Sashe 52
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwance take Tana juyi wasu hawaye masu dumi suna bin kumatunta saboda takaicin abinda yarima ya fada Mata,Aiko Dole t Rama Domin bazaici bagas ba,tun kafin ayi aure ya fara fada Mata idan Bata kula dashiba kenan yanada Mai kulawa dashi?yasan yanada ita yazo wajenta kenan?to meyasa beje deejahmar ta dafa Masa abincin yaciba yazo wajenta?....da tsaki tayi ta juya ta kifa kanta a pillow takaici ya hana bacci daukanta...."aikuwa zakasha mamakina Domin bazan yarda da hakan ba tun kafin a daura ko?"...Dole in Rama Dan ya kamata Nima kasan darajata kasan abinda zaka rinka fadamun Wanda bazai rinka batamun Rai ba....sai sambatu takeyi ita kadai bacci ya kauracewa idanuwanta sai maganganu takeyi ita kadai saboda tsabar takaicin yarima....
********
Washe gari da safe bayan ta Gama ayyukanta ta hada musu breakfast itada ummu da sadik tayi Masa wanka ummu tayi wanka tacewa Fatima idan tayi wanka ta sameta cikin gida kasantuwar yau dinner zasuyi don gobe daurin aure ne kawai...
Bayan tafiyar ummu Fatima ta fada bayi tayi wanka Mai Rai da lafiya ta fito tazo wajen kayanta ta Ciro wasu Riga da sket na atamfa jajaye da adon yellow yellow a jiki ta ajiye a gefen gado ta wawwaiga Babu kayan kwalliya dakin ta shiga dakin ummu taci Karo da body spray ta fesa sanan ta dauko powder da lip gloss ta fito ta shiga dakinta ta shirya tsaf tai kyau tamkar wata Yar baby har ta daura dankwalinta ta warware tayi parking din gashinta da dankwalinta ta nade ta shafa hodar tasa man baki ta zizara kwallin man da ta shafa a bakinta ya karawa bakinta kyau ya canja kala zuwa pink Wanda dama haka kalar bakinta yake...gyalenta ja medium size tayi rolling dashi Wanda ya tsaya iya kafadarta ta zura flat shoes jajaye ta fito tayi mugun kyau ....ta kukkule ko Ina sanan ta Miki hanyar cikin gidan...
Tunda ta doso harabar cikin gidan kallo ya koma kanta wasu maaikatan gidan sun ganeta wasu Basu ganetaba haka take keta jamaa Tana tafe Tana kada makullin hannunta fuskarta a Dan daure haka ta shiga babban parlorn cikin gidan inda dik Yan matan gidan ke zaune suna breakfast ciki kuwa harda Yan matan amarya da amaryar ita kanta...kamshin turarenta da sallamarta yasa kowa juyowa ganin wacece,
Deejahmah dake kishingide ta dago kanta suka hada ido da Fatima take ta kauda kanta gefe,ganin haka yasa Fatima karasowa wajensu ta zauna gefen kawar amarya tace cikin zazzakar muryarta "sannunku da hutawa Kun tashi lafiya"
"Lafiya kalau"Sunita da farida suka hade baki suka amsa Mata Banda khausar da teemah dollar wadanda ke jifanta da kallon Tsana,
Ko a jikin Fatima ta gyara zamanta Tana cigaba da wasa da makullin hannunta ta waiga Sukai arba da rahane,take tayi murmushin mugunta tacewa rahane "kawomin abin karyawa"..
Rahane kallon inda deejahmah ke kishingide tayi wadda idanuwanta suke lumshe tamkar me bacci,
Shiru rahane batace komiba Fatima ta Kara magana a karo na biyu "ki kawomin abin karyawa Nima don babu abinda naci na fito sauri nakeyi"
Jiki Babu kwari rahane ta Mike Sumi Sumi ta shiga kitchen,Jim kadan sai gata da plate da cokali da cup a hannunta tazo inda flask din suke tasa mata siyayyen dankalin turawa say kwai da ketchup a gefe ta dire Mata a gabanta sanan ta hada Mata tea Mai kauri Rabin Kofi ta mikawa Fatima,
Babu kunya Fatima ta amsa ta faracin dankalin a hankali Tana kurbar ruwan tae din Wanda tayi hakan ne Dan kawai ta muzanta rahane ...
