← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 80

Sashe 21

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka har suka iso kofar da zata sadasu da babban sashi na gidan inda bayi ke tsattsaye masu tsaron kofar sashin take suka zube kasa suna kawo gaisuwa hannu kawai ya daga musu ya wuce Fatima na biye dashi.....

Shi kansa uban gayyar cikin faduwar gaba yake saidai a fuskarsa ya tsare gida da jarumtaka irin tasa tun kafin su saka kafa a parlorn ya jiyo muryar gwaggo rahi....dammm gabansa ya yanke ya fadi haka kawai yaji zuciyarsa na bugawa sauri da sauri haka ya jajurce ya daga labulen dake zagaye a kofar yayi sallama"Assalamu alaikum"...fuskarsa a dake,

Labewa Fatima tayi a bayansa taki shigowa dukkansu suka zuba Masa ido ganin yanayin yadda ya daura fuska Yana waige waige kamar Mai neman wani Abu a dake yace"Fatima shigo Mana ya kika tsaya a baya"

Fatima da kafafuwanta da ilahirin jikinta ke rawa tamkar ta saki fitsari haka ta daga kafarta ta daga labule ta shigo da sallama a ciki.....

Wani zabura da hajiya babba tayi nikaina saida na koma gefe a guje na labe a bayan labule Ina kallon ikon allah😂😂😂....gogan na hango ya dake fuskarsa babu annuri

Hajiya babba da dik wani mahaluki dake dakin saida ya furgita tamkar sunga abin tsoro jikin hajiya babba Yana tsuma kamar anayi Mata gangi tace"lallai kabiru ka cika Dan halak ka nuna Mana cikakken Mara kunya ne kai fitsararee wato matsiyaciyar yarinyar Nan wulakantacciya ita ka dakko ka kawo Mana muma ta biyo dare ta kashemu?kamar yadda ta kashe habibu Kuma ka goyi bayanta to karyarka Tasha karya kayi kadan wallahi"bakinta har kumfa yakeyi....

Da sauri gwaggo rahi ta juya Tana kallon yarima dake tsaye kamar an dasashi Fatima a guje ta koma bayan yarima ta makale ganin yadda hajiya babba ke surfa balai,

Dafe kirji gwaggo rahi tayi tace"kabiru tsintacciyar mage ka dauko ka kawo masarauta?kabiru Anya ka shirya gaskiya a lamarinka"

Da sauri hajiya babba ta karbe zancen tace"Ina gaskiya a lamarinsa,aini tunanina gabaki daya ya canja akala Akan hada baki sukayi ta kashe habibu ya daukota ya kawota ta biyo dare ta kashe Mai martaba to kayi kadan wallahi kayi tsararo"

Zuciyar yarima zuwa wannan lokacin ta Gama konewa tamkar zata Kama da wuta yakeji tunda yake be tabaganin mutane masu son Kai da son zuciya kamar mutanen masarautarsuba,

Bude baki yayi zaiyi magana"hajiya...."

Daga Masa hannu hajiya babba tayi tace dakata kabiru ai *ANYI WALK'IYA* asirinka ya tonu wanan abun da kayi Kai Mai tausayi Mai Jin Kai na maraya kaiga malam sarkin son lada da musulunci ya nunawa duniya inda ka dosa sanan hakan ya tabbatar munda da hadin bakinka aka kasheshi dana uwarka don dik abinda kuke kullawa Yana dawowa kunnena,yanzun Kun kulla makirci Akan a daukota a dawo da ita Nan saita karasa contract din daka Bata na kashe sarki da habibu Dan ka hau karagar mulki ko to kayi kadan wallahi kasake sabon shiri"

Wasu irin zafafan hawayene ke gudu a idanuwan mama karama wadda ta kafe yarima da ido tun shigowarsa sai yanzun tasamu halin magana"burinka ya cika kabiru abinda nake guje maka gashi ka daukowa kanka Nima ka daukomi"

