← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 80

Sashe 45

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Taunar chewing gum takeyi cike da yanga da kasaita yayinda ake Zane Mata kafa da hadadden lalle Mai shegen kyau domin ita kanta me lallen daga wani gari aka daukota musamman don tayiwa Yan biki lalle,..

Gefen kawarta teemah ta kalla ta Dan yatsina fuska "ka'wata nake ganin kamar lallen Nan ya bushe ko?ya kamata a baremun na kafafuwan sanan akawo ruwa a wankemun kafar"

Jinjina Kai teemah tayi tana kallon kafar "ya kamata Kam ai sai ayi Miki,...juyawa teemah tayi gefen da rahane kuyangar deejahmah take tsugunne ta Dan kalleta a wulakance "Rahane ki kawo Mana ruwa"

Yunkurawa Rahane tayi zata Mike da sauri deejahmah ta dakatar da ita "Rahane wanan ba aikinki bane aikin tsintacciya ne,kije dik inda take ki kiramun ita tazo ta kankaremun lalle ta wanke kafar matar uban dakinta"...ta karashe maganar Tana murmushi hade da hada ido da teemah dollar ta daga Mata hannu hade da jinjina 👍🏼"yayi ranki ya dade ya kamata ta fara bautawa uwargijiyata kafin ta fara ainihin bauta Nan gaba"

Kallon juna faizah sukai da fauziyya wadanda suke gefe waje daya idan ka kallesu zasu iya juyar maka da Kai saboda tsabar kamanninsu,

Fatima na cikin kitchen suna hakilon aikin abinci dik tayi zufa tayi bakin Kirin ta gaji Domin aikin da takeyi yafi karfinta,

Direct wajenta Rahane ta nufa ta tabota,da sauri ta juyo "uwar gijiyata nada bukatar ganinki yanzun a sashen baki"....Bata jira cewar Fatima ba ta juya abinta....

Dafe kirjinta tayi tana tambayar kanta a zuciya "wacece Kuma uwar gijiyarta?"...jiki a sanyaye tabi bayan rahane da sauri har tana tuntube gudun karta bace Mata,..

Sashen dataga Rahane tabi ne ya Sanya gabanta ya yanke ya fadi take taji wani Abu na Shirin tasowa a kirjinta tabbas yanzun ta Gane fuskar Rahane Dan ta taba ganinta tare da deejahmah,

Dakewa tayi tabi bayanta har cikin dakin da sallama dauke a bakinta ta nemi gefe ta tsaya batare da tace komiba,

Dukan wadanda ke cikin dakin suka zubowa Fatima na mujiya wasu nayi Mata kallon wulakanci wasu nayi Mata kallon ko in kula,

A fusace deejahmah ta kalli Fatima dake tsaye kikam zuciyarta na tafasa "ke kinfi karfin ki tsugunna a gabana nasa a kiraki?ko kin manta matsayinki na kaskantacciyar baiwa ne?Koko ni saarkice da zankiraki ki tsayamim a Kai batare da kin rage tsawoba?"

Batare da Fatima tace komiba ta rage tsawonta ta tsugunna Amma fuskarta a daure tamkar Bata taba dariya ba,

Da yatsa deejahmah ke nunata Tana fadin "ba yanzun Zaki wannan iskancin ba kibari sai Kinga cikar burinki,..sanan ni ba kaunar kallon wanan mummunar fuskar Taki nakeyi ba infact ko ganinki banason yi yanzun ma dalili ne yasa nakiraki aiki zansaki ,kije kisamo ruwan zafi ki sirkashi kizo ki kankaremun lalle sanan kisa kafata ciki ki wankemun yanzun Nan idan ba hakaba kinsan sauran"

Tsananin bacin Rai ya Hana Fatima cewa komi Banda idanuwanta da suka kada sukai jajir tamkar zata fashe da kuka haka ta Mike tsaye ta fice,....deejahmah tabita da uwar harara tamkar idonta zai fado kasa....

"Niko deejahmah Ina suka samo wanan kyakkyawar yarinyar tamkar ita tayi kanta kuma a matsayin kuyanga?gata yarinya karama wallahi"...

