← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 80

Sashe 72

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

********
"Wani daliline yasa kika cewa Mai martaba ya sassauta hukuncin da yayi niyyar dauka akan azzaluman?"yace a fusace,

Rungumesa tayi jikinta Tana shafa fuskarsa a hankali idanuwanta kirrr akansa "bazanso ace ta sanadiyyata an yakewa surukata hukunci Mai tsauriba saboda hajiya karama uwace a gareni uwa ta gari,batada wasu laifi cikin abinda ya faru Amma nasan Babu yadda zaayi sarki ya yanke hukunci batare da itaba nikuma bazan iya juran hakan ba shiyasa kawai na sadaukar da farin cikina don surukata"ta karashe maganar tana kallon kwayar idonsa Wanda shima ya kafeta da Ido,

Jikinsa ne yayi sanyi da Jin furucin Fatima Wanda tabbas yasan maganarta a Kan hanya take,idan kuwa hakane Fatima tayi Masa halarci dikda irin wulakanci da cin kashin da akayi Mata,

Muryarsa a sanyaye yace "gaskiya samun irinki a wanan zamanin abune Mai matukar wuya bintu,dikda irin rashin adalcin da akayi Miki akayiwa mahaifiyatki dama tasameki Wanda Zaki iya samun farin ciki idan Mai martaba ya yanke hukunci Amma kika gwammaci ki yafe don mahaifiyata....nagode..."

Shhhhhhhhh tasa yatsanta Akan bakinsa "karkace komi habeeby,don Nima kayimun abinda harabada banida abinda zan biyaka dashi,don haka banida riba idan na Bari an wulakanta mahaifiyarka a matsayinta na matar sarki"Tana karashe maganar ta kankamesa ta hade bakinsa da nata ta shiga aika Masa da sakwannin wadanda suka gigitashi a wanan lokaci,Nan da Nan jikinsa ya saki abubuwa suka shiga yawo a dik sassan jikinsa,

Sun dauki lokaci a haka kafin ta zare bakinta daga NASA Tana dubansa yadda dik jikinsa ya saki idanuwansa suka kankance,Shirin kwacewa takeyi ya janyota,

"Dakata malam ka manta?bafa girkina bane umm?Kar muzo mu aikata Haram kayi hakuri kaji?"ta kashe Masa Ido ta janye jikinta Tai waje abinta Tana dariya kasa kasa ya fadi jagwaf Akan kujera Yana maida numfashi..

********
"Hmmm tsuguni Bata Kare Mana ba hajiya nikam na tsorata da wanan lamari Domin tabbas inada yakini akan gaskiya zata bayyana Dan wanan hoto fa ba hadashi akayi ba?"

"Idan gaskiya ta bayyana an gabatar da matar da sukace din shin kinada tabbacin zaasamu ita zahraun ne?ai inhar baasamu dangin zahrau ba baasanetaba to Dole sarki yayi watsi da lamarin"

Gauron numfashi hajiya rahina ta sauke "nikam hajiya inada tabbacin sarki ya watsar da maganar ne yayi bakan saboda jin munada yawa wadanda bamu yardaba Amma ya rigada ya amince da zancen Fatima diyar zahrau ce Dan kinjifa abinda ya fada"

"Naji sai me?Wai har yanzun rahina bakisan abinda duniya ke cikiba koh?wallahi wallahi makirci suka hada Babu wata Mata da tabasu hoto da rubutu a ciki,tunda kikaga shegiyar ta janye da wuri harda cewa kqda ayi Mana hukunci"

Fatima har zatayi hanyar dakin mama karama ta juya ta nufi sashin hajiya babba,batare da wata fargaba ko tsoroba ta daure fuskarta tamkar Bata taba dariya ba ta tura kofar bakinta dauke da sallama ta shiga,

Deejahmah wadda ke gefe ta rafka tagumi ganin fatima yasata saurin gyara zamanta Tana binta da kallo cike da faduwar gaba,

Tsaye tayi tana binsu da kallo daya bayan daya batare da tace uffan ba,

Hajiya babba wadda ke faman kada kafa Tana girgiza hade da yamutsa fuska ta dubi Fatima shekeke tace "rasa kunya beran tanka?kinzo ne kiyi Mana Rashin kunya savida Rashin samun saa da kikayi?"..

"Ke kike ganin haka a Rashin samun saa hajiya safiya?"

