Sashe 6
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****"Bilkisu ya kamata ki daina tada hankalinki Akan batan Fatima domin Fatima ta tafi da wuya muganta,Dan hajiya tace tunda aka fita Dasu xana jarabawar jamb da aka Gama baasan inda tayiba sunyi nema harsun gaji"
Fuskarta jike da hawaye tasa tsumman zaninta ta share hawayenta ta maida dubanta gareta tace "Maryam kenan a cewarsu hajiya ba,Amma su sunsan inda take,komenene yasamu Fatima sune sanadi Allah ya saka Mata sanan Allah ya kawo karshen wanna masifar dake faruwa Allah ya kawo sadin da zaayi *WALK'YA* halin kowa ya bayyana asirin kowa ya tonu Allah yayi Mana sakayya ,saboda muma baason ranmu kaddararmu ta Fado a Zama marayuba"kuka sosai bilkisu takeyi Tana Jin radadin rashin aminiyarta Yar uwarta Fatima....
Batare da Maryam ta fahimci komiba a kalaman bilkisu ta cigaba da lallashinta da ban hakuri Akan ta cire Fatima a zuciyarta tayi Mata addua....
********
Zaune yake bayan sallah ishai a babban parlorn gidan barrister Abdul,bakajin karar komi Sai karar fanka Sai Kuma bayani da yarima yake korowa barrister da matarsa har ya Gama,
Tabbas sun jinjinawa al'amarin Kuma jikinsu dik yayi sanyi da Jin labarin da abin ya faru Akan Yar gidan marayu ne,barrister hauwah CE ta Lula duniyar tunani,tabbas wanan al'amari akwai rikitarwa,tanajin karfin gwiwa akan wanan shariar Koda yarinyar ta aikata,sanan wannan shariar tamkar jihadi CE fatanta Allah ya Basu saa....
Barrister Abdul ne yayi ajiyar zuciya yace "ka kwantar da hankalinka barrister Ni da madam insha allahu zamuyi iya bakin kokarinmu wajen shariar Nan zamu tsaya bakin Rai bakin fama wajen yin wanan jihadin,babu wata alfarma da xaka nema a wajenmu wadda bakasameta ba barrister"....
Gyara Zama barrister hauwa tayi matar Abdul tace"barrister kayi addua kawai Amma insha allahu Koda Fatima ita tayi kisan Nan zamu samu hanyar da zata kubita da yardar Allah,insha allahu gobe nida oga zamuje kotu mukai takaddunmu mu shigar da sunayenmu a matsayin wadanda zasu tsayawa Fatima a sharia"
Jinjina Kai yarima yayi cike da Jin Dadi yace "Allah ya saka muku da alheri Allah ya bamu saa"
"Ameen"suka hada Baki dukansu sanan barrister Abdul ya kalli matarsa yace "gobe idan mun bar kotu zamuje station din kece Zaki zanta da Fatima cikin hikima da wayau inaso kiyi amfani da kwakwalwarki da fasahar da Allah ya baki wajen yin tambayoyi da ita"
Jinjina Kai hauwah tayi tace"insha allahu bazaa samu matsala ba"
"Allah ameen"suka hada Baki ,Nan suka cigaba da tattaunawa.....
******
Washe gari barrister Abdul da madam dinsa sukaje kotunda aka Kai takadda,yarima yayi musu Tex massage ya sanar dasu Shima Yana wajen,aikuwa Basu Bata lokaciba sukaje suka gabatarwa kotu abinda ya kawosu,Nan aka shiga kallon kallo kowa a wajen kallonsu yakeyi a matsayinsu na masu tsayawa wadda ake tuhuma da laifi,Nan aka rattaba sunansu tare da sanar musu da gobe zaa gudanar da shariah karfe goma,
Yarima tamkar besansuba haka yayi acting sanan ya mikawa barrister hannu suka gaisa suka wuce suka bar kotun Shima yarima Yana barin wajen gida yayi....
*****
A babban parlorn sarki ya tarar da iyayen nasa duka ya tsugunna har kasa ya kwashi gaisuwa sanan ya gabatarwa da Mai martaba da iyayen nasa yadda akayi,
Mama babba Allah Allah takeyi tayi magana jikinta har rawa yake wajen tambaya"kabir Yaya ansamu masu tsayawa almurar yarinyar can kuwa"
Batare da want shakka ba yarima yace "ehh ansamu mama,Mata da miji ne ma su biyu xasu tsaya Mata"
Jikinta na tsuma tace "what?kana nufin yanzun da lawyoyi biyu zaka fafata a kotu?"
