← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 80

Sashe 46

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kalli bilkisu Tana murmushi tace "Bari insa ruwan zafi inje inyi sallahr laasar kafin Nan ya tafasa yarima keso sai inzo mu zanta ko?"

Jiki Babu kwari bilkisu ta amsada "toh shikenan ki sameni wajen magwarori"

"Naga jikinki dik yayi sanyi ne ko akwai wani Abu ne Yar uwa?"

Girgiza Kai kawai bilkisu tayi ta juya abinta....

**********
Sauri sauri tayo alwala ta zo inda ta Saba zuwa tayi ibada ta shimfida dankwalinta ta tada sallah cikin natsuwa take sallahr ta ta fuskanci alkibla

Tafe suke Tana rike da hannun yaronta karami sun fito sashin Mai martaba yaron ya kalli mahaifiyarsa Yana nuna Mata Fatima dake sallah "ummu laa duba sallah takeyi ankira sallah ne?"..

Juyawa hajiya zainab tayi tana kallon inda yaron ke nuna Mata tabi yarinyar da kallo wadda ke sanye da Kaya irin na kuyangin gidan "sadik ankira yanzun zamuje muyi muma kaji?"..

"Toh ummu muyi sauri"

Batace masa komiba takebin Fatima da kallo Tana jinjina Kai cike da mamaki ta furta a Fili "ikon Allah "...haka suke tafe Tana saka da warwara har suka shigo sashen hajiya karama ko Zama batayiba ta kalli hajiya cike da al'ajabi tace"hajiya dama maaikatan gidan Nan suna sallah ne?ni tunda nake bantaba ganin wata baiwa ko kuyanga na sallah ba a iya rayuwata a cikin gidan Nan sai yau Naga wata Yar farar yarinya bandai lura da fuskarta ba Tana sallah can baya"

Fuska dauke da damuwa hajiya karama ta kalli hajiya zainab sanan ta kauda kanta gefe tace"wacece kika gani Banda Fatima?yarinyar da kikejin labarin ta kashe Miki d'a habibu ?itace wadda danki yake Shirin jajubowa a matsayin matar aure tsintacciya Mara asali itace surukarku"

Zama hajiya zainab tayi gefen hajiya karama sanan ta nisa tace "hajiya insha Allah wanan yarinyar alheri ce a rayuwar kabiru Domin naji hakan a jikina,Koda ta kasance Mara asali tsintacciya ba yin kanta bane laifin iyayenta ne sanan ba ita ta halicci kanta ba Allah ne ya halicceta yasa kaddararta tazo a hakan....sanan maganar kisan Kai kusan gaskiya saidai ku take sani tunda kungani a video lalata danku yajeyi da ita Allah ya Aiko Masa da ajali,be Dace ku tsaneta ba Dan Babu Wanda yafi karfin kaddara ta fada Masa wallahi tunda ta kasance Mai ibadah ni Ina kaunarta Ina sonta a matsayin suruka kema Kuma inaso kada kibiyewa tsegumin mutane ki riketa amana bakisan me Allah ya boye a wajenba bakisan tarin baiwar da Allah yayi Mata ba"

"Aike dama dik abinda kabir yakeso to fa kina sonsa,komi kabiru yayi daidaine a wajenki"

Dariya wanan karon hajiya zainab tayi "saboda shi din yarone Mai biyayya da hankali da sanin ya kamata shiyasa,Kuma ninasan Dole yanada hujja da dalilinsa na yin hakan,nidai Ina kaunarta Kuma inayin suruka da ita"

Ajiyar zuciya mama karama ta sauke "ai sai kiyitayi"

Girgiza Kai kawai hajiya zainab tayi tana murmushi...

*******

"Wai bintu sai wani sauri kikeyi kin hadamun tea ko ki tsaya kibani ma insha sanan kitafi"

Dariya yabata Tana kallon yadda yayi maganar tamkar wani yaro karami "inbaka tea sai kace jariri"..

"Toh ni ba jaririnki bane?ai mijinki tamkar jaririnki ne Domin kece keda hakkin kula dashi"...

Mikewa tayi tana dariya"kaga tafiyata"

Da sauri ya Kai Mata cafka zille cikin azama ya damkota da dayan hannunsa ya janyota Yana dariya itama dariyar takeyi "kaga bama saika rikeniba zauna da kyau inbaka,Amma kanaganin zaka iya Shan tea kana kallon wanan jikin nawa Mai dauda?"ta dage Masa gira daya hade da kyafta Masa Ido..

