← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 80

Sashe 22

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyada Masa Kai tayi ta juya ta nufi inda motar yarima take ya biyo bayanta......

*********
A can gida kuwa wajen hajiya babba da gwaggo rahi sungama tsara komi Akan auren na yareemah da deejahmah sanan tayiwa gwaggo rahi alkawarin da zarar Mai martaba ya diro masarauta zata gabatarasa da wanan shawarar da suka yanke insha allahu zatasan yadda tayi ta kullawa yarima makirci Akan auren deejahma kodan ta Rama Mata abinda yarimah yayi Mata,a haka sukai sallama gwaggo rahi ta baro masarauta.....

*******
"Niko Ina mamakin wanan al'amari ranka ya dade ace wai mutane babu abinda suka sawa zuciyoyinsu sai son Kai da son zuciya,menene aibun Fatima?meye abun kyama a wajen wanna yarinya data kasance baiwar Allah ?"....kwalla ce ta ciko a idanuwan ablah Tana rungume da fatyma Tana kuka Mai ban tausayi....

"Niko ranka ya dade mazai Hana kabarmun rukon Fatima a wajena na harabada aure ya rabani da it's tunda kaga halin da ake ciki mutanen gidanku basa kaunarta idan ka kaita bakasan irin zaman da zatayi a can ba"

Gwauron numfashi yarima ya sauke hade da furzo iska daga bakinsa sanan yace"kiyi hakuri barrister bazan iya bar Miki rukon Fatima ba alkawarin Dana daukarwa kaina akanta insha Allah ko Ana muzuru Ana shaho saina cikashi.....nafi so ta zauna a kusa Dani daidai da minti daya banaso Fatima tayi Nisa Dani,yau ma nakawotane ta kwana anan zuwa gobe idan Mai martaba ya sauka da safe idan mun tattauna da yamma zanzo in dauketa,akwai dalilin dayasa nakeson Fatima ta zauna a can din na gaba kadan zaku sani"

Harga Allah Ablah bataso ba da wanan shawarar da yarima ya yanke Amma babu yadda ta iya ya fita iko da Fatima.....

********
Sai misalin karfe takwas na dare ya shiga gidansu direct bangaren mama karama yayi da sallamarsa ya shiga, a ciki ta amsa Masa sallama sanan ta juya baya....."mama...."

Da sauri ta katsesa ta hanyar daga masa hannu sanan tace"tashi ka fita indai wanan maganar ce bana bukatarta yanzun"...kofa ta nuna Masa ya Mike jiki a sanyaye ya kalli afee yace"say dafamun ruwan zafi ki kawomin"...kallonsa tayi cike da tausayin Dan uwan nata tace"toh Yaya"....ya fice...

Afnan ta biyo bayansa har bangarensa a kofar shiga side dinsa tayi kicibis da baiwarsa dake kula dashi hannunta dauke da fruits zata Kai mishi afnan tayi gyaran murya da sauri ta zube a kasa Tana kawo gaisuwa, batare da ta amsaba tacee"lantana koma ki fadawa saade ta dafowa yarima ruwan zafi akawo Masa"

Kara durkusawa lantana tayi tace"angama ranki ya dade".....wucewa afnan tayi ta shige bakinta dauke da sallama lokacin Yana tsaye ya cire kayan jikinsa ya Sanya jallabiya cream colour Yana kokarin Zama a kujerar dake karamin parlornsa,

Wuri ta nema itama ta zauna fuskarta dauke da alhini tace"Allah ya huci zuciyarka yaayah Ashe abinda ya faru kenan yau, a gaskiya na tausayawa Fatima irin cin zarafi da cin mutuncin da akayi Mata,Abu dayane nakeso Yaya ka kwantar da hankalinka ni na tabbatar da cewa abun Nan da kake shirinyi abune Mai kyau Kuma hakan zai jawowa masarautar mu kima da daraja a idon mutanen gari wadanda sukasan da abinda ya faru saidai fa gaskiya Fatima babu Wanda zai kaunaceta saitayi hakuri Dan gaskiya lamarin akwai sarkakiya"

Tunda afee tafara magana ya kureta da ido tamkar Mai nazarin wani Abu harta karasa sanan yace"nasani little sis Kuma bazan taba canja kudirina ba Akan abinda nayi niyya"

Girgiza Kai kurum afnan tayi Sarai tasan taurin Kai irin na yayanta bazai taba canja kudirinsa akan abinda yayi niyya ba inba yanzun bama da wanan Abu ya faru shi ko magana ma Bata damesaba balle shiga hurumin mutane....

