Sashe 12
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jinjina Kai haruna yayi yace "to sauran yaran da zaa fita dasu yaufa?kinsan fa nafada Miki shekaran jiyan Nan da Kika nemeni Kika rasa wajen taro Ina can Ina Kai talla"
Dariya hajiya tayi tace"haruna nawa,haruna baka da dama Sai hagu,dik abinda ka fada nasan zaka aikata ka kwantar da hankalinka wanan ba matsala bace inada sababbin Yan Mata gal a Leda"suka Kara fashewa da dariya....
Mukuwa tsuru tsuru mukayi muna kallo da sauraron ikon Allah mun fahimci wadansu maganganun wadansu kuwa bamu fahimta ba ,juyawa nayi nace "kuzo mutafi Dan Allah nagaji da tsayuwa a wajen Nan ga hayaki muba fahimtar abinda suke fada mukeyi ba"
Tabe Baki Maryam tayi tace"kece dai Baki fahimta Amma mu muna fahimta"
Batare da nace komiba nayi gaba abuna suka biyoni a baya....A daki tunani kala kala nakeyi Wanda nakasa gano bakin zaren abinda su hajiya ke nufi.....
******
Muna bin layi Ana zuba abincin Rana,maaikatan kitchen ke zuba abincin yayinda hajiya na gefe ta cokalo dauri yadda ta Saba har akazo kanmu nida Yan uwana,
Maryam CE a gaba Sai bilkisu saini,Ina Mika robata hajiya ta kalleni ta washe Baki tace "Fatima anzo karbar abincin ne?"
Murmushi nayi nace "ehh hajiya"...aka zubamin har na juya Zan wuce hajiya tace"Fatima"na juyo da sauri ta yafitoni da hannu naje inda ta koma gefe ta tsaya,ledar hannunta ta bude ta dakko soyayyen nama tasamun nan da Nan na zaro Ido,cike da mamaki nake kallonta ta gyada Kai tace"nakine Fatima daga gida aka kawomun nace Bari insa Miki kema"
Washe baki nayi cike da farin ciki,don rabona da nama tun sallah Wanda ake kawo Mana tallafi akesa Mana yanka daya da'ya,dan durkusawa nayi nace nagode na juya abina,
Kirana tayi a Karo na biyu tace "anjima bayan laasar kizo office din haruna kisameni idan Kun fito islamiyya kinji?"
Gabana ne ya Yanke ya Fadi jiki a sanyaye nace "to hajiya"na tafi abuna....
Tasa abincin nayi a gaba Ina tunani kala kala,domin tunda hajiya ta furta Tana nemana na shiga fargabar da damuwar da bansan dalilinta ba.....
*******
Tafe muke muna Hira mun fito islamiyya nida sauran Yan uwana,Sai surutu sukeyi Amma Ni shiru nayi ina sauraren surutunsu Dan gabaki daya hankalina na wajen Kiran da hajiya keyimun Dan bansan meke faruwa ba,
Waigowa nayi inda Maryam da bilkisu suke hirarsu nace "Dan Allah Maryam kuyimun rakiya Mana wajen hajiya?"
Dafe kirji sukayi a tare sanan suka hada Baki sukace "tabdijan idan kin ganmu a lahira kaimu akayi ,kedai da take Kira kije kiji ko menene Amma bandamu,ki rufa Mana asiri"
Kallonsu nakeyi dukansu,Suma kallon nawa sukeyi Ganin yadda na canja fuska tamkar zanyi kuka yasa bilkisu cewa "muje mu rakaki Amma a waje zamu tsaya gaskiya"
Da sauri nace "eh na yarda"
Nan muka rankaya zuwa ofishin malam haruna Wanda yake can gefe Shi kadai akwai Dan tafiya Mai Nisa daga inda muke takowa,
Muna Yar hirarmu har muka iso wajen,sukaja suka tsaya nikuma ilahirin jikina Babu inda baya rawa dakyar nake daga kafata na shiga office din da sallamata....
*******
Ina tsaye gefen hajiya Ina sauraron maganganun da takeyimun su kasa kasa tamkar wani na jinmu,
"Ki tsaya ki kwantar da hankalinki kici arziki kibarshi a mazauninsa,Sai kiga sanadiyyar wanan mutumin Allah ya kawo waadin zamanki a gidan Nan Fatima,ki kwantar da hankalinki ki saki jikinki kamar sauran Yan uwanki,Kinga su zainab su fauziyya dik suna wanan harkar,Kuma wallahi ba karamin arziki suke samu ba,sanan suci Mai kyau subarku da wanan kamiyamiyar da ake dafa muku"
Kallonta nakeyi cikin rashin fahimtar inda maganganunta suka dosa nace "hajiya ban fahimcekiba kiyimun yadda zangane wani irin aikine zaakaini yi?"
