Sashe 55
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dan leko da kanta tayi Tana kallon Fatima wadda ke faman shasshekar kuka kafin daga bisani ta budewa ummu kofar mota suka shige taja motar zuwa gida.....
*********
Akan idon yarima Ahmad ya shigo cikin hall din shi kadai ba tare da Fatima ba wani irin kugi cikin yarima yayi lokaci daya fargaba da tsoro ya darsu cikin zuciyarsa....
Wasu irin yayan zufa ne Suka shiga karyo Masa ta ko Ina dikda sanyin ac dake cikin hall din saboda tsabar haduwarsa ta cikin dummm light din inda suke zaune kallo daya zakayiwa yarima kasan Yana cikin rudani,minti minti yake share zufar dake tsattsafowa a fuskarsa,
Dan kallonsa deejahmah tayi hade da Dan darkewa a jikinsa Tana kallonsa cike da kissa tace"lafiya dai ranka ya dade?meke faruwa?Naga yanayinka tamkar kana cikin damuwa menene fadamin"...yadda tayi maganar kadai yasa jikinsa mutuwa take ya Kara nutsa cikin tsantsar shaawarta har baisan lokacinda yasa hannu yadan shafi gefen fuskarta ba take waje yadau sowa hasken camera kawai ke giftawa a wajen,
Bakin hajiya rahina yaki rufuwa saboda Dadi Dan waigawa tayi gefen hajiya babba ta rada mata a kunne"turaren baba Sudan yayi aiki dan banza Kinga yadda yake lumshe Ido?"
Girgiza Kai kawai hajiya babba tayi ta sauke murmushi cike da kasa tace"fada da aljani Babu Dadi rahina munyi da manyanshi balleshi karamin alhaki?hmmm hmm kadan kenan sai ya kusanceta yaji yadda take sanan idan har Tasha ruwan dadin Nan na baba Sudan angama sanan sauran hade haden a can zaiyi a binsa to daganan labari zai canja Domin shida wata mace harabada Kuma balle tsintacciyar mage shigiya Yar gaba da Fatima"
Wani irin dariya hajiya rahina takeyi Tana jinjina Kai cike da nishadi "Kinga idan ta mallakeshi shikenan sai muga ta tsiya,sanan burina be wuce ta haifawa sarki magaji ba kafin ta sheka Dan banza lahira"
Jinjina Kai hajiya babba tayi ta Kara kasa da kanta kadan "yadda Dana ya bakunci lahira wallahi sai kabiru ya bakunci lahira,....kisa Mai sauki deejahmah zatayi mishi Wanda harabada Babu Wanda zaisan cewa itace ta kasheshi"
Dan murmushi kawai hajiya rahina tayi tana jinjina Kai Tana ayyana abubuwa da dama cikin ranta"....
Dik wata natsuwa yarima baya cikinta ya rasa abinda keyi mishi Dadi Allah Allah kawai yakeyi a tashi a wajen party din ....
********
Kuka sosai Fatima keyi Tana mayarwa hajiya zainab abinda ke faruwa ta karashe maganar da fadin"na hakura da aurensa inhar hKan shi zai samamin farin ciki Domin a bisa alamu sun nuna Yana aurenta zai manta da alkawarina ,zai manta da wata Fatima marainiya wadda yayiwa alkawarin kasancewa da ita har karshen rayuwarta,gara in hakura ummu tunda ni banida sauran gata"ta karashe maganar hawaye na gudu a fuskarta "Babu ranan da zan huta kenan?tunda nataso nake cikin wahala har yanzun Ina cikin azaba daga wanan sai wanan shi kuma Wanda nakeso ya fara canjamun"ta rushe da kuka Mai ban tausayi...
Ita kanta hajiya zainab Saida kwalla ta tarun Mata a idanuwa,Fatima na tsananin Bata tausayi,kalamanta suna caja Mata kwakwalwa Saidai dik ba wani Abu ya kawo hakan ba harda kishi data fahimci Yar tanadashi...
Janyo Fatima tayi jikinta ta rungumeta ta shiga share Mata hawaye "kiyi Shiru ki kwantar da hankalinki kinji?Allah gatanki nice gatanki ko kabiru zai juya Miki baya ni bazan juya Miki ba kinji yarinyana?"
