Sashe 34
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nan gaba kadan kanki zaifi haka girma lokacinda magana ma zatayi Miki wuya saidai ki rinka bawa bayi da kuyangi umarni da hannu suna aikatawa ba saikinceba diyata"
"Mama nikadaice matar Yaya yarima...nikadaice zan Haifa Masa magaji"
"Ko a lahira bana fatan ayi Miki kishiya yadda nake nikadai wajen mahaifinki nake juyashi kamar waina haka kema Zaki juya kabiru sai yadda kikace don shi ma Yana sonki"
"Dagaske mama Yaya Yana Sona?idan kuwa hakane nafi kowa saa a duniya sanan daukar fansan jinin habibu bazaimun wahala ba"
"Ai alamu sun Gama nuna Yana sonki kedai kawai karki nuna Masa komi a fuskarki idan yazo ki saki jiki kuyi soyayya"
Murmushi deejahmah takarayi ta gyadawa mahaifiyarta Kai...ta Dora kafa daya Kan daya Tana faman zuba kamshi....
********
Zazzaune kowa yake a fadar Babu abinda kakeji sai tashin kamshin turare Wanda aka turare fadar dashi kowa Yana zaune wannan karon harda waziri da sarkin fada Suma sun kawowa sarki ziyara....
Matsaloli ake tattaunawa hade da maganar auren yarima Wanda hajiya babba ta Roka a maidashi Nanda wata daya sarki yayi naam da maganarta...
Yarima na gefe sarki ya kallesa kansa na sunkuye,...Dan gyaran murya sarki yayi cike da sarauta da mulki yace "kabiru Babu wata damuwa ta kudi ko ta wani Abu dangane da bangarenka?"
Dan rusunawa yarima yayi "akwai ranka ya dade"
"Menene bukatarka"
"Ina rokon adalin sarki Mai adalci da ya amincemun bayan nayi wanan auren na biyayya in gabatar da matar da nakeso in aura a matsayinta na zabina ta biyu"
Da sauri kowa ya zubawa yarima idanuwa bakajin karar komi sai fanka da AC Dake aiki...kansa a kasa yayi maganar zuciyarsa na harbawa sauri da sauri...
Gyaran murya sarki yayi hade da murmushin kasaita "na baka umarni ka gabatar Mana da wacece wanan yarinyar da kakeso ka aura a matsayin Mata ta biyu?Yar wace masarauta ce?sanan waye mahaifinta a wanan kasar"
Dammmm gaban yarima ya fadi Nan da Nan zuciyarsa ta karye Jin abinda sarki ya ambata,...da kyar ya Tattaro jarumtarsa yace cikin hardewar murya "ba Yar kowa bace face baiwar Allah ce ita ranka ya dade nasan cewa mahaifina adalin sarki ne Wanda yasan adalci da cancanta sanan baya kyamar talakawansa a Koda yaushe burinsa be wuce ya kyautatawa na kasa dashiba,...shiyasa na yanke shawarar isarda bukatata zuwa gareka don nasan kaidin Mai adalcine"
"Fadi wacece ita kanka tsaye zansa a nema maka aurenta matukar Kun Dace "
"FATIMA CE Yar gidan marayu wadda rukonta yake a karkashinka yanzun haka".....