Ajiyewa tayi a gefenta ta kalli wadanda ke wajen kowa ita yake kallo sanan ta Mike tsaye ta Tana duban rahane da dik abin duniya ya isheta tace "ki kwashe kayan ya isheni haka idan kuma zakici to Bismillah Bari Inga ummu"
"Aikin banza Kare da gudun layya,Wai samin yancin bawa yasa kwana daya kacal yake neman yiwa mutane iskanci bayan ba gidan ubansa bane"khausar tace cike da masifa da takaicin Fatima kamar ta shaketa...
Bude idanuwa deejahmah tayi "bedace ace idan dabba yanayin Abu ki rinka kulasaba little Domin akwai banbanci tsakanin cikakken mutum da dabba,sanan akwai banbanci tsakanin bawa da Mai yanci,sanan akwai banbanci a tsakanin Dan asali da shege Kinga bedace ki tsaya kina maidawa shegiya martaniba"
Har Fatima ta juya batace komiba ta juyo ya dawo ta Dan durkusa daidai kusa da deejahmah da khausar wadanda ke zaune waje daya tace"cikar Zama mutum ne yasa ya aikata dabbancin daya jefashi a cikin danasani Wanda awanni kadan da faruwar hakan yasa wanan cikakkem mutum din ramewa da fada babban tashin hankali,sanan Kuma shi Wanda ake Kira dabban shine akejin shakkar yin kishi dashi Domin a wajen mijinsa cikakken mutum ne kamar kowa,Ina Mai shawartarki da ya kamata ki zauna kiyi nazarin abinda wanan dabban yakeyi ake kaunarsa fiye da cikakken mutum yantacce Dan asali....idan har kin iya dabbancin to tabbas Zaki samu soyuwa a zuciyar mutum daya tamkar da dubu"Tana Gama fadin haka ta Mike tsaye tana faraa Wanda har hakoranta Saida suka bayyana,
Cikin azama khausar ta Mike ta daga hannu zata wanke Fatima da Mari da sauri Fatima ta rike hannun khausar tace "kullll da taba kyakkyawar fuskar sarauniyar masarautar barayar Zaki?wanan fuskar tafi karfin Mari a wajenki Domin fuskar matar yayanki ce"ta yarfe hannun khausar kaasa ta juya tai tafiyarta ko waiwaye Babu....
Rike kugu khausar tayi Tana sauke numfashi cike da takaici "yau kadai yarinyar Nan ta canja salo?tabdijan zataci ubanta kuwa Domin wallahi tallahi saita Raina kanta"...
Tsabar takaici ya hana deejahmah motsin kirki sai jinjina Kai kawai takeyi maganganun Fatima sunayi Mata yawo a tsakiyar Kai....
Bayan yarima yayi wanka ya shirya ya shigo cikin gida Domin gaida iyayensa,babu kunya ya wuce sashen hajiya babba da sallamarsa Tana zaune suna tattaunawa da mutanen dakinta ya shigo da sallamarsa,a ciki suka amsa Masa Koda ya gaishesu dakyar rahina ta amsa ita kuwa hajiya babba ko kallonsa batayiba ya mike har zai fita ya juyo muryar hajiya rahina Tana fadin "ya kamata kasa a kawowa Deejahmah magani Domin batada isasshiyar lafiya"
Da sauri ya juyo ya durkusa Yana fadin "meyasameta?"..
"Inaga gajiya ce kasai tasa Mata zazzabi da ciwon Kai jiya daddare"
"Owk Bari indubata sai inkira waya akawo Mata magani"..harara ta bishi tashi batare da tace komiba ta saki kwafa ya fice....
********
Suna zaune a parlor ya fito Yana tafe Yana takama har ya karaso inda suke zaune har zai wuce ya tunada cewar deejahmah batada lafiya ya dawo ta wajensu ta nemi gefe ya tsaya dukkansu suka shiga gaishesa daya bayan daya tanaji Taki bude ido,
Kallonta yakeyi kawai yadda idanuwanta ke rufe sanan fuskarta kanta ta Dan fada jiya zuwa yau kadai wannan kadai ya shaida Masa da batada lafiya kamar yadda uwartata ta fada Masa,
Ganin Taki bude ido yasashi Dan tsaki kadan yace "deejah ya jikin naki"....Saida yayi magana sanan ta bude jajayen idanuwanta ta sauke akansa Tana yatsina fuska da kyar ta bude baki tace"naji sauki"..