"Babu ruwana da dattinki ko cikin ruwan kwata kike kwana ke nakeso ba dattin ba"

"Shikenan"ta dakko kofin tea din Tana juyawa Tana kallonsa ta dibo a cokali takai bakinsa Babu kunya yarima ya kurbe Yana dariya kasa kasa haka taita bashi har tea din yakai Rabin Kofi ta Mika hannu ya karba Yana fadin "oya Dole a ramawa kura aniyarta kema ki bude baki in baki naki"

Rufe ido tayi yabita da kallo ya dibo tea din yace "oya ha baki"aikuwa Fatima ta bude Tana murmushi yasa Mata a baki yayita Bata harta shanye sanan ya ajiye kofin Yana kallonta Yana dariya,

Turo baki gaba tayi hade da Dan canja fuska "yanzun da ka koyamin ciyar Dani idan katafi wajen matarka waye zai rinka bani abinci?bayan nasaba da yayana ke bani"

Da sauri ya amsa da "nine Nan zan rinka zuwa Ina baki bintu,lokacin cin abinci nayi zanzo"

Ta saki fuska Tana murmushi ta Mike ta dauke cup din ta juyo ta Dan kalleshi "ni natafi bakin aikina kaga bilkisu na can Tana jirana nasan ta cika tayi famm"

Dage mata gira yayi batare da yace komiba ta juya tayi waje yabi bayanta da kallo,komi na Fatima na Burgesa...

******
Kicibis sukayi da bilkisu "malama nagaji da jiranki kintafi soyayya ko ?kunje satarwa sarauniya deejahmah hanya ko?Tana can tana kuri ku Kuna Nan Kuna soyewa"..

Dariya Fatima tayi hade da yin kasa da murya "ai tunda ta bullo da hakan ni zata rinka tozartawa ni Kuma zan mantar da mijinta ita"

Mamakine ya kashe bilkisu ta rike habarta Tana jinjina Kai Tana fadin "Allah ya kawomu Fatima tayi baki haka nakeso ta wajena jeki Kai kofin kidawo"

Fatima ta shige Tana dariya....

*******
Maryam dake dakin hajiya karama Tana rabe a gefe hajiya zainab ta kalleta tace "ke,kinsan wata kuyanga Fatima?"
Da sauri Maryam ta daga Mata Kai "ehh ranki ya dade"

"Tashi ki kiramun ita"...

Ta Mike da sauri,
Hajiya karama tace dake gefe ta ce "hajiya lallai kinason surukar Nan Taki yanzun me zatayi Miki?"..

"Inaso inganta ne sanan insata ta je bangarena ta bude ta gyaramun Kinga yamma tayi...."

Jinjina Kai kawai hajiya karama tayi cike da gamsuwa...

*******
A zabure deejahmah ta Mike daga kishingiden da take cikin tsananin tashin hankali take duban Rahane dake durkushe a gabanta tace"kikace takai awaya a dakin yarima? Kin tabbatar da maganar da kika fadamun ?"

"Bana baki labari saina tabbatar ranki ya dade"

Da sauri ta Mike tsaye tana zura flat shoes dinta,

"Dakata princess ai martabarki da kimarki ta wuce kibita a matsayinta na baiwarki kece Zaki sa ai kiranta kici zarafinta yadda ya Dace"

Huci kawai deejahmah takeyi Nan da Nan fuskarta ta canja kala ta dubi Rahane "kiramun ita"...

Da sauri rahane ta Mike ta bar dakin ta barta Nan tsaye Tana huci hade da girgiza Tana furzar da iska a bakinta cike da bacin Rai...

A parlor suka hade da Rahane Fatima na biye da Maryam Dan zuwa Kiran hajiya zainab Rahane ta tsaidasu "Fatima kizo inji uwargijiyata"

Wani kallo Fatima tayiwa Rahane wanan karon sanan ta kauda Kai tace"zan fara zuwa Kiran hajiya zainab kafin inzo nata"....Tana Gama fadin haka ta wuce....Maryam tabi bayanta...

