Sashe 16
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani malalacin kallo yarima keyi Mata har ta Gama bayani sanan ya yadanyi murmushin karfin Hali yace "wallahi babu hannuna a ciki matukar kika daukaka Kara saidai ki nemi Wanda zai tsaya Miki a kotu Dan badai niba wallahi,munje munsha kunya a kotu Bata ishemuba Kuma sai mun daukaka Kara to wallahi wanan karon bazansa hannuna a cikin abinda zaa wulakanta marainiya ba bayan yunkurin Bata Mata rayuwa da akayi sanan gaskiya tayi halinta Kuma a bita da wani sabon bita da kulli Dan batada kowa?"
Kallon mamaki hajiya babba takeyiwa yarima yadda yadda balai Yana daga murya ya manta da wadda yake magana ne?
"Kabiru kasan me kake fadamun kuwa?kasan da wadda kake magana kuwa?to ka iya harshenka sanan ka sauya kalamanka Dan wallahi kaima zan iya daukar mataki akanka"
Murmushi yarima yayi lokacinda ya dago rinannun idanuwansa Wanda suka sauya lokaci daya "mama ya kamata ki hakura da maganar Nan tunda Mai martaba kansa ya bada umarni akan abar maganar Nan ni Kuma wallahi bazan taba tsallake umarnin mahaifina ba"
Cikin kakkausar murya hajiya babba tace "karya kakeyi wallahi baka isaba me akai akayika da zakaja da umarnina to wallahi shi kansa mahaifin naka da kake tutuya da sarautarsa sai abinda nace yakeyi,saboda haka ka shiryawa shariar Dole"
"Zan shiryawa shariar Dole ammafa marainiyar Allah zan tsayawa wanan Karo"
Da sauri khausar ta kalleshi itama hajiya babba kallonsa takeyi Tana jinjina Kai lokaci daya ta shiga tafa hannu Tana fadin "to kace Kaine ma ka turata ta kashe Dan uwan naka kenan don ka gaji mulki shiyasa yanzun kake ikirarin tsaya Mata a shariah"
Zuwa wanan lokacin ran yarima yayi kololuwan baci idanuwansa,jikinsa na rawa bakinsa na kwrkarwa kamar maijin sanyi yace"meye ribata idan na aikata hakan?meye ribata da akan mulki zanyi sanadiyyar Dan uwana bayan inda yaje zanje?gaskiya hajiya kinbani kunya sanan kinbani mamaki ban taba tunanin Zaki wannan furucin akainaba,sai gashi lokaci kankani kina neman banbantani da habib"
Mama karama ce ta shigo da sauri har Tana hardewa itada afnan kanwar yarima,
Karasowa tayi cikin parlorn ta tsaya cikin kidimewa tafara magana"kabiru ya najin muryarka sama sama akan ta maman naka?meyafaru ne"
Kallon raini hajiya babba keyiwa mama karama sanan tace"yazo ne ya nunamin cewa yagirma ban Isa nasashiba ko na hanashi,sanan yazo ne ya sanar Dani abinda nake bukatar sani a kwanakin baya,yazone ya fadamun cewa yanada hannu akan kisan Dan uwansa yarima"
Dafe kirji mama karama tayi tace"ban fahimci inda maganar Nan ta dosa ba ku warwaremun ita"
Murmushin takaici yarima yayi yace"maganace ta daukaka Kara da mama kesonyi nace babu hannuna a cikinta tunda mahaifina da kowa yace ya cire hannunsa,Kinga ko bazan sabawa mahaifina ba abinda nasani guda daya shine nine zan tsayawa Fatima Zahra a wanan shariar ta supreme Court insha Allahu Kuma muke da nasara"
Da sauri mama karama ta wanka mishi mari Yana dagowa ta Kara Kai Masa wani Marin"kana hauka ne?kabiru kasan abinda kake fada kuwa?ko kayi shaye shayene?to wallahi bada yawunaba inhar zaka tsayawa Fatima wadda tayi sanaddiyar zuwan Dan uwanka lahira shariah"
Dafe gefen kuncinsa yayi zuciyarsa na tsananin tafarfasa yace"owk saboda ita batada gata?saboda ita batada Wanda zai tsaya mata?to kada ku manta Allah ne ya fiddata a wanan shariar Kuma shine zai tsaya Mata a gaba Kuma Nima zan tsaya Mata babu gudu babu ja da baya"
"Ina magana kana magana Kabir?idanuwanka sun rufe ko?to wallahi baka isaba"
Itadai hajiya babba kasa magana tayi zuciyarta cike take taf da mamakin haukacewar da yarima yayi musu Wanda tunda suke dashi be taba yi musu hakanba,
Hawayene yake gangarowa a idanuwansa Yana kallonsu dafe da kuncinsa"wallahi ko kowa zai juyawa Fatima baya a duniya ni bazan juya mataba,saboda marainiya ce ake Shirin cutar da ita,Kuma rikon Fatima zai dawo hannuna a cikin gidan Nan"
"Kana haukane kabiru ai babu mahalukin daya Isa yazo da Fatima ko kofar gidan Nan ballantana maganar shigowa da ita,idan kaga Fatima ta shigo gidan Nan ta rayu saidai tazo a matsayin baiwa Mai bauta,Kuma idan ta kuskura kafarta ta shigo gidan Nan a matsayin baiwar ma saita da'n da'na kudart,saitayi data sanin zuwa duniya,Kuma maganar daukaka Kara idan har kaga ban daukaka karaba to mutuwa nayi mu zuba".......
