← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 80

Sashe 20

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallo Fatima tabi barrister hauwa dashi Tana murmushi ta maida kanta kasa,shiko yarima Yana gefe Yana aikin kallon Fatima wadda ta canja tayi kyau abinta dikda ramar data bayyana da damuwar dake tare da ita be hanasa ganin tsantsar kyau da Allah yayiwa yarinyar ba.....

Kula da plates guda biyu Ablah ta gabatar musu sanan tasa Aysha ta kawo juice da ruwa Mai sanyi dukkansu suka bar musu parlorn....

Da kansa ya zuba abincin sosai fried rice ce taji kayan lambu da hanta da aka yanka kanana sai kamshi takeyi....cokali biyu yasa a plate din sanan ya kalleta fuska a daure yace"Bismillah"

Rau Rau idanuwanta sukayi tamkar zatayi kuka tace" nifa na koshi"...ta turo baki gaba...

Tsare gida yayi yace"Allah xan mareki idan baki matso munci abincin Nan ba to zanyi Miki dura"

Da sauri ta dago Kai ta kallesa,Aiko ya kashe Mata ido daya ta dukar dakai kasa tace"Toni kadai nakeso inci"

"Malama practice nakeso ki fara"

"Na me?"tace da sauri...

Sai ya basar yace"idan na kaiki gidan Miji Mana"....tura baki kawai tayi babu yadda ta iya haka ta matso sukaci abincin tare suka Gama....

Ablah ce ta fito daga daki tace cikin tsokana"iyyee Fatima dik kece kika cinye wanan abincin?Koda yake ai ranka ya dade ya iya lallashi"

Dariya sukasa dukkansu Banda Fatima da murmushi kawai takeyi kanta a kasa,can cikin zuciyarta tunani kawai takeyi Akan makomarta....

Nan yarima ya zauna sunata Hira da barrister hauwa har yamma sanan yayi haramar tafiya ya kalli Fatima yace "bintu"gabantane ya yanke ya fadi ta dago Kai da sauri Tana jiran yace ta zo ya mikata gurin hukuma sai taji yace "kishirya da wuri zanzo gobe mutafi wajen daukaka karar Nan a wankemun ke dakyau a tabbatarwa da duniya kedin baiwar Allah ce....

Wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke Nan da Nan idanuwanta Suka kawo ruwa tace"toh" kanta a kasa....

Sallama yayi musu Ana Kiran magriba ya fita badan yaso ba don yau jinsa yake tamkar sabon ango haka kawai yake tsuntar kansa cikin farin ciki Yana driving Yana murmushi shikadai.....har ya iso gida,Yana ajiye motarsa ya wuce masallaci don yin sallah...

*********
Bayan ishai can gidan galadima gwaggo rahi ce zaune cikin yaranta suna Hira sama sama,

Deejahma ce tace"wai mama naji kinyi shiru da maganar da mukayi ranan nifa na kagara a fara kirana da matar Dan sarki Kuma sarki Mai jiran gado"

Murmushi mahaifiyarta tayi tace"to rasa kunya beran tanka,wato kin kosa kitafi kibarni ko?har kike iya fadamun?to ai nakira hajiya babba na fada Mata shawarata Akan hadaki da khabir tace zatayi tunani gobe nakeso inje gidan da yamma in Kara tattaunawa da ita kafin sarki ya dawo,sanan inaso in jiyo ya takasance Akan maganar daukaka Kara inji yadda sukayi,inaso inji Mara kunyan ya tsayawa shegiyar ne Koko Dan uwansa Dan bansan me Kabir ke nufiba"

"Mama dik duniya Babu Wanda nakejin haushinsa kamar shegiyar yarinyar Nan da tayi sanadiyyar rabani da habib dina,waini ya Kabir ma mamaki yabani har wani tausayinta yake mtsewwe"

"Kyale banza shiyasa ai da yazomin da maganar na gwasaleshi zanyi maganinsa"

Deejahma ta tabe baki tace"can ta matse Mai"

********
Washegari da sassafe ya shirya ya fita babu Wanda yasan fitarsa a gidan direct gidan barrister Abdul yaje Yana zuwa Fatima ta fito already a shirye take dama shi take jira,Tana ganinsa cikin bakaken Kaya saida gabanta ya fadi haka ta daure ta gaisheshi ta shiga gaban mota ta zauna,sama sama suka gaisa dasu barrister sukai mishi fatan alheri da nasara sanan sumabar gidan.

karfe 10 na safe Kabir ya isa supreme Court a mota yabar Fatima a parking space ya fice ya tafi ciki,

Yana cikin manya manyan judges da zasu tsaya game da karar Fatima Zahra,sanan shi kansa Yana matsayin Wanda zai kareta a wajen

lawyoyin da haj babba ta dauka basuyi mamakiba ganin yarima Kabir cikin manya manya judges waanda zasu duba previous case da akayi a court of appeal ba...maana hukuncin da aka yanke a court of apeal.....

