Sashe 73
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rufe idanuwanta tayi cike da kunya Tana murmushi,shima murmushin yakeyi ya dagata cakkk Yana juyi da ita a cikin parlon tanata famar dariya sanan ya sauketa a kujera Yana maida numfashi,
*******
Jingina tayi da jikin kofar dakinta ta rufe idanuwanta hawaye na ambaliya a idanuwanta,
Dafe kirji deejahmah tayi saboda yadda take Jin zuciyarta nayi Mata suka tamkar Ana tsira Mata allura a kirji,..kuka sosai takeyi me ban tausayi data rufe idanuwanta yarima take gani lokacinda yake wurgawa Fatima kallon soyayya,
Wani irin abune yake Shirin samunta a rayuwa ya zatayi da sonsa bayan zuciyarsa na can wani waje daban?
Kuka sosai takeyi meban tausayi taji kamar Ana kwankwasa Mata kofa,
Da sauri ta share hawayenta ta say hannu ta murda key din ta bude,
Ganinsa ya sata saurin bashi hanya ya wuce ta gefenta ta rufo kofar,
Kallonta kawai yakeyi yadda dik ta sauya Sanan daga ganin idanuwanta tayi kuka sai tabashi tausayi,
"Deejah"
"Naam"ta amsa hade da kallonsa lokaci daya ta kauda kanta gefe gabanta na faduwa,..
"Meke damunki ne?"
"Meka gani?babukomi kawai na shigo nadan kwantane"
Sai kawai ta kauda kanta ta Haye gado,ya juya a sanyaye ya Haye gadon ya janyota jikinsa ya rungumeta yaana shafa kanta...
******
Da ruwan sama aka wayi gari Dan haka basu tashi da wuriba har karfe daya saura na Rana Sanan Suka hadu a wajen breakfast,
"Ki gaggautafa bintu banso muyi yamma Dan inaso muje gidan matar Nan don muga yadda zaayi"
Sauri sauri sukai breakfast suka shirya suka fice a gidan..
******
Basu Bata lokaciba wajen Isa gidan inda yarima yake directing driver har unguwar,
Bayan sun gabatar Mata da kansu ne ta jinjina kanta Tana Dan murmushi "ai naganeku yara karku damu meke tafe daku?"
Yarima ne yayi magana "dama Mai martaba ne yakeda bukatar Karin bayani akan wanan hoton da baiwar allahr Nan da kikace a gidan Nan ta haihu shine mukazo,gashi Kuma kince Wanda ya kawota ya rasu"
"Tohhhh nidai banida wani cikakken Karin bayani saidai a bisa alamu da bayaninku ya nuna cewa baa gamsu da maganar Ku ba koh?to Waqa a bakin me ita yafi Dadi dikda cewa akwai alkawari a tsakanina da malam sani suleman shi Wanda yasan komi dangane da yarinyar"
Kuri sukai suna kallonta hade da saurarenta dik zuciyoyinsu cike suke da tsoron abinda zata fada,
"A gaskiya yara malam sani ba mutuwa yayi ba tashi yayi daganan yabar garin gabaki daya,kafin yabar garin ne yabarmun sallahu Akan yasan koba Dade koba Jima zaazo nemansa tunda da hannunsa ya dauketa yakai gidan marayu shiyasa saboda bayaso wani Abu ya faru yasa yace dik Wanda yazo ince mutuwa yayi Amma hakikanim gaskiya be mutuba Yana Nan da ransa Yana can wani kauye gabanmu"..
Bakin yarima har rawa yakeyi wajen fadin "mama ki tabbatar da abinda kike fada?kin tabbatar da cewa shi ya Riki mahaifiyar yarinyar Nan?"
"Kwarai dagaske yaro"..
"Yanzun ya zaayi musameshi Sanan idan munsameshi akwai hujjoji da zasu nuna cewa shidin ya riketa?"..
"Zaku iya samu yaro Sanan ni zan taimaka muku kusameshi din"
Jikin Fatima a sanyaye tace "mungode mama"
Mikewa tsohuwar Nan tayi ta Shiga ciki ta dauko hijabinta ta fito tasa Sanan ta dauki takalmin a slipas tasa a kafarta "muje"
Shine abinda tace musu dukkansu suka Mike a tare suna gaba Tana binsu a baya,...
