Sashe 49
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wani mugun takaicine ya rufeta wato yafi karfin ya kirata a waya ma saidai yayi Mata Tex,kwafa tayi hade da girgiza Kai cike da takaici a cikin ranta tace "zaka shigo hannu Dan rainin hankali"...a zahiri kuwa dago idanuwa tayi cikin mayafinta tana kallon su teemah dollar suna kashe selfi,haushi ne ya lullubeta dakyar ta bude baki cike da takaici tace "Sunita kubar daukar hoton Nan haka mu ake jira a wajen Nan yanzun haka prince ya turomin Tex suna waje"
Dariya Sunita ta kamayi "soyayya wanan wani irin ango ne da baya Kira sai Tex"
Teemah dollar ta karbe zancen "kedai Bari zee baby wanan amgon da abokanansa Yan Jin Kai ne domin Basu nemanmu sai amaryarsu zamu Rama wajen siyan baki"suka sheke da dariya suka tafa
A k'ule deejahma tace"Kun fiye son magana muje da Allah"
Saida suka kakkashe hoto da deejahmah sanan suka fito Tana tafe tamkar bazata taka kasaba ga wani uban takalmi me shegen tsini da kyau Wanda tasa Tana takawa a hankali mutum biyu suka tsaya gefe da gefenta daya na biye dasu a baya...
A kofar harabar gidan sukaga motoci reras na abokanan ango cike da xumudi Sunita ta bude bakar mota zata shige Ahmad ya juyo da sauri ya dakatar da ita "motar amarya da ango ce wanan".turus tayi ta juya Tana kallon yarima Wanda ya hada girar sama da ta kasa tamkar be taba dariya ba haka ta juya ta wuce,
Deejahmah na sako kafa cikin motar kamshi ya baibaye motar tamkar anyi barin turare,..ta gyara zamanta a baya kusa da yarima ta zauna Ahmad ya rufo kofar ya zagayo gefen driver ya zauna ta glass din mota yake kallonsu Yana dariya kasa kasa cike da zolaya yace "ranki ya dade,sarauniya deejamah amaryar sarki Mai jiran gado Allah ya Sanya alheri"
Murmushi cike da kasaita Sanan ta amsa cikin sassanyar murya "nagode"...
Fuska a daure yarima yace "Ahmad ka manta uwar gida ce?nan gaba kadan amaryarta zata shigo Wanda zataci girma ta barwa amarya Zama sarauniya tunda ita babba ce"...ya waigo ya kashe Mata ido...
Takaicine ya lullubeta suna tafe a hankali a mota kusan second talatin tamkar bazatace komiba tsulum yaji tace"sai na so na bada kofa wata zata shigo gidan mijina,Domin mijina nawa ne ni kadai Kuma baayin sarauniyoyi saidai ace sarauniya,mulki da sarauta na ya'yan asaline ba tsintattu ba"
Ta wurga Masa harara daidai lokacinda suka karaso wajen mota ta tsaya tayi parking ....
*********
Da sauri sauri Fatima tayi wanka ta fito bayan sunkammala ayyukansu dikda ranta da yake abace Amma bazai hanata zuwa wajenba kodan farin cikin yarimanta,
A dakinsu ta tararda bilkisu rike da Kaya Tana jujjuyawa,...turus Fatima tayi tana kallon kayan dake hannun bilkisu Tana juyawa Wanda akanbisu akayi musu sala Sala yankan wulakanci da almakashi,
Dafe kirji Fatima tayi zuciyarta na tsananin bugu "innalillahi wa yayi wanan aikin?"..
Girgiza Kai bilkisu tayi tace "ninasan zaa Rina Wai an Ari zanin mahaukaciya Domin dazun da safe Naga lokacinda rahane ta shigo dakin Nan Kuma zato zunubi Koda ya kasance gaskiya itace ta shigo tayi mugun aikin Nan"
Hankalin Fatima ba karamin tashi yayiba ta karaso inda bilkisu ke zaune hannu rike da Kaya ta amshi kayan ta shiga jujjuyawa Tana girgiza Kai ,take hawayen bakin ciki suka shiga zubowa a idanuwanta tasa gefen dankwalinta ta goge sanan ta dago Kai ta dubi bilkisu wadda ta tsareta da idanuwa...
