Sashe 77
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru hajiya babba da hajiya rahina sukayi suna duban Yar tasu wadda gabaki daya ta canja ta rame tamkar ba deejahma me Isa da izza ba tamkar ba Deejahma me mulki da sarauta ba dik ta susuce,
"Deejahmah be kamata ki tada hankalinki Akan kabiru ba bayan kinsan auren yarjejeniya akayi"
Da sauri deejahmah ta juyo ta dubi hajiya babba,
"Ehh Khadija kin manta kin auresa ne saboda ki ramamin abinda akayiwa Dana marigayi?kin manta ba sonsa kikeyiba kin aure shine Dan ki kasheshi ki samamun farin ciki?banida wani buri a duniya Wanda ya wuce Inga gawar kabiru a kwance kamar yadda Naga ta d'ana habibu"
Shiru deejahmah tayi tana nazarin kalaman hajiya babba,shin Anya zata iya kashe kabiru yanzun bayan bakin abubuwa da takeji game dashi?idan akwai Wanda ta tsana takeso ta kashe be wuce ta kashe Fatima ba ta hutawa rayuwarta ta zauna daga ita sai kabiru,.... Yama zaayi ta kashe kabiru yanzun bayan batada burin da ya wuce a duniya ta ganta dauke da ciki.....gashi yanzun wata biyu da aurensu batada ciki,
Hajiya rahina ta kafe Yar Tata da Ido ganin yadda ta fada duniyar tunani gabaki daya,
"Deejahmah kinyi shiru kiyi magana Mana"
Mgnr mahaifiyarta ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data fada,
"Hajiya kin manta da cewa kisan kabiru ba yanzun zaayishiba sai nasamu cikin magajin sarki?idan na kashe kabiru yanzun menene ribata to ta aurensa"
"Inaji a jikina kece zakisamu ciki ki haifama sarki jika ba Fatima ba"....
Rahane dake durkushe a gefe tayi tsulum tace "Allah ya taimakeku da badan karkice nayi muku shisshigi a lamarin ba da na sanar daku wani Abu da nake hasashe kuma nake hange"
Dukkansu suka maida hankalinsu ga Rahane wadda ke magana kasa kasa Tana jinjina Kai,
"Umhmm meye kike hange?me Kuma kika gani Rahane"
"Hajiya bana fada muku labari saina tabbatar dashi"
"Rahane kiyi maganarki kin Tsaya kina Mana kwana kwana ni banson iskanci"
Jiki na rawa Rahane tace"Ina Mai tabbatar muku da Fatima matar kabiru Tana dauke da ciki yanzun haka"
"Karya kikeyi Rahane,waya Gaya miki Fatima Tana dauke da ciki?Fatima bazata taba samun ciki ba nice xansamu ciki"
"Hajiya wallahi Fatima ciki gareta"....
A zabure hajiya babba ta Mike tsaye tana dafa kirji.....
********
"Ka tabbatar da ka kawomin matata har gida Dan ni ya kamata tazo ta gani ba ni zanje ganinta ba tunda ka kwaceta"....liman yace cike da tsokana,
"Insha Allah zaakawota ta ganka Amma karfa ka ganta ka rude kace saina sakar maka ita"
Dukkansu dariya sukeyi a parlon Banda mahaifiyar Fatima wadda murmushi kawai takeyi cike da kunya....
*********
Tunda Fatima ta tashi take kallon agogon bango Tana dubawa har wajen karfe shida na yamma yarima be dawo ba?Yana can Yana soyayya da matarsa....haushi ya sake lullubeta,
Bilkisu ta dubeta "yadai ranki ya dade"
Galla Mata harara Fatima tayi idonta taf da hawaye "kina ganin yarima Yana can wajen matarsa ni ya barni anan suna Shan soyayya saboda ni banida lafiya,lallai namiji wato yaci moriyar ganga"
Toshe bakinta bilkisu tayi tana Yar dariya,yadda Fatima tayi maganar ba karamin dariya ta Bata ba Amma gudun kada tayi fushi yasa bilkisu shanye Yar dariyarta,
Kwantar da kanta tayi a pillow hawaye ya Shiga gangarowa a gefen idonta,
Sallama yarima yayi da Ahmad suka shigo ciki,
Jin hakan yasa Fatima saurin Jan bargo ta lullube kanta......
