Sashe 37
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan yareema yayi breakfast daga bangarensa fada ya nufa wajen Mai martaba don ya tunasar dashi Akan maganar Fatima....
Bayan sun taba Hira sosai sanan yarima ya shigo da bukatarsa ,yauma Mai martaba fafur yaki yarda da maganar kamar jiya haka yarima bai gusheba Yana rokonsa Yana tunasar dashi game da maraya da dumbin ladan da zaisamu da rahmar da Allah zaiyi Masa sanadiyyar hakan....
Shiru yayi Mai martaba Yana tunani Akan wanan lamari sanan yayi Yar gyaran murya yace "dik na fahimceka kabiru Kuma na gamsu,Koda zan yarda da maganar aurenka da Fatima sai Akan sharadi daya"
Da sauri yarima ya dago Kai cike da tsananin farin ciki yace "ko menene sharadi zan yisa matukar zaka amince mun mahaifina"
Murmushi Mai martaba yayi ganin yadda yarima ya rude "sharadin shine bazaka auri Fatima yanzunba sai ka auri deejahmah har saita haihu"
Damn kirjin yarima ya shiga lugude....shida ya yanke shawarar ko auren deejahmah yayi bazai taba hada shimfida da ita ba?yanzun Mai martaba yasa Masa sharadi akai Kuma matukar yanason Fatima Dole ya aikata hakan?.....
Gumi ne ya shiga karyowa a fuskarsa ya gyara zamansa ya Kara durkusawa yace "na amince ranka ya dade"
Murmushi irin na manyan sarki yayi ya Dan gyada kansa "shikenan na amince maka da aurenta Allah yasa ta Zama alheri a gareka da rayuwarmu baki daya Allah ya baka ikon rike Amana yasa ta zame Mana hanyar shiga aljannah'
Wani irin farin cikine ya lullubesa bakinsa har baya rufuwa yace "ameen ranka ya dade Amma Dan Allah Ina neman alfarma daga gareka"
"Fadi bukatarka kanka tsaye"
"Allah ya taimakeka inaso ka fadawa kowa hukuncin daka yanke da kanka a Zama na gaba "
"Idan na fahimceka iyayenka Mata kake tsoro"
"Karkaji komi insha Allah komi zaizo da sauki Allah ya Kara maka hikima da kaunar na kasa da Kai Domin babu tantama Kaine ka biyo halina"
Murmushi yarima yayi "nagode mahaifina Allah ya Kara maka lafiya da nisan kwana zan shiga cikin gida"...
Daga Masa Kai kawai Mai martaba yayi.....ya Mike ya fice,...a hanyar sa ta komawa ya hadu da gwaggo rahi zasu shiga fada....da sauri ya tsugunna a gabanta ya gaisheta Amma ko kallonsa batayiba sai harara ta watsa Masa deejahma na biye da ita,....murmushi yayi ya waiga ya kallesu "nayi nasara"....shine abinda ya furta a Fili zuciyarsa fara tass fuskarsa dauke da walwala....Yana tafe Yana murmushi Wanda shi kadai yasan dalilin yin hakan burinsa be wuce yaga bintu ba sanyi idaniyarsa...
********
"Fatima dik yadda zaayi ki gudu ki boye Dan bazan iya ganin muguntar da ake Shirin yi Miki ba Domin kinji....."....Nan bilkisu ta kwashe abinda taji a wajen rahane ta fadawa Fatima tas Bata rage Mata komiba
Ai dafe Kai Fatima tayi ta Fadi jagwaf ta zauna da duwawunta,tashin hankali Wanda baasa mishi Rana....
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun na shiga uku ni Fatima wanan wani irin balai ne nake fuskanta ciki rayuwata daga wanan sai wanan?dik wahalar Nan da nake ciki Bata ishesuba sai an hada da nakasani?"...ta fashe da kuka Mai ban tausayi,
Itama bilkisun batasan lokacinda tasa kukaba sukayitayi har suka gaji bilkisuce ta tsagaita da kukanta tace "me zai Hana ki shiga dakin tsohuwar ajiya cikin Kaya ki boye ayita nemanki a rasa a cikin gidan ke idan kwana ya kamaki ma ki kwana a can kawai ninasan mezan fadawa yarima Amma bazan fada Masa abinda zaayi mikiba kika guducan zance mishi aiki aka sa ki"
Da sauri Fatima ta Mike tsaye fuskarta sharkaf da hawaye ta rungume bilkisu "nagode Yar uwata hakika zuwanki gidan Nan alherine a gareni da babu ke da bansan yadda zan kasanceba"..