Bayan duk sun zazzauna a cikin court din , (bcoz a kaida na supreme Court mutane basa zuwa kuma baa kawo Mai laifi)....

Cikin kwarewa ta aiki yarima Kabir yagabatar da hukuncin da aka yanke a court of appeal da shedun da aka gabatar a can da komi,ya gabatarwa sauran judges, Tun daga Nan lawulyoyin Haj babba sukasan bazaasuyi succeeding ba,ko wannensu zare ido kawai yakeyi Yana kallon sauran judges dinn,

Bayan dogon nazari da babban alkali yayi sanan yayi gyaran murya yace "yace abisa laakari da akayi da manya manyan shedu da aka gabatar, Kuma sannan a criminal case na kisa inde kan self defense ne accused person will be on d basis of liability,"saida gabansu duka ya fadi dikda dunsan dama hakan zata kasance,...alkali ya cigaba da cewa "abisa haka wannan decision na court of appeal yayi Kuma is valid, ......Kuma an wanke Fatima Zahra on d basis of self defense"....

Abinda alkali yace kenan ya dauko file din takaddun da aka gabatar yasa hannu sanan ya mikawa kowa ciki yasa hannu na angama shariah ya Mike ya fice ya barsu zaune,

Bakajin karar komi sai fanka,yarima ya mikawa sauran Barristers din hannu suka gaisa sanan ya fice Yana murmushin nasara,

Ko cikakken minti arbain beyiba ta hangosa ya fito hannunsa dauke da takaddu Yana tafiyar Nan tasa ta takama da sarauta,bugun zuciyarta ne ya tsananta tunda ta hangosa tashin hankali ya bayyana karara a fuskarsa har ya bude motar ya shigo....

Idanu ya kafa Mata ganin yadda ta furgice sanan ya saki kayataccen murmushi yace "you are free".....ajiyar zuciya takeyi akai akai take hawayen farin ciki ya fara zarya a idanuwanta,hannunsa ya Sanya ya dago kanta Yana share Mata hawaye da hannunsa sanan yasa hannu yana shafa kanta cike da lallashi....juyawa tayi gefe Tana dariya ,shima gyara zamansa yayi yaja motar a guje......

****
Hajiya babba ce zaune Tana jiran feed back Dan already barrister Nasir ya sanar Mata da suna kotu,

Ta kosa taji me yafaru Aiko wayarta dake gefenta ce tayi ringing da sauri ta dauka khausar ta kafa Mata ido....

Mikewa tayi tsaye daga zaunen datayi tace cikin kakkausar murya"barrister kana nufin bamuyi nasara ba?hukuncin da aka yanke kenan tabdijan nasan haka zata faru nagode"kawai tace ta kashe wayarta ta shiga kaiwa da komowa Tana fadin "fada da aljani babu Dadi,lallai khabir kayi kuskuren yin fada Dani Domin ka dauko balain da yafi karfinka saina tabbatarda na wulakanta rayuwarku dukanku"

"Yanzun mama dik kudin da kika kashe a banza kenan"

"Ba kudi bane a gabana khausar daukar fansa yanzun itace a gabana".....

*********
An shirya motoci daga gidan galadima zuwa masarauta inda gwaggo rahi ta fito cikin kayan alfarma irin na manyan masu kudi Kuma masuji da sarauta,har wajen mota yaranta suka rakota deejahmah tace"to mama saikin dawo a tattauna lafiya"

"Ameeen"tace yayinda driver yaja mota su deejahma Suka koma cikin gida.....

*********
Tafe suke daga court ko wannensu baya magana Fatima nata kalle kalle a gefen titi,juyowa tayi tace cikin sassanyar murya "yanzun Yaya yarima Ina zaka kaini gidan Ablah?"