*Muje zuwa*
*SLIMZY😍*
[9/6, 19:54] 🥰slimzy🥰: 🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
49
Da sauri ya karasa inda Fatima ke kwance a bargo ya ja bargon sai kawai ta runtse idanuwanta zuciyarta na cigaba da bugawa,
Tallabota yayi yakai idonsa fuskarta yaga yadda hawaye ke kwance a fuskarta sai ta bashi tausayi ga yadda jikinta yayi xafi Rau alamar zazxabi,
A raunane ya dubi Ahmad "Anya doctor zazzabin Nan zai barta kuwa?kaji yadda jikinta yake da tsananin zafi?"
"Wai meyasa kake haka ne friend bayan kasan fa dik inda akace ciki Yana karami musamman nata Dole ne sai anyi hakuri da kanana kananan ciwon da zatayi tayi saidai kawai a Bata drugs Wanda zata Dan samu saukin jikinta Amma bawai ya Bari ba sai cikinta yayi kwari"
Beso jin wanan amsar daga bakin Ahmad ba Amma sanin shi din doctor ne yasashi Dole amincewa da hakan dikda yadda yakejin tausayin nata,
Fatima kuwa a zahiri wani haushin yarima takeji tamkar ta shake shi yazo Yana wani kuri yanajin tausayinta bayan Yana can wajen matarsa ya biya bukatarsa ita tunda yayi Mata ciki ai shikenan...
Bude idanuwanta tayi ta saukesu akansa ,"yadai Fatima ya jikin"
Bata amsa masaba sai kokarin kwacewa da takeyi daga rukon da yayi mata,....mikewa Ahmad yayi ya dubi bilkisu Wadda ke zaune a gefe a takure yace "zo muje ki dakkowa Fatima sako a mota,..."
Ba musu ta Mike ta fice,...juyawa yayi ga yarima "to malamin soyayya malamin Mata biyu Allah ya sauwake ni nayi Nan"...ya fice abinsa,
Yana fita Fatima ta kwace jikinta ta jingina daga jikin kujera watsa Mai harara,
"Baby Wai lafiya kike wanan Harare hararen haka?meya faru?ko kina bukatar wani Abu ne?"
"Ko Ina bukata ya zanyi tunda mijina bani kadai ke dashi ba ya tafi saukewa wata bukatarta...Koda yake Kila kaima kana bukatar ne"ta karashe maganar hade da Shan murrrr
Shiko mamaki da tsoron Allah ne suka Kara lullubesa yana binta da kallon takaici,lallai ma wanan yarinyar wato Yana can Yana nema Mata farin ciki ita Tana Nan Tana zarginsa,ya rasa dalilin da yasa Fatima ke irin wanan mugun kishin hakax
Haushi ne ya Kara kamasa ya Mike daga tsugunnon da yayi ya fice abinsa,sai kawai ta sa kuka a zaune wiwi tamkar karamar yarinya....
*********
"Wanan cikin bazata taba haihuwarsa a gidan nan ba inhar Ina numfashi deejahmah kidaina wanan kukan da kikeyi Domin wanan karon na shiryawa lamarin zakisha mamaki"
Kukan deejahmah ne ya tsananta Babu abinda take da buri a duniya sama ta ganta da jikan Dan sarki a hannunta,ya zamana itace ta Soma bawa sarki jikan fari.....batada hope Akan abinda hajiya babba ke Fadi Domin zuwa yanzun ta Gama sarewa da lamarin gabaki daya musamman data fahimci dik abinda suka sa gaba basa nasara akai sai wani Abu ya gifta Wanda zaisa basuyi nasara ba,....hawaye be daina gudu a idanuwanta ba,....Anya wanan tafiyar da hajiya babba ke tunani zata yuwu na su Bata cikin Fatima?shin idan Sukai kokarin hakan akwai nasara kuwa?menene basuyiba Akan shi aurem gabaki daya,
Zuwa yanzun zuciyarta ta karaya batada wani hope Wanda ya rage Wanda ya wuce ta nemi zuciyar mijinta ta yada makaman yaki ta zauna lafiya,dama ita batada burin cutar da kowa a rayuwarta iyayenta sune suke sata a hanya....jikinta yayi sanyi dakyar ta motsa ta goge idanuwanta ta maida dubanta ga mahaifiyarta tace a raunane "Babu ruwana da zancen cikin Fatima,babban burina be wuce Nima in ganni dauke da juna biyu ba,....idan har zanyi wani Abu be wuce inyi abinda zansamu ciki ba"ta karashe maganar da share hawaye,