Yadda ta Kira sunan a gadarance yasa dukkansu suka dubeta cike da tsananin mamaki,

"Saa Tana gareni hajiya safiya,bakomi bane kake samunsa a take batare da kasamu kalubale ko Shan wahala ba,Dan haka ki fara shirya cin kashinki da hannunki Dan saina shayar dake mamaki"
.

"Bakida wani karfi da Zaki iya shayar Dani mamaki fatima,saboda nidin ba Saar wasanki bace ba tsararki bace,ita uwar takima Bata iya daniba balle ke da Rana daya zan kulla abinda zan Gama dake....tsoro ne yasa kika dakatar da Mai martaba wajen daukar hukuncin da yayi niyya,saboda ke kanki kina gudun makircin da kuka kulla Kar asirinki ya tonu a Gane cewa hada hoto kukayi"

Dariya sosai maganar hajiya babba tabawa Fatima ta shiga kyalkyala mata dariya cike da shakiyanci Tana nunata da yatsa,

"Yanzun gashi kince uwata ta gagara zaman gidan Nan saboda azabarki yanzun kuma kince makirci muka hada to kinsan cewa kenan uwar tawa Dana gabatar ita ta haifeni kenan Amma kike fadin makirci?"..

Zuface take karyowa hajiya rahina sai faman zare Ido takeyi cike da rashin gaskiya "ke Fatima me kikazo kiyi Mana anan?rashin kunya ko cin mutuncin?

"Wanan zufar da kikeyi da zare Ido ya nuna alamar kina cikin tashin hankali Domin tun a fada kike yinsu,shiyasa ma no banida lokacin tsayawa sainsa dake rahina"..

Fatima na Gama fadin hakan ta juya ga hajiya babba wadda ko motsi Fatima tayi sai taji gabanta na faduwa Amma saboda jarumta irin Tata takasa gasgata cewa tsoron yarinyar takeyi,

"Hajiya safiya na dawo gareki ba tsoro bane yasa na janye Akan hukuncin da Mai martaba yayi niyyar yi muku,arzikin surukata kukaci Dan bazan iya Bari ta tozarta a idon duniya ba yin hakan da nayi na siya Mata mutunci da kima ne Amma indanku ne baki sarki ya watsaku a kurkuku ba ya azabtar daku har ku mutu,....Sanan Ina meyi muku albishir da nidakaina zan hukuntaku ni zan wulakantaku kamar yadda kuka wulakanta mun mahaifiyar sai kunyi danasanin aikata hakan"....Tana karashe maganarta Bata jira cewarsu ba ta fice zuciyarta na yi Mata tsananin zafi,

Karo sukai da yarima lokacinda ta fito sashen hajiya babba don dik abinda ya faru Yana sauraronsu kuma yaji Dadi da take maida musu da martani,

Ruko hannunta yayi ganin zata wuceshi batare da tace komiba "Ina zakije?"cakk ta tsaya batare da tace komiba,

"Yamma tayi kuzo mu wuce gida"..

"Zanyi sallama da ummu da hajiya"

"Ok kitura zaituna ta Kira mun deejahmah mu wuce"....

Ta gyada Masa Kai batare da tace komiba Tai gaba abinta,

Kuka sosai deejahmah keyi saboda tsananin takaicin abinda ya faru dik jikinta yayi sanyi ga tsoron Fatima daya darsu cikin zuciyarta,

"Banaso ki karaya khadeejah kisawa zuciyarki jarumta zakici ribar rayuwa,karki kuskura yarinya karama taci galaba akanki"..

Ta jinjina Kai hade da share hawayenta,...zaituna ce tayi sallama ta isar Mata da sakon yarima ta fice...itama bada jimawa ba ta kimtsa ta gyara fuskarta ta fito suka tafi...

********

Da dawowarsu gida Fatima ta fada sashenta ta rufo kofa kowa bangarensa ya nufa,..

Wanka tayi ta fito ta bude wardrobe dinta ta Shiga dube duben kayan da takeso ta Sanya,....

