Sashe 43
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya Ahmad keyi kasa kasa Dan Harga Allah wanan cika da batsewar da yarima keyi dariya abun yake bashi....
********
Kuka sosai Fatima takeyi Babu kakkautawa haka takeyi Tana wanan wankin da ko zanin gado guda daya ta kasa wankewa kirjinta zugi yakeyi Mata Bata tabajin irin wanan ciwonba tunda take....
Tana murza kayan Tana hawaye haka amai ya taso Mata da sauri ta Mike daga wurin ta fice can wajen wata bishiya ta. Tsugunna ta rinka amai Wanda ruwane zalla babu abinci a cikinsa gashi yellow Shar da shi haka ta rinka yunkuri tamkar zata mutu tanayi Tana kuka haka ta juya ta koma wajen wankin Tana hada hanya....
********
"Deejahmah Niko gani nakeyi tamkar kina son yariman Nan naki bazaki iya daukar fansa akansa ba kamar yadda kike fada"
Murmushi deejahmah tayi hade da mikewa zaune daga kwancen da take Tana fuskantar kawarta dake gefe "teemah dollar a ganinki kenan Amma wallahi saina kamashi a hannuna sanan zan aikasa lahira Dan nariga na tanadi makaman yakina tsaf Kuma yanzun haka kwantar da kaina zanyi sai anyi auren zanfara yi Masa kisan mummuke a hankali a hankali zanyiwa rayuwarsa illar da kafin ya farga na rigada na kasheshi a tsaye...."
Murmushin mugunta deejahmah keyi Tana kallon aminiyar Tata wadda rabonta da ita sunkai shekara daya Saida zancen aurenta ya tashi sanan ta nemeta...
"Ni wallahi deejah Babu abinda nake jiye Miki kamar kishi da kuyanga baiwa haba da girmanki da ajinki da iliminki a kasashen duniya inane baki lekaba dik wani gata da wayewa a gurinki muka koya Amma ki bige da kishi da baiwa"
Wani ma yaudarin murmushi deejahmah ta saki sanan ta gyara Zama ta riko hannun teemah dollar wadda ta zubawa deejahma Ido Tana jiran amsar da zata Bata,
"Ba kishi da ita zanyiba teemah Yar aikina zata zama Dan azabata ce zata koreta da kafafuwanta kafin in kulla Mata abinda shi kansa yarima sai yaji ko sunanta bayason ji"
Kyalkyalewa da dariya teemah tayi hade da tafa hannuwanta "lallai k'awata da shirinki kenan"
Gyada Mata Kai kawai deejahmah tayi batare da tace komiba....suka cigaba da hirarsu...sai yamma sanan sukayi sallama teemah ta wuce gidansu...
******
Hangen shigowarsa gidan tayi ta kafe motarsa da Ido hade da sauke ajiyar zuciya,
Kallon yadda yake tafe Yana amsa waya takeyi cike da kwanciyar hankali babu wani Abu daya nuna Mata cewar Yana cikin damuwa itace ya Dasa Mata sonsa ya juya Mata baya,
Kuka ne Mai karfi ya taso Mata lokaci daya ta shiga rera kuka harda shassheka idanuwanta akansa har ya bace Mata....
Sauri sauri bilkisu ta fito daga sashen hajiya zuwa wajen Fatima sukai arangama da yarima da sauri taja da baya ta tsugunna "barka da dawowa ranka ya dade"
A dakile ya amsa Mata da "barkadai".....Jin yadda ya amsa Mata ita kanta Saida gabanta ya fadi Amma ta daure ta bude baki cike da fargaba tace "dama dazon nazo nemanka infada...mak...a ne faty bata...da lafiya"dik a inda inda take maganar saboda yadda taga fuskarsa Babu walwala....
Gabansa ne ya yanke ya fadi Jin furucin da Bilkisu tayi sai jikinsa yayi sanyi lokaci daya yaji tausayinsu su duka biyun ya kamashi,...kallon yadda take a durkushe jikinta na rawa yakeyi da kyar ya saisaita kansa yace "ki shiryata bayan ishai zan fita daku cikin sirri zan kaita asibiti"
Daga Masa Kai tayi "to ranka ya dade".....