"Wai dik wanan wulakancin da akemun saboda na fito a matsayin shegiya ne?ko ko saboda kaddara ta fadamun Akan habibu shiyasa ake kokarin aga bayana?shin Nina dorawa kaina rayuwar gidan marayu?ko ko ganin da sukamin a can sunada tabbacin nidin shegiya ce?kaddarar data fada mun Nina dorawa kaina?Koko Allah ya Riga ya kaddara cewa mutuwar habibu a hannuna take?menayi haka wani irin balai ne wanan?tsirara akeson a ganni a wajen kenan?"ta rushe da kukan ta kaici tayi jifa da rigar hannunta,hade da durkushewa a wajen Tana kukan bakin ciki...
Janyo jiki bilkisu tayi ta matso kusa da ita ta shiga lallashinta"haba Fatima ai ya kamata zuwa yanzun kisaba da dik wani bakin ciki da takaici da ake kunsa Miki saboda kabiru,azabarki ta Karu ne saboda Kabir Yana sonki da badan haka ba da wani Abun zaa raga Miki,nasha fada Miki Akan ki Zama jaruma wanan koke koken dik ba naki bane ya kamata ki Zama idanuwanki sun bushe kema ki fara Rama wasu abubuwan"
Dago Kai Fatima tayi tana jinjinawa idanuwanta manne da guntun hawaye "bilkisu lokacinda zan Rama wanan bakin cikin da nake kunsa Yana Nan tafe,lokacinda kowa na gidan Nan zai fara tunanin Anya nice kuwa Yana Nan zuwa Domin nayi alkawarin dik Wanda ya zalunceni ya cutar Dani bazan cuceshiba bazan zalunceshiba Amma inada hanya mafi sauki da kowa sai yaji a jikinsa wallahi zakice na fada Miki ko yanzun ma ba tsayawa zanyi a cigaba da cutar daniba abinda yake tauyeni be wuce kasantuwata a matsayin baiwa ba"
Jinjina Kai bilkisu tayi cike da Jin dadin kalaman Fatima tace"Ina goyon bayanki dari bisa dari Yar uwata Allah ya cika Mana burinmu"
"Ameen bilki"tasa hannu ta share hawayenta sanan ta Mike taje inda kayanta suke ta Ciro wata doguwar Riga baka Mai adon fulawas farare Yar kanti ce ta say a jikinta da Dan mayafinta Mai girma ta yane jikinta dashi ba karamin kyau tayi ba....
Itadai bilkisu sai bin Fatima da kallo kawai takeyi Tana girgiza Kai hade da guntun murmushi...
Uniform dinta bilkisu ta mayar a jikinta ta shirya tsaf suka fito yare suka nufi wajen bikin....
********
Isowarsu wajen wuri ya kacame anata famar ciye ciye da lashe lashe masu serving mutane abinci sai kaiwa da komowa sukeyi,
Idanuwan rahane ne suka sauka Akan Fatima wadda take tsaye can gefe Tana karewa kowa kallo a cikin gidan Tana murmushin takaici,
Yarima kuwa tunda ta kallesa sau daya Taji wani mugun kishi ya taso Mata ta Kauda kanta saboda Yar kwallar data ciko a idanuwanta,
Durkusawa rahane tayi ta bayan deejahmah inda dama Nan ne wajen tsayuwarta kasancewarta baiwarta ,ta danyi kasa da murya kadan tace"ranki ya dade ga Fatima cen tsaye ta gefen hannun Daman mu a bangaren da aminanki suke"
Da sauri deejahma ta dago Ido ta maida dubanta inda rahane ke fada Mata aikuwa direct idanuwanta suka sauka Akan Fatima wadda ke tsaye tamkar balarabiya tayi matukar kyau Wanda ita kanta deejahmar Saida ta shagala da kallonta sanan ta danyi tsaki ta kwanto da kanta cikin izzah tacewa Rahane "kiramun ita"...
Rahane jiki na rawa ta kukkutsa cikin mutane ta karasa wajen da Fatima ke tsaye tasa hannu ta tabata hade da cewa "ke hawainiya Mai rikida?kije uwargijiyarki na kiranki"
Murmushi ne ya subucewa Fatima Jin abinda Rahane tace"nakoyi rikida ne kafin lokacin rikidar tawa yayi Domin Nan gaba kadan zan rikida in koma hawainiya kamar yadda kikace"....galala Rahane tayi tana kallon Fatima wadda ta soko wadanan maganganun fuskarta dauke da murmushi,
"Muje ko?"ta daga Mata gira daya,jiki a sukwane Rahane tayi gaba Fatima na biye da ita suna kukkusawa cikin mutane,take idon fauziyya ya sauka Akan Fatima wadda take ta Raba Ido tun tuni Tana nemanta dama,
Har inda suke zaune Fatima da Rahane sukaje....