********
Mai martaba ne zaune a parlonsa gabansa jakadiyarsa ce gefensa Kuma wani Dan matashin yaro ne sanye da jajayen Kaya irin na dogarawan gidan Yana gurfane,
Kofi sarki ya dauka ya kurbi ruwa ya ajiye a gefensa Sanan yayi Dan gyaran murya,
"Maga takadda kace kaje can gidan tsohon limamin garin Nan kayi bincike Akan abinda nasaka?"
"Ehh ranka ya Dade nayi bincike abinda nasamo shine sunbar garin Nan tun shekarun baya saidai inada labari Akan dik wata suna zuwa Kuma suna sauka a wanan gidan nasu "
"Yanzun rabonsu da garin kwana nawa kenan a binciken ka?"
"Kwana goma Sha hudu kenan kaga a lissafi saura kwana goma Sha hudu Nan gaba"..
Jimmm kadan Mai martaba yayi "sati biyu kamar yau ne idan Allah ya kaimu"....
******
"Yanzun meke tafe daku me kukeso a wajena da kuka kwaso jiki kukazo?"
"Taimakon mu mukeso kayi yadda Allah ya taimakeka"
Dan dattijon ya sauya fuskarsa "nifa banason ku kaini inda zaa hallakani a banza gara ku fadamun gaskiyar lamari Dan ni inajin tsoron Kar ace wanan baiwar Allah laifi tayo dama daga garinsu tazo wajena na amsheta ya zamemun matsala"
"Babu wata matsala sai alheri baba ka taimaka Mana kazo muje a warware wannan matsalar Dan Allah"....
Shiru yayi Yana Dan tunani ,Fatima kuwa dik hankalinta ya Gama tashi,
"Injidai idan nakawo bayani shikenan zaa kyaleni indawo?"..
"Insha Allahu"cewar yarima cike da kosawa Yana duban yadda garin ya hade da hadari...
"Muje to Allah ya bamu saa"
"Ameen"suka hada bakinsu , a tare suka yunkura harda wanan tsohuwa suka nufi motar su yarima....
*Muje zuwa*
*SLIMZY😍*
[9/2, 20:09] 🥰slimzy🥰: 🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
47
Basu iso gidan Mai martaba ba sai bayan sallar magriba,
Sai bayan an idar da sallah Sanan Mai martaba ya umarci sarkin fada da yayi Masa Kiran iyalansa dake cikin gidan,haka kuwa akayi hajiya babba da mama karama da afnan da khausar tare da yarima sai Fatima dake wajen dik suna zazzaune,
Gyaran murya Mai martaba yayi ya dubi malam sani dake gurfane Yana faman hada zufa saboda tsananin furgici da yake ciki a wanan lokacin,
Gyaran murya Mai martaba yayi Sanan yace "malam sani sunanka bawan Allah?"
Gabansa ya fadi ya Kara rusunawa "ehh ranka ya Dade sunana kenan"ya fada a furgice,
Ganin yadda dik ya tsure yasa sarki sassauta murya "ka kwantar da hankalinka bawan Allah Nan masarautace Mai cike da adalci da kaunar talakawa Dan haka Babu abinda kayi Babu abinda zaayi maka cikakken bayani mukeso kawai kayi Mana game da wanan baiwar allahr dake cikin hoton Nan"ya mikawa malam sani hoto,....jiki na rawa ya karbi hoton ya Kara dubawa,
Sarkin fada dake gefe yace "ka natsu kayiwa sarki bayani kadaina rawar jiki a gaban Mai martaba kake"
Shiru yayi na Dan wani lokaci yayinda parlon yayi tsit bakajin karar komi sai fanka,
Wata Rana,
"Na fito gabanin sallah asuba ta lungun dake jikin gidana dan zuwa masallaci sallah kawai cikin duhu na hangi mace tsaye ta raba hanya da tsohon ciki a jikinta farko na tsorata Dan tunani nayi ko gamo nayi Ina rike da carbina sai na Soma Kiran sunan Allah Ina kokarin karasawa inda take,
Tsayawa nayi daf da ita dikda tsananin tsoron da nake ciki be hanani yin jarumtar bude baki inyi Mata magana ba,