Harara deejahma ta watsawa kawarta da tayi wanan maganar sanan tace"tsintacciya ce shegiya uwar ta da tai cikinta yarda ita tayi a bakin kwata Yan gidan marayu suka tsunceta suka sata cikinsu shine mijina ya daukota a matsayin baiwa Yar aikina"

Daidai Nan Fatima ta shigo hannunta dauke da Dan karamin baho ta ajiye a gefe ta shiga kankarewa deejahmah kafa,....tanayi zuciyarta nayi Mata Kuna takaici da bakin ciki duka suka lullubeta a haka har ta Gama,ta sa hannu Tana Shirin tsoma kafar cikin ruwan zafin,...da sauri deejahmah ta dago Kai ta Kai Mata Mari cikin tsawa tace "kin taba kinji zafinsa ne da kike kokarin samun kafa cikin ruwan zafi?konani kikeson yi?kin kashemun tsoho mijina dik be ishekiba Nima sai kin konani kenan"

Aikuwa idon kowa dake dakin ya dawo Kan Fatima wadda tayi tsumu hade da sunkuyar da kanta kasa,take kwallar bakin ciki suka shiga silalowa a kumatunta,....daurewa tayi tasa hannu cikin ruwan sanan ta dago Kai ta kalleta hawaye na zuba a idanuwanta "Babu zafi na surka kafin inzo"

Murmushin nasara deejahmah tayi Domin burinta be wuce ta nuna mulki da Isa a gaban kawayenta ba burinta be wuce ta wulakanta Fatima taga Tana hawaye ba,...tabe baki tayi sanan ta watsa Mata harara "ki samun"

Haka tasa kafar cikin ruwan Tana wankewa hawaye na gudu a idanuwanta har ta Gama ta Mike ta fice a dakin....

Tausayin Fatima ne ya lullube faizah dake zaune a gefe Tana ganin dik abinda ya faru,wayarta da Jakarta ta mikawa fauziyya ta Mike ta kalleta fuskarta Babu walwala tace"rikemun fauzy Ina zuwa"..

Da sauri deejahmah ta kalli faizah cikin Isa tace"ke Kuma Ina Zaki?ko kin fasa lallen ne?bakiga k'awata ake mawa ba yanzu?shine kikai fushi Zaki futa kika canja fuska?"

Girgiza Kai faizah tayi tana murmushi "ah ah wallahi anty deejah Ina Dan Jin yunwa ne zanje insa a zubomin abinci"..

Murmushi deejahmah tayi tana kallon faizah "kiyi sauri fauziyya Dan idan tagama ku zaayiwa Dole ayiwa Yan biyun innah,...."

Dariya sosai faizah tayi "anty deejah ga fauziyya Nan gefenki"...duka Yan dakin suka sa dariya...yayinda deejahmah ta tabe baki "ni ba ganeku nakeyiba kamanninku yayi yawa kiyi sauri dai"

"Owk"shine abinda faizah tace a takaice ta fice....

*******

Kitchen ta shiga tanata dube dube Bata ganta ba ta fito ta kofar baya na kitchen sai ta ganta tsaye ta hada Kai da bango Tana hawaye hannunta daya dafe da jikin bango,...ta Dade tsaye a bayanta sanan dakyar ta karfin Hali ta ambaci sunanta cikin sanyin murya "Fatima"...

Jimm kadan Fatima tayi sanan ta juyo fuskarta jike da hawaye da sauri tasa hannu ta share hawayen ta tsugunna gaban faizah "ranki ya dade me kike bukata?"

Dukawa faizah tayi ta dagota ta mikar da ita tsaye fuskarta dauke da murmushi ,....kallo itadai Fatima ta bita dashi batare da tace komiba,

Faizar ce ta fadada faraarta "sunana faizah,....na Dade inaso inzo in kebe dake inyi magana dake ta fahimta ni bazan cutar dake ba Domin Harga Allah ni Ina kaunarki tsakanina da Allah ne bansamu nazo ba saboda makaranta da muke zuwa nida Yar uwata,ni Yar waziri ce Nan bayanku kadan gidanmu yake kusan gida dayane Amma kofa CE ta rabamu"

Murmushi Fatima ta kirkiro dikda bacin ran da take ciki a wanan lokacin ta mikawa faizah hannu su gaisa,babu kusu faizah ta mikawa Fatima hannu suka gaisa sanan faizah ta cigaba da magana "kiyi hakuri dik abinda ya sameki mukaddari ne daga Allah kinsan bawa baya wuce kaddararsa a rayuwa sanan kiris ya rage kema ki fara farin ciki kamar kowa,ki daure ki jure anzo karshe Domin kema Nan gaba kadan Zaki fara zuba mulki har mu da muke a matsayin kannen mijinki dole muyi Miki biyayya"....