Koda tasamu Fatima Tana kuka ta Dade tsaye kanta Tana kallonta cike da tausayi har saida Fatima ta tsagaita da kukan da kanta sanan bilkisu ta sauke ajiyar zuciya ta kwashe yadda sukayi da yarima ta fadawa Fatima....
Girgiza Kai ta shigayi "bilkisu saidai ke ya kaiki Amma ni bazanje ba bazanbishi ya Kara jefani cikin wani balain ba sanan bazan barshi wanan karon yayi nasara akainaba zanyi kokari in cire sonsa daga zuciyata,....ki koma ki fada Masa ba sai ya kaini ba zan warke Allah Yana sane Dani"
Tasa hannu ta share kwallar dake gudu a idanuwanta...ita kanta bilkisu jikinta yayi matukar sanyi Fatima ta Bata tausayi matuka ji takeyi tamkar tayi Mata kuka,....rasa abinda zatace tayi haka ta tsaya akanta kamar an dasata.....Tana Nan tsaye Fatima ta karasa wankin ta tafi wajen shanya daga can ta nufi baya wajen alwala....cak Taji an dagata ta baya tamkar jariya hade da rufe Mata idanuwa.....ta shiga shilla kafafuwanta Tana ambatar sunayen Allah a zuciya.....
*Muje zuwa*
Kuyi hakuri da jina shiru kwana biyu uzurine ya rikeni Amma insha allahu zaku cigaba da jina....yanzun muka fara tafiyar insha Allah
*SLIMZY😍*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
31
A mota ya jefata ya rufe murfin motar be jira cewarta ba yaja motar a guje.....Hagen fitarsu bilkisu tayi Tana murmushin mugunta....ta juya abinta,
Saida suka hau Kan titi sanan ya waigo ya Dan kalleta har yanzun kuka takeyi kamar wadda akaiwa mutuwa gashi ta dunkule waje daya Tana rawar sanyi alamar zazzabi ne ke damunta....
Kada kansa kawai yakeyi minti minti Yana juyowa ya kalleta tausayinta ke ratsa sassan jikinsa,
Be tsaya ko inaba sai asibitin su Ahmad,parking space yayi parking motarsa sanan ya Ciro wayarsa ya Kiran ahmda minti kadan sukai magana ya kashe....
Kallonta yakeyi yadda ta juyar da kanta gefe Tana hawaye yakai minti biyu a haka sai da ya gaji yace "muje ko?"
"Bana bukatar taimakon kowa sai na Allah da ka maidani kawai ai Allah Yana sane Dani tunda mantawa Kayi Dani"
Kamo hannunta yayi ta kwace "Fatima dama abinda ya janyo Miki zazzabi kenan?abinda yasamun ke rashin lafiya kenan?kika rame kikai baki tamkar wadda tayi ciwon shekara daya?....dafe kansa yayi take tausayinta ya Kara ratsa zuciyarsa cikin sanyin murya ya cigaba da magana "kiyi hakuri banyi hakan da ganganba sai Dan wani uzuri,Kuma Allah ya rubuto hakan zai faru insha allahu bazan sake barinki ba kinji?na tuba bintu"...ya karashe maganar cike da lallashi.
Sai yanzun ta juyo da dubanta gareshi idanuwanta na fidda hawaye...."karka sake yimun haka idan ka barni bansan yadda zata kasance da rayuwata ba Kaine jigon rayuwata,idan ka nisanceni Yaya zanyi inyi rayuwa Babu Rabin rayuwata a tare Dani?"kafesa tayi da ido har yanzun hawaye ke zuba a idanuwanta
Hannunsa yasa ya shiga share Mata hawaye cikin sigar lallashi yake fadin "ya Isa bintu Nima na shiga halin da kika shiga kanki kikasani juriyace kawai da jarumta irin ta da namiji Amma kiris ya rage in zubar da hawayena"...ya kashe Mata ido daya
Cike da shagwaba ta langabar da kanta a jikin seat Tana jifansa da wani irin mayen kallo da idanuwanta ko kiftawa batayi yayinda yaji wani shaukin soyayyarta na dibarsa ji yakeyi tamkar ya rungumeta ya lallasheta,ji yakeyi tamkar ya dawo da kwanaki ukun da sukayi ba a tare ba....dakyar ya saita kansa ya matso daf da fuskarta Yana jiyo sautin futar numfashinta Mai zafin gaske "bintu Anya zan iya rayuwa da wata mace bayanki kuwa?"