"Sakarya kafin kisamu cikin naki ya kamata ki lalata cikin shegiya"
Girgiza kanta tayi tana cigaba da sharar hawaye sai kawai ta Mike tsaye "ni zansa a maidani gidana sai na sake dawowa"Tana gama fadin haka ta Mike Rahane tabi bayanta,
Tsananin tausayin yarta ya hanata motsi jinjina Kai kawai takeyi zuciyarta cunkushe da tsananin bakin ciki da takaici dakyar ta dauke wani gawuron numfashi ta dubi hajiya babba wadda ke faman jijjiga kafa,
"Bansan meyasamu deejahmah ba hajiya,Kinga dik yadda yarinya ta Kare ta lalace anason nema Mata mafita Amma Tana ki?to gaskiya idan ita bazatayi ba ni zan tsaya Mata tunda ita batada hankali mahaukaciya ce"
Tabe baki hajiya babba tayi ta dago daga kishingidar da tayi "rahina kenan aini na Dade da fahintar deejahmah son Kabir takeyi Sanan matacciyar zuciya gareta"
"Hmmmm hajiya nidai ki taimakeni ki duba lamarin Nan ayi wani Abu akai"
Jinjina Kai hajiya babba tayi batare da tace komiba ta maida dubanta gefe daya.....
*********
Tun barinsa wajen Fatima gidansa ya nufa Koda yaje babukowa ya manta da deejahmah Tana gidansu dikda tare sukaje takaicin Fatima ya mantar dashi ita,
Yana zaune Yana kallon news din yamma deejahmah tayi sallama a parlorn baiwarta na biye da ita,
A ciki ya amsa saboda tsananin takaici da ya tsunta kanshi ga wani sonta da yake yawo a sassan jijiyoyim jikinsa,
Gefensa ta zauna Tana duban yanayin nasa hade da karantar halin da yake ciki,
"Sweet heart"shine sunan data kirashi dashi yaune farkon da yaji ta ambaceshi da wani suna Wanda mamakin hakan yasashi juyowa da sauri Yana dubanta batare da yace uffanba,
Juyowa tayi gefenta na dama taga Babu kowa a parlorn sanan ta matso daff dashi tasa hannu ta dago habarsa ta hada bakinta da nashi ta Shiga kissing dinsa cikin wani irin salo Wanda tasashi suman zaune,....ta Dade Tana kissing dinsa kafin ya fara mayar mata da martani ya rukota sosai Yana tsotsar bakinta hade da sauke numfashi sama sama,
A hankali ta zare bakinta daga NASA Tana fuskantarsa Tana kallonsa cike da salon soyayya,
"Sweet heart kafadamun menene yake damunka umm?akwai wani Abu ne?"
Girgiza Mata Kai kawai yayi da rinannun idanuwansa,batare da yace komiba....
Rungumesa tayi ta Dora kanta a kirjinsa ta Soma magana cike da natsuwa "hmmm nasan ni ban cancanta insan matsalar mijina ba saboda bani bace a zuciyarsa...naso ace inada matsayin da zansan abinda ke damun mijina kodan in faranta Masa Rai ta wata hanya davan,saidai Kash nidin ba kowa bace a gidansa face matar kallo "....
Hannu yakai Yana shafa gefen fuskarta zuciyarsa nayi Masa sanyi a hankali a hankali....ya zaayi ya sanar da ita matsalarsa Fatima ce bayan yasan ba shiri sukeyi ba?sanan be cancanci ya kwashe sirrin Fatima ya sanar Mata ba....
Dago fuskarta tayi tasa hannunta Tana shafa sajen fuskarsa tanayi Masa yawo a fuskarsa Wanda hakan ya haifar Masa da tsananin kasala....
"Mijina ka fadamun matsalarka in magamce maka ita karka damu,ka kwantar da hankalinka I am ready in sama maka farin ciki inhar xaka sanar Dani damuwarka"
Dakyar ya hadiyi wani mugun miyau ya numfasa yace "Fatima ce"...