*Muje zuwa*
*SLIMZY😍✍🏼*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
25
Da sauri hajiya babba ta tari numfashinsa "wace fatimar kabiru?Fatima tsintacciyar mage?wadda take a matsayin kuyanga baiwa itace zaka aura?ok yanzun muka ganoka yanzun nagama fahimtar dik inda ka dosa dama dalilin dayasa ka daukota ka kawota kenan?kunyi alkawarin zaka aureta bayan ta kashe Dan uwanka ko"
Dakatar da ita Mai martaba yayi da sauri "dakata mun ba hayaniya na taraku kuyimun ba a Nan sanan ku baku Isa Ina magana kuna magana ba"
"Allah ya huci zuciyar Mai martaba hakan bazai sake faruwaba"...cewar sarkin fada dake gefe
Maida dubansa Mai martaba yayi ga yarima dake durkushe kirjinsa na tsananin harbawa gumi na karyo Masa ta ko Ina,...gyaran murya sarki yayi hade da yin shiru na Yan dakiku sanan ya nisa ya ce "bakada hujja ko dalilin da zaisa ka auri Fatima a matsayin Mata ta biyu kabir Domin ita ba Saar aurenka bace,mutuncinka da darajarka da kimarka sun wuce ka auri tsintacciya Kai ko Fatima ba tsintacciya bace bazaka auretaba saboda ba darajarku daya ba"
Zuciyar yarima ce ta cigaba da bugawa yayinda duk wata gaba ta jikinsa Babu inda Bata rawa,daurewa yayi ya Tattaro dik wata natsuwa tasa da jarumta ya sawa zuciyarsa ya Kara rusunar da kansa kasa yace "Ina naiman agajin sarki Akan ya duba lamarin wanan yarinya,inaso sarki ya tunada cin zarafi da Dan uwana yayi niyyar yi Mata da keta haddi Allah be nufi hakan ba nakeso in huce Mata takaicin kallon kanta da takeyi a matsayin marainiya yasa akaso ayi Mata haka,...inaso sarki ya duba wannan lamarin ya ajiye matsayi ko cancanta ya duba dumbin ladan da zamu samu wajen killace rayuwar maraya sanan inaso Mai martaba ya tunada matsayin kowa a wajen Allah daya ne Babu Wanda yafi wani a wajen Allah sai Wanda yafi tsoronsa,zata iya yuwuwa idan Fatima ta fimu kusanci da Allah wajen bauta Masa da tsoronsa ya zamana tafimu babban mukami tafimu rabo ranan gobe kiyama,..Allah Babu ruwansa da mulki ko matsayin bawansa abinda Allah yakeso shine ka Zama maiyi Masa biyayya da zuciya daya ka Zama Mai bauta Masa danshi ba riyaba dik wadanan abubuwan idan Fatima ta fimusu ta fimu a wajen ubangijinmu ,sanan Allah Yana kaunar Wanda dik yake kyautatawa maraya ya rike maraya da zuciya daya har mutuwa Allah kadai yasan abinda ya tanadar Masa gobe kiyama.....mahaifina inaso adalcin da kakeyiwa talakawanka ya dawwama har zuwa mutuwarka ya kasance bayan gaskiya da Amana da ka rike na mulki ya zamana ka rike amanar maraya kasanyashi farin ciki Wanda Allah sanadiyyar hakan sai ya gafarta maka wani zunubi naka Kuma yayi maka rahma da mu baki daya...Ina rokon adalin sarki da ya duba wannan lamarin"
Ba karamin sanyi jikin Mai martaba yayiba Domin tunda yarima ya Soma magana ya kafesa da idanuwa yake sauraronsa har ya Dasa Aya a zancesa,
"Dik naji maganganunka Kabir kuma na gamsu dasu dik abinda kafada gaskiya ne Amma kasani akwai abinda komi cancantarsa Baya yuwuwa ga mutum domin akwai abubuwa da yawa da sun cancanta Amma abinda zai biyo baya a gaba shi ake kallo,da watace ba Fatima ba da gobe zansa a je a nema maka aurenta"
Gwauron numfashi yarima ya sauke hade da hadiyar wani mugun miyau sanan ya Kara gurfanawa gaban mahaifin nasa ya nisa yace "bazan ja da hukuncin Mai martaba ba Amma inaso sarki yayi dogon nazari da bincike Akan wanan al'amarin"
Jinjina Kai sarki yayi tare da fadin "zan duba lamarin sanan zan duba yuwuwar hakan a Zama na gaba zuwa jibi"
Murmushi yarima yayi "nagode ranka ya dade Allah ya Kara maka lafiya da nisan kwana"
Daga Masa Kai kawai Mai martaba yayi sanan ya juya ga matansa dake gefensa ko wacce yana kallonta Yana nazarinta sanan yace "Babu wadda takeda abin cewa?"
Hajiya babba uffan bataceba sai yunkurawa da tayi ta Mike hade da Dan durkusawa "a tashi lafiya"shine kawai abinda tace ta fice Rai a bace,mama karama kuwa murmushi kawai tayiwa Mai martaba tace "babukomi ranka ya dade umarni kawai zaka bada ayi"
Jinjina Mata Kai yayi shima murmushin yayi irin na manya,....babu wata tattaunawa data biyo baya Domin maganar yarima ita tai sanadiyyar wargaza dik wani maganganu da sukeyi da ta shafi masarautar......haka kowa ya watse jiki babu kwari waziri da sarkin fada da sauran fadawan fada kowa gulmace cike da cikinsa......