Jinjina Kai yarima yayi ,Sai a sanan Mai martaba yace "ai yaron naki gwarzone a wanan fannin ki kwantar da hankalinki,bazaa samu matsala ba"
Jinjina Kai yarima yayi yace "insha allahu ranka ya Dade"
Itadai mama babba batace komiba Sai rudani data shiga da tsananin tunanin yadda zaayi a tsayawa Mai laifi bayan an tabbatar matada iyayen yarinyar basu bayyana ba....
*****
Koda aka fito da Fatima don ta gana da barrister hauwa ,data fito tayi mamakin ganin kyakkyawar mace Fara tas da bazata wuce Shekaru ashirin da shida ba a duniya ,Fatima Tasha jinin jikinta data fito cike da fargaba take saidai ganin matar nayi Mata Dan murmushi yasa tadan samu relief dikda bawai ta kwantar da hankalinta bane tsayawa tayi kikam a kanta Tana Kare Mata kallo,
Murmushi barrister hauwa tayi ta nuna Mata gefenta tace "zauna Mana Fatima"samun kanta tayi da kasa yi Mata musu ta zauna a darare....
Sunana barrister hauwau muazu Amir nice lawyer da Zan tsaya Miki a shariah nida mijina barrister Abdul Amma shi Yana waje shi ya turoni wajenki don in zanta dake Akan abinda akeyi Miki kazafi dashi ake zarginki wato kisan Kai!!!"
Shin menene gaskiyar lamarin?already hauwa ta seta recorder dinta Wanda zata gabatarwa da barrister yarima ya saurara,
Girgiza Kai Fatima tayi cikin sanyin murya tace"nice na kasheshi ba kazafi bane ba Kuma zargi bane"
Gyara Zama barrister tayi tace "haba kanwata Fatima?banaso ki rinka kirkirowa kanki laifi kina dorawa kanki koda kece kikayi kisan Nan be kamata ki rinka amsawa haka ba cike da kwarin gwiwa shin kinaso a kasheki ne?hukuncinki fa kisa ne"
Juyar da Kai Fatima tayi Nan da Nan hawaye ya shiga zarya a idanuwanta tace "dama kun fitar da hannunku daga wanan shariar,Kun mikani ga hukuma a kasheni a matsayina na Mai laifi sanan Koda an kasheni banida wani Amfani a wanan duniyar dama ,niba kowa bace face marainiyar da aka tsinceni a bakin kwata wadda batada wani gata a wanan duniyar"
Kalamanta sun taba zuciyar barrister Nan da Nan jikinta yayi sanyi tace"Fatima ki daure ki fadamin yadda akayi kikayi kisan Nan da dalilin da yasa kikayi kisan Nan ninayi Miki alkawarin kubuta,sanan nida mijina mu zamu zame Miki gata a wanan duniyar"
Girgiza Kai Fatima tayi tace"nagode da karamci da kauna nasan dik kaunar da kukemum Bata Kai ta mutum daya da yakemun ba a wanan duniyar Shima hakuri zaiyi ya Bari a kasheni"ta fashe da kuka Mai ban tausayi,
"Kiyi shiru Fatima kidaure ki sanar Dani dalilin dayasa kikayi kisan Kai,idan wanine yasaki kiyi kisan ki sanarmun"
"Babu Wanda ya sani nice kawai nayi kisan Dan kaina,banida sauran amsan da zanbaki"...
Dik yadda barrister hauwa tayi Akan Fatima ta sanar matada yadda abin yafaru Taki,tayi iya kokarinta Amma abun yaci tura,Sai kuka kawai da Fatima ke rerawa,hakanan lokacin da aka Basu yayi,barrister tanaji Tana gani haka aka tasa keyar Fatima aka wuce da ita....
Jiki a sanyaye ta fito tasamu mijinta a mota yaja motar,a hanya take sanarda shi yadda sukayi da Fatima,
Waya yasa yakira yarima ya sanar dashi yadda barrister sukayi da Fatima hankalinsa a tashe yace gashinan zuwa......
*Ku biyoni don Jin yadda zata kasance...ya wanan baudaddiyar shariar zata yuwu?*....