Nisawa tayi ta sauke sassanyar ajiyar zuciya tace"Allah yasa mudace"

"Ameen"kawai yace ta Mike tayi Masa saida safe lokacinda lantana ta shigo hannuta dauke da babban faranti da jug da cups akai....

*******
Gwaggo rahi ce can kuryar dakin yaranta yan Mata sunyi Shirin kwanciya dukkansu Amma xantawa sukeyi kus kus a kuryar daki...

"Wai mama yanzun Yaya Kabir ne ya hakikance Akan wanan yarinyar da gaske?to meye hadinsa da ita?"

Kasa da murya gwaggo rahi tayi tace"wayasani deejahmah aimu tunanin da muke ma yanada sa hannu a kisan habibu Kila shiyasa ya hakikance Akan sai yarinyar ta dawo gidan sarauta ni wanan kyakkyawar yarinyar ma zargin da nakeyi babu wata marainiya Kila budurwarsa ce yayi Mata alkawarin aure bayan ta kashe habibu"

Zumbur deejahmah ta Mike ta dafe kirji tace"mama?yanzu kina nufin bayan ya goya Mata baya a kotu Kuma ya daukota ya kawota masarauta da Zama?meyake nufi da hakan?"

"Shikadai yasan kudirinsa shida uwarsa,aini yanzun Raina fess tunda akai haka kan kowa zai rabu a gidan Kuma hajiya babba tayi naam da maganarki to nasan babu makawa aurenki da kabiru"

Murmushi deejahmah ta sauke tace"aikuwa nice zan ramawa habibu duk abinda akayi Masa na sanaddiyar ransa da akayi na kuduri aniyar saina salwantar da rayuwar kabiru matukar Ina numfashi...."

Zaro ido gwaggo rahi tayi tace"kina haukane?kinsan me kike fada kuwa deejahma?"

Jinjina Kai deejahmah tayi ta kalli uwarta tace"nasan Shirin da zanyi akansa kafin in kasheshi saina haifi magajinsa sanan kafin in kasheshi saina nakasa rayuwarsa ya Zama tamkar mutum mutumi....."

Jinjina Kai gwaggo rahi tayi Tana murmushi tasan niyyar yartata...

"Aini gobe da yamma da gayya zanje gidan yiwa Dan uwana barka da zuwa inji mezai faru....."

*Muje zuwa*

*SLIMZY✍🏼🥰*🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

*NA:SLIMZY✍🏼*

_wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

*HURRAY🎉* _it's d birthday party of my one in_ _millions,infacts billion's,sweet mommah...,u are spacial and morthan capable of achieving everything u put in ur mind,😍I want to hear lots of ur success stories dis new age and_ _always......I am so glad to have u🥰and u are such a_ _soul whom I will be loving through out_ _my entire life...._ *HAPPY BIRTHDAY WORLD CUTTEST MOMMAH* ...( *_Billy_* *_Galadanci_* )🍰🎂🎉

18

Tun sassafe maaikatan gidan suke kaiwa da komowa wajen shirye shiryen kayan abinci Wanda zaa tarbi Mai martaba dashi na girke girke da kayan ciye ciye...dik inda kabi sasan masu aiki kamshi ke tashi kasantuwar kowa yasan idan sarki yayi tafiya rangadi to da safe yake sauka....

Misalin karfe Tara da rabi ,gida ya kacame da hayaniya da busa irin na algaita kasantuwar masarautar barayar Zaki masarautace ta gargajiya Mai dumbin tarihi....dik Wanda yaji wanan busar yasan cewa sarki ne zai shigo ko zai fita.....yarima na kwance a dakinsa yaji hayaniya taki karewa gashi yanaso yadan runtsa saboda rashin samun isasshen bacci da beyiba Daren jiya ga matsanancin ciwon Kai days kwana dashi.....gyara kwanciya yayi ya janyo bargo ya lullube har tsakiyar kansa amma inaaa hayaniyar Yar rakiyan sarki dake shigowa da dawakai wasu da mota bazasu barshi yayi baccinba....kafarsa ya zura kasa ya Mike ya fada bathroom don yayi wanka.....

