← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 80

Sashe 36

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon yadda hawaye yake gudu a idanuwanta yayi besan lokacin da shima hawayen tausayinta suka fara zubo masaba suna diga Akan fuskarta,

Idonta ta dago ta kallesa Ido cikin ido "meyasa kake hawaye Ina tsammanin inji kasanya hannayenka masu albarka kana sharemun nawa hawayen sai Kuma ka tayani?Haba yarimana kaifa jarumine yayana kabar hawayen kaji?inhar akaina kakeyi azaba ko kyama ko kaskanci bazai taba canja matsayinka a cikin zuciyataba,nasan kana tunanin zan iya tsanarka saboda Dan Kai ake wulakantani,ko?babu wanan ranan harabada Kaine gatana Kaine farin cikina Kaine sirrin zuciyata"

Kirrrr yayi da ido Yana kallonta ,tunda yake Bata taba fada Masa wadanan kalamaiba sai yau wani irin dadine ya ziyarci zuciyarsa Dan har cikin zuciyarsa Yana tsoron kada azaba tasa Fatima ta tsanesa....

Da kanta ta kamo gefen karamin hijabinta Tana share Masa hawaye lokaci daya murmushi kwance a fuskarta dikda itama hawayen takeyi....

Hannunsa yasa Yana share Mata hawaye shima Yana maida Mata da martanin murmushin ta,"hakika Fatima ke baiwar Allah ce ,Allah kadai yasan dumbin baiwar dake tattare dake Yar aljannah,babu abinda zai hanani cika burina akanki sai ikon Allah inama in bude idanuwana inga kin rikide kin Zama matata"..runtse idonsa yayi Yana murmushi,

Dariya takamayi Masa Tana kallon idanuwansa a rufe tasa baki ta hura Masa iska a ido....ya shiga budesu a hankali Yana saukesu Akan kyakkyawar fuskarta dake faman yi Masa dariya,...mikewa tayi daga jikinsa da sauri ya janyota ya rike hannunwanta Yana murzawa a hankali..."inasonki bintu"

Dan tura baki tayi sanan ta kashe Masa Ido tace"Niko banasonka Yaya"

Da sauri ya kalleta ta sakar Masa murmushi "kaunarka nake"

Yasa hannu ya lakuce Mata hanci sanan ya saukta a jikinsa ya Mike "kamar kada ki tafi"

"To ko in kwana a Nan"...tayi Masa gwalo..."karki cika baki zan iya rikeku har safe"

Sai lokacin Fatima ta zaro Ido "ashefa mu biyune nida masifatu,nasan tanacan ta cika tai famm"

"Kin manceda ita kinata soyayya bintu ashedai kin iya soyayya"ya ruko kugunta Yana dariya kasa kasa

Ture hannunsa tayi tai gaba har takai kofa ta juyo"Saida safe yarimana"ta kashe Masa Ido...

Kallo ya bita dashi har ta rufo kofar Yana murmushi yasa hannu Yana shafa kansa,...ajiyar zuciya ya sauke a hankali "alhamdulillah burina ya cika nasanya marainiyar Allah farin ciki....bintu insha allahu sai kin Zama matata Domin kece burin Raina"

Zama yayi da baya Akan kujera ya Dan kishingide da bayansa ya runtse idanuwansa Yana ganin fuskarta tanayi Masa murmushi...

********
Bacci barawo ya dauki gwaggo rahi da deejahma tun sassafe misalin karfe goma na safe hajiya rahina tayi shirinta tsaf Dan zuwa gidan sarki,

A shirye deejahmah ta sameta a daki tace"inaso inbiki gidan sarki don in Rama takaicin da yarima ya kunsamun jiya"

"Tayaya Zaki Rama?mezakiyi mishi ya bakanta ransa bayan shi kuka yasaki da hawayenki"

Murmushi deejahmah tayi ta daga hannunta dauke da Yar karamar aska irinta wanzamai Tana murmushi tace "tunda safe nasa baiwata rahane taje gidan sarkin aska na bukaci da ta karbomin aska Mai kaifin gaske don inada abinda zanyi da ita"

Kallonta uwarta keyi Baki bude da kyar ta saisata mamakinta tace"me Kuma zakiyi da aska?"

"Wanan askar da kike gani da ita zanyi amfani wajen aske gashin Kan Fatima tass,sanan in zaunar da ita lungu da sako na fuskarta sainayi Mata tsage dashi na wulakanci,saina tabbatar da ko makaho bazaiso hada ido da fuskartaba,wanan kyawun da take dashi yau zai Zama tarhi".....