Murmushi hajiya tayi tace "bawani aiki zaa kaikiba,kwana daya kacal zakiyi a can idan munkaiki sanan kada ki kuskura kiyi mishi gaddama don babban mutum ne,tunda ya ganki ya kasa sukuni ya kwadaitu da ya kebe dake"
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun,hajiya iskanci fa kenan"
Kallon yadda na furgice hajiya keyi sanan ta Mike ta tsaya a tsaye Tana kallona shekeke tace"iskanci ma zakice?to tunda kince haka Shi nake nufi Sai me?ai iskanci Fatima Dole kuyishi tunda Shi iyayenku sukayi suka watsar daku a titi ake tsintarku daya bayan daya,saboda haka Ina Mai shaida Miki ki shirya don Shi zankaiki kiyi kisama Mana kudi da dukiya Mai yawa dominke kinzo da farin jini"....
Ja da baya na shigayi ina girgiza kaina,yayinda hawaye suka shiga gudu a idanuwana Wanda bansan Ina yinsu ba bakina na rawa na Soma magana "Koda iyayenmu sukayi iskanci suka haifemu,hakan Bai bamu lasisin aikata abinda su sukayiba,sanan bamuda tabbacin Zina akayi aka haifemu hajiya,Dan Allah Dan annabi kiyiwa Allah ki janye kudurinki Akaina domin Ni banida wanan raayin,Kuma harabada bazan taba aikata iskanci ba"
Wasu kyawawan Mari hajiya ta saukemun guda biyu a kumatuna lokaci daya na nemi natsuwata na rasa"ke harkin Isa kicemun bakida raayi Akan abinda zansaki kiyi?wacece ke?ke asuwa to wallahi Fatima?to wallahi Baki Isa ba zamusa kafan wando daya Dani dake a gidan nan,bace mun daga gani"
Juyawa yayi Ina kuka na fito a office din,waige waige na shigayi Ina neman Yan uwana,
Can jikin bishiya na hangesu xaune nasan sun gaji da jirana ne sukaje wajen suka zauna,wajen na nufa nasamesu ,dukkansu kallon fuskata sukeyi da alamar tambaya yayinda na cigaba da sharar hawayen da ke zubowa a idanuwana ba kakkautawa.....
Cikin tsananin damuwa da tausayawa bilkisu tace"Fatima lafiya?meke damunki?meyasameni?"
Lokaci daya take jeromim wadanan tambayoyi,hannu nasanya na goge hawayen dake zubowa daga idanuwana,cikin shasshekar kuka na kwashe dik abinda hajiya ta fadamun na fada musu"
Girgiza Kai kawai bilkisu keyi tace "wallahi nasan haka zata faru,domin tunda hajiya tace Tana nemanki nasan cewa akwai wani Abu a kasa,shikenan tafaru takare munfada balai,abin da muke Ganin anasanya Yan uwanmu ya dawo kanmu".....
....Maryam dake gefe tace"Niko a ganina wallahi ba wani Abu bane karuwarmuce Fatima kudi xaki samu sanan itama hajiya tasamu nata,Kinga kema Zaki shiga jerin yaran da hajiya keji dasu a cikin gidan nan,Kinga kin huta muma dake gefenki zamu ci arziki"
Wani irin kallo na Kebin Maryam dashi,hartagama magana sanan nace "Amma bakida hankali Maryam,Zina fa?ita malamin islamiyyarmu yanzun ya Gama waazi akanta Amma kike cewa bawani Abu bane?to harabada Ni Fatima bazan taba aikata zinaba don Ina marainiya banida gata in aikata mummunan aikin da Allah zaiyimun azaba dashi ranan gobe kiyama,Wai don Ina ikirari da rashin gata!!"
"Idan kikace zakija da umarnin hajiya wallahi Zaki kurbi azaba a cikin gidan Nan kinadai San halin hajiya Sarai,haka kawai ma hajiya ta azabtar da mutum balle ta bashi umarni yakiyi"
"Umarnin hajiya ba fadar Allah bane sanan Bata Isa tayimun abinda Allah beyimunba,wallahi ko mutuwa zanyi saboda azaba bazanyi iskanci insaida mutuncina ba don Ina neman abin duniya"
Kuka sosai Fatima keyi Tana fadin "nashiga uku,Allah kana gani kasan dalilin da yasa ka kaddaro Mana wannan rayuwar Allah ka dubamu"
Ita kanta bilkisu hawaye takeyi a gefe Tana Mai tausayin Zahra domin tasan Babu makawa tunda hajiya halima ta bada umarni to Dole abishi
Munkai Rabin awa muna zaune Saida magriba ta kawokai sanan muka Mike dukanmu muka nufi hanyar masallaci,.....