Kuka yakeyi a fusace ya fice a cikin parlorn yayi hanyar waje.....
Mamakine da al'ajabin hade da tsoron kalaman yarima,sanan ga babban tashin hankali Yana neman jafa kansa cikin masifa.....rigima da hajiya babba bakaramar masifa bace Dan macece Mara imani da tausayi......."innalillahi wa Inna ilaihi rajiun kawai mama karama ke furtawa a ranta"ga gumi da yake karyo Mata ta ko Ina......
*Dis is d beginning of d battle😂... Ya wasan Nan zai kasance a gaba?muje zuwa.....yanzun labari ya fara* 🏃🏻♀
*SLIMZY🥰✍🏼*🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*NA:SLIMZY✍🏼*
_wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
14
Kan yarima yayi zafi da kyar yakejan mota tunanin inda zai nufa kawai yakeyi ya samu sanyi,haryayi kwanar da zata sadashi da unguwarsu barrister abdul,wani tunani ya fado kasa take yaja burki kuuuuuuu,hade da tada kura ya Sha kwana a guje mutanen dake zagaye a unguwar sukabi motar da kallo bayan motar kadai ya nunawa jamaa cewa Dan sarkine.....tambarin gidan sarkine manne a bayan motar da alamar Doki a jiki.....
Wani gida Naga yarima ya Isa Mai zubin ginin gargajiya irin na da shima zubinsa tamkar gidan sarauta ga dogarawa ko Ina a harabar kofar gidan suna Kai komo....
Horn yayi aka bude Masa gate ya shiga a guje tamkar zai tashi sama yaja burki ya fito ko karasa rufe motar beyiba ya nufi hanyar da zata sadashi da ainihin hanyar shiga gidan,dik kofar daya gifta masu tsarone da jajayen Kaya suna zubewa kasa Dan girmamawa,saidai kawai ya daga musu hannu,
Wani babban parlor ya shiga a fusace da wata irin murya yayi sallama "Assalamu alaikum"fuskarsa a daure tamkar be taba dariya ba,
Da sauri dukkansu suka bishi da kallon yanayin nasa dake Nuna yana Cikin tsantsar tashin hankali,
Wata dattijuwar macece gefenta zagaye da kuyangi da Yan Mata wadanda ko baa fada ba yaranta ne,durkusawa kowa yakeyi Yana Mika gaisuwa Amma ko kallo Basu ishesa ba,
Dattijuwar dake kwance a kishingide jikin kalisa Tana Kare Masa kallo tsaf ta fahimci Yana yin NASA sanan tace cike da kasaita"Kai Kuma lafiya ka shigo haka kamar korarre"
"Inafa lafiya goggo rahi,akwai babbar matsala"
Dan yatsuna fuska tayi sanan tace"ban fahimceka ba khabir karamun haske"
Cikin wata iriyar murya ya fara yi Mata bayani daga farkon abinda ya faru a masarauta har karshe da abinda ya hadasa da hajiya babba ya baro gida,....
Kallonsa goggo rahi takeyi shekeke har ya Gama bayani sanan ta Mike daga kishingidar da tayi ta zauna"meye matsalarka Kai?ko kanada dangantaka da ita tsintacciyar magen ce?"