Dago Kai tayi idanuwanta na zubda hawaye hajiya zainab tasa hannu ta share Mata hawaye zuciyarta tayi rauni gabaki daya dakyar ta bude baki tace "kiyi Shiru kidaina kuka Babu Wanda ya Isa ya rabaki da Kabir yadda Allah ya hadaku,idan sunsan wata basusan wata ba kinji ni zanyi musu abinda zan shayar dasu mamaki zan tabbatar musu da din sammakonsu wani a hanya ya kwana ki kwantar da hankalinki zan kwatar Miki yancinki sanan kema zanbaki damar da Zaki kwaci yancinki da hannunki dik abinda sukai Miki zan wargaza shirinsu a Daren yau zuwa gobe.....
Kallon mamaki kawai Fatima take bin ummu dashi Tana tunanin yadda zaayi ta wargaza musu shirinsu bayan alamu sun nuna wasu abubuwan da yarima yakeyi yau kadai tamkar Mara hankali Wanda yasha wani Abu ya nuna an rigada an asirceshi....tayaya ummu zata warware asiri cikin awanni bayan washe gari da safe karfe Tara na safe sunan yarima ango?...wasu zafafan hawayene suka shiga gudu a idanuwanta tausayin kanta ya lullubeta,....ga wani irin soyayyarsa dake dawainiya da ita dik bugun da zuciyarta zatayi hade da numfashinta sonsa karuwa yakeyi cikin zuciyara.....ajiyar zuciya ta sauke yayinda hajiya zainab ta kafeta da idanuwa,tausayin yarinyar na Kara ratsa sassan jikinta jinta dafa ta tayi taji jikinta yayi zafi rau alamar zazzabi nason kamata "Fatima tashi kicire kayan jikinki ki wanke fuskarki kizo kiyi sallah kinji tunda baayi ishai ba muka tafi nasan bakiyiba,koh?"
Jinjina mata Kai Fatima tayi sanan ta zare jikinta daga rukon da hajiya zainab tayi Mata ta Mike jiki Babu kwari ta nufi toilet ummu girgiza Kai kawai takeyi hade da tausayin karamar yarinya kamar Fatima wadda take fuskantar kaddarori kala kala....
Mikewa hajiya zainab tayi ganin Fatima ta shiga bayi yasa ta tuna da bakinta dake parlor da sauri ta Mike Tana fadin "asha assha hajiya nabarku a parlor nazo lallashin diyata ne"..
Dariya kawar ummu kawai tayi tace "Babu damuwa hajiya aini ba bakuwa bace"
Kallon abincin da aka ajiye musu hajiya zainab tayi "bakuci abincinba hajiya"
"Wallahi munkoshi sallah zamuyi ma mutafi...."
"To ku shiga wancan dakin akwai toilet sai kuyi alwalar,wallahi hankalina dik ba kwance yakeba an kunnowa Yar autata wuta ga autar tawa da shegen rigima"
*********
Wajen karfe Tara su hajiya babba suka shigo gida hayaniya ta kacame cikin harabar gidan inda Yan matan amarya keta fitowa daga cikin mota suna yo hanyar gidan hajiya zainab inda suka ajiye kayansu,
Ganin haka yasa Fatima saurin gyara fuskarta dikda kumburin da idanuwanta sukayi,
Bubbuga kofa Suka shigayi,da sauri ta sakko daga Kan gadon lokacin ummu tabi kawarta tayi Mata rakiya ta fito ta bude musu kofa,
Suka shigayi shisshigowa ciki,faizah ta dubi Fatima tace"malama saiki tafi Babu ko sallama?ganin fitarki kawai mukayi"
Karbe zancen teemah dollar tayi da fadin "ai maki gani ya kauda idanuwansa Domin irin soyayyar da deejah suka nunawa duniya yau Dole dik wani makiyinsu yabar wajen Wanda bazai iya ganiba"
"Ahayyeeeee yau munga soyaya har wani narkewa deejah take a jikin yarima gaskiya sun Dace sosai'cewar Sunita Tana wurgawa Fatima harara,
Sororo Fatima tayi tsaye tana kallo da sauraren ikon Allah yadda suke zubo zance tamkar suna jiranta,zuciyarta babu Dadi Amma haka ta daure ta cije tace "ai soyayyar gaskiya itace soyayyar da ake kebewa anayinta ba don ganin idon mutaneba Dan su tafi da abin a baki suna Fadi yazama son asani kenan Domin ko ibadar Allah ce kayita don ganin idon mutane inda kayita anan zaka barta,saboda haka tafiyata tanada nasaba da kishina da mijina yakeyi gudun kada wani ya kulani kafin ya mallakeni in mallakesa a matsayin maaurata"