Bangarensu mama karama da hajiya babba kuwa ko waccensu sanye take da hadaddiyar lafaya Mai tsadan gaske sun hallara a babbar fadar sarki inda dik jamaar gidan suke shigowa suna kawo gaisuwa suna fita,fuskar Mai martaba dauke da murmushi yake karba gaisuwa har kowa ya watse ya kasance dagashi sai iyamensa,inda afnan ke zaune ya kalla Tasha kwalliyrta tai kyau da ita murmushi ya sakar Mata yace"uwata ummul khair autar masarautar barayar Zaki ya akayi ne umm?"

Rankwafawa afnan tayi cike da ladabi tace"nayi matukar farin cikin ganin abbahna cikin kosasshiyar lafiya Allah ya Kara maka lafiya da Nisan kwana"jinjina Kai Mai martaba yayi cike da Jin dadin kalaman afnan ya juya ga khausar wacce ta hade fuskarta babu yabo babu fallasa yace"nayi farin cikin ganinki zinariyar masarautar barayar Zaki ya ga Mai martaba"....murmushi Mai kayartarwa khausar tayi hade da Jin dadin wanan kirari da dukkaninsu kowa da irin Wanda yakeyi Masa cikin zolaya ,Dan rankwafawa tayi tace"barka da zuwa mahaifina fatan kana cikin koshin lafiya,Allah ya ja da ran Mai martaba"Tana murmushi ta karashe zancenta,jinjina Kai sarki yayi yace"lafiya kalau alkhausar"

Juyawa yayi inda matansa ke zaune wuri daya jere ya kalli hajiya babba cikin murmushi yace"nayi matukar farin cikin ganin uwar gida sarautar Mata ta wanan masarauta ta barayar Zaki Ina fatan nasameku lafiya keda kanwarki sarauniyar masarautar barayar Zaki"

Mama karama murmushi tayi ta dukar da kanta kasa alamar girmamawa da gaisuwa,...jinjina Kai sarki yayi ya amsa gaisuwarta sanan hajiya babba cikin faraa ta kawo Tata gaisuwar dukkansu ya karba musu cike da farin cikin ganin iyalen NASA....

Shiru ne ya gauraye fadar babu Wanda yace uffan sarki ne yayi gyaran murya yace"kowa yazo ya Miko gaisuwa a gareni Amma Banga Dan autan sarki ba Kuma sarki Mai jiran gado kabiru"

Karaf hajiya babba tace cike da izza"yaushe zaizo Yana tashen rashin kunya da rashin mutunci".....murmushi kawai Mai martaba yayi batare da yace uffan ba Ana haka saiga Kabir yayi sallama cikin fadar cike da natsuwa Yana sanye da Riga da Wando na jamfa irin na yaran gidan sarauta bakake sun matukar amsar fatan jikinsa a matsayinsa na farin mutum......

Har kasa ya tsugunna a gaban mahaifinsa fuskarsa dake da tsadajjen murmushin Nan Nasa yace"barka da zuwa ranka ya dade fatan ka sauka lafiya?nayi matukar farin cikin ganin mahaifina cikin kosasshiyar lafiya,Allah ya karawa sarki lafiya da nisan kwana"

Murmushi kawai Mai martaba yakeyi Yana jinjina Kai farin cikin ganin tilon Dan NASA yaki boyuwa a fuskarsa sai jinjina Kai yakeyi Yana kallon yarima Wanda ke tsugunne a gaban mahaifin nasa kansa a kasa cike da girmamawa.....

********

"Niko Fatima gani nakeyi zamanki a gidan sarauta zaifi Miki,Domin a fahimtana akwai wani kuduri da Yaya yarima yakeso ya cimma koma Dole saida hakan"

Murmushin takaici Fatima tayi hawaye na sulalowa a idanuwanta tasa gefen hannunta ta share sanan ta Soma magana"Aysha kenan a naki tunanin Amma babu wani kudurin daya wuce alkawarin da yayimun na zamemun gata a wanan duniyar,Kuma indai haka ne to dik inda nake zai iya Zama gata na tunda Ablah tace yabarni a Nan gidan yace ah ah bankuma San me hakan ke nufiba"

Murmushi Aysha tayi Wanda har saida side dimple dinta ya lotsa tace"Niko a tawa fahimtar kenan zamanki a gidansu shine zaibashi damar aurenki"
Chapter 22 · 0% Book details