Sashe 29
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nazo bangankiba to sako hajiya ta bani ki koma dakin da aka saki ki gyara kicigaba da aiki idan baki gamaba ki kwana a can".....
Kallo Fatima Kebin saade dashi harta kule bayan tagama fada Mata tai tafiyarta....runtse idanuwanta tayi ta budesu sanan ta juya da sauri ta nufin sashen da aka turata dazun Dan ta gyara.....
Aiki takeyi babuji Babu gani Amma Rabin abikin da takeyi Tana tunanin yarima ne Bata taba tsuntar kanta a yanayin data tsunci kantaba dazu wasu sababbin abubuwa ne takeji game dashi Wanda yasa taji tamkar su kasance a haka harabada....
Har dare Tana aikin a haka duhu ya risketa tsoro da fargaba dik suka ziyarceta ganin har duhu yayi Bata gamaba gashi ance a wurin Nan zata kwana ihunka banza,....can gefe ta rakube ga sauro dake faman Kai Mata cizo Tana bugesu ta ko Ina.....kukane ya kwace Mata Wanda ita kanta batasan tanayinsa ba,.....lokaci daya Yan uwanta suka Fado Mata su bilkisu da Maryam ko wani Hali suke ciki oho?kallon kanta tayi a cikin duhu ta tunada dik inda zasu shiga tare suke zuwa da bilkisu har bayi saboda yadda take da masifar tsoro sai gashi yau ita kadaice zaune cikin duhu sauro na Kai Mata cizo Babu Wanda ke debe Mata kewa......Tana Nan zaune tsoro Mai tsanani na karuwa Mata savoda yadda dare yafarayi gashi harta da tafin hannunta Bata gani saboda duhu dunkulewa tayi waje daya ta hada Kai da gwiwa sanyi na kadata sai adduoi take kamowa Tana saki.....haka dare ya tsala Tana Nan dunkule idanuwanta Gam ta rufesu Tana kamo adduoi kala kala har asuba batare da tayi bacciba.....
**********
Washe gari da safe
Misalin karfe goma na safe gwaggo rahi na zaune suna breakfast da yaranta kowa da abinda yakeci deejahmah ta ajiye cokali ta kalli mamanta tace "Wai nikam mama ko Yaya ake ciki da shegiyar yarinyar can ooho"
"Ohon musu mudai ai burinmu ya cika tunda abinda muke bukata ya karbu a gidan sauran yakin dik Mai saukine"
"Nifa mama na tsani yarinyar Nan wallahi hankalina bazai kwantaba idan har ban batawa yarinyar Nan wanan fuskar me kamada ta mayu ba"
Kallonta gwaggo rahi tayi sanan ta kurbi ruwan tea Saida ya fada mata tace "ki aiwatarda dik abinda kikai niyya Yar lelen"
Murmushin Jin Dadi deejahma tayi sanan tacee"zan kaiwa hajiya ziyara da yamma"
"Hakan nada kyau"
*********
Koda Fatima ta tashi dakyar ta iya mikewa saboda yadda jikinta yayi tsami tun asuba takarashe aikin wajen ta fito Tana tangal tangal har sashensu hajiya har kasa ta gaida su Amma Babu Wanda ya amsa Banda kallon kyama da khausar tabita dashi haka ta Mike jiki a sanyaye ta fice ta nufi wajen zamanta dake can baya kayanta sunyi dukun dukun jikinta dik cizon sauro yayi jajir hannuwanta ga yunwa dake kwakularta.....
Sanin inda take Zama yasa yarima Yana fitowa bangarensa har ya nufi sashin iyayensa ta dawo da sauri ya canja hanya.....Aiko can ya hangeta da jajayen kaya zaune ta kurawa sashe daya Ido ko kiftawa batayi ta Lula cikin duniyar tunani....har ya iso wajen Bata saniba ya Dan tsaya akanta ganin batasan yanayiba yasa ya Sanya hannunsa ya shafi gefen wuyanta da sauri ta Mike a razane
"Ke nine"....ajiyar zuciya ta sauke sanan ta turo baki gaba tace "shine zaka bani tsoro"
"Yi hakuri bintu na fito saboda nasan wajen zamanki yasa ke nakeso infara gani nayo Nan ko bakiji dadiba"ya daga Mata gira daya
Murmushi tayi tace "Nima ai Kai nakeson gani don inada wata bukata a wajenka"..da sauri ya gyara tsayuwa yace "Fadi bukatarki ko wace irice"
Shagwabe fuska Fatima tayi har Tana shirinyin kuka cikin shagwaba tace"Ina maraicin Yan uwana"
Matsowa yayi daf da ita yace "suwaye"
"Su bilkisu....inaso sudawo Nan da Zama Dan Allah ka taimakeni ka hadani dasu ko zanji Dadi"
Kallonta yakeyi cikeda tausayawa yasan Dole ta bukaci kasancewa da wani ko Dan tasamu sanyi ta wani bangaren to tayaya zai kawosu bilkisu gidan Nan?"