Dan durkusawa rahane tayi tace "gata ranki ya dade"...
Dago Kai deejahmah tayi ta watsa Mata wani mugun kallo sanan ta bude baki cike da wulakanci da gadara ta Soma magana "waya baki umarnin canja Kaya daga kalar ja zuwa wani kala?....ko kinsamu yancine daga bauta zuwa cikakkiyar ya'"
Daurewa Fatima tayi ta danne abinda takejin zuciyarta ta bada amsa da "ya kamata in sabunta kayan jikina ranar bikin iyayen gijina Domin intayasu farin ciki a wanan Rana data kasance ta farin ciki a garesu"...
Amon sautin muryar Fatima ne ya sauka a kunnen yarima Wanda ke zaune a wajen kamar mutum mutumi,Jin muryar Fatima ya haddasa Masa faduwar gaba Wanda besan dalilinsa na hakanba,kasa jurewa yayi ya juyo gefen da yakejin wanan satin juyowarsa tayi daidai da dagowar idanuwan Fatima Wanda suka hadu Dana yarima take yaji wani Abu tamkar shocking na yawo cikin jikinsa tozali da kyakkyawar fuskar Fatima ya haifar Masa da hakan,...ajiyar zuciya ya sauke Yana Kare Mata kallo yayinda ita kanta fatimar dakyar ta Tattaro natsuwarta ta kawar da idanuwanta daga cikin nasa,
Yan matan amarya dake gefe idanuwansu suna Kan yarima da Fatima da sauri Sunita ta zunguri teemah dollar "Wai Kinga kallon da prince yakewa waccen kyakkyawar yarinyar kuwa?Kuma a gaban deejahmah"
Cikin kasa da murya teemah dollar ta Bata amsa "tsohuwar budurwarsa ce wadda take a matsayin baiwa a gidan yanzun haka,ni naji a majiya Mai karfi ma ita zai aura Nan da watanni kadan"
Zaro ido Sunita tayi tana jinjina Kai "tabdijan Aiko deejah ta Gama yawo dik ranan da wanan yarinyar ta shigo gidan,Dan daga ganin yadda suke jifan juna da kallon soyayya kinsan Yana sonta"
Dariya suka kamayi kasa kasa suna karewa deejahmah kallo wadda ta cika tayi famm tamkar zata fashe...
Juyawa Fatima tayi da tafiyar Nan Tata Mai daukan hankali,yarima yabita da kallo hade da lumshe idanuwansa ya saki sassanyar ajiyar zuciya sanan ya juyo da kallonsa ga deejah wadda idanuwanta suka kankance saboda tsantsar kishi "ya kamata ki koyi yadda ake kallon soyayya kodan mijinki saboda gaba"....abinda ya rada Mata a kunne kenan ya koma ya jingina da jikin kujera...
Can gefe Fatima ta nemi table ta zauna Tana sauke numfashi minti minti Tana sauke ajiyar zuciya wadda batasan dalilinta nayin hakanba murya tajiyo a gefenta Ana magana da sauri ta waiga cikin masu kawo abincine ya tsaya "ranki ya dade me xaa kawo Miki"
Khausar dake tsaye a gefe ta karbe zancen da "waya ce maka bakuwa ce a wajen Nan?baiwa ce ta canja kamanni ta shigo Domin yin basaja saboda haka ba sai ka kawo Mata komiba matsayinka yafi nata a wajen Nan"ta karasa maganar da watsawa Fatima wata uwar harara hade da Jan tsaki tabar wajen....takaicine ya lullube Fatima batare da tace komiba ta cigaba da Zama wajen,
Minti kadan fauziyya ta karaso table din Fatima taja kujera ta zauna hade da Mika Mata hannu Tana murmushi "assalamu alaikum"
"Waalaikumussalam"Fatima tace hade da maida Mata da nata murmushin sanan tace"sai yanzun nake ganinki?haba faizah nadauka zakizo muzo tare?"