Dariya gwaggo rahi ta sheke dashi "lallai kinsan kan mugunta deejahmah shirya muje"

"A shirye nake zamu iya tafiya"....

*Muje zuwa*

*SLIMZY✍🏼😍*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

*SAKO DAGA KUNGIYAR HASKE WRITERS* *ASSOCIATION💡*

*ZUWAGA DUMBIN MASOYAN MU MUKE SHAIDA MUKU WANI BAKON AL'AMARI DAGA MAHASSADA*, *AKWAI WANI SABON LITTAFI DA SUKA KIRKIRA ZAKUGA A SAMANSA AN AMBACI ...BILLY* *GALADANCI (MAGAJIYAR KARUWAI)....TO BA WRITE UP DINMU BANE BA RUBUTUNTA BANE ANYI HAKA NE DOMIN A BA'TA SUNAN TA, SHIYASA MUKA YANKE HUKUNCIN SANAR DAKU DA WURI KAFIN LITTAFIN YA FARA YAWO....* *BABU RUWAN BILLY GALADANCI DA WANAN RUBUTU BA NATA* *BANE....MAHASSADANE KAWAI...*

26

Motoci suka shirya tsaf da Yan rakiyarsu suka nufi gidan sarki cikin mintuna da Basu wuce arbain ba suka Isa....

Tun daga nesa Fatima ke hangen motoci na shigowa kasantuwar Tana can baya inda ake jibge Kaya idan ankawo Tana kwashewa Tana kaiwa dakin tsohuwar ajiya tun Daren jiya take aikin Abu daya har bacci ya kwasheta a wajen ta Dora daga inda ta tsaya da safe......

Hagensu takeyi suna tafe suna tunkaho Yan rakiyarsu na biye dasu haka dik inda suka wuce maaikata na zubewa a kasa suna kawo gaisuwa Babu Wanda suke kalla ballantana su amsa har suka shiga sashin cikin gidan.....haka kawai Fatima ta tsinci kanta cikin matsananciyar faduwar gaba.....ta Dade a tsaye Tana tunani kafin daga bisani ta cigaba da aikin da takeyi....

Bangaren hajiya babba suka yada zango tayi musu tarba Mai kyau Nan bilkisu ta shiga kawo musu kayan motsa baki Tana jerawa,

Sai wani Shan kamshi deejahmah takeyi Tana yatsina fuska...

"Hajiya barka da tashi Kinga nayi zuwan sassafe ko?"

"Ehh wallahi kin rigani zuwa ne Amma nikaina yau nayi niyyar shirya zuwa gidan naki'

"Muhimmiyar magana ta kawoni hajiya,wani mugun labari mukaji a bakin wanan jairin yaron kabiru har yasa deejahmah kuka"

Girgiza Kai hajiya babba tayi hade da yin murmushi Mai ciwo ta cije bakinta sanan ta fuskanci hajiya rahina "wanan maganar ki dauketa a ruwan kwando Domin harabada kabiru bazai auri shegiya Mara iyayeba"

"Cewafa yeyi yakai maganar gaban sarki....hmmm hankalinmu ba karamin tashi yayiba shiyasa na yanke shawarar zuwa gaban sarki infada Masa cin mutuncin da kabiru yazo har gida yayi Mana"

Kurriii da ido bilkisu tayi Tana kallon bakin kowa a cikinsu karaf sukai Ido hudu da deejahma a hassale tace'ke ubanwa kike kallo haka munafuka?tashi ki fita waye ya baki izinin Zama muna magana kina kallon bakinmu!"

Haushi ya Kama bilkisu Amma hakanan ta durkushe a gabanta Tana fadin "tuba nakeyi ranki ya dade waneni da shiga huruminku iyayen gidana"

Harara deejahmah ta wurga Mata ta nuna Mata kofa "tashi ki fita"

Sumi Sumi bilkisu ta Mike ta fita badan ranta yasoba.....

Ajiyar zuciya hajiya babba ta sauke "deejahmah kada hankalinki ya tashi Domin Nina tanadar Mata azabar da dakafafuwanta zatabar gidan Nan Domin yanzun haka tana can baya wajen ingiricin Doki nasata kwasar kayan da sukafi karfinta ta Gama in cigaba da azabtar da ita'

Askar dake boye cikin Jakarta deejahma ta Ciro Tana jujjuyaya "hajiya Kinga wanan askar?"