"Kaji yaayaah"....firgigit ya dawo daga tunanin da yakeyi kallon fuskarta yayi yaga hawaye na sauka da sauri yasa hannu Yana share Mata ya riketa sosai yace "ya Isa zan kawosu Babu abinda Zaki nema a wajena ki rasa Amma da sharadi"
Da sauri ta kallesa "Ina sauraronka,ko wani sharadine zanbi inhar zan kasance da Yan uwana ka taimaka ka cetomunsu Dan nasan baa lalata musu rayuwaba"
"Shhhhhh naji sharadin shine zan kawosu bilkisu Amma daga ke harsu bazaku nuna kunsan juna ba saboda dabarar da zanyiwa su hajiya"
Da sauri tace "na amince"
"Oya share hawayenki banason kukan Nan a koke gwamnan kuka"
Murmushi tayi Masa tasa hannu ta share hawayenta yabi hannunta da kallo Wanda dik cizon sauro yayi rudu rudu...ya girgiza Kai yace "zantafi wajensu hajiya insha Allah zankawo Miki Yan uwanki"
Murmushi tai Masa ta gyada kanta ya juya tabishi da kallo Tana murmushi....
*******
Bayan sun gaisa dasu hajiya Sama sama yarima gabansa na faduwa ya gyara Zama yace "hajiya nikam bayin gidan Nan sunyi kadan ya kamata a karo wasu"
Jinjina Masa Mai hajiya babba tayi tace"kayi yadda ya Dace"
Murmushin nasara yayi batare da yasha wata wuyaba....
*Muje zuwa*
*SLIMZY✍🏼😍*🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*NA:SLIMZY✍🏼*
_wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
*Wanan shafi kyautace zuwa gareki mommah* ( *_BILLY_* *_GALADANCI_* )... *kiyi yadda kikeso* *dashi, Ina yi Miki* *son so...* ❤😍
22
Kallon mahaifiyarsa yayi a fakaice,bama ta kallon inda yake don yadda ta nuna tamkar batasan da zamansa a wajenba,
Yakai minti goma a zaune sanan ya Mike har ya juya hajiya babba ta tsaidashi ta hanyar yi mishi magana "A Ina zaka samo bayin kamar yadda kace"....batare da wata faduwar gaba ba yace "akwai wani kauye da Ahmad yacemun anyi rigima a wajen an zube mutane Kara zube wasu Ana dibarsu aikatau wasu Ana shigowa dasu cikin gari suna bara shine nace zanje in duba ko Yan Mata biyu ne asamo tunda Naga kuyangi sunfi yawa a gidan"
"Hakan yanada kyau"....juyawa yayi batare da yace komi ba ya fice abinsa....
********
Office yasamu Ahmad abokinsa Nan suka zauna yake bashi labarin shawarar da ya yanke....
"Yanzun kana ganin dakko yaran Nan ka kawo gidanku baka kinkimowa kanka wata rigima ba?"
Dan Bata fuska yarima yayi yace "wace irin rigima"
"Dik ranan da asiri ya tonu har sarki sai yayi fushi dakai Kuma zaka Kara jefa kanka cikin zargin da akeyi maka"
Murmushi yayi yace "dik halin da zan shiga zan shiga matukar zansa Fatima farin ciki,sanan kafin insamu hajiya na gindaya Mata sharudda Akan hakan".....Nan yarima ya kwashe yadda sukai da Fatima ya fadawa Ahmad,
"Allah ya baka ikon rikon maraya cikin gaskiya da Amana ya baka lada"
"Ameen yanzun inaso in zauna a Nan ne zuwa ka tashi office dinka sai ka rakani muje can gidan marayu idan mun daukosu mukaisu gida tare da Kai Dan na fadawa su hajiya kauye zanje daukosu"
Dariya Ahmad ya sheke da ita sanan yace "dadina dakai fasaha,ni wanan tunanin be shigomin a raiba,shiyasa ka zabi dik inda zakaje kaje batare da excort ba ko?"
