaifiyarta Wanda Nan da Nan jikinta yayi zafi rau zazzabin Dole ya rufeta,
Hannu hajiya rahina taka jikin deejahmah Taji yadda ya dau zafi tamkar wuta ga kuka da deejahmah keyi Wanda hakan ne ya haifar Mata da zazzabin tsabar kuka muryarta har dishewa tayi,
Tunda Taji hukuncin da Mai martaba ya yanke tayi jifan bori a tsakar dakin hajiya babba tamkar Mai aljanu ta shiga rera kuka,
Dago fuskarta tayi wadda tayi jajir saboda tsananin kuka ga hawaye ya wanke Mata fuska tace cikin dasasshiyar murya "mama da hajiya kuyi wani Abu Akan wanan lamarin,banaso Fatima ta shigo gidana a matsayin kishiya hakan babban ci bayane a wajena"
Hajiya babba na tsaye hannayenta goye a bayanta ta sauke gwauron numfashi "ni saina haddasawa zainab da Fatima takaicin da har su mutu bazasu manta ba Domin wanan abun da zainab tayi ta farkar Dani daga gyangyadin da nakeyi da farko na farka Kuma din sainaci uban Yan iska"....
"Hajiya yanzun me kike ganin zaayi"hajiya rahina tace cike da kosawa,
"Akwai abinda na rigada na amso wanan ruwan wanda a lissafi gobe zatasha ta wanke fuskarta dashi,sanan akwai abinda zansa ayi, Wanda ba sai wani yayi amfani da shi ba, turen aljanu kawai zansa ayiwa shegiya ta haukace tabi bola uban kowa ma ya huta"
Ruko kafar hajiya babba tayi tace"ki taimakeni hajiya Kar wanan auren ya yuwu"ta rushe da kuka durkusawa hajiya babba tayi ta zauna ta janyo deejahmah jikinta Tana lallashinta.....
Ko wannensu sakawa kawai yakeyi Yana warwarewa yayinda ko wani sashe na cikin gidan Shiru kakeji kowa da gulmarsa cike da cikinsa,haka bayi da kuyangin gidan suka hade kansu suna famar gulma sai kuss kuss ke tashi cikin gidan,dik wata hayaniya da akeyi a cikin gidan biki ranan Babu ita daddare tamkar anyi mutuwa....
********
Bayan sun shiga sashensu hajiya zainab ta umarci Fatima da taje ta dauko kayanta wadanda tace Mata tanadasu,
Babu musu Fatima taje dauko kayanta dik inda ta gifta sai a bita da kallo tamkar wata sabuwar halitta,ita kanta sai takejin kanta wani iri haka ta ciccibo akwatinta tayo gidansu dashi ciki kuwa harda jakar ledar da fauziyya ta Bata ta dawo ...
Wani daki Mai dauke da madubi da gado madaidaici da bayi a ciki hajiya zainab tacewa Fatima shine mallakinta Dan dadi Fatima batasan lokacin da ta rungume hajiya zainab Tana kukan farin cikiba"Allah ya bani ikon faranta Miki Rai kamar yadda kike faranta mun,Allah ya bani ikon yi Miki biyayya tamkar uwar data tsugunna ta haifeni nagode Allah ya saka Miki da mafificin alherinsa uwata"....ita kanta hajiya zainab Dan Dadi batasan lokacinda kwallar farin ciki ta taru a idanuwanta ba take kaunar yarinyar ta Kara shiga zuciyarta ta shiga bubbuga Mata baya Tana shafawa a hankali sunkai minti uku a haka kafin hajiya zainab ta zaunar da ita a gefen gado Tana murmushi tace "ke bakisan nauyi garekiba ai saiki yarda umman Taki"
Murmushi Fatima tayi"Kai ummu ya zaayi in yardake bayan banida nauyi"
Dariya sosai hajiya zainab keyi lokacinda Taji kwankwasa kofa ta tsagaita ta waigo ta kalli agogo Sha daya saura na dare tace "bintu tashi kije kiga wake buga Mana kofa"
"Toh ummu"ta yunkura zata Mike ummu ta dakatar da ita da cewa "ko shiga kiyi wanka dare nayi ki tsaftace jikinki kicire wanan muguwar rigar idan kinfito ki duba waccen drawer akwai sababbin kayan bacci irin na Yan Mata kala kala ki duba ki dauka kisa Ina zuwa Bari inje"
Ta fice daidai Ana kwankwasa kofar Tana fadin "waye wanan zai karyamun kofar gida"ta karasa ta sa key ta bude,tayi tozali da yarima tsaye Yana yatsina fuska ta watsa mishi wani kallo "me Kuma ya kawoka gidana daddaren Nan me kazoyi"..
Ratsa gefenta yayi ya wuceta Saida ya shiga parlorn yake fadin "wallahi yinwa nakeji tun safe banci komiba"....
