← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 80

Sashe 47

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikin a sanyaye deejahmah ta juya batare da tace komiba zuciyarta nayi Mata suya,Bata da wani damar daukar hukunci a gaban ummu saboda sanin halinta Bata daukar raini haka ta fice cike da takaici,Mai makon tayi sashen da friends dinta suke sai tayi sashin hajiya babba.....

Juyowa hajiya zainab tayi tana zazzaga masifa "wallahi wanan yarinyar da ake Shirin aurawa kabiru an hadashi da aiki,Domin batada tarbiyya ko kadan tun suna yara nasan halin deejahmah Bata laifi komi tayi daidaine a wajen rahina,banji Dadi ba ko da can da akace zata auri habibu balle yanzun da lamari ya juya Kan kabiru mutumin kirki"

Tsaki taja ta juya ga Fatima wadda ke durkushe ko motsin kirki takasayi,zuciyarta cike da fargabar abinda zai biyo baya,muryar ummu ce tadawo da ita daga tunanin data fada

"Makulli zan baki kije wancen sashin na can cikin gida ki bude ki gyaramun shi,tun shigowarmu nasa aka kaimun kayana can,Amma kafin kije kiyi aikin ki tabbatar kinje kinyi wanka kin cire wadanan kayan na jikinki kin wanke su dan bana kaunar datti ko kadan bazakije gyaran gidaba kema jikinki kaca kaca"...ta karashe maganar da kafe Fatima da idanuwa....

"Ranki ya dade kayana guda daya ne idan na cire wanan Babu Wanda zan canja sai Kuma kayan gida da nake dashi"

Juyowa ummu tayi ta dubi Maryam dake durkushe a gefe "ke jaki kitchen kisamu lantana kice nice nace taje wajen jakadiyya tace a Bata Kaya irin na jikin faty ki kawomin yanzun Nan"

"Toh ranki ya dade".....

Cikin mintuna da Basu wuce goma ba saiga Maryam ta shigo hannunta dauke da Kaya jajaye irin wadanda kuyangin gidan ke sawa ta shigo ta durkusa ta mikawa ummu

"Mika Mata su"

Hannun Fatima na rawa tasa ta amshi kayan,sanan hajiya zainab ta Miko Mata makulli ta Mike da sauri ta fice.....

**********

Kuka sosai deejahmah keyi a jikin mahaifiyarta Tana fadin "kamar ni mama a wulakantani gaban baiwa kuyanga?baiwar ma kaskantacciya cikin sauran bayi?wallahi bazan yardaba sai na dauki fansa a wajen Fatima"

Cikin tsananin bacin Rai da tashin hankali hajiya rahina ta ture deejahmah daga jikinta ta Mike Tana huci ta fice a dakin hajiya babba ta rufa Mata baya basu zarce ko inaba sai dakin hajiya karama,..

Koda suka shiga ummu na zaune da mama karama suna taba Yar hirarsu suka shigo dakin Babu ko sallama,

Daga tsaye hajiya rahina ta juya baya cike da rashin mutunci tace "nazo inji baasin wulakanta Yar sunnah Akan shegiya"

Murmushin kasaita ummu tayi ta dago Kai ta kalli rahina kadan sanan ta girgiza Kai "banyi mamaki ba da Khadija ta shigo Mana daki kerere babu ko sallama ta zuba rashin mutunci Ashe gado tayi a wajen uwarta,shiyasa masu iya magana ke cewa barewa bazatayi gudu ba danta yayi rarrafe yanzun kinzo ramawa yarki ne kenan rahina?to Bismillah"....ummu ta cigaba da kada kafa,

Hajiya babba ce a fusace tafara magana "haba zainab wanan abin da kikayi kin dauka abune Mai kyau?a tunaninki bare yafi Dan uwanki ko?baren ma shegiya tsintacciyar mage?ke har kinada bakin wulakanta diyar Yar uwarki a gaban bayi?"....

"Dakatamun hajiya,ke matar Dan uwana ce Kuma Dole in mutuntaki saboda haka ki rike bakinki wanan abinda ya shafi Yan uwa ne ki rike matsayin da Allah ya baki"...