Murmushin gefen fuska yarima yayi ya shafa Dan sajen fuskarsa ya ce'ka cika sa ido"
***********
A gidan Ablah kuwa tunda ta tashi take tunanin yadda zaayi taje taga Fatima,...aikace aikace takeyi itada Yar uwarta Aysha Saida suka Gama suna zaune a parlor suna hutawa ablah ta kalli Aysha tace"Niko Aysha inaso inje Inga yarinyar Nan Fatima Inga halin da take ciki"
"Ablah kina ganin zaabarmu muganta?gidan sarauta fa?"
Dan jinjina Kai Ablah tayi sanan ta jingina da jikin kujera tace "zaabarmu insha Allahu ai yarima Yana Nan ki shirya anjima zankira oga a waya in sanar Masa da inason zuwa ganin Fatima sai muje da yamma ko"
"To Allah ya kaimu"
"Ameen"
*********
Tsaf deejahmah ta shirya ta dibi bayi da kuyangin gidansu Yan rakiya ta shiga mota Suma suka shiga tasu aka jata zuwa gidan sarki........
Tafiyar mintuna kadan ta kawosu gidan kasantuwar Babu wani tazara tsakanin gidan sarki da gidan galadima Wanda ya kasance shine mahaifin deejahmah.....
A parking space sukayi parking deejahmah ta fito Tasha kwalliya ta kece raini Tana sanye da super English atamfa anyi Mata dinkin Riga da skirt ya zauna Mata dasss a jikinta ta kawo mayafi ta yane kanta dashi Wanda ya rufe har Rabin jikinta,fuskar Nan Babu annuri sai yatsina takeyi bayi da kuyangin ta suna biye da ita wasu a gabanta wasu a bayanta tamkar itace Yar sarkin yadda take taka kasa ma abin kallo ne dik inda ta gifta maaikatan gidan sarki zubewa kasa kawai sukeyi suna kawo gaisuwa,saidai kawai ta daga musu hannu,a haka har ta Isa babban sashin gidan....
Bayin dake tafiya a gabanta suna zuwa kofar babban parlor suka zube a gefe da gefen kofar ta shiga da sallamarta a ciki ciki......
Da faraa dauke a fuskar hajiya babba takeyiwa deejahma marhabun....
Gefen hajiya babba ta zauna inda khausar ke zaune ta kishingide Tana famar daddana waya,
Fatima ce a gefen hajiya ta durkusar da Kai a lokacin hajiya na Bata umarni Akan wani aiki da zatayi....
Deejahmah Bata lura da Fatima ba Dan batada masaniya Akan komawarta kuyanga,....kallon hajiya tayi sanan ta sunkuyar da kanta kasa tace"barka da hutawa ranki ya dade uwar gida a wajen sarki Mai masarautar barayar Zaki"
Murmushin Jin Dadi hajiya babba tayi sanan ta amsa da"barka da zuwa diyata deejahmah"
"Barkadai hajiya na sameku lafiya?"
"Lafiya kalau diyar albarka".....
Shiru ne ya Dan biyo baya kafin hajiya tasa kafa ta hankade Fatima cike da izzah tace "baki iya gaisuwa bane?Koko saarki ce ta shigo da kika kasa bude baki ki gaisheta isasshiya?ke komi sai an nuna Miki saboda dabbanci ki manta da matsayinki na kuyanga baiwar gidan sarki"
Da sauri Fatima ta gyara durkuso tace "tuba nakeyi ranki ya dade"
Wani kallon Tsana deejahmah ta jefawa Fatima Saida tayi magana sanan ta ganeta ta hanyar muryarta Dan bazata manta da shegiyar muryar yarinyar ba Mai kama da an hura usur....
Da sauri deejahmah ta tarbeta ganin Fatima ta Kara durkusawa Tana shirin gaisheta "dakata Yar matsiyata bana bukatar gaisuwarki a matsayinki na shegiya wadda batada iyaye.....gaisuwarki a matsayinki na kazanta Babu abinda zai karamun saboda haka ki rike gaisuwarki"