.
Kada Masa idanuwanta tayi hade da murmushin karfin Hali "Dole zaka koyawa kanka rayuwa da wata mace bayan ni dikda naso ace nice kadai zan mallakeka"
Hancinta ya ja cike da zolaya "matsoraciya keda kikace bakiso Mai martaba yasan da ke?cewa kikayi Kar infada Masa saboda kina tsoron Kar deejah ta zauneki ni bansan yadda zaayi ki koyi zama jaruma ba"
Turo baki gaba tayi Tana Masa hararar wasa"nidai muje kaga ka kawoni a dubani ka cikani da surutu"
"Malama kin fa warke dama ciwon soyayya ne Ashe dai haka akesona"
Hannu tasa ta rufe idanuwanta Tana dariya,lokaci daya sukaji Ana kwankwasa glass din motar.....
Da sauri yarima ya zuge glass din ya motar gaba daya,Ahmad ne tsaye sanye da labcutt wuyansa rataye da abin daukar numfashi irin na likitoci,hararar yarima ya shigayi "malam ka kirani tun daxun zaku shigo Kun kwashe kusan Awa daya bangankuba nagaji na harhado Mata magungunan zazzabi na biyoku dashi Dan nasan soyayya kukeyi....
Tabe baki yarima yayi hade da dage kafadarsa sama sanan ya Mika Masa hannu ya karbi ledar "zamuyi maneji Amma na rigada na Bata maganin ciwonta dama ciwon nawa ne ko bintu"
Sadda kanta kasa tayi kunya ta lullubeta ganin yadda jikinta yayi dauda haka ta fito Babu kyaun gani wani ma sai yace ta shekara batayi wanka ba....murmushi kawai takeyi kasa kasa....
"Kaidai kasani sai nazo Mata allura"
Da sauri ta dago ta kalleshi,dukansu suka kwashe Mata dariya ta sunkuyar da kanta da sauri....
Hannu yarima ya dagawa Ahmad hade da tayar da mota ya jasu a guje....
Tunda suka hau hanya gabanta ke tsananin faduwa Dan ta manta da shaff cewa wannan gidan zasu koma,idan Tana hare da yarima jinta takeyi a wata duniyar ta daban....
******
"Ranki ya dade a idona ya dauketa suka fice Kuma motarsa yasata ya ja da kansa suka fita"
Kaiwa da komowa kawai hajiya babba takeyi hannunta rungume a bayanta.....tsananin takaici ne ya hanata cewa komi tunda saade ta Soma magana,
Kasa gasgata maganar saade tayi Saida tasa Mami ta binciko Mata ko Ina ta tabbatar Mata da Bata gidan,
Iska Mai zafi ta furzar daga bakinta "lallai yaron Nan nema yakeyi ya nuna mun iyakata,lallai kabiru ya cika Mara kunya ya tabbatar mun da shi Dan halak ne ni Kuma zanyi maganinsu dukansu su biyun bawai na rasa yadda zanyi dasu bane...."
********
A parking space yayi parking motarsa ya kashe motar ya kunna fitilar cikin motar ya dan kalleta Yana nazarin yanayinta,ya lura da dik yadda take a tsorace a firgice,shi mamakinta yakeyi yadda takejin tsoron wadanan bayin Allah Jin shiru yasa tasa hannu zata bude kofar taji a rufe ta juyo da sauri suka hada ido ya sakar Mata murmushi kasa mayar Masa tayi sai kallonsa da takeyi cike da kosawa tace"yaayah Dan Allah ka budemin in fita kafin wani ya ganmu"
"To meye idan anganmu nidin ba mijinki bane?Mai martaba ya mallakamin ke ya yarjemun da aurenki"
Raurau tayi da idanuwanta Tana kallon yadda yake magana hankalinsa a kwance....ita ko dik inda hankalinta yake a tashe yake "haba mana yaayah Dan Allah ka budemin kofar Nan infita"
Key yasa yayi unlocking motar da sauri ta bude kofar jiki na rawa tasa kafarta ta jiyo muryarsa "tunda kika tafi baki tsaya nagama kallon kyakkyawar fuskarki ba to tabbas wajen wata zanje yanzun Nan "