Takaicine ya lullube hajiya rahina jikinta har kyarma yakeyi ta juyo ga ummu Tana fadin "ai ni dama nasan cewa bakya kaunata baki kaunar abinda na Haifa,wayasani ma ko bakin ciki kikeyi da deejahmah kikai Mata wanan wulakancin a gaban wanan matsiyaciyar yarinyar"

"Rahina matsiyaci shine Wanda zai tashi ranan tashin kiyama bashida komi na ladan ubangiji,ke baki Isa ki kalli wani kice Masa matsiyaci ba wallahi,sanan yarki gyara nayi Mata na dauka ta dauki gyaran Ashe wuta taje hasowa to tayi daidai Kuma zan gamu da ita,saboda haka ki bacemun daga gani tunban Bata Miki Rai ba kema Dan niba saarki bace "...

Gyara tsayuwa hajiya rahina tayi tana tafa hannu Tana fadin "kome Zakice kice Amma a kiyayarmum yarinya Babu ruwanki"...Tana karasa magana ta fice Tana surfa balai ,hajiya babba juyawa tayi ta bi bayanta cike da takaici....

*******
Deejahmah kuwa ganin tijarar da iyayenta sukayi yasa tasamu sassaucin takaicin da takeji a zuciyarta dikda ta kudiri aniyar Rama abinda akayi Mata a Kan Fatima kota halin Yaya,

Dakin kawayenta ta shiga dukkansu suka bita da kallo,saboda dik Wanda ya kalleta babu tantama sai ya fahimci Tasha kuka,

Neman wajen zamanta tayi ta zauna,....teemah dollar ta Dan kalleta cike da tsaigumi tace "haba ranki ya dade,daga tafiya sai Muji shiru?kodai kinfara kukan rabuwa da momy ne Kinga yadda kyawawan idanuwanki suka canja kala?"....takaicine ya lullube deejahmah Jin abinda kawarta ke fada,

Shiru tayi Tana girgiza kafa minti minti Tana sauke kwafa daga bakinta sanan ta juyo gefenta ta ruko hannun teemah tafara magana cike da bakin ciki muryarta a dishe"wallahi tallahi saina wulakanta yarinyar Nan saina tabbatar da ta Zama abar kwatance saitayi data sanin shiga Ramin damusa"...

Cikin rashin fahimta teemah ke kallon deejahma yayinda ilahirin Yan dakin friends dinsu suka baza kunnuwa Dan Jin kanun labari,....cije lebe deejahmah tayi "Zaki fahimci abinda nake nufi Nan gaba kadan idan na aikata Mata abinda na kudura a zuciyata"

Matse hannun deejahmah tayi tanadan girgizata"haba princess bai Dace ki tsaya furta Zaki dauki fansa akan baiwarkiba wadda kikeda yancin sawa a tsireta ma kowa ya huta fadin Zaki dauki fansa tamkar cewa tafi karfinki ne yasa kike wanan ikirarin,ai aiwatar da abinda kikeso a lokacin da kika gadama saboda ita mallakinki ce"

Takaici ya Kara rufe deejahmah tamkar ta fashe da kuka,babban bakin cikinta be wuce tunanin abinda Fatima sukayi da yarima ba a dakin da akace ta shiga,....bisa alamu ta rigada ta fahimci Yana son yarinyar soyayya suka makale sunayi kenan?....Nan da Nan fuskarta tayi jajir saboda takaici da bakin ciki....

*********

Gyaran sosai Fatima keyi a bangaren hajiya zainab Wanda yasha Kura saboda dadewa da yayi baa budeshiba,...dakuna uku ne cikin sashin dik Saida tabi ko wani daki tayi gyara na musamman ta shimfida musu zannuwan gado tayi mopping dik inda wata kura ta makale ,sanan ta shiga ko wani toilet ta wankeshi tass suka fita,

Har kitchen Saida ta fidda duka wanke wanken sashen ta wankesu Tass ko wanne ta jera shi a mazauninsa,

Fadin yadda ta gyara parlorn hajiya zainab Bata lokacine dik uban kurar da dattin ciki Saida ta share tayi goge goge,..wajen drawer din gadonta taga burner da turaren wuta Nan da Nan ta hada ko Ina ya dauki kamshi cikin gidan Wanda tamkar be tabayin dattin da yayiba,

Koda ta Gama aikin can barandar bayan dakin hajiya zainab ta nema ta zauna Tana maida numfashi,minti minti takan tsinci kanta cikin faduwar gaba Wanda batasan dalilinta na yin hakanba,har magriba ta risketa a Nan tayi sallar magriba sanan ta rufo gidan ta fito ta nufi sashen cikin gida....