"A mafarki Zaki mallakeshi Fatima Domin Dan asali sai Yar asali ba tsintacciya Yar kwararo Yar rukon gwamnati ba tsohuwar Yar taada wacce tayi kwana da kwanaki a kurkuku"cewar deejahmah Tana murmushi,
Takaicine ya rufe Fatima Wanda take taji jiri na Shirin dibarta saboda cin mutuncin da deejahmah tayi Mata cikin mutane,Koda yake ba laifinta bane dama yarima munafuntarta yakeyi Yana xagayawa suna soyayyarsu tunda ya kasa controlling kansa cikin mutane....hawayene ya taru a Ramin idanuwanta Amma saita daure ta juya batare da tace komiba har ta shiga daki abun ya ciyoya ta fito fuskarta Babu walwala lokacin suna zazzaune suna kallo,har gefen deejahmah Fatima ta karasa ta zauna gefen kujera ta watsa Mata manya manyan jajayen idonta Wanda Saida gaban deejahmah ya fadi ta dago Kai Tana binta da kallo,daf da fuskarta Fatima tasa fuskarta ta Soma magana,
"Ki tabbatar da dik ranan da aka dauramin aure da Kabir kashinki ya bushe da dik wani Wanda ya goya Miki baya kikeyi dik ku shirya ku daura dammarar fada Dani Domin kubar ganina haka abinda na kudura a Raina sai ya Dade Yana baku mamaki nidake sai min Zama tamkar damusa da ya'yan kura, ki kiyayi gamona dake Domin Yar karuwa saitayi Miki abinda baki taba tunani ba saina tabbatar Miki da tabbas ni Yar kwararoce a Nan ne zaa banbace mowa da Bora a wajen miji"
Kallo kawai sukebin Fatima dashi kowa fuskarsa shaye da mamaki,...dagowa deejahmah tayi tadanyi murmushin karfin Hali "idan nabaki damar shiga gidana kenan dik kike wanan furucin"
Mikewa Fatima tayi tana Taku daidai dik suka bita da Ido kamar wata tv gashin ganta na Lilo a bayanta yadda tayi parking dinsa da ribom...
Tayi hanyar dakinta aka turo kofa bilkisu ce tayi satar hanya ganinsu deejahmah yasata tayi turus zuciyarta ta shiga bugawa da sauri ta zube a gaban Fatima Tana fadin "afuwan ranki ya dade kiranki ya iso gareni bansamu damar zuwa bane Saida na karasa aikin da nakewa hajiya a cikin gida"
Kauda Kai Fatima tayi tamkar bazatace wani Abu ba dakyar ta bude baki tace"keta shafa Amma kisani bazaki bar gidan Nam ba sai kin karasa mun dik aikin da nake Shirin saki Dan Banga dalilin da zaisa nakiraki tun Rana kimun aiki kiki zuwa ba ,ki shiga kitchen akwai wanke wanke kiyi kafin inzo"
Da sauri bilkisu ta Kara rusunawa "angama ranki ya dade na tuba"....
Kallon takaici khausar kebin bilkisu dashi sanan ta taba deejahmah tace"Wai saboda tsabar raini irin na wanan shegiyar Wai har baiwar hajiyarmu take Kira tasata aiki tasamu wajene"
Yunkurawa deejahmah tayi "kutashi muje bazan iya cigaba da ganin kayan takaici ba"
Dukkansu suka Mike suka shiga fita daga gidan Fatima dake daki wajen goma saura tanajin sahun fitarsu ta fito da sauri ta kalli kofar dakin da suka Bari a bude ta rufe ta dawo tayi kitchen,
A tsaye ta samu bilkisu kawai saita fashe da kuka ta rungumeta "Yar uwata Ina cikin matsala Domin kabir ya juyamin baya bakiga abubuwan da yakeyiba jiya har cemin yakeyi Wai dadin abun yanada wata"kuka sosai Fatima keyi a jikin bilkisu wadda itama hawayen ne ya wanke Mata fuska da kyar ta lallashi Fatima suka dawo parlor kasan carpet suka zube...