← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 80

Sashe 40

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya sosai Ahmad yayi sanan ya tsagaita "wallahi rigar jikinta ce tabani dariya kamar wata Mai daddawa ga idanuwanta Dara Dara sai zaresu takeyi"

Shidai yarima bece komiba da kansa ya hada tea ya shige daki ya nemi gefen gado ya zauna ya ajiye cup din a gefe yasa hannu ya tallabota ya rike ta dakyau ya Mika hannu ya dauko kofin tea din da kansa yake Bata da cokali Yana hura Mata tanasha harta koshi,....sai zufa dake karyo Mata....

Ganin haka ya Sanya hannunsa ya shafo wuyanta yaji Babu zazzabi sanan ya kashe Mata ido "yanzun Kinga kin koshi saikiyi wanka ki shirya domin Mai martaba na nemanmu a fada"

Da sauri ta kallesa ya daga Mata gira daya hade da murmushi ya kashe Mata ido daya.....

"Nidai gaskiya bazanjeba"

"sai a fadawa sarki sakonki na bazakijeba"

"Nidai ah ah "ta makale kafada...

Dariya yakeyi Yana kallonta,kwalla sun ciko a idanuwanta yasa hannu yaja hancinta ya ce "maza ki gasa jikinki Bari muje mudawo nida Ahmad"

Ya Mike ya fice a binsa ta bishi da kallo....

********
Isowarsu deejahmah yayi daidai da fitarsu Ahmad a mota daga gidan...

Murna sosai deejahmah keyi na Jin labarin abinda ya faru ....tarasa inda xata tsoma kanta sai wani rawan Kai takeyi Tana nishadi....

Suna zaune suna Yar hirarsu da hajiya babba akayi sallar laasar,dukkansu babu Wanda ya Mike Domin yin sallah saima tattaunawa sukeyi Akan abinda deejahmah zata fadawa Mai martaba....haka sukai shiri tsab suna haramar zuwa fada.....

Saida akayi sallah sanan yarima ya shigo masarautarsu a gaggauce yayi hanyar zuwa fadar sarki don yayi latti....

*Muje zuwa*

*SLIMZY✍🏼😍*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

29

A gaggauce ya shigo fadar da sallamarsa a bakinsa ya karaso deejahmah dake gefe gabaki daya ta maida hankalinta akansa Dan ba karamin kyau yayi Mata ba da kwarjini,ta manta shaf a inda take har ya zauna Tana binsa da wanan mayen kallon Wanda har uwarta dake gefenta Saida ta Dan zungureta cikin rada tace Mata "ki natsu Mana karki bada kanki".....a hankali ta sunkuyar da kanta hade da wayancewa ta fara Wasa da yatsun hannunta,yayinda zuciyarta ke Kara azalzalarsa da ta dago kanta ta kalleshi ko Allah zaisa su hada ido Amma tabbas idan tayi hakan to kowa zai ga maitarta a Fili......ta rasa dalilin dayasa matukar kabir Yana waje to Tana neman natsuwarta ta rasa ta kasa gasgata abinda zuciyarta ke fada Mata na ta fada tarkon sonsa,....idan kuwa haka ne zuciyarta batayi Mata halarciba Domin Koda Tana sonsa bazata janye kudurinta na daukarwa habeeb fansa akansa ba.....ajiyar zuciya ta sauke sassanya wadda tayita ne a dalilin maganar Mai martaba data dawo da ita daga duniyar tunanin data afka na wucin gadi....

Gyaran murya Mai martaba yayi yau fuskarsa Babu yabo babu fallasa a bisa alamu yau din Nan sarki Yana Jin sarautar,kasaitar Yan maza ta motsa shi kansa dakyar ya motsa labbansa yayinda ya maida dubansa ga waziri dake gefe yace "waziri ka bude Mana taro da addua"....Nan take babu Bata lokaci waziri ya cika umarnin Mai martaba ta hanyar yin addua kamar yadda ya umarcesa hade da shafawa da salatin annabi (s.a.w).....