*SLIMZY✍🏻🥰 🌩 *ANYI* *WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS* *ASSOCIATION* 💡
*NA:SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga* *k'awata faty D'an* *maliki*
06
Yarima Wanda ke zaune a dakinsa bayan ya dawo kotu Yana tunanin yadda shariah zata kasance,ya Mike a fusace Jin bayanin da barrister Abdul yayi mishi na Fatima Taki Basu wani bayani Yana fitowa gidansu yayi cikin tsananin tashin hankali ya Isa gidan,
A parlor ya tarar dasu da alama Basu Dade da shigowa gidan ba,suna zazzaune barrister hauwa Tana Yan rubuce rubuce a takaddarta,bayan sun gaisane barrister ta gabatar mishi da recording din muryar Fatima na tattaunawa da sukayi ,Dafe kansa kawai yayi bayan ya Gama dauraren komi Nan da Nan hankalinsa yayi kololuwar tashi ga wani haushin Fatima da ya ziyarci zuciyarsa a Karo na farko,
Da'go rinanun idanuwansa yayi ya saukesu Akan barrister Abdul dakyar yake motsa labbansa yace "barrister me yarinyar Nan take nufi?ta zabi a kasheta Ni in shiga uku Koh?me take nufi?"
Dan murmushi barrister Abdul yayi yace "kadaiji abinda take fada sanan barrister ta tabbatar mun da yadda take maganar cike da confidence Akan itace tayi kisan shi zai baka mamaki"
A fusace yarima yace "to idan ma itace tayi kisan meyasa bazata fada Mana dalilinta nayin kisanba ko kuwa Ana kisa Babu daliline?idan wani ne yasata tayi kisan ta fada Mana ta tsaya Tana wahalar damu,fatyma na neman in rasa farin cikina a Karo na biyu,Fatima na nema tasa zuciyata ta buga in mutu inbarta cikin kunci da masifar da take ciki,Fatima Taki tausayawa kanta ta tausayamun Nima"zuwa yanzun yarima yakai karshe cikin tsananin damuwa da tashin hankali....hannu yasa ya Dafe kansa zuciyarsa na harbawa tamkar zata faso kirjinsa ta fito,da yanada dama da ya cireta cikin zuciyarsa,Amma ta Yaya hakan zai kasance bayan Fatima itace jinin dake yawo a jikinsa har zuwa cikin zuciyar tasa?runtse idanuwansa yayi Yana tuna abubuwan da dama dayasa bazai iya barintaba...
Tunda ya Dafe kansa,barrister Abdul da madam dinsa suke kallonsa cike da tausayawa barrister hauwa CE ta Nisa tace
"Ka kwantar da hankalinka yarima insha allahu Fatima zata kubuta da yardar allah"
Da'go kansa yayi cikin kosawa yace "ta Yaya"
"Addua zamu dukufa yi sanan mu hadu a kotun gobe"
"Shikenan baristers nagode allah ya kaimu goben,Ni zanje gida"
"Ka tsaya muci abinci Mana,don daga ganinka bakada lokacin abinci ma"cewar barrister Abdul,
Girgiza Kai kawai yarima yayi tare da sauke ajiyar zuciya yace "naci dazun a gida Bari inje kawai"
"To shikenan Sai Allah ya kaimu goben"
Gyada musu Kai kawai yayi ya juya ya fice jiki a sanyaye dukkansu kallo suka bishi dashi Mai cike da tausayawa...
******
Washe gari da sassafe yarima yayi shirinsa tsaf cikin kananan Kaya Riga jeans da polo shirt masu kyau Wanda sukai matukar amsar jikinsa,Amma hakan be hana Rama fitowa a jikinsa ba fuskarsa tayi fayau kamar yayi zawo da amai,
A can fadar sarki ya tarar da a halin gidan dukansu,bayan ya gaida iyayen nasane sukayi Masa adduar samun nasara sanan kannensa biyu suka fada Masa bukatarsu nason zuwa kallon shariar,jinjina musu Kai yayi a shirye suke Nan da Nan aka bada Motoci da matakan tsaro wadanda zasuyi musu rakiya zuwa kotun....
*******
*COURT*
Mutanene cike da kotun har waje wadanda keso suga yadda wanan shariar zata kasance,
Kallo daya zakayima kotun, ka tabbatar ba karamar Sharia za'ayiba ,duba da yadda take cike makil da da'n adam.....
*Courtttttttt*
Kowa ya mike a lokacin da Alkali abubukar assadiq yashigo kotu ....
Bayan ya zauna sannan kowa ya Sami matsugunni ya zauna ...