Shiru tayi tsaye tana daure da towel lokacinda wasu Kaya suka Fado Mata Wanda ummu ta Aiko Mata dasu bayan abkawota da kwana biyu,

Da sauri ta bude side drawer dinta na gefen gado ta Ciro katuwar jakar ledar da tunda aka kawo Bata budeba ta Shiga zazzage kayan ciki,abinda taganine ya Bata mamaki da dariya savoda kananan Kaya ummu ta siya Mata masu shegen kyau da tsada ta Shiga budesu daya bayan daya harta Kai hannunta Kan wata Yar doguwar Rigar da bazata wuce Mata iya cinyoyinta ba ta ajiyeta a gefe,

Ta maida sauran kayan ta ajiye a gefen gadonta ta dauki rigar tasa dakyar ta kugata a jikinta ta shige saboda robace,

Rigace Mai shegen kyau da rubutu I love u a gaban rigar wadanda akayi su da kalar baki,.. juyi sosai tayi tana kallon kanta,lokaci daya tasa hannunta ta rufe fuskarta Tana dariya Dan ita kanta tabawa kanta kunya,

Ta Dade gaban madubi Tana shafe shafen turarruka kala kala a jikinta ciki harda Wanda ummu ta Aiko Mata dashi ta baza gashinta a bayanta Tai masifar kyau tamkar wata baturiya,

Wayar ta tadauka da earpiece dinta ta makala a kunnenta wayar na rike a hannunta ta fito ta rufo kofarta,

Dakyar take taka kafarta ta sauka cike da yanga ta karasa parlorn lokacin deejahmah na zaune gefen yarima ta Dora kanta a kafadarsa,

Kamshin turarenta ne ya kauraye wajen shi yaja hankalinsu gabaki daya suka maida dubansu gareta,

Wani irin kallo take jifan yarima dashi Sanan ta sauke Masa Kaya taccen murmushi tayi mishi throwing kiss ummuaahhhh ta kashe Masa Ido ta juya cike da kwankwasa ta zauna a kujerar dake kusa da tasu ta Dora kafa daya Kan daya,

Dakyar yaja numfashinsa dake kokarin kwace Masa saboda wanan sako da Fatima ta aika Masa ya nemi natsuwarsa ya rasa,

Wayarta ta rike Tana tattabawa Sanan ta dago Kai a karo na biyu,..."ranka ya dade nifa banason kallo ga matarka a jikinka Amma idonka na kaina?"a shagwabe tati maganar ta turo babki,

Sosai abubuwan da Fatima keyi yakeba yarima mamaki saboda gabaki daya ta sauya a yadda yasanta,

Wayancewa yayi ya Dan kalli deejshmah yaga itama shi take kallo,

"Bintu ke dawani Ido kika kalleni zakice na kalleki?"

"Abin ne da mamaki bayan ga matarka a jikinka kana Bina da kallo ,in gaskiya ne ka kalleta Mana"

Shan murrr yayi ganin Fatima nayin maganar cike da gayya ga yadda deejahmah ta cika ta batse,

Hararta yayi hade dayi Mata kallon zamu hadu,

Makale kafada tayi "nidai ah ah banso dik ka Gama luguiguitani bayan kasan wanna abun bazai yuwuba tunda ba girkina bane shiyasa ma yau bazakamun rakiya daki ba"da gayya tayi maganar,

Kasa boye kishinta Deejahmaj tayi Tai saurin cire kanta daga kafadarsa Tana kallonsu daya bayan daya zuciyarta na tafarfasa ,wato dama munafuntarta sukeyi a kwananta suke makalewa suna soyayya?idanuwanta suka kawo ruwa ta kallesa Ido cikin ido Yana hango Yar kwallar dake Shirin zubo Mata Tai tafiyarta a fusace,

Toshe bakinta Fatima tayi tana Yar dariya cike da mugunta da gayya,

Tasowa yayi yayo kanta a guje ya Mike suka Shiga zagaye parlon Tana kyalkyala dariya tun baya dariya shima ya Shiga yin dariyar ta bullo ta bayan kujera Tana Shirin Hawa sama ya cafketa ta fada jikinsa Tana dariya sosai,

"Haba bintu meyasa kikeyin irin haka umm?so kikeyi kisawa diyar mutane hawan jini?Babu kyau fa Kinga yanzun kin hadamu"ya kashe Mata ido,

Turo baki tayi kadan ta hararesa "to tunda bakason bacin ranta sai kaje ka lallasheta ai ramawa nayi"ta Dan hararesa Tana ture hannunsa daga jikinta,

Ya Kara rungumota jikinsa Yana shinshina wuyanta zuwa kirjinta Yana shafata,sanan ya dago kansa Yana dubanta,"ya kikeso inyi umm?Wai kinsan menakeji kuwa?"..

Kashe Masa Ido daya tayi "mekakeji?"..

"Ina muradin zumarki bintu"
Chapter 72 · 0% Book details