Bubbuga Mata baya bilkisu tayi "ai ba surutu zamu tsayaba kitafi kawai muyi musayar Kaya inbaki nawa insaka naki inyita aiki anan tunda nasan hajiya bazata nemeniba tunda tanada baki Kuma akwai su saade"..
"Haka zaayi"....da sauri bilkisu tayi gaba Fatima na binta a baya suka nufi dakin tsohuwar ajiya don suyi musayar Kaya har sun shiga bilkisu tai sauri tace"ke na tuna idan mukayi musaya zaazo nemanki tunda ansan inda kike aiki asirinmu zai tonu karmu canja kiyi zamanki kawai a Nan din"
Shiru Fatima tayi Tana kallon bilkisu Tana mamakin yadda takeda masifar hikima da wayau koda yake ko dama can bilkisu akwai wayau ga basira.....Tana gani bilkisu ta fice da sauri Fatima ta bita da kallo hawaye na gangarowa a idanuwanta....
********
"Isiyaku na tabbatar maka da inhar ka aikata abinda nasaka to zanbaka babbar kyauta Mai tsoka,....kayi yadda nace kada asamu matsala Domin yau dik runtsi can zata kwana kayi tafiyarka kayi aikinka daddare zakaje ka gudanar da abinda na saka don so nakeyi yarinyar Nan yadda ta kashemun gudan jini in nakasa rayuwarta sai tayi danasanin zuwanta duniya......"
"Insha Allahu ranki ya dade zaa aikata yadda kikace idan kasheta kikace ayi ma zaayi ai kinfi karfin haka"
Gyada Kai hajiya babba tayi "zaka iya tafiya bakin aikinka sai dare zaka gudanar da abinda nasaka"
"Dakin tsohuwar ajiya kikace ko ranki ya dade?"
"Ehh"
Ya Kara durkusawa da har kasa "angama ranki ya dade"
Ya mike ta fuce Yana murmushi,...
A bakin kofar fita yayi kicibis da bilkisu zata shigo fuskarsa dauke da murmushi ya giftata ya wuce ta bishi da kallo har ya kule,....haka kawai jikinta bai bataba take taji jikinta yayi sanyi da kyar ta daga kafa tayi sallama ta shiga parlorn....
*Muje zuwa*
*BONUS KUKASAMU YAU PAGE BIYU GASKIYA SAI NAN DA SATI BIYU ZAKUJINI😜*
*SLIMZY✍🏼😍🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
_Wanan shafi kyautace zuwa gareki Yar uwata Rabin jiki bazan iya_ _musalta matsayinki da kimarki a idanuna da zuciyata_ _ba_ *SOPHIE GALADANCI* _Ina yi Miki son so Allah ya Kara Mana dankon zumunci....Allah ya barki da *N* dinki ya nuna mun bikinki in kwashi rawa harda shoki😹😹😹...._
27
********
Bangaren sarki kuwa tunda hajiya rahina da deejahmah suka gurfana a gabansa hajiya rahina ke koro Masa bayanin abinda ya faru Daren jiya na karya da gaskiya Wanda akayi da Wanda baayiba har cewa Mai martaba tayi yarima yace da gangan ya kawota gidan dama Dan ya aureta....shidai Mai martaba shiru yayi Yana saurarenta har ta Dasa Aya a zancenta,
Gwauron numfashi ya sauke hade da Dan murmushi sanan yace "ai rahina be kamaceki ki kawo karar danki ba bayan kinada yancin da Zaki hukuntashi da kanki batare da kin fadamun ba,ni yanzun banida abin cewa da ya wuce kiyi hakuri da su duka Dan yarane kanana wani abun yaro yakan fadesa ne batare da tunanin mezaije ya dawoba ,to ke babba ce matsayin uwa Kuma suruka saboda haka kiyi hakuri kibarni da shi kabirun"
Gyara Zama tayi "ranka ya dade yanzun maganar da kabiru yakeyi dik ya Gama zagaye gari Wai zai auri wannan tsintacciyar yarinyar Mara iyaye wadda baasan asalintaba,baasaniba ta hanyar aure aka haifeta?ko ba ta hanyar aure ba?"..