"Saikace wani jariri dik bayi da kuyangin dake sashenku a rasa Wanda zai dafaa maka abinci sai kazo Nan da tsohon Daren nan?to uban wa zai dafa maka anan din badai niba ko?"
Sosa keyarsa ya shigayi Yana dariya kasa kasa "Kai ummu ga Fatima a Nan?"
"Au Yar aikinka ce ita?Koko ka aureta ne da zakazo kace tayi maka dahuwar abinci?"
"Ummu Wai yau kadai kin canjamun saboda kinsamu Diya kin yaye yaronki?haba ummu nine fa kabiru autan ummu"
"Kaidai kasani kaji da gulmarka diyata wanka take saita fito"
Ta wuceshi ta shige dakinta,Jim kadan ta fito da Shirin bacci ta zo parlor ta zauna ta dauki remote ta canja Tasha sanan ta kwalawa Fatima Kira...
"Bintu"....Jin sunan da ummu ta Kira yayi sauri ya kalleta Domin a iya saninsa shi kadai ke kiranta da hakan,Koda yake ba abin mamaki bane don yaji hk a bakin nata Domin kusan halayyarsu daya....
Fitowa tayi sanye da Wando da Riga na kayan bacci milk colour masu taushi da shegen kyau fuskarta fayau ko Mai Bata shafaba Amma hakan be hanata yin kyau ba,
Sarai hancinta ya sanar Mata da kamshin turarensa Amma saita kauda kanta wajen da ummu take ta Dan durkusa cikin ladabi tace"gani ummu"
"Wanan fitinannen ne Mai kamar Dan yaye yazo ya fitineni Wai yunwa yakeji shine nace ki dafa Masa ko indomie ne"
"Akwai Miya a fridge wadda nayi shekaran jiya nasan batayi komiba Bari a dafa farar taliya"....
Mikewa ummu tayi tana zabga hamma "to Bari inshiga ciki idan kin Gama Masa kisa mishi a flask ya tafi Dashi don dare yayi"
"Owk".. kawai tace ta wuce ya bita da wani mayen kallo,ummu na kallonsa ta gefen ido ta girgiza Kai Tana murmushi ta shige dakinta....
Kusan minti uku da shigan Fatima kitchen ya kurawa kofar kitchen din Ido ko zata fito shiru tsulum ya Mike ya shigo kitchen din ya tokare hannunsa a kofa Tana fadin "Wai har yanzun baa Gama abicin bane?"
Batace masa komiba ta cigaba da aikinta,ya karasa shigowa ciki ya tsaya daf da ita ya tsareta da idanuwa kamar zai cinyeta dik inda ta motsa sai ya kalleta,..
Gajiya yayi ya sauke ajiyar zuciya yace "malama sarautar ta motsa kenan yau baajin kulani?"..
Harararsa tayi ta gefen ido batare da tace komiba ya ko Kai hannu ya rike hannunta ta kwace hannunta tace cike da tsiwa"kaje ka rike hannun matarka cikin mutane ni ka lallabo kazo zaka rikeni kayimun wayau bayan aure zakayi ka barni wayasani ma ka Gama tabani kazo baka aureniba"
Da sauri yasa hannu ya toshe bakinta da hannunsa"idan nasakejin wanan kalmar a bakinki saina datse harshenki"
Tasa hannu ta cire hannunsa daga bakinta ta turo baki gaba "ni kazo ka Hana mutum bacci kanasani aiki"
Yar dariya yayi hade da gyara tsayuwa "Kuma Dole kiyimun ba Kuma ki bani abincin inba haka ba inje wajen wata tunda na fahimci kishi kikeyi"...
Dago Kai tayi tana kallon fuskarsa tana sauraron abinda yace Wanda Nan da Nan ranta ya baci wani kishi ya turnuke ta da kyar ta janye idanuwanta daga fuskarsa Wanda yake jifanta da murmushi,ta kada Kai kawai ta kashe gas ta tsiyaye ruwan taliyar ta wanke Tass ta tsane a kwado ta ciro flask ta zuba Miya daban taliya da ban da Dan karamin flask na ruwan zafi Wanda yaji citta da kayan kamshi ta harhada Masa ta janyo basket ta sasu ciki ta ruko ta wucesa a bakin kofar kitchen ya bita da kallo ya dage kafadarsa sama ya biyota a tsakiyar parlor ta dire Masa ta dago jajayen idanuwanta ta jefesa da wani mugun kallo tace "Allah ya ta shemu lafiya"....Bata jira cewarsa ba tayi wucewarta ta shige dakinta ko kafin yayi wani yunkuri ta rufo kofar dakin garammmm
Kamar wani Wawa haka yake kallon kofar dakin ya Dade tsaye sanan ya dauki basket dinsa ya fice ya rufo musu kofa....