Hajiya na fuskatar deejahma ta amsa Mata da Kai "ehh Ina sauraronki"

"To da ita zanyi Mata azaba sanan zan aske kanta tsaf da ita Kuma in Zane Mata fuskarta da ita tamkar bayan kwarya"

Dariyar mugunta hajiya babba tayi Wanda rabonta da yinta har ta mance "lallai yata kinsan kan mugunta,....sanan nayi Miki alkawarin bayan kinyi Mata wanan azabar nikuma yau zan turata dakin tsohuwar ajiya a can zata kwana zan hada baki da daya daga cikin dogaren gidan Nan ya shiga ya far Mata cikin dare yayi Mata fyade,ya tabbatar yayi Mata kaca kaca yadda bazata moruba"

Sai wanan lokacin hajiya rahina tayi murmushi tasamu sassauci Akan takaicin da take ciki tun Daren jiya.....a gefenta ta ajiye askar sanan tacewa su hajiya tanaso sai tayi breakfast zata aiwatar da nufinta....

********

Bilkisu ce ke faman kaiwa da komowa a bayan kitchen cikin tsananin tashin hankali Domin taso ace taji tattaunawar su hajiya har karshe Domin da alamu sharri ke tafe da wadanan mutanen ba alheriba....

Dafa bayanta taji anyi da sauri ta juyo sukai ido hudu da wata kuyanga wadda daga gani ba Yar gidan bace,...murmushi ta sakarwa bilkisu ta Mika Mata hannu alamar su gaisa,...murmushin yake bilkisu tayiwa wanan kuyangar,

"Sunana rahane ni kunyanga ce a gidan galadima maana kuyangar sarauniya deejahmah ce tun dazun nake kallonki a Nan wajen shine Naga yanayinki kin burgeni nakeso muyi abota tunda Naga kema baiwar hajiya babba ce uwar gidan sarki Kinga abotarmu zatazo daya tunda iyayen gijinmu daya"

Murmushi bilkisu tayi hade da Jin Dadi Domin koba komi zatasamu wani labari a bakin rahane...."ni sunana bilkisu bakuwace ni baadade da kawoni Nan ba gudun hijira mukayi daga kauyen takanda"

"Ayya Allah sarki"...

Shiru sukai ko wanne fuskarsa dauke da murmushi kafin bilkisu ta cije lebenta ta Dan kalleta ta gefe taga ita take kallo saita washe baki "Niko Yar uwa kinganni Nan inada son Jin labari tunda kuka shigo Naga alamar kamar iyayen gijinki suna cikin damuwa"

"Kedai Bari Yar uwa "waigawa rahane tayi gefe da gefe sanan ta juyo ta cigaba da magana"wallahi uwargijiyata ce ke cikin damuwa jiya Dan sarki yazo wajenta shine yake shaida Mata da bayan ya aureta wai akwai wata kuyanga da zai aura,kinsan me itafa kuyangar ita ta kashe Dan uwansa Amma da yake butulune Wai aurenta zaiyi"

Da sauri bilkisu ta dafe kirji tayi kasa da murya "turkashi Amma lallai anyi Mara tunani Allah sarki deejahmah tabani tausayi nice ita wallahi sai na dau fansa Akan shegiyar kuyangar"

Waigawa raihane ta karayi tazo daf da kunnen bilkisu cike da tsaigumi tace"ai daukar fansar mukazo,Domin da safen Nan sarauniya tasa naje gidan sarkin aska na amso Mata aska wadda zatayiwa shegiyar aski sanan ta batawa shegiyar fuska"

Wani irin faduwar gaba ne ya ziyarci bilkisu take taji tanajin fitsari jikinta ya dauki rawa dama abinda takeso taji kenan "tabdijan gaskiya ba karamin fansa zata daukaba don idan tayi Mata hakan ta Gama da ita....."

"Sosaima aini nakosa a Kira shegiya a fara yi Mata aiki"

"Kice zamusha kallo zamu kashe kwarkwatar Ido"

Dariya rahane tayi tace"kedai Bari ai nakosa barima inje inji ko suna nemana suna bukatar wani Abu"....Tana Gama fadin haka ta dagawa bilkisu hannu da sauri ta wuce.....daskarewa bilkisu tayi tsaye a wajen Tana tunanin mafita....

********
"Hajiya ya kamata mu aiwatar da komi kafin mubar gidan Nan yanzun zansa deejahmah a gaba muje fada insanarwa da Mai martaba abinda yarima yayi ta hada harda Kuka ke kuma yanzun kisa a Kira Miki daya daga cikin maaikatan gidan Nan kuyi maganar kafin mu dawo yasan da maganar tunda wuri Dan ya shaida"

Jinjina Kai hajiya babba tayi tai murmushi ta kwalawa saade Kira...

*********
Chapter 36 · 0% Book details