Hankalin yarima ba karamin tashi yayiba ganin mahaifiyarsa na kuka,cillar da Curt dinsa yayi dake hannunsa ya ruga da sauri ya zube a gabanta ya fashe da kuka Yana fadin"Dan girman Allah ki daina zubar da hawayen Nan a gareni Domin hawayen uwa a wajen danta dafi ne daidai da second daya kikayi fushi Dani bazanga da kyau ba ban dauko Fatima na kawota gidan Nan Dan intozartaku intozarta martabarku ba nayi hakan ne Dan in nemawa masarautarmu kima da daraja a idon mutane duniya zatasan cewa ku masu adalcine tunda danku shi yayi kokarin lalatawa marainiyar Allah rayuwa ta kasheshi kuka daukota kuka inganta Mata rayuwa har a wajen Allah kunada lada Mai yawa wallahi summa tallahi bazan iya Bari rayuwar Fatima ta cigaba da wulakantaba"

Dariya hajiya babba tayi maicin Rai tace"ai rayuwarta ta Gama wulakanta tunda uwarta cikin shegenta tayi ta haifeta ta Yar a bakin kwata gwamnati ta tsunta wulakanta ta karewa Dan kwararo Dan Fatima batada maraba da yayan kwararo"

Runtse idanuwa Fatima tayi hawaye na gudu kamar an bude famfo a idanuwanta tunda Allah ya halicceta Bata taba tozarta irin na yauba dik wulakanci da cin kashin da hajiya halima keyi musu a gidan marayu be Kai wanan ba inama ace Allah ya dau ranta da wanan wulakanci da tozarci datake fuskanta a cikin wannan duniyar Mai cike da kalubale kala kala.....kuka Fatima ta fashe dashi Mai karfi....

Wani kallon tsana Mai hade da kyama hajiya babba ta wurgawa Fatima jitakeyi kamar ta shaketa a duniya batada makiyin da yakai Fatima bayan mutuwarta,takowa takeyi Tana wani girgiza tamkar giwa tazo har inda Fatima ke tsaye Tana rizgar kuka ta nuna Fatima da yatsa a wulakance tace"jibeta kamar ta Allah,har wani kuka kikeyi irin na munafukai tsofaffin kilaki masu shegen makirci ko kinzone ki yaudaremu kici amanarmu to kinyi kadan wallahi Ina Mai gargadinki da babbar murya tun wuri kisan inda dare yayi Miki ko ki koma can gantalin kwararon ko ki nemi wani wajen Amma ba gidan Nan ba shima Wanda kuka hada baki dashi aka kashemun gudan Jini kijira sakamakonsa"....takaiwa Fatima hankada jikin bango ji kake kummmmmm.....dafe Kai Fatima tayi juwa na dibarta ta zube a kasa ta saki kuka....

A zuciye Kabir ya kalli hajiya babba yace"menene aibun maraya?menene illar Dan da aka tsinta aka mikawa gwamnati ta Zama uwarsa da ubansa?shin kunada tabbacin Fatima tsintacciyace?bakwa tunanin iyayenta a tafarkin sunnah suka haifeta wata kaddarace ta rabasu?kunsan makomar Mai wulakanta maraya da cin zarafin maraya kuwa?Allah yayi alkawari dik Wanda ya zalunci maraya daidai da kwayar zarra sai Allah yayi masa sakayya bai kamata Fatima ta Zama abun kyama a wajenmuba mu masu gata Dan ita takasance Mara gata,Ina Mai tabbatar mukuda wallahi summa tallahi sai Fatima ta dawo gidan Nan"

Jinjina Kai kawai gwaggo rahi keyi Tana tafa hannu cike da mamaki da al'ajabin yarima take fadin"lallai kabiru alamarinka yayi Nisa bakajin kira lallai ka tabbata Mara kunya fitsararee wanan maganar kake duban tsabar idonmu iyayenka kake fada mana saboda tsintacciyar mage kilaki daka tsunta Koda yake ba laifinka bane laifin uwarkane tinda a gabanta kakeyi takasa kwaba maka wai ita Mai kawaici da hakuri"

"Bakinsu daya rahina wallahi uwarsa bazata iya ce Masa komiba kila ma ita tasashi ya kawota tasan komi karma kice wani Abu nidaidai nake dasu gobe Mai martaba zai dawo zaayita takare Amma wanan tsinanniyar Bata Zama a gidan Nan"

Cikin daga murya mama karama ta na kallo yarima Rai a bace tace"dauketa kubar gidan Nan yanzun Nan tunban Bata maka Rai ba kabiru bazaka daukomin fitina ba kujecan kukarata idan mahaifinka ya dawo"

Tana Gama fadin haka ta juya ta fice a parlorn tayi bangaren ta,kallonsu yayi daya bayan daya yace"Fatima batada wajen xama sai gidan Nan da yardar Allah insha Allah saita zauna a gidan Nan Bari Mai martaba ya dawo"....