Murmushi Fatima takeyi Tana kallon faizah....ya fito ta kofar kitchen hannunsa dauke da leda yanata waige waige Dan sauri yakeyi zai fita sai yaji magana kasa kasa ya juya da sauri gefen da yakejin maganar take sukai Ido hudu da Fatima ta sakar Masa murmushi,

Bayan faizah yakebi da kallo don besan ko wacece ba Saida ya karaso wajen ya bita da kallon mamaki,murmushi faizah tayi take yarima ya Gane itace ya maida Mata da murmushi hade da nunata da yatsa cikin wasa yace "idan banyi batan Kai ba faizah ce ko?Domin kece sarkin murmushi"

Dariya faizah takeyi Tana gyada Masa Kai "nice Yaya barka da zuwa"

Cikin kosawa ya Dan kalli Fatima ya kalleta "me kukeyi a Nan ne? injidai lafiya"...faizah zatayi magana Fatima ta rigata cike da shagwaba ta amsa da "nida faizah ne Yaya tazo Tana lallashina itace sabuwar k'awata Tana Sona"

Dadine ya cika yarima Jin Fatima tasamu kawa me kaunarta bayan bilkisu koba komi zata samu sassauci..."gaskiya naji Dadi faizah Dan Allah ki rikemun amanarta ki rinka kulamin da ita kinji?Kinga ita zan aura Kuma marainiya ce batada kowa saini saike yanzun da kike kaunarta kinji'

Gyada Masa Kai faizah tayi tana murmushi "insha allahu zaka sameni da rukon Amana yaayah Domin inason halin Fatima"

Murmushi yayi ta mikawa Fatima ledar hannun sa "ankon wajen kamu ne da zaayi gobe Kuma a gidan Nan zaayi nasan sauran kuyangin ma sarki ya bada kudi a siya musu Kaya su sabinta saboda biki shine na siya muku keda bilki"

Wani irin kallon soyayya take jifansa dashi Tana murmushi Wanda ganinsa ya mantar da ita bakin cikin da take ciki "mungode Allah ya saka da alheri Allah ya Kara girma"

Dadi ne ya kamashi yayi murmushi "ki kawomin ruwan zafi daki zan Dan Sha in warware cikina tun safe banci komiba"

"Angama ranka ya dade"...

Hannu yasa ta Ciro wallet dinsa a aljihu ya Ciro kudi Yan dubu dubu ya kirga dubu goma ya mikawa faizah "ga wanan faizah kema ki siyi abinda baki siyaba na biki"

Ta Dan durkusa "nagode Yaya Allah ya Kara girma"

"Ameen"kawai yace ya wuce ya barsu Nan tsaye da Fatima,
Kamo hannunta Fatima tayi ta hada "Allah ya barmu tare faizah nagode da kauna....Allah yasa ki rikeni Amana"

Ta bayansu bilkisu tace "Fatima me kikeyi a Nan tun dazun hajiya na nemanki nazo kitchen bangankiba shine na biyo ta baya ko zan ganki"

Karasowa bilkisu tayi tanabin faizah da kallo yayinda ta maida dubanta ga Fatima tanayi Mata kallon tuhuma,itadai faizah batasan tsakaninsu ba yasa tayiwa Fatima sallama tace Tana zuwa zata Kara dawowa ta wuce,

Harara bilkisu ke jifan Fatima dashi "Mara zuciya wanan Kuma wacece tazo kika ruko hannunta kdmar wata Yar uwarki"

"Ke da'alla faizah ce Yar waziri tanada kirki sosai yanzun aka Gama wulakantani a gabansu shine ta biyoni Tana bani hakuri take cemin ta Dade tanaso tazo wajena Domin Tana kaunata"

Girgiza Kai bilkisu takeyi hade da rike kugu "kauna fa kikace Fatima?dama wadanan mutanen zasu kaunace ki?a tunaninki ba wani tuggun ake son hada Miki ba"

"Ah ah bilkisu ka kyautata zatonka Akan kowa,kuma yadda tazomin ban kawo komi a rainaba Dan bakiga abinda deejahmah tayimun a gabansu ba"...Nan ta kwashe komi da ya faru tsakaninta da deejahmah ta fadawa bilkisu,

Ajiyar zuciya bilkisu tayi murya a raunane tace"Allah yasa dagaskene "

"Ameeen"...
Chapter 45 · 0% Book details