********
Suna zaune sun idar da sallah suna zazzaune da wasu kannen hajiya karama wadanda sukazo biki daga kasar Sudan ta shigo bakinta dauke da sallama,

Ta zube a kasa ta gaida kowa a dakin,sanan ta juya inda hajiya zainab ke zaune tanajan carbi ta tsugunna hade da Mika Mata key din gidan tace cikin sanyin murya "na Gama ranki ya dade"

Daga Mata hannu hajiya zainab tayi batare da ta amshi makkulinba Saida ta shafa adduar ta sanan tace "yauwa Fatima ko ki dauki wata daga cikin kuyangar gidan Nan kice nace kuje ki dafamin abinda zanci Dan bazanci abincin gidan Nan ba Kuma nawa nakeso a dafa min"..

"Mai zaa dafa Miki ranki ya dade"..

"Jeki min couscous da miyar hanta kije friege din gidan Nan ki dauki hanta Dan yau na dawo Babu komi a gidana kuje ki dafamin"..

Fatima ta Mike Dan cika umarninta ta juya hajiya zainab ta dakatar da ita "kin ma iya abincin kuwa?karkije kimun shirme "

Tsugunnawa Fatima tayi daga inda take sanan tace"na iya ranki ya dade a kitchen nake ai a Nan din "

Daga Mata Kai tayi hade dayi Mata nuni da hannu da taje.....

*********

Fridge Fatima taje ta bude ta ciri dik abinda take bukata sanan ta juya ta nufi sashen hajiya inda bilkisu ke Zama,

Can ta taddata rakube gefe daya da sauri ta karaso cikin kasa da murya tace "kizo muje wancan sashin na waccen bakuwar tasani inyi girki Amma tacemun in nemi Dan rakiya saboda duhu ya farayi"

Mikewa bilkisu tayi tana waige waige sanan tayi kasa da murya tace "jeki zanzo akwai abinda nake saurare a Nan"...batare da Fatima tayi musu ba ta juya tai tafiyarta,

Daga can cikin dakin hajiya babba bilkisu ta kasa kunne Tana sauraronsu,

"Inhar tayi amfani da wanan ya kwanta da ita to tabbas shida wata mace harabada,sanan babu makawa zata dauki ciki Kinga burinmu ya cika dan wata Fatima ma mantawa da ita zaiyi"

"Amma hajiya Naga wanan abun tamkar ruwa beyi kamada magani ba"...

"Ehh Mana bazakisan amfaninshiba sai deejahmah Tasha komi ya faru zakice nabaki labari tafiyayya aka kawoshi daga can a balaq garin buzaye nasa akayoshi ga Yar aminiyata Nan shiru a gidan miji Kuma infada Miki anayi tasamu ciki"

"Kai hajiya nagode Allah ya saka Miki da alheri banida kamarki a rayuwata wallahi.....burina ya kusan cika kenan yata zata haifawa sarki jikan fari"

Dariya Suka kwashe dashi sanan hajiya babba tace "bude drawer dincan kisa shi ciki gobe bayan sungama kamu sai tazo Tasha ta wanke fuska,to harshi tsoronta zai rinkaji"

"Hajiya kin tabbatar idan ansaka a drawer din can bawani Abu?"

"Babu karki damu Babu me shigomin daki sai bilkisu itama na amince da yarinyar ne don ko shiga shirgin sauran bayin gidan Nan batayi kullum muna tare da ita,itakadai yanzun nake Bari ta shigomin daki Kuma idan ta ganshi zata dauka zam zam ne,...yanzun ki tashi mune fada wajen sarki Dan ya Aiko jakadiyyarsa kiranmi inaji anfada mishi abinda ya faru ne dazun"

"Owk"....

Jin alamun zasu fito da sauri bilkisu ta koma can cikin parlor inda babu Wanda zaiyi zargin taji wani Abu...

Zuciyarta ke tsabanin harbawa sauri da sauri tunanin yadda zatayi takeyi take mafita tazo Mata...

A parlor suka taddata a rabe tayi shiru,hajiya babba ta kalleta tadanyi murmushi tace"bilki bakije cikin Yan uwanki ba tunda Babu abinda zakimun?"
Chapter 47 · 0% Book details