Tunda muka doshi masallaci na ke hangesa tsaye yau ma da waya sagale a kunnensa Yana waige wage kamar me neman wani,
Dukaninmu mamakine dauke a fuskokinmu muka kalli juna,....bakin Maryam har rawa yakeyi wajen fadin "Fatima Kinga mutumin mu na ranan ko?wallahi shine "
Bilkisu tace"shine Mana ,Allah yasadai ba aljani bana mukadai muke ganinsa"
Nidai bance komiba Sai kallonsa kawai da nakeyi har muka karasa wajensa zamu wuce...."Fatima"....shine abinda yace cikin sassanyar muryarsa kamar ranan...
Tsayawa mukayi dukanmu muka juyo a tare,kallonsa mukeyi shiko murmushi yayi yace "ku nazo nema fa tun dazun,bangankuba ban kuma San inda Zan sameku ba"
Karasowa yayi wajen da muke tsaye yace "Ina wuninku"
Dukanmu kunya CE takamamu yayinda lokaci daya yayi Mana kwarjini a tare muka hada Baki wajen gaishesa,murmushi yayi ya amsa sanan yace "Hira nazo wajenku bangankuba nakasa Zama a gida,kasantuwar yau lahadi Babu aiki yasa nace Bari inzo indubaku"
"Mungode"muka hada Baki mukace sanan muka juya zamu wuce,da sauri ya Sha gabanmu yace "ya zaku tafi ko sallama Babu"
Cikin kosawa da zancensa nace "malam sallah zamuje lokacin sallah yayi"
"Ba sunana malam ba sunana kabir,..."
Juyawa nayi batare da nace komiba nabarsu tsaye a Nan,inda su bilkisu suka tsaya wajensa nayi tafiyata na barsu domin zuciyata Babu Dadi....
******
Muna kwance a daki gefena bilkisu ke shaidamun wanan mutumin yace zaizo Mana Hira gobe da yamma ya tambayesu inda zai samemu ta nuna mishi wajen zamanmu,
Na kalleta a Dan fusace nace "daga Ganin mutum bakusan ko wayeba Kun tsaya zuba zance dashi kune harda cewa yazo to Allah ya Baku saa ya hadaku da hajiya Ni Babu ruwana wallahi".....
******
Washe gari kabir yazo gidan marayu wajenmu ,su bilkisu ke zuba surutu nidai saidai inyi murmushi ,tundaga wannan lokacin muka Saba da kabir yake fada Mana Shi Dan sarkine,abinda na Lura da kabir shine yanada tausayi sanan bashida yawan surutu Kuma akwai kwarjini.....
*******
Na fito Ina sauri zanje bayi ,na gamu da zainab take shaidamun hajiya na nemana,gabana ne ya Yanke ya Fadi Nan da Nan hankalina ya tashi nasan kwanan zancen,fitsarin Dana fito zanyi ne naji ya koma nayi wurgi da gwangwanin dake hannuna natafi Kiran hajiya.....
"Fatima"
Na da'go Kai na kalli hajiya sanan na sunkuyar da kaina kasa Ina Wasa da yatsun hannuna,
"Nakiraki ne Akan maganar da mukayi dake kwanakin baya,Kika cemun bakida raayi ko?"
Na daga Mata Kai idanuwana suka kawo ruwa,
"Fatima kitaimakeni ki dubi girman Allah ki amsa bukatarmu wallahi nayi Miki alkawari daga wanan bazaa sake fita dake ba Sau daya kacal zaayi abin Nan a Gama,mutumin Nan babban mutum ne bakisan koshi wayeba kidaure ki amince da wanan bukatar tamu Fatima"
Kuka na sanya Mata batare da nace komiba Dan bansan mezance mataba,
"Kiyi shiru ba kuka nace kizo kiyimunba a Nan ,bazan taba tilastaki Akan aikata hakan ba Amma Ina Mai shaida Miki da kanki Zaki kawo kanki kice kina bukata......"
A Raina nake Raya "aikuwa baxan taba kawo kaina domin aikata sabon Allah ba harabada Ina me addua Allah ya kareni daga mummunan aikin"