Da karfin gaske ya tako daga inda yake ya daga Fatima dake durkushe hannunta akanta ta dafe inda ta buge Tana famar kuka kamar numfashinta zai dauke.....janta yakeyi suka fice a dakin hajiya babba ta biyosu Tana yayyafa balai Tana fadin 'aida ka barta da yanzun nabada umarni sarkin baka ya soketa kowa ya huta shashasha mu zuba"......

Haka ta juyo parlorn Tana kumfar baki gwaggo rahi Tana tayata suna zagin yarima tasss....

Fitowa sukayi harabar masarautar suna tafiya a hanya sukai kicibis da khausar da affee andawo dasu daga gidan waziri masu tsaronsu suna take musu baya,...tun daga naisa affee ta kafe yayan nata da ido ganin yadda yakejan yarinya a hannu har sukazo zasu gifta su,kallo afee tabisu dashi hankalinta a tashe ganin yanayin yayan nata yayinda khausar ta tabe baki ta bisu da harara......

*********

Gudu kawai yake shararawa a mota kamar zai tashi sama,be taba tsintar kansa a mummunan bacin Rai irin na yau ba,sanan babban tashin hankalinsa mahaifiyarsa tayi fushi dashi harda zubar da Hawa akansa,

It's kuwa Fatima kuka yin kansa yakeyi zuwa wanan lokacin kukan da takeyi ya dauke diff kamar anyi ruwa an dauke babu abinda takeyi sai ajiyar zuciya.....wani gida daban taga sun nufa da sauri ta waigo Tana kallonsa ko kallon inda take beyiba parking motarsa yayi ya fito har ya nufi hanyar shiga gidan sai ya hangi wata mota a can gefe tanayi Masa horn da alama mutum ne a ciki juyowa yayi da sauri ya nufi wajen motar....

Ahmad ne ciki abokinsa shima ganin yarima da sauri ya kashe motar da dama fita zaiyi ya fito.....Fatima ma fitowa tayi Tana takowa a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki,

Cikin kidimewa Ahmad ya kalli yarima yace"ranka ya dade lafiya naganka a yamutse haka?"

"Inafa lafiya Ahmad Ina cikin damuwa friend nida Fatima ne gatanan"

Da sauri Ahmad ya juyo Yana kallon wadda aka Kira da Fatima,kallonta yake sosai daga sama har kasa a zuciyarsa yace"lallai babu karya wanan yarinya kyakkyawace"......irin kallon da Ahmad keyi Mata ya bawa yarima haushi a fusace yace "dalla malam wanan wani irin kallo ne saikace tsohon maye".....Dan Sosa Kai Ahmad yayi ya wayance ya juyo yace "yanzun meke faruwa"

Nan yarima ya kwashe abinda ya faru ya fada Masa komi be boye Masa ba,jinjina Kai kawai yakeyi Yana jinjina irin wanan karfin Hali na yarima sanan yace"to Kai abokina Mai zai Hana ka maidata gidan Abdul zuwa wani lokaci".....

"Dakata malam ai nasan da gidan Abdul din nakaita gidanmu saboda ninasan abinda nake nufi da hakan,Kuma a gaskiya bazan iya bawa kowa rukontaba,bazan iya Bari Fatima tayi Nisa Dani ba saboda abinda na kudura araina akanta......nazo kabani shawara kanamun wata magana Mara dadi mtseww"

Murmushi Ahmad yayi yace"to yanzun shawarar da zanbaka ka dauketa ka kaita gidan Abdul zuwa gobe,kafin Mai martaba ya dawo kamar yadda kafada"

Ajiyar zuciya yarima ya sauke yace"to shikenan zanyi hakan,Kuma nasan Mai martaba baya kyamar talakawansa shi Mai tausayine Kuma Mai adalcine ga nakasa dashi nasan saidai idan ban bayyana Masa bukatataba da hujjojina zaiyi naam da maganata nagode Bari muje"

Juyawa yayi inda Fatima ke tsaye a rakube ya kalleta Nan da Nan tausayinta ya kamashi "Fatima muje ko inkaiki wajen Ablah"....
Chapter 21 · 0% Book details