Shiru fada tayi kowa da sake saken da yakeyi a zuciyarsa gyaran murya Mai martaba yayi sanan yace "nataraku a Nan ne a bisa dalilai biyu zuwa uku Amma kafin in zartar da hukuncin sai na tabbatar da kowa Wanda keda hakki a taron Nan Yana wajen Nan"

Shiru ne ya biyo baya Babu Wanda yace komi sanan Mai martaba ya cigaba da magana "kabiru Ashe abinda ya faru kenan?"

Rasss gaban yarima ya yanke ya fadi Domin be fahimci inda maganar Mai martaba ta dosaba,Amma sai ya Dan gyara Zama cike da biyayya da ladabi yace "Allah ya baka yawan Rai ban fahimci maanar maganarka ba"

Jinjina Kai Mai martaba yayi sanan yace"wani mugun labari ne yasameni dazun jakadiyyata ke sanar mun da cewa an nemi yar Amana an rasa ta gudu,maana Yar daka daukota ka kawota gidan Nan a matsayin Yar riko Wanda taron Nan musababbinsa saboda Kai da ita ne da Kuma Khadija"

Wata xuface ta ke karyowa yarima Wanda ya Gama shiga rudani a maganar Mai martaba ta farko ,kansa a kasa ya Kara gurfanawa "Allah ya baka yawan Rai Babu inda Fatima taje Tana cikin gidan Nan yanzun haka"....

Da sauri hajiya babba ta kallesa tayi maxa tace"maganar banza kakeyi bayan Babu inda baa dubana baaga yarinyar Nan ba har cikin tsohuwar rijiya an leka babu ita,karya kakeyi saidai idan nemanta zaka fitayi ka fakeda Tana Nan to idan gaskiya ne ai taron harda ita akace zaayi Tana Ina?"

Shiru yarima yayi batare da yace komiba,kansa na sunkuye a kasa ya tsinkayo muryar Mai martaba na fadin ,

"Dakata hajiya dik maganar Bata fada ko hayaniya bace,Nasha fada Miki da banaso idan kinamun magana kinamun hayaniya"

Jiki a sanyaye hajiya babba ta sunkuyar da Kai itama sanan tace "Allah ya huci xuciyar Mai martaba"....

Juyawa yayi ga yarima ya cigaba da magana "kabiru kace Tana gidan Nan,gashi ance an duba Babu ita meye gaskiyar lamari"

"Ranka ya dade kunama ce ta harbeta jiya daddare yau da asuba na fito zanje masallaci na gamu da ita zatayi alwala kafarta a daure shine na dauketa na kaita gidan waziri wajen malam ya'u ya yi Mata addua dagacan na kaita asibiti yanzun haka Tana waje nace tabari a Bata umarnin shigowa"

Kallon juna hajiya babba da rahina sukayi sanan suka jinjina Kai ko wanne ya maida kansa kasa ya sunkuyar....

"Na baka umarni a shigo da Fatima"....

Durkusawa yarima yayi 'nagode ranka ya dade"....sanan ya Mike a nutse yayi hanyar waje.....wani mugun kallo hajiya babba ta bishi dashi har ya fita,

Fatima na tsaye jingine da jikin kofar shigowa kirjinta sai bugawa yakeyi ji takeyi tamkar ta gudu Bata kaunar abinda zai hadata da wadanan mutanen ,Bata ankaraba taga mutum a gefenta tsaye Yana binta da kallo don Harga Allah yayi tunanin ganinta a cikin muguwar Kama Sai ya ganta sanye da dogon hijabinta har kasa Babu wata alama da zata nuna Tana bauta a gidan ajiyar xuciyar daya sauke ita ta Sanya ta juyowa a furgice ai Tana ganinsa Taji tamkar ta saki fitsari,

Ganin yadda ta tsorata yasashi daure fuskarsa tamkar be taba dariya ba ya Mika hannunsa ya damki kunnenta ta cikin hijabi a gaggauce yace "Saura idan kin shiga ki kasa cewa komi kiyi kuka wallahi saina Bata Miki Rai".....zafi ne ya isheta ta tura baki gaba batare da tace komiba ya saki kunnen yayi Mata wani kallo yace "muje ciki"....ya fadin haka ya juya tabishi a baya dakyar take taka kafafuwanta haka suka yi sallama a tare suka shigo Tana dingisa kafarta wadda ta kumbura tayi suntum.....