********
Dama yarima ya sanar da excort dinsa da fadawa hade da bayi zasuyi Masa rakiya zuwa gidan galadima,Domin bashida wani zabi daya wuce cika umarnin hajiya babba matukar yanason zaman lafiya,Haka sukai kungiya da motoci na rakiyarsa suka fice daga gidan sarki misalin karfe takwas da minti arbain na dare....
Babu inda suka yada zango sai gidan galadima kasantuwar ansan da zuwan nasu akai musu iso zuwa babban parlor na tarbar baki Wanda yasha kayan alatu na more rayuwa hade da kayan ciye ciye Wanda aka ajiye su cike da babbar daddumar dake shimfide a tsakiyar parlorn gidan.....
Ciki bayin gidan sukai Masa iso Yana tafe suna biye dashi wadansu na gabansa sunayi Masa jagora fuskar Nan tayi fess yayi kyau har ya gaji saidai ko faraa bayayi dik gaisuwar da bayin gidan da kuyangi da maaikatan gidan ke zubewa sunayi mishi ko daga Kai ya kallesu beyiba wajen Zama ya nema ya Dan kishingide da jikin kilisar dake parlorn.....
Deejahmah ta kalli mahaifiyarta ta Dan Bata fuska "haka kawai na tsinci kaina da faduwar gaba,ji nakeyi tamkar haduwar farko zamuyi dashi"
Murmushi gwaggo rahi tayi Wanda har hakoran ta suka bayyana ta dafa kafadar Yar Tata "wanan itace haduwar ku ta farko idan baki mantaba,itace zuwa ba musamman dayayi gidan Nan Domin ke Kuma zuwa yayi Dan ya tabbatar Miki da akwai wata kyakkyawar alaka a tsakaninku saboda haka ki dake ki cire faduwar gaba ki fuskanceshi Domin shine abokin rayuwarki Nan gaba kadan"
Gyada Mata Kai deejahmah tayi hade da mikewa ta sakarwa mahaifiyarta murmushi "sai na dawo"
"Da kyau Yar albarka"....
Juyawa tayi Tana tafe bayi na binta a baya tamkar wadda kejin tausayin kasa haka take takawa cike da yanga da daukar hankali,...har cikin babban parlorn,
Masauki tayiwa kanta a gefe Saida ta zauna sanan ta kalli kuyangin dake gefenta tayi musu alama da su fita,...da sauri suka watse daya bayan daya.....
Tunda ta shigo take satar kallonsa,babu karya yarima kyakkyawa ne ajin farko gashi matashi Wanda keji da mulki da sarauta ga baiwar kwarjini Wanda Allah yayi Masa,...tunda ta shigo take satar kallonsa shiko idonsa na gefe daya yayi murtuk da fuskarsa tamkar tunda Allah ya haliccesa bai taba dariya ba....sun kusa minti goma babu Wanda yacewa Dan uwansa ko kala,...gajiya tayi da shirun ta bude baki cike da yanga da kasaita tace "barka da zuwa ranka ya dade"
Shiru yayi Mata batare da yace komi ba,har tsawon minti biyar haushi da takaici suka lullube deejahmah tamkar ta fasa ihu takeji ga danasanin fara kulashi da tayi ya Raina Mata hankali,....ganin Shirun yayi yawa yasa ta Dan hararesa ta gefen Ido "kayi shiru bakace komiba Kuma har maraba nayi maka"
"Da kin Mike kin fita kin koyo sallama kin dawo Dana amsa Miki tarbar da kikaimun"
Wani kululun bakin ciki ya Kara turniketa Wanda ya fusatata ta kallesa cike da takaici"yanada kyau ka maidani makaranta a matsayina na matarka sai in koyo sallamar"
"Akwai wadda nasani wadda ta taso ba a karkashin kulawar iyayentaba ba a karkashin kowaba tsintacciya Amma tasan muhimmancin sallama"..