"Masarauta xamuje rikonki ya dawo hannuna yanzu"

Dafe kirji tayi hado da zaro ido waje,Jin maganarsa tayi tamkar saukar aradu yayinda taji kamar an Sara Mata gatari a tsakiyar kanta......

Ko kallonta beyiba ya cigaba da driving dinsa....yashanyo kwanar gidansu ta Kara kwalalo ido waje......

Kofar gidan aka bude musu aikuwa Fatima ta fashe da kuka suna shiga wata mota ta wuce a guje cikin gidan da Yan rakiyata da tambarin sarauta a jiki an rubuta *GALADIMAR BARAYAR ZAKI* .....

*muje zuwa yanzun* *zaafara wasa*....... *wayyoo* *hajiya babba🤭*

*SLIMZY😍✍🏼*🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

*NA:SLIMZY✍🏼*

_wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

*HAPPY BIRTHDAY IN ADVANCE MOMMAH....*( *_Billy_* _*galadanci* )_ ~Shaku shaku don~ ~start from today~ 💃🏻😍😍

17

Kuka Mai sauti wanan karon Fatima ta fashe dashi a cikin motar ta riko hannunsa Tana kallonsa cikin ido,kauda kansa gefe yayi ya zura kafarsa daya waje yace "ummhmm Ina sauraronki akoke gwamnan kuka me kike nufi kika rikeni kina rusamun kuka kamar nayi Miki wani Abu"

Kuka ta cigaba dayi batare da tace Masa uffan ba haushi ya Kara kulesa a zuciye yace"Kinga idan bakida abinda zakice ki sakarmun hannuna in shiga gida idan Kinga Zaki biyoni ki biyoni idan Kuma cikin mota Zaki kwana to Bismillah"

Baki na rawa idanuwanta a rufe hawaye kawai ke gudu tace"Yaya yarima kayimun Rai ka rufamun asiri wallahi zamana a gidanku zai zamemun tamkar kabari,bazan tabajin dadin zaman gidan Nan ba bayan kowa ya Gama tsanata,ka rufamun asiri ka maidani gidansu Ablah ko ka maidani ainihin gidan mu"

Wani haushine ya turnikesa ya kalleta fuska a daure yace"wato ni kike kallon tsabar idona kina cewa wai zaman gidanmu zai zame Miki tamkar kabari?wato baki shirya fuskantar dik wani kalubale akainaba ko?nine na shirya hakan ko?hmmmm to Fatima kisawa ranki bakida wajen Zama sai Nan gidan Dan wadanda kikeson Zama dasu babu abinda na hada Dasu sai soyayya da mutunci da sukemun Kuma koba hakaba wallahi bazan iya barinki kiyi Nisa Dani ba,idan Kuma kinga ke Zaki iya rayuwa babuni saki fadamun"....Yana fadin haka ya Juyo ya kafeta da idanuwansa da suka canja kala lokaci daya....

Girgiza Kai kawai takeyi Tana kuka zuciyarta na wani irin harbawa sauri da sauri lallai yarima so yakeyi a kasheta a cinye namanta Danye,ta kashe musu da' Kuma ya dakkota yace tazo cikinsu tayi rayuwa?sanan a matsayinta na tsintacciyar mage?yadai kawota kawai tayi bauta.....batada yadda zatayi ta bijire Masa don ita kanta bazata iya rayuwa a wani wajeba Babu shi....

Kukan kawai takeyi Babu kakkautawa hannu yasa ya cire makullim mota yace "share hawayenki ki biyoni"....fitowarsa yayi ya rufe bangarensa,

Hakanan ta sako kafarta ta fito waje tasa hannu ta share hawayenta,shiko kulle motar yayi ya Kara hada ransa tamkar wani Zaki tamkar tunda yake be taba dariya ba yayi gaba,dakyar take cira kafa Tana binsa a baya.

Babban gidane gidan sarauta dik inda suka wuce kallonsu akeyi daga maaikata har bayi da kuyangi kowa kallonsu yakeyi yadda take binsa tamkar tsomammiyar kaza ga uban hijabi har kasa.....

Kuskus kawai ke tashi wajen bayi dik inda suka gifta har lekensu ake yayinda zuciyarta ta cigaba dayi Mata lugude ji takeyi tamkar ta hadiyi zuciya.....
Chapter 20 · 0% Book details