"Allah ya Kara lafiya"....
"Ameeen"tace a takaice....
Har ya juya zai tafi ya juyo ya dubeta kadan yace "zaa kawo Miki magani anjima kadan ki tabbatar da kinsha"...yayi wucewarsa...
Sashen mahaifiyarsa ya nufa a can ne ya tararda gwaggwaninsa da ummu da Fatima dake gefenta Tana ganinsa ta kauda kanta gefe shima bai lura da itaba ya durkusa har kasa ya shiga gaida iyayen nasa wadanda ke amsa Masa cike da kulawa...
Ummu ce tace "kabiru waye zakasa yakaimun diyata Fatima wajen telar ya gwadata dinkin lace na wajen dinnar Dan inaso itama ta shiga anko kamar kowa"
"Sai in kaita ai wajen telan inace wajen inda nake Kai su afee ne ake musu dinki"
"Ehh Nan ne"
"Owk toh ta shirya sai muje "...
Kallon Fatima ummu tayi tace Mata "ya kamata kije gida ki shirya kizo ya kaiki ko"
Jimm kadan Fatima tayi sanan tace cikin sanyi murya "ummu ni banjin Dadi dama anyimun girma daya Dana afnan idan yaso sket din sai a Kara innci hudu Kinga ba sai munsha wahalar zuwaba ki kirashi kinji"
Tunda ta Soma magana yaji wani Abu nayi Masa yawo a sassan jikinsa,cikin dabara ya dago idanuwansa ya sauke akanta.....Aiko idanuwansu suka hade waje dayata wurga Masa harara ta kauda kanta gefe,shi kuwa gogan mutuwar tsugunne yayi Dan tunda yake da Fatima bai taba ganinta da Koda Hoda ba ballantana kwalli da man baki kwalliyar ta amshi fuskarsa,take ya nemi dik wata natsuwa ta jikinsa ya rasa kokari yakeyi ya dago idanuwansa ya Dora Akan nata Amma Koda ya dago batashi takeyi ba juyar da kanta tayi Tana Wasa da sadik dake gefenta....
Dakyar ta yunkura ya Mike yaja kafarsa ya fice a dakin ya nufi sashinsa....
Koda ya shiga dakinsa ya nemi natsuwarsa gabaki daya ya rasa Fatima keyi Masa yawo a kwayar idanuwansa lokaci daya ya nemi natsuwarsa ya rasa babu abinda yake bukata kamar yayi tozali da ita a idanuwansa....
********
"Ummu Bari inje gida inyi sallah in sake wanka in Dora Mana abinci ko?"..
Jinjina Mata Kai ummu tayi tana murmushi,Fatima ta Mike tayiwa jamaar dakin sallama tayi ficewarta
A hanyar fita suka hade da fauziyya da afnan sundawo daga cikin gari,dukkansu Saida sukai shock ganin Fatima a haka take hassadar fauziyya ta bayyana karara a fuskarta ta kasa boyewa tace"iyyeee k'awata an fita a kangin bauta gaskiya nayi Miki murna"
Ruko hannunta Fatima tayi Tana murmushi "nagode k'awata"....itadai afnan wadda ta gaji murmushi kawai taiwa Fatima ta wuce yayinda fauziyya ta cigaba da jifan Fatima da wani irin kallo Wanda yasa Fatima yin mamakin hakan Amma sai batace komiba....
"Ashe haka kike da kyau?gaskiya kin hadu gashi kinsha kwalliyarki,Allah yasadai kinsa turare Dan cikon kwalliya Saida turare"
"Laaa Kinga dazun inata neman turare na mance da Wanda kika bani gara da kika tunamin kuwa Dan anjima idan anyi Shirin dinner shi zan shafa"
Takaicine ya lullube fauziyya najin har lokacin Fatima Bata shafa turaren ba saita danne tace "gaskiya ya kamata"...
"Bari inje gida inyi sallah inyi wanka,ke inayin wankan ma shi zan shafa turaren aminiya"..
"Yauwa gaskiya ki rinkasa turare kafin mamanki ta siya Miki"...fauziyya ta shige gida ta dagawa Fatima hannu...