Murmushi Mai martaba yayi irin na manyan sanan ya danyi gyaran murya,jimm kadan yace "yanzun dai a jira hukuncin da zan Yanke zuwa gobe"
Dan shiru hajiya rahina tayi na Dan lokaci sanan ta Kara durkusawa"Allah ya taimakeka ya Kara maka lafiya ka duba yuwuwar wanan lamari ga Dan sarki jikan sarki"
Daga Mata Kai kawai Mai martaba yayi batare da yace komiba.....
Jiki a sanyaye tayiwa Mai martaba sallama suka baro fada jiki Babu kwari....
A hanyarsu ta komawa cikin gida suna tafe deejahmah na bambami tamkar zata Ari baki "wallahi tallahi sai yarinyar Nan tayi datasanin shigowa rayuwarmu,saina yi Mata abinda bazata taba mantawa daniba"
"Kidaina Bata bakinki Domin na tanadi sabon makami Wanda zamuyi yaki dashi azabtarwa Mai sauki ne Allah dai ya Bata ikon yin kishi dake"
Kwafa deejahma tayi ta gyada Kai lokacin sun shigo sashin hajiya babba,
Tsayuwa deejahmah tayi rike da kugu sai hura hanci takeyi Tana huci,a fusace ta juyo inda bilkisu da Rahane ke tsugunne ta watsawa Rahane mugun kallo sanan tace "ke jeki kiramun Fatima"
A kidime jiki na rawa Rahane ta Mike tayi hanyar ficewa harta Kai kofa ta tsinkayo muryar deejahma na fadin "ki tabbatar da kin kawota Nan kunzo tare"
"Toh ranki ya dade Allah ya huci zuciyar sarauniya"....ta juya ta fice....
Zare ido kawai bilkisu takeyi a zaune tamkar zata saki fitsari Dan ta tsorata da ganin yanayin wadanan azzaluman,addua kawai takeyi a zuciyarta na Allah ya kar yasa aga Fatima...
*********
"Mamana ki fahimceni wallahi auren Fatima a gareni tamkar jihadi ne a gareni daku baki daya,ke mahaifiyatace banaso kiyi wani mugun furuci Akan wanan lamarin Domin ke uwace a gareni yardarki itace bukatata kiyimun addua Allah ubangiji yasa sanaddiyar hakan Allah yayi Mana rahma Dani daku baki daya"
Tunda ya fara magana tai shiru Tana fuskantar sa,Harga allah dik maganganun daya fad'a a fadar sarki gaskiya ce Amma yuwuwar hakan fa?shin me hakan ke nufi?idan wasu sun fahimci wanan lamari wadansu bazasu fahimtaba....
Ajiyar zuciya mama karama ta sauke,hade da Jan gwauron numfashi "kabiru na fahimceka na fahimci dik abinda kake nufi yanzun idan harni na amince ka aureta mahaifinka fa?"
Murmushi ya yi kadan"mama nasan shima Mai martaba zai fahimceni insha allahu zan koma Masa da maganar tunda gobe yace zaa sake sabon zama bayan sallahr laasar"
Jinjina Kai tayi "Allah ya zabi abinda yafi Zama alheri a garemu baki daya"
Wani Dadi ne ke ratsa sassan jikin yarima,addua takobin mumini kullum yayi sallah sai ya roki Allah Akan wanan lamarin,idan mahaifiyarsa da mahaifinsa sun amince dik yakin da zai biyo baya Mai saukine Domin yasan cewa alheri yake Shirin yi ba sharri ba,....lumshe idanuwansa yayi sanan ya Kara durkusawa gaban mahaifiyarsa yace "nagode uwa tagari adduarki itace kariya a gareni "
Murmushi kawai tayi batare da tace komiba....
Yunkurawa yayi zai Mike mama karama ta dakatar dashi "naji Mai martaba nacewa su hajiya zainab suna Nan dawowa gab da bikinka jikin Mai gidan nata ya fara samun sauki umarah zasuyi su dawo dasu zaayi biki"
Dadi ne ya cika yarima da jin kanwar mahaifinsa wadda ke matukar kaunarsa zata dawo Nigeria gata da son mutane da kaunar talakawa,ya tabbatar hajiya zainab bazata bada goyon bayaba Akan wulakanta Fatima sanan Fatima zata samu sassauci....
"Allah ya dawo da ita lafiya"
"Ameen"....