Da sauri ya juyo ya kalleta da tsananin mamakin kalmar data fada bai taba tunanin zaiji wannan furucin a bakin goggo rahi ba wadda ta kasance kanwar babansa Kuma Mata a wajen galadiman barayar Zaki....Nan da Nan zuciyarsa ta cigaba da tafarfasa,shiru yayi Yana kallonta ta cigaba da magana cike da Isa da kasaita Wanda dabiartace hakan dik abinda zatayi cikin izza da Isa takeyi "kabir yanzun kazone kafadamun cewa saboda an gano gaskiya ka koma bayan tsintacciyar mage ko me kake Shirin yi"
Cikin tsananin bacin Rai yace "haba goggo banyi tunanin zanzo wajenki da wanan matsalar ki watsamun kasa a ido ba,kada ki manta cewa fa wanan yarinyar da ake Shirin tozartawa batada hakki akan wanan kisan illa tayisa ne Akan Kare kanta,sanan Kuma bayan gaskiya tayi halinta ace wai an daukaka Kara Kuma zuwa kotun gaba?sanan hajiya na fadamun cewa nine zan Kara tsayawa a wanan shariar?gaskiya bazai yuwuba Dan wallahi bazan tsayaba a wulakanta marainiyar Allah ba,inhar hajiya ta daukaka Kara to tabbas ni zan bugi kirji in karbi shariar in tsayawa yarinyar sanan Kuma in dawo da rikonta masarauta"
Cikin kakkausar murya gwaggo rahi tace"wanan ne baka isaba wallahi kayi kadan ka dauko najasa ka dawo da rikonta cikin zuri'ar tsarkakakku Kai harka Isa me akayi akayika ballantana uwarka?ai dik naji abinda ke faruwa a masarautar Kuma Ina Nan tafe Dan dole ma inzo Akan maganar auren Dan uwanka marigayi Wanda da zaayi da deejamah tunda ya rasu zaka maye gurbinsa"
Wani irin faduwar gaba ne ya ziyarcesa Wanda be taba Jin irinsa ba ya juyo ya kalleta sanan ya Kara maida dubansa ga deejamah dake gefe Tana ya mutsa fuska tamkar taga kashin....zuciyarsa ce ta Kara bugawa a karo na biyu sanan yayi karfin Hali cikin sassanyar murya yace"ai bani na nemi deejamah ba saboda haka Koda habib ya rasu bani zan maye gurbinsaba akwai sauran yara a masarautar ai ni yanzun ba wanan bane a gabana"
Murmushi gwaggo rahi tayi sanan tace"maganar tsintacciyar magece a gabanka koh?to wanan maganar ruwan kwando ce kadauketa a matsayin mafarki,Dan baka Isa ka dauko Yar kwararo ka kawota cikinmu ba wai Nan ita marainiya,ka maidata can cikin kazantarta tajecan ta cigaba wadanda iyayensu sukai cikinsu a hanyar banza Sukai masu mazauni a titi aka tsinta aka rufawa asiri gwamnati ke rikonsu batare da sanin tsatsansuba ita zaka dauko kabiru?to kayi kadan kadaukota watarana a wayi gari ta kashemu"
Girgiza Kai yakeyi Yana Jin zafin munanan kalaman da ake jifar marayun Allah dashi bayan Suma ba su sukai kansuba Allah ne ya haliccesu Kuma babu Wanda keda tabbacin cewa a hanyar banza dukansu aka samesu shine zaa dauki tsanar duniya a Dora musu.....runtse idanuwansa yayi sanan ya budesu,takawa yayi a hankali ya nemi kujera ya zauna saboda yadda dakin ke juya Masa jiri na neman kadashi.....wanan wani irin balai ne ke neman fada Masa lokaci daya?bai Gama kashe wata wutar ba wata ta kunno Masa.....tagumi ya rafka idanuwansa jajir ya kurawa side daya na falon ido Yana kallo,ya fada duniyar tunanin yadda zai bullowa wanan lamarin ga sarki zaiyi Yar tafiya zuwa ran gadi....ga balai na Shirin barkewa....
Mikewa deejamah tayi daga zaunen da take Tana daddana waya tun shigowarsa,taku tayi kadan a yangace ta juyo ta jefa Masa wani kallo Wanda ita kadai tasan na menene sanan tace cikin siririyar murya cike da yanga "Bari insa lantana ta kawo maka alkubus your favorite"