Jinjina Kai Rahane tayi ta juya zuwa dakin da deejahma suke Tana shiga ta zube a gaban deejahmah "ranki ya dade tace ankirata saita Gama wancen uzurin zatazo naki"

Cikin tsawa deejahmah ta ce"ita a wa?nidin inyi kiranta tacemun bazakazoba?lallai yarinyar Nan ta Kira Mai alewa batada kudin siye".....a fusace deejahmah ta wuce tamkar kububuwa har tana bangaje Rahane dake gurfane a gabanta ta fice a dakin....

Kallo suka bita dashi ko wanne da abinda yake rayawa a zuciyarsa.....

*Muje zuwa*

*SLIMZY😍*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

*_Allah ya maimaita Mana ya Kara Mai maita* *Mana shekaru_ _masu yawa_* *EID MUBARAK*

_Anty rabi sakonki ya iso gareni nagode sosai Allah ya saka da alheri..._

33

Cike da natsuwa ta shiga dakin yayinda zuciyarta ta tsananta bugawa,fargabar abinda zai biyo baya takeyi Dan batasan laifin da tayiba ake Kiran nata...

Gefe kadan ta tsugunna hade da sunkuyar da kanta kasa,..zuciyarta na tsananin bugawa ta bude baki a hankali tace "gani ranki ya dade ance kina nemana"

Hajiya zainab wadda ke gefe ta kafe Fatima da Ido tunda suka shigo take binta da kallo har ta nemi waje ta tsugunna,...kallon yadda kayan jikinta sukai makal makal takeyi saboda datti sanan ta maida dubanta ga fuskarta wadda take a sunkuye ta kafeta da Ido....

Shigowa dakin yasa dukkansu suka daga Kai su kalli waye ya shigo Babu ko sallama bare neman izini,

Deejahmah Bata damu da wadanda ke wajenba Dan batasu takeyi ba Fatima kawai takeso ta ciwa mutunci saboda yadda idonta ya rufe,....tsaye tayi Akan Fatima hade da rike kwankwaso jikinta har rawa yakeyi savida masifar dake cinta,

"NA aika akiramun ke shine kika dawomin da Yar sakon kikace bazakizo ba saboda ninayi Kama da Saar ubanki?shegiya har ta Kai matsayin da Yar sunnah zata kirata tace bazatazo ba?ko kuwa aikin bautar da kikeyi an yantaki ne?"cikin tsawa take magana,

Bude baki hajiya karama da hajiya zainab sukayi suna kallon ikon Allah,

Dakyar Fatima ta hadiye wani mugun miyau na bakin ciki sanan tace cikin sanyin murya "kiyi hakuri lokacinda kika Aiko kirana,Nan anrigada an Aiko kirana ko kafin tazo shiyasa nace Mata tace Miki zanzo idan nazo Nan naji Kiran da akemun"

Fincikota deejahmah tayi ta baya ta Fadi kasa,da sauri hajiya zainab ta Mike tsaye cike da masifa "dakata Mara kunya,kibari idan tazo saikiyi Mata cin mutuncin da zakiyi Mata Amma baa gabanmu ba wallahi tunda rashin kunyarki takai kishigo Mana daki Babu ko sallama,sanan ki rufe idonki kina kokarin ciwa Yar mutane mutunci to baki isaba kinyi kadan Khadija ai mafarkina be taba bani fitsararki ta Kai haka ba,Dan haka ki bacemun daga gani tun kafin nawa borin ya tashi insauke akanki"....

Takaicine ya lullube deejahmah wani kululun bakin ciki yazo ya tokare Mata wuya Wanda yasa idanuwanta suka rufe ruf saboda tsananin bakin cikin abinda hajiya zainab tayi Mata gaban Fatima Amma dikda haka be hanata bude baki tayi magana ba

"Ummu karya takeyi tun dazun na aike kiranta Taki zuwa saboda ni ta rainani shiyasa"

"Da kika aika kiranta batazoba sai kika shigo Mana ko arzikin sallama bamu samuba ballantana gaisuwa dagani kuwa har uwar mijin Taki Anya Khadija wannan halin naki Zaki canjashi kuwa?rahina tayi Miki muguwar tarbiyyar da sai kinyi danasani Mara amfani a rayuwarki Nan gaba kadan,ki bacemun daga gani tunban gaggaura Miki Mari ba Mara kunyar banza"
Chapter 46 · 0% Book details