Tunda ta shigo yadda take takawa kowa ya bita da kallo har deejahmah wanan karon haka take watsa Mata kallo Mai cike da tsantsar tsana da kyama,

Jiki na rawa Fatima ta nemi can gefe ta tsugunna a hankali Tana cije kafa saboda yadda kafarta keyi Mata azaba,

Kallonta Mai martaba yayi tausayin yarinyar da kaunarta ya darsu a zuciyarsa take tun rananda ya fara ganinta ya fahimci cewa yarinya ce Mai hankali da natsuwa,tunda aka fara wanan Zama Mai martaba baiyi murmushiba sai yanzun daya kalli Fatima wadda kanta a kasa yake yace "tahonan ya'ta ki zauna kusa da Yar uwarki Khadija"..yayi Mata nuni da gefen da deejahma ke zaune zuciyarta na harbawa sauri da sauri,....jiki a sanyaye Fatima ta Mike Babu musu ta dingiso kafarta ta dawo gefen deejahmah ta zauna Akan kafarta ta sunkuyar da kanta gabanta sai tsananin faduwa yakeyi,idanuwanta farare Tass ta dago ta kalli gefen da deejahma ke zaune Kai a sunkuye Aiko kamar hada baki suka hada ido,wani irin kallo deejahma ta watsa Mata kallon zamu hadu,Saida hantar cikin Fatima ta kada cikinta ya shiga murdawa tamkar ta saki zawo a inda take.....gyaran muryar Mai martaba itace ta saita tunanin kowa a wajen Wanda kowa ya maida hankalinsa Akan abinda Mai martaba zaice....

"Da farko dai ba wani abubane ya taramu a Nan face Akan magana muhimmiya wadda kabiru ya gabatar a zaman daya gabata Wanda na bada umarni Akan zan yanke shawara,.....kabiru ya gabatarmun da magana Mai muhimmanci Wanda a farko ban dauketa da muhimmanciba Saida na zauna nayi tunani na auna maganarsa da bukatarsa ta auren Fatima a karo na biyu,.....to nayi tunani na auna Naga cewa tabbas abinda yake shirinyi tabbas abune Mai kyau kuma jihadi ne gareshi damu baki daya,a bisa hakan ne yasa ya yanke hukuncin amince Masa da ya aureta a karo na biyu na yarda na amince dari bisa dari Domin nasan tabbas kabiru zaiyi adalci a tsakaninsu Domin nasan halin abinda na Haifa"......

Shiru tamkar anyi ruwa an dauke a wajen.....Babu Wanda ke iyayin motsin kirki tunda Mai martaba ya Soma magana.....bedamu da hakanba ya cigaba da maganarsa,

"Saboda haka na yanke shawarar aurawa kabiru wanan marainiyar Allah bayan ya auri Khadija da Dan lokaci,yin hakan shine adalci ga ita khadijat Domin da badan haka ba hada auren zanyi,Amma bayan kabiru ya auri Khadija ni zan sa lokacin aurensa da Fatima,wanan hukuncin shine abinda na yanke akan bukatar da kabiru yazo da ita,sai abu na biyu shine daga gobe insha Allahu zan wakilta waziri akan sabon ginin da zaayi a babban filin dake can gefen gidan Nan Wanda zai Zama a Nan ne kabiru zai zauna da matansa ,irin ginin da kakeso kabiru zaka iya samun waziri kuyi magana bayan taro ya tashi"

Bakin yarima yakasa rufuwa yakasa boye farin cikinsa,yanan durkusa "nagode ranka ya dade Allah ya Kara girma da daukaka,Allah ya Kara maka lafiya da nisan kwana"

Jinjina Kai Mai martaba yayi sanan ya Dora da "Fatima Ina fatan hukuncin da muka yanke akanku keda kabiru kin gamsu Zaki amince da hakan?"...kallonta Mai martaba yakeyi cikeda tausayawa....
Chapter 40 · 0% Book details