"Assalamu alaikum"...shine abinda na ce Mata sai Naga yadda ta waigo gareni a furgice tamkar wadda ta samu tabin hankali Tana neman hanyar gudu yayinda lokaci daya take fadin,
"Dan Allah kada ka kasheni ka taimakeni sun biyoni abinda ke cikina sukeso su cire su kasheshi ni Kuma Ina son abuna bawan Allah ka taimakeni Kila Allah ne ya jehoka cikin rayuwata Dan ka Taimakeni"....Tana maganar ne Tana waige waige ta furgice tamkar me neman wani Abu,
"Ina fatan mutum ce ke ba aljanah ba"....da sauri ta amsa da ,
"Ni mutum ce kamarka ka taimakeni bawan Allah "
"Ki kwantar da hankalinki zan taimakeki Amma da sharadi Akan bazan taimakekiba daga baya ni kizo ki saka mun da sharrri daga taimako Dan duniyar yanzun abin tsoroce"sai kawai ta fashe mun da kuka harda durkusawa kasa Tana fadin "wallahi bazan saka maka da sharrri ba sai alheri bawan Allah ka rufamin asiri"
Jinjina Mata Kai nayi dikda zuciyata dake waswasi akanta Amma hakan be hanani samun karfin gwiwar Taimaka Mata ba nan nayi Mata umarni da ta tashi muje gidana inkaita Dan anata kiraye kirayen sallahr asuba ta Mike Babu musu ta bini muna tafe Tana sharar hawaye har gidana na kaita wajen matata shaawa,
"Shaawa!"
Da sauri matata ta fito daga daki Tana fadin "malam ko kayi mantuwa ne gashi anata Kiran sallahr asuba"...Bata karasa zamcenta ba ganina da mace yasa Tai shiru Tana Bina da kallon tuhuma da tambayea,
"Ki ajiyeta har indawo masallaci"shine abinda nace Mata na juya abuna inda ta Kama hannun wanan baiwar allahr suka Shiga ciki,
Bayan na dawo sallahr asuba ne na taddata Kan dadduma itama tayi sallahr suna zaune da matata Tana Bata labari Akan ita din matar sarki ce tsangwama da azaba ya korota daga masarautar su take bamu labarin irin azabar da Tasha na baaso ta haifi cikin jikinta,mun matukar tausaya Mata nida matata inda mukai Mata alkawarin riketa har ta haihu tunda muma ba karfi garemuba,ni lebura ne matata Kuma Tana kitso Tana wanki da guga dashi muke ci da kanmu tunda ba yara Allah ya bamu ba,
Malama zahrau tunda taga sanaar da matata keyi dikda cikin dake jikinta ta zage Tana wanki da gugar Nan itama saboda zaman haka har cikinta ya Shiga watan haihuwa,
Wata ranan alhamis da asuba ta wayi gari da ciwon nakuda Mai tsanani gashi bamuda yadda zamuyi mukaita asibiti muna tsoron mu kaita mu hadu da wani nata Dan haka sai muka yanke shawarar ajiyeta a gida ta haihu kawai sai Mai dakina ta Kira wata makociyarmu da tayi karatun likitanci cikin ikon Allah Bata dauki lokaciba Tana nakuda ta haifi yarta mace kyakkyawa kamar ta farin ciki wajen wannan baiwar Allah baa magana,
Bayan an gyarata komi ya Lafa suna zaune Yar na nade cikin tsumman zani wasu Yan riguna ta siya Wanda su akasawa yar dagasu batada wasu kayan saita yanke shawarar Ciro Dan kunnen zinari na kunnenta ta mikawa Mai dakina "amshi wanan a Saida idan yaso sai a sissiyi abinda bamu dashi harda kayan abinci dik mu siya Naga zaifi koh?"
Shiru Mai dakina tayi Sanan ta sauke ajiyar zuciya "Niko zahrau da kinbar dan kunneki ko saboda gaba Kila Zaki bukaci wani taimako"
Hawaye ke gudu a fuskarta cikin kuka tace"Babu wani Abu da nakeda bukata a yanzun sama da mijina Amma ya rigada yayimun nisa banida wani Abu da zanyi yanzun Dan idan nakoma kasheni zaayi da Yar Dana Haifa Dan